Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 36

Ahankali zazzabi Mai qarfi ya kwantar da ita kwana biyu Dole yasa anty Sa’adah ta takurata sukai booking appointment da wani likita a asibitin da Abba yake akan washe gari zasu.

Kafin suje asibitin Kuma sai gashi tasamu Dan sauki Dan Haka taso qin zuwa asibitin Dole Anty Sa’adah Tai Mata Suka tafi tashin farko Dr na Gama dubata ya sanar dasu she’s 7weeks pregnant…

Wani mummanan tashin hankali da matsananciyar kunyar duniya tashiga gaban Anty Sa’adah har batasan lokacinda hawaye Suka ringa gangarowa Kan fuskarta ba takasa dagowa ta kalli Anty Sa’adah.

Anty Sa’adah ganin hawaye da Kuma halinda Laylan tashiga Kan sakamakon da aka Basu yasa hankalinta mugun tashi gabanta yashiga bugawa da qarfi cikin fargabar me hakan ke nufi?

Ita kanta zancen cikin ya firgitata sosai saidai Kuma kukan Laylan yafi Bata tsoro indai cikin bana wanine dabanba Dan kuwa Turakin dabai Gama sanin kamar laylanba bare daukanta matarsa tayaya zaace cikinsane? Dan Haka itama hawayen tafara cikin tsananin tashin hankali da fargabar wannan wane abune yake Shirin faruwa dasu suna zamansu cikin rufin asiri da qaunar mutanannan ace wannan Abu ya bullo.

Gida suka koma Suka zauna Palo jigum jigum kowacce na tsiyayar hawaye musamman anty Sa’adahn datake hango inda wannan tashin hankalin zai kaisu..

Sun Jima ahakan kafin Laylah dataga kukan Anty Sa’adahn yayi yawa Kuma idan ta fahimceta tasan tunanin dayake ranta baifi na inda ta samu cikiba Dan Haka ta share hawayenta tareda kallon anty Sa’adahn ta bude Baki cikin kunya da sanyin jiki tace”

Anty Sa’adah ba abinda kike tunani bane,
Wlh bazan taba aikata zinaba duk inda nasamu kaina da yardan Allah…..

Wani kallo anty Sa’adah Tai Mata tanason magana Amma Tama kasa sbd batasan me zataceba.

Itama shiru tayi takasa fadar yanda cikin yake,
Ba fadawa anty Sa’adahn ba shin tayayama zatai da cikin?
Wannan cikin bayyanarsa masifar Dake lafe ce zata farka Dan a duniya bayan Haj Zinat Aminiyar mum Na’ima itace tafi kowa sanin irin masifar Dake cikin mum din akan Abban Dan kuwa tasha fada agabanta kisa ma zata iyayi akansa…

Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro Mata ba masifar mum ba kunyar bayyanar cikin kansa wani tashin hankaline gareta.

Anty Sa’adah da ranta yafara baci da quluwa da Shirun tace”

Bana buqatan wani dogon sharhi ko bayani amsa daya zakiban cikin waye????

Kasa dagowa tayi da fuskarta ahankali ta furta”

Abba.

Tana fadar hakan anty Sa’adah batace komaiba ta miqe jiki a salube tayi daki,
Al’amarin farin ciki mai girma Amma tsoron abinda ke bayansa ya Hana murnar.

Haka suka kwana gidan Babu Mai dogon motsi sbd damuwa sai washe garin bayan sun Gama breakfast jiki amace anty Sa’adah ta saki Bayyanannar ajiyan zuciya tareda cewa”

Jiyan halinda kikaga nashiga Jin ciko ajikinki wlh Bantaba zarginkiba da alfashaba ko makamancinta Laylah,

Samuwar ciki a irin yanayinda aurenki yake ciki yanzu akwai hadari wlh Laylah,
Idan Matar Nan tasan kinada alaqar da Bata uba da ‘yaba tsakaninki da Turaki komai zata iya aikatawa Dan Haka Ni wlh duk kinsa hankalina tashi Kuma yanzu,

Ni kaina wlh kunyar sanarda Anne nakeji,
Amma dai duk da hakan karki Bari kowa yasani mubar maganar ahakan tunda kince Nanda wata biyar Zaki samu zuwa Nigeria dogon hutu idan kinje ma fadawa Anne komai
Saidai wlh kiyi kokari Kar Wanda yagane ciki a jikinki.

Kallonta Laylan tayi jiki sanyaye tace”

Anty Sa’adah zai boyu kuwa har wata biyar?

Zaiyi Mana idan kinyi kaffa kaffa tunda ita uwar Taki ba wani zama takeba kullum tana gantalin yawon kasuwanci.

Ajiyar zuciya Laylah ta sauke tareda cewa”

To anty Sa’adah Amma Dan Allah karki fadawa Momy da Anne wlh kunya zanji, bansan ya zanyiba.

Murmushi Sa’adah tasake sai alokacin takejin kaunar cikin sbd tuno farin cikinda Anne zatai da cikin sbd kullum burinta Laylan tagama karatu tadawo ayi gagarumar walimar aurenta da Turakin kowa yasan ita matarsace saita tare da sunan matarsa, Ashe bidirin banza suke can.

MAMUH

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button