Kama kanta tayi daga kusantar inda mum din take sbd fushinta a kusa yake yanzu,
Ba ita kadaiba har su siddika da Cindy a kame kowa yake da gudun bacin ranta.
Makaranta ma idan Laylah ta tafi dai kusan magrib take dawowa gidan Sam gidan ba Dadi koina kayi motsi masifar mum ce ke ci ga Abban Bai dawoba bare ya iya sanin matsalarta ko zata sauko dan Haka kowa ya kame kansa Ana kaucewa fushinta.
Sai datai kwana biyar kafin tasamu wuce Nigeria data matsu Bata isaba Dan har wani tsalle zuciyarta take na zaquwa sai dataga jirgi ya saukar da ita airport din Lagos tafara jinta daidai,
Bata kwana agarinba ta hau wani flight din ta isa Abuja kafin ta sauke ajiyar zuciya tareda Jin nutsuwa da kwanciyar hankali sun shigeta.
Asibiti anso sallamar Sa’adah bayan tayi kwana biyu taji sauki sosai saidai test din da akai Mata wasu suna nuni da wata matsalar Dan Haka ba Bata lokaci Suka sake diban jininta Dan yimata wasu test din kafin aka sallamesu kafin result na test din su fito.
Bayan dawowarsu gida tayi waya da Laylah wadda ba’a fadawa abunda yafaruba sbd karta damu,
Itakuma Sa’adah abin dayasa ta nace akan Kar afadawa Laylan sbd yanayinta da lafiyarta..
Ms Na’ima ko data iso Nigeria anriga an sallami Sa’adah daga asibiti Dan Haka tana isowa Bata shigo gurin Anne ba sai data kwana ta wuni tagama danne kanta da zuciyarta sbd karta Bari Annen tagane tasan da komai sbd tunda Sa’adah ta dawo gida bazata iya komai akantaba Kai tsaye Saida wata dabarar.
****Tafiyar mum da kwana uku Abban yadawo daga tasa tafiyar murna gurin Laylan Bata boyu ba musamman dayake mum Na’ima da siddika tadawo Nigeria tunda itace Mai aikinta Koda yaushe Dan Haka Yana dawowa da kanta ta fito da gudu tayi kansa
Ba Bata lokaci ya dauketa Kan jikinsa Yana kallon haske da cikar data qara Bai sauketa koinaba sai palonsa na sama Yana kallon fuskarta datasha simple makeup sai qamshi takeyi,
Ga wata qaramar chiffon free half gown a jikinta data qara Mata kyau kaman yarinya Yar Sha uku.