NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????

   *_SARAN ƁOYE!!_*

Bilyn Abdull ce????????

ƊANƊANO DAGA ZAFAFA BIYAR 2021

No. 1

………..Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin.
Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma.
Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.
Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama’ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.

   Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.
      Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama'a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za'a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.
     Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa. 
      “Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o'e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”. Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙyalewa da dariya suna tafawa.
         Ƙaramin tsaki wadda ke zaune can gefen mirror tana kwalliya taja tare da taɓe baki, taɗan hararesu idanunta cike da ƙwalla, cike da fushi ta ajiye hodar da take shafawa ta fice daga ɗakin.
      Bama susan tanayiba, dan sukam hankalinsu nakan amarya suna cigaba da mata ihun “Gobe zata fashe!! Gobe zata fashe!!!”. Faɗi suke da ihu sosai suna dariyar tsokana irinta ƙawen da ƙuruciya ke ɗawainiya da su, dan gaba ɗaya yarane ƙanana da bazasu wuce 16-17 ba.
   Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Bata motsaba, kamar yanda bata buɗe ido ta kalli ƙawayen nata dake mata shaƙiyancin ba. Ita kaɗai tasan mi takeji a ranta tun daren jiya. Tabbas wannan ranace data daɗe tana fatan zuwanta itada masoyinta Yah Abdallah tun bata gama sanin ciwon kanta ba. Sai dai batasan miyasa tunda aka shiga satin bikin jikinta yay sanyi ba kuma. Tasan hakan bazai wuce nasaba da sabuwar rayuwar da zata wayi gari a cikinta gobe idan ALLAH ya kaimu ba. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe...........
       “Ya salam! Yaran nan lafiyarku kuwa!!?”. Akafa faɗa a bayansu da ƴar kakkausar murya. Tsitt ɗakin yayi, duk suka juya suna kallon mai maganar. Ta sake tafa hannayenta tana riƙe haɓa. “Oh ku ɗin nan, yanzu nan bama ku sakata ta shiryaba kuka zauna shiriritar da kukafi ƙwarewa akai?”.
     “Afuwan Addah”. Ɗaya ta faɗa tana ɗan sosa bayan wuya na alamun jin kunya. Girgiza kai Addah tayi tana ƙarasowa gaban gadon, “To naji, ku fita ku bani waje na kimtsata”. Ɗai-ɗai suka ringa fita suna ƙananun ƙunƙunai na alamar ba haka sukaso ba, amma sanin yau Addah babu fuskar wasa tattare da ita yasa babu wanda ya iya cewa komai. Ita dai bata kulasuba, dan yau babu ƴan wasan a kanta. Kamo ƙyaƙyƙyawar budurwar tayi ta zaunar tana faɗin, “Tashi kinji dear, kukan ya isa haka, kefa amaryace, amaryarma mai tsada ga ƙyaƙyƙyawan miji irin Abdallah. Ko bakison auren a fasa ne?”.
   Baki budurwar ta tura gaba tana sake matso hawayenta, sai kuma ta faɗa jikin Addah ta sake fashewa da kuka. Karan farko Addah tai dariya tana shafa bayanta. Tace, “Oh Rabbi, yau ga Nu'aymah shugabar tsiwar gidanmu tayi laushi darajar aure”. Ita dai sakema ƙarfin kukanta tai tana narkewa jikin Addah. Sunja kusan mintuna huɗu a haka kafin Addah ta ɗagota tana sake faɗaɗa fuskarta da murmushi, zaunar da ita tai sosai ta kama bakin mayafinta ta share mata hawayen fuskarta tas duk da wasu na silalowa kaɗan-kaɗan.
     “Haba Nu'aymah'n Abbah kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. “To wani waje ke miki ciwo ne?”. Nanma ta girgiza mata kai. “Ikon ALLAH, to minene ya sakaki kuka irin haka? Keda zakiyi auren soyayya Nu'aymah?. Ki duba kowa a family ɗin nan cikin tsantsar farin ciki yake da auren nan naku, dangi ta ko ina sun iso gobe idan ALLAH ya kaimu kawai ake jira. Umm. Hajjo, su Abbanki damu baki ɗaya kowa yana cike da farin cikin wannan alkairi. Ɗazun nan mukai waya da Angon shima jirgin ƙarfe uku zasu biyo daga Abuja, yanzu hakama sun taso inaga shi da abokansa. Ai nazata yau ranar farin cikice a gareki mara misaltuwama Nu'aymah. Uhhmm?”.
  Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Addah wlhy inajin tsoro ne?”. Da mamaki Addah tace, “Tsoro kuma Nu'aymah? To tsoro akan mi Uhhmm?. Ko wani abune ya faru dake bamu saniba?”. Nanma kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi.
   Addah ta sauke nishi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Nu'aymah”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Addah”. “Kukan ya isa haka kinji daughter, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsoro da kikeji ki ciresa a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan ALLAH ya kaimu, fatanmu ALLAH ya sanya albarka a al'amarin ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, ALLAH yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”.
     A zuciyarta ta amsa da amin, a zahiri kuwa sai tai ƙasa da idanunta alamar jin nauyin ta. Lura da hakan yasa Addah yin murmushi da lakace dogon hacinta. Tace, “Yauwa tagaban goshin Hajjo tashi ki shirya gashi can har an fara walima babu amarya”. 
 Ɗan murmushin yaƙe kawai tayi da miƙewa bisa umarnin Addah. Dama tayi wanka tuni, dan haka ta sake wanko fuskarta yanzu kawai ta dawo inda Addah ke jiranta. Ƴar kwalliya taimata da bazata takurataba, kafin ta sata ta shirya cikin atanfa zani da riga pitch da ratsin Maroon. Ɗinkin yay mata ɗagwas ajiki kasancewarta mai murzajjen jiki, dan sam Nu'aymah ba siririya bace, badai za'a kirata mai ƙiba ba, amma jikinta a mulmule yake babu alamar rama sam duk da kasancewarta yarinya ƙarama sosai. Baƙar riga mai zubin alƙyabba da tasha ado da pitch zare aka bisa da stones ta saka mata, da ɗan turare kaɗan, ta bata flat takalmi baƙi ta saka wanda yayma farar ƙafarta data sha ƙunshi jaa da baƙi ɗas. “Masha ALLAH amaryan ɗana Abdallah” Addah ta faɗa tana mata alamar tayi ƙyau???????? da hannu. Ɗan murmushi tayi da maida kanta ƙasa na alamar jin kunya.
    Yarinyar ɗazun dake jikin Window a laɓe tana kallonsu ta share hawayen da take faman yi tun ɗazun, duka maganar Addah da Nu'aymah akan kunnenta da idonta suka faru, ta taune leɓenta da ƙarfi tamkar zata hudashi tana ƙoƙarin danne kukan dake neman kufce mata da ƙarfi...
  Babu ɓata lokaci Addah ta taimaka ma Nu'aymah suka fito harabar gidan, inda sukaci karo da wasu tsoffin mata su kusan biyar. Da ɗan faɗa farar ciki ta watsa musu harara tana faɗin, “Wai mi kuke da amaryar a cikin gida da har yanzun an gaza kaita wajen walima Fauza?”. Cike da girmamawa Addah tace, “Ayi haƙuri Hajjo, mun tsaya shirine shiyyasa”.
     “To wane shiri kuma nikam kamar wadda za'a kai ɗakin miji yau, kinga taho Zainabu”. Tai maganar da kama hannun amarya Nu'aymah. Babu musu Addah ta sakar mata ita tana murmushi da binsu da kallo har sai da suka isa gab da gate sannan ta sauke ajiyar zuciya. Yunƙurawa tai zata bi bayansu itama......... 
   Caraf aka riƙe hannunta. Juyawa tai da sauri, sai dai ganin wadda ta riƙotan yasa taƙi cewa uffan. Kallon gefe da gefe tai, ganin mutane nata ɗan kai kawo yasa ta sake tsuke fuska tana kallonta.......
         “A'ah! Adawiya lafiya kuwa? Fauza mi akai mata haka?”. Firgigit Addah tai da ture hannun Adawiya daga kan nata tana harararta, sai kuma ta kalli mai maganar fuska a narke. “Umm bar wannan ƴar taki kinji, bansan mike damun kansuba daga ita har Nu'aymah, canfa na iskesu sun haɗe kai a ɗaki sunata dirzar kuka ko shiryawa basuyi ba, ni wannan shaƙuwa tasu har tsoro take bani wlhy, gashi kuma mai rabawa yazo....” ta ƙare maganar da sharce hawaye tana kallon Adawiya dake jikin Umm tana kuka tamkar ranta zai fita.
  Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar mai tsananin kamanni da Amarya Nu'aymah tayi, ta sake rungume Adawiya a jikinta tana ƙoƙarin haɗiye nata hawayen da suka ciko mata idanu. “Ya isa kukan haka Daughter, kiyi haƙuri, namiki alƙawarin insha ALLAH duk yanda zanyi sai nayi dan kibi ƴar uwarki sai kuje can kuyi karatunku tare kamar yanda kuka fara a tare kafin ALLAH ya baki naki mijin kema musha biki”. 
 Maimakon Adawiya tai murna sai ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Umm. 
   “Oh ALLAH, ya isa haka mana daughter, ko sokike muma ki sakamu kukan ne uhhhmm?”. Ɗagowa Adawiya tai zatai magana Addah tai saurin tarar numfashinta tana harararta ta ƙasan ido, “Faɗa mata dai Umm, tundama ance mata ga mafita an samu ba sai tai haƙuriba, nifa banason shashanci kuma, a haka zaki bama Nu'aymah ƙarfin gwiwar yin farin ciki? Haba mana, k........”
    “A'a Addah ya isa haka mana, a barta taji da abinda ya dameta dan ALLAH, ɗiyata muje ki shirya kinji, tarema zamu fita wajen walimar da anyi sallar la'asar”. Ɗan satar kallon Addah Adawiya tayi, ganin harar data watso mata ƙasa-ƙasa ya sakata saurin ɗagama Umm kai alamar to. Kamata Umm tai suka bar Addah a wajen, tabisu da kallo ƙasa-ƙasa tana ɗan murmushin jin daɗi......
    “Uhhm Fauza! Dama ke naketa nema ashe kina anan”. Wata mata dake tunkarita ta faɗa. Juyawa tai da sauri ta kalli matar, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Oh! Ya salam Yaya, wlhy namafa manta na barki kina jirana a kitchen, rigimar ƴaƴanki ta ɗaukemin hankali”. Ƴar dariya sukai a tare, tare da barin wajen suna cigaba da maganarsu.

     A waje kam dai har yanzu ba'a kai ga fara gudanar da komaiba, sai dai wata ɗaliba a cikin ƴammatan da zatai sa'anni da amaryace ke karatu cikin zazzaƙar muryarta, wanda hakan yasaka wajen yin tsitt ana saurarenta.
     Wasu zafafan motocine guda biyar suka shigo cikin layin, duk da mutane hakan bai hanasu kutso kaiba kansu tsaye jikin ƙofar babban gate ɗin harabar massallaci. a take mafi yawan mutanen dake a wajen walimar hankalinsu ya koma ga kallon motocin da sukai parking a jere abin birgewa. Kowa ya zuba ido yaga su wanene zasu fito a ciki?....
   Ni kaina sai da na sauke numfashi da faɗin Masha ALLAH, saboda fitowar wasu samari masu ji da lokaci da gayu daga motar, da gani babu tambaya waɗanan abokan angone dama angon kansa, bankai ga cankar angonba wani mafi ƙyawun haiba da tsarin kwalliya a cikinsu ya fito a motar tsakkiya waya manne da kunnensa yana murmushi. Sanye yake cikin ɗanyar shadda Maroon color sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ya saki lallausan murmushi yana gyaɗa kansa alamar amsa mai maganar daga can, sai kuma ya sauke wayar ya tura aljihu dabin abokansa dake tsaitsaye suna kallon ƴan taron walimar da suma mafi yawansu su suke kallosu da kallo. Kafin yace wani abu ɗaya daga cikinsu ya juyo yana faɗin, “Woow Ab harfa na canko amaryarka”. Ɗan hararsa yayi da ɗauke kai kamar bazaice komaiba, sai kuma ya sake kallonsa yana wani furzar da numfashi. “Malamai dalla kallon ya isa haka, ku bakwa ganin su Baba Malam duk mu suke kallo suma”. A tare duk suka juyo da kallonsu garesa suna dariya, wanda yay magana ɗazunne ya sake faɗin, “Hahh! Go gefe malam, kai dai faɗa mana kishi kakeyi dan ance anga Angel ɗinka”. “Shashasha, to idan nayi kishin laifine?”. Abdallah ya faɗa yana ratsa tsakkiyarsu yay gaba. 
 Cike da shaƙiyanci sukabi bayansa suna dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Shege uban zumuɗi, anya kuwa zaka cika alƙawarin da kaima su Baba Malam na barin ƙwailarnan taka tai karatu? Karfa muji nanda wata tara ana nemanmu a labour room”. Duk da yana jinsu sarai bai tankaba, sai dai ya ƙawata fuskarsa da wani sassanyan murmushi daya ƙara fidda ƙyawun fuskarsa...

      “Huuhm Nu'aymah! Gafa Soulmate ɗinki nan tafe tamkar wani ɗawisu a tsakkiyar furanni”. Iman ta faɗa a hankali cikin kunnen Nu'aymah da kanta ke'a duƙe lulluɓe da abaya batasan wainar da ake toyawaba. 
 Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan ɗagowa kaɗan, idanunta ne suka sauka akansa. Taja ajiyar zuciya tana lumshe idanunta wani sanyi na ratsa mata ƙirji. Sosai take tsananin son Yah Abdallah, kamar yanda tasan itama yana sonta fiyema da yanda take sonsa. Yah Ab farin cikinta ne, jinin jikinta ne, nutsuwarta ne, shiɗin na musamman ne a gareta, dan yana ɗauke da mataki uku ne na martaba a gareta. Shi ɗin jininta ne ɗan uwanta, sannan masoyinta tun batasan kantaba. Malaminta kuma na farko ta ɓangaren ilimi. Shiyyasa komai nasa abin girmamawane a gareta......
   “Hy Baby! Kallon ya isa haka karki cinyesa mana”. Nanah ta faɗa tana ɗan mangare kan Nu'aymah. Karon farko da tunda aka wayi garin yau Nu'aymah tai murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana, ɗan harar Nanah tayi da Iman da suke mata dariyar shaƙiyanci. Ta maida kanta ƙasa tana faɗin, “Sa'idiniyya kawai”. Nanma dariyar sukayi, ita kuma ta lumshe idanunta daga cikin hular abayar tana maijin nutsuwa da farin cikin isowar angonta lafiya bayan tsahon shekaru biyu kenan basuga junaba sai dai a waya da hoto da video call.

    Isowar ango Abdallah da abokansa tayi dai-dai da shigar lokacin sallar la'asar, dan haka aka sanar da zuwa ai salla.
   Mimmiƙewa mazan suka shigayi suna nufar bayan masallacin domin yin alwala, masu alwalar zuhur kuma da bata karyeba suna shigewa ciki. Matanma ba'a barsu a bayaba, wasu cikin gida sukaita shiga, wasu kuma sama inda massallacin mata yake.

★★★★★

   Baƙi da suka janyema Umm hankali ya saka Adawiya samun damar silalewa ta nufi ɓangarensu. Nan ɗinma akwai mutane babu laifi, musamman da a yanzu aketa shigowa domin gabatar da sallar la'asar. Sashen Abbansu ta shige, inda ta tabbatar bazata samu kowaba sai su ƴan gida. Ilai kuwa babu kowa sai ƙamshi dake ta tashi mai daɗi. Ɗakin farko dake a falon sashen ta buɗe ta shiga, babbane yasha kayan more rayuwa tsaf, ta zube a saman gadon tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai tafiya da kuka mai ƙarfi da hasala zuciya.......
         Turus Addah data fito daga bayin ɗakin fuskarta jiƙe da ruwa alamar tayo alwalar yin salla tayi a bakin ƙofa tana kallonta, a take idanunta suka rine da ɓacin rai, cikin faɗa tace, “Wai wane kalar shashancine wannan kikema mutane haka Adawiya?!!”.
    Adawiya da sai yanzu tasan da shigowarta ta taso da gudu ta faɗa jikinta da sake fashewa da wani sabon  kukan, “Addah Wlhy ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wlhy saina kashe kaina Addah. Dan nafita sonshi ku taimakeni.............”
   Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Addah ta bita harta zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Adawiya tai zaune ta riƙo hannunta. “Wlhy Addah inhar baku aura masa niba saina kasheta!!”.
   Baya Addah tai da sauri zata faɗi ƙasa tana mai waro idanu waje sosai akan Adawiya, bakinta na ɓari tace, “Ki kasheta Adawiya?!”.
       “Da hannun nan nawa kuwa”. Adawiya ta faɗa tana zazzaro idanu waje itama da ɗaga hannunta tana nunama Addah............✍

Hummmmm!!!! Turƙashi. Masu karatu wannanfa shine ana dara sai ga dare yayi????. Mi kuke tunani akan wannan labari? Wacece Adawiya? Sannan wacece Nu’aymah? Wanene Kuma Abdallah?. yaya zata kasance? Minene zai faru kuma? Wace amsa Addah zata bama Adawiya?……
Amsar waɗanan tambayoyin duk suna a Littafin SARAN ƁOYE!! da ke cikin tawagar littatafai biyar na zafafa 2021 dake shirin zuwa muku insha ALLAHU nan bada jimawa ba????????.

Wlhy karku bari ayi babuku, dan ZAFAFA BIYAR 2021 fa da zafinsu suke tafe, na tabbatar muku tafiyar wannan shekarar ta dabance MASOYAN AMANA????????????????????.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????

       *_SARAN ƁOYE!!_*
Read more: SARAN BOYE COMPLETE

Bilyn Abdull ce????????

Free page????

No. 2

……………..Tsaki Addah taja tana ballama Adawiya harara, ta tsallaketa ta wuce tana faɗin, “Sai kije ki kashetan shashasha kawai mara tunani”.
Kuka sosai Adawiya ta sake fashewa da shi. Ta rarrafa har inda Addah take shirin kabbara salla ta riƙe mata ƙafafu. Cikin fushi Addah ta ƙwace ƙafafunta tana nuna Adawiya, “Wlhy idan baki shiga hankalinkiba Adawiya zan bala’in saɓa miki, wai wane irin iskancine wannan? Ki shiga hankalinkifa tunkan nai miki abinda zakiyi dana sani a taron bikin nan. Dalla tashi ki ficemin anan, ba kashe Nu’aymah ba ki babbakama gidan wutama mu ƙone ƙarewar hauka. Wawuya kawai!!”.
Yanda Adawiya taga ran Addah ya ɓaci tasan zata iya cin ubanta kamar yanda ta faɗa, tana ganin ta kabbara salla saita tashi ta fita tana kukanta. Addah mace ce mai yawan wasa da fara’a, idan har kaga fushinta to lallai an kaita maƙura, shiyyasa idan tai fushin dolene kaji shakkarta. Su kansu ƴaƴanta tana rayuwa da sune tamkar ƙawayenta, hakama sauran yaran gidan. Wannan halayar tata tajan yaran a jiki yasa kowane yaro yazama ɗan ɗakin Addah a gidan, suna sonta sosai, hakama iyayensu sunajin daɗin yanda take son ƴaƴansu da basu lokacinta.

     Can bayan ɗakunan sashen samarin gidan Adawiya ta nufa, dan tasan canne kawai babu mutane. Waje ta samu ta zauna tasha kukanta, yayinda zuciyarta ke shirya mata mugayen abubuwa game da Nu'aymah da matakin da zata ɗauka a kanta na dakatar da wannan auren, tayi alƙawarin kota halin ƙaƙa saita mallaki Abdallah a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai kuma ta rabashi da Nu'aymah, idan kuma har hakan bata tabbata ba to sai dai suyi zaman kishi ita da Nu'aymah kokuma kowa ya rasa. Dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazata barma Nu'aymah Abdallah ba wlhy........
    “Adawiya! Adawiya!!”. ta jiyo ana ƙwala mata kira. Tsaki taja mai ƙarfi kafin ta miƙe tana kakkaɓe jikinta daya ɗan ɓaci da ƙasa, duk da ma ita ko shiryawa batayiba. Fitowa tai inda zata iya ganin mai kiran nata. Da sauri taja baya saboda karo da suka kusa ci da Yah Abdallah. Ƙirjinta yay wani mugun harbawa, a take ta fara neman nutsuwarta ta rasa. Kwarjininsa da matsanancin son da take masa suna neman birkitata gaba ɗaya ta kasa riƙe kanta....
     Sassanyan Murmushinsa ya sakar mata yana ɗan ware idanunsa a kanta, “Oh Hassanar amaryace haka bata ko shiryaba?”. Duk da maganarsa batai mata daɗiba saita saki masa murmushi, ta matsa kusa da shi tana shaƙar ƙamshin turarensa mai daɗi, “Yah Abdallah dama ka iso?”. 
   “Ya za'ayi ki sani tunda ance kina nan kinata kukan rabuwa da Husainar ki”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa tana kallon Amal data rako Yah Abdallahn. “Kiranmi kike ƙwalamin ke kuma?”. Baki Amal taɗan taɓe tana cigaba da latsa wayar hannunta, “Kiranmi zan miki ni kuwa, dama Yah Abdallah ne ke nemanki, shine akace anga kinyo tanan”.
  Kafin tace wani abu Yah Abdallah yace, “Nine na sakata, wani aiki zakimin, Amal jeki abinki”. Kai Amal ta jinjina masa, tai gaba abinta batare data sake kallon inda Adawiya take ba. Sai da tai nisa da su sannan Abdallah ya sake kallon Adawiya, ganin shi take kallo sai yay murmushi. 
   “Yaya dai ƙawar amarya na canja miki ne?”. “Sosaima kuwa Yah Abdallah”. Adawiya ta faɗa cike da yanga tamkar ba itace ta gama darzar kukaba yanzun.
  Murmushi yayi yana ɗauke kansa da faɗin, “To na gode. Kinsan aikin da zakimin?”. Kai ta girgiza masa batare da tace komaiba. “Sonake kije wajen Walimarcan ki satomin amaryata nan inason ganinta”. Wani takaicine ya soki zuciyar Adawiya har fuskarta sai da ta nuna hakan. Da mamaki Abdallah yace, “Yaya dai?”. “Babu komai Yah Abdallah” ta bashi amsa da rawar murya.
      “Okay, to maza ki shirya saiki ɗakko min ita, karfa ki bari kowa ya ganki musamman ma Hajjo”. Kanta ta ɗaga masa kawai, dan tasan idan tai magana kukane zai ƙwace mata. Da kallo Abdallah ya bita harta ɓacema idanunsa, haka kawai tausayin yaran ya kamashi, kowa yasan irin shaƙuwar dake tsakanin Adawiya da Nu'aymah tun ƙuruciya, sun tasone tamkar tagwaye a gidan, komai tare ake musu shi, yanzu kam ace zasu rabu rana tsaka ai dolene kaji tausayinsu.

    Adawiya kam koda ta bar wajen sashen Hajjo kakarsu ta nufa, babu kowa duk ana wajen walima, dan ana idar da salla kowa ya koma, daga cikin gidanma kana jiyo lecture ɗin da aka fara. Kwanciyarta tayi dan ta rantse bazata kira Nu'aymah ba.

★★★

    Tun Abdallah na kallon hanya na jiran ɓullowar amaryarsa Nu'aymah da Adawiya harya koma duban agogo. Kamar wasa sai ga mintuna ashirin sun shuɗe babu Adawiya balle Nu'aymah, abinda zuciyarsa kawai ta basa Hajjo ta hana Adawiya ɗakko Nu'aymah ne, maybe kuma tanacan tana wayon yanda zasu baro wajen. Ɗan murmushi yayi yana lumshe ido, sosai yake cike da ɗoki da ƙaguwar son ganin Nu'aymahr sa, yanason yaga yanda ta sake komawa yanzun........
     Kiran da ake masa a wayane ya katse tunaninsa, ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa ya duba. Zaid ne, kamar bazai ɗagaba sai kuma ya amsa tare da ɗorawa a kunnensa. “Hello Jibiya wai kana inane?”. Kamar bazaice komaiba sai kuma yay guntun tsaki da kallon agogon hannunsa. “Ina cikin gida mana, miya faru?”. “Cikin gida kuma? To mi kakeyi acan bayan kowa duk yana nan har amarya. Gashi nan Baba malam na nemanka to”. Baice masa komaiba ya yanke wayar. Badan yaso ba ya baro cikin gidan ya koma wajen walimar.
     Inda Nu'aymah ke zaune kusa kakarsu Hajjo ya kalla, tana zaune a yanda ya barta tun ɗazun, babu kuma alamar Adawiya a wajenma. Ɗan tsaki yayi a ransa ya ƙarasa inda Baba Malam yake.

         Masha ALLAH, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka ragargaza lectures masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya.

ZAFAFA BIYAR 2021


             Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070


    Tunda aka tashi jikin Nu'aymah sai ya sake yin sanyi, maimakon ta nufi ɗakinsu da suke zaune da ƙawayenta sai ta nufi wajen Umm. Kanta tsaye ɗakin Umm ta wuce, sai dai bata ciki sai ƴan uwanta. Gaishesu tayi suna tsokanarta da amarya-amarya, ita dai kanta a ƙasa ta sulale ta fito. Sashen baba malan ta nufa, dan tasan Umm bazata wuce tana a canba ko wajen Addah.    
     Tun shigowarta corridor ɗin daya shiga tsakanin falon Baba malam dana Umm taga takalman Umm da Addah, ɗan murmushi tayi tana sake jinjina wannan irin ƙauna ta iyayensu, ƙofar falon ta ƙarasa tare dayin sallama, daga ciki suka amsa mata da bata iznin shiga.
   “Ah ah! amarya da kanta. Miya farune?”. Addah ta faɗa tana murmushi. Kallon Umm da batace komaiba Nu'aymah tayi, sai kuma ta duƙar da kanta hawaye na cika mata ido. Addah tace, “Kinga zonan”. Takawa tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ƙasa jikin ƙafafun Umm data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan da shigowar Nu'aymah ba. 
    “Ƴar albarka miya farune? Ko kewar Umm ne ya motsa?”. Maimakon Nu'aymah ta bama Addah amsar tambayarta sai hawaye suka gangaro mata a kumatu, ta kwantar da kanta bisa cinyar Umm tana jan ajiyar zuciya a jajjere. 
  Dauriya kawai Umm keyi dama, taja ɓoyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Nu'aymahn. “Ke kuma wannan shashancin fa?......”
  “A'a babu wani shashanci Umm”. Addah ta faɗa tana kamo hannun Nu'aymah cikin nata. “Baby faɗamin miya faru? Ko har yanzu tsoron dai?”. Kai Nu'aymah ta ɗaga mata, sai kuma ta ɗago ta kalli Umm da itama kallonsu takeyi. “Umm dan ALLAH ni banason auren a fasa kawai”.
     “Afasa kuma Nu'aymah?! Miyasa?”.
   “Addah wlhy ni naji banaso yanzun kawai”.
    Sosai abin ya bama Addah dariya, ita kanta Umm sai da tai murmushi tana girgiza kai, dan babu komai a maganar Nu'aymah sai zallar ƙuruciya da sakarci. Umm ta janyeta a jikinta tana miƙewa da faɗin, “Wannan shashancin ba daniba, Addah bara nayi nan kinji”.
  Sauri riƙeta Nu'aymah tayi tare da sake cukuykuye ƙafafunta tana kukanta, “ALLAH Umm nidai banaso, gara na zauna a wajenku Please”.
   “Oh ALLAH, Nu'aymah banason sakarci kinji, sakarni naje nayi abinda zai amfaneni”.
      Kallon Umm Addah tayi, cikin magana da yaren ido taima Umm alamar ta lallasheta Please. Umm zatai magana Addah ta girgiza mata kai tana miƙewa ta fice ta barsu. Ajiyar zuciya Umm ta sake saukewa a sanyaye, kafin tai guntun murmushi da komawa ta zauna a inda ta tashi. Kama Nu'aymah tai ta tadata ta maidota kan kujerar kusa da ita ta zaunar. Hakan ya bama Nu'aymah damar faɗawa jikin Umm ta rungumeta.
     Karan farko Umm tai ƴar dariyar ƙarfin hali da rungume ɗiyar tata itama. “Ke wai bakisan kin girmaba Nu'aymah? Aurefa za'a ɗaura miki gobe idan ALLAH ya kaimu amma kike halin yara har yanzun?”.
    “Umm ni wlhy na fasa, zan zauna a wajenku nayi karatun kawai”. Dariya Umm ta sakeyi da ɗago fuskar Nu'aymah ta share mata hawayenta. “To naji ya isa haka nan kukan ko”. “To Umm za'a fasa ɗin?”. “Tambayi Abbanki ga shinan”. Umm ta faɗa tana kallon Abba daya shigo kusan mintina biyu kenan harya zauna kusa da Nu'aymahn bata saniba yana kallonsu kawai. Tashi Nu'aymah tayi daga jikin Umm takoma jikin Abbanta. 
     “Maman nan nawa dai shagwaɓanta yayi yawa”. Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana shafa kanta. Ɗagota yayi ya zaunar sosai, tare da saka hannu ya share mata hawayenta gaba ɗaya. “Kinga faɗamin miya faru?”.
     “Abbah a fasa kawai”. 
Waro idanu ya ɗanyi cikin mamaki, “Mamana mi za'a fasa?”. “Abbah aur.....” sai kuma ta kasa ƙarasawa tai ƙasa da kanta.
      “Ina jinki faɗamin mana!”.

“A…Abbah auren, ni yanzu na fasa”.
Kallon juna sukai shi da Umm dake kallon Nu’aymah cike da damuwa, Sosai ta basu tausayi da dariya, amma duk sai suka danne kayansu. Abbah ya riƙe hannayenta da sukasha ƙunshi cikin nasa, cikin muryar lallashi yace, “Mamana kin daina son yayan nakine?”. “A’a Abbah”. Ta faɗa kanta a ƙasa. “To miyasa kikeson a fasa?”. “Abbah banason rabuwa daku nidai”.
Murmushi Abbah yayi tare da sauke ajiyar zuciya, “To ai ba rabuwa zakiyi damuba Nu’aymah, kuma shima Abdallah ai ɗan uwankine mai gatantaki ma fiye da kowa a gidan nan, duk kuma sanda kikeso ya kawoki wajenmu zai kawoki”. Idanunta cike da kwalla ta kalli Abbah, “To Abbah ina zai samu kuɗin jirgi yayta kawoni kullum tun daga Saudia?”. “To ai dama ba kullum ba Mamana, keda zakiyi karatu tayaya za’ace za’a kawoki gida kullum koda anan zaku zauna ma. Duk dai sanda kuka sami hutu sai ya kawoki, kuma muma zamu dinga zuwa ganinku ai ko”. Shiru tai batace komaiba, sai hawaye keta sake mata zarya.
Cikin hikima da wayo Abbah da Umm sukaita mata nasiha da ƙara ƙarfafa mata gwiwa harta daina kuka ta koma dariya kamar ba ita ba, kusan awarta ɗaya da rabi a wajensu sannan ta tafi kiran da hajjo ta aiko Farida tai mata.

          Tafiya take tana ƙunƙunin haushin Hajjo, dan tasan kiran datai mata bai wuci sakata shiga cikin ruwan lalle ba, itako ta tsani abun dan ƙyanƙyami takeyi, amma jarabar kakar tasu bazai bari ta fito ta faɗa ba.
     Gabanta ne ya faɗi jin an kamo hannunta, ta juyo a firgice zata wage baki tai ihu aka rufe bakin.
  Cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa yace, “Matsoraciya nine. Na gaji da wasan ɓuyar da kikeyi dani malama”.
  Ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke jin Yah Abdallah ne, ya saketa yana cigaba da ƙawata fuskarsa da murmushi da ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. “Saboda kinsan kin sake haɗuwa fiye da da shiyyasa kiketa faman ɓoyemin kanki ko?”. 
   Hannu Nu'aymah tasa ta rufe fuskarta da shi tana murmushi, “Yah Ab banfa san kazo ba”.
    “Kutt!”. Ya faɗa yana zaro idanu waje, “Wato bama kisan nazoba?”. Kai ta jinjina masa da ƙyalƙyalewa da dariya. 
      “Lallai yarinya na yarda kin girma kam, idan ba tsoroba buɗe fuskar ki faɗamin ido da ido mana”. “A'a ai basai na buɗeba tunda dai kaji na farko”. “Hahyh! Zaki min bayani gobe idan ALLAH ya kaimu ai”.
    Kasa cemasa komai tai a kan hakan, saima ta risina kawai ta gaidashi. Ya amsa mata cike da kulawa idanunsa na cigaba da yawo a jikinta, duk da akwai ƙaramin hijjabi tare da ita, rayawa kawai yake a ransa ‘anya baiyi gangancin ɗaukar alwashin rinon Nu'aymah ba kuwa? Kai da sakel wai anbama mai kaza kai’.......
      “Yah Ab bara naje hajjo ke kirana”. 
 Maganarta ta dawo dashi hayyacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke daɗan kallon gefensu, sai kuma ya kalleta sosai yana gyara tsaiwarsa. “Babie kinga manta da tsohuwar can kinji, musamu guri mu zauna muɗan zanta na yaushe gamo, ke koma ɗokin ganina baƙyayi bayan kuma shekara biyu kenan baki ko ganniba”.
      Murmushi tayi tana ɗan kallonsa ta gefen ido, a ranta godiya takema ALLAH daya mallaka mata Yah Ab matsayin masoyi, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma iyanzu mijine. Ya haɗa abubuwa masu yawa na gwaranzan mazaje da kowacce mace zatai alfahari da samunsa, ita kanta tasan ta cika mai sa'a ta gaske, dan ba'a wajeba ko'a cikin yayyenta, ƴan uwanta tasan akwai masu tsananin sonsa, amma ya dage kai da fata sai ita, tun batasan kantaba, tun ana masa faɗan yay aure idan ta girma sai ya ƙara da ita har kowa ya zuba masa ido dan yaƙi amincewa, a cewarsa ita kaɗai ta ishesa rayuwa, dan haka zai jirata ko tsahon shekara nawane. Damuwa da rashin auren nasa ya saka iyayensu yanke hukuncin aura masa ita bayan sun kammala secondary wata uku kenan, acewarsu taje ta cigaba da karatun a ɗakinsa kawai..........
       “Ina kika tafi kika barni Noor?”. Ya faɗa yana kaɗa mata hannunsa saitin fuskarta. Ajiyar zuciya ta sauke da duƙar da kanta tana murmushi. “Muje” ya sake faɗa yana nuna mata hanya.
  Babu musu ta bisa zuwa can bayan sashen Hajjo, inda kuma ya kasance gaban sashen Abbansu Musbahu. Zama sukai a fararen kujeru dake a wajen, basufi mintuna uku da zamanba sai ga Adawiya. Sosai Nu'aymah taji daɗin zuwan ƴar uwar tata, dan dama a takure take da kasancewarsu su biyu kawai ita da Yah Abdallah. Shiko sam baiso hakanba, amma sai bai nunaba ya biye musu sukaita zuba masa shirmen surutunsu.
   Ganin hirar dai bazata yuwu shida Nu'aymah kawai ba sai ya miƙe bayan kamar mintuna 35 da zamansu, umarni ya basu suje su kwanta, shima zai koma wajen abokansa suna jiransa. Sam Adawiya bataso hakaba, dan wani irin farin ciki ta tsinta kanta a ciki na kasancewa da Yah Abdallah a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Sai da yaga sunbar wajen sannan shima ya miƙe ransa duk babu daɗi, dan yaso su tattauna abubuwa masu muhimmanci shi da Nu'aymah amma Adawiya tazo ta tsare ko ina.

       Ɗakinsu dake a sashen su Nu'aymah suka nufa, inda ƙawayensu suke. Wasu sunyi barci, wasu ko na hira a waya da samarinsu, wasu kuma cheating, ƙalilanne ke hira a tsakaninsu.
    Yusrah data fito daga bayi tace,  “Aymah wai ina kika shiga Hajjo nata nemanki? Sai masifa takeyi tun ɗazun, dan tazo ɗakin nan yafi sau goma”. 
        “Yah ilahi, dan ALLAH da gaske Yusrah?”. “Wlhy karkiji wasa, tambayi su Nanah ma kiji, har Addah ma sai da tazo nemanki. Ina kikaje to ke?”.
        “Muna tare da Yah Ab ne fa da Adawiya”.

“Ohhh! Kice soyayya ce ta lula dake sama. Aiko daga ke har Yah Ab ɗin kunga banu da jaraban Hajjo da safe idan ALLAH ya kaimu, ga ruwan turare can Addah tace idan kin dawo ki shiga ciki”.
A sanyaye ta amsa da “to”, sauran kuma suka sanya mata dariyar tsokana.
Bata kulasuba ta nufi toilet ɗin, Adawiya kuma taja tsaki ta fice daga ɗakin batare dasu sunma lura da itaba.


ZAFAFA BIYAR 2021


     Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

Muna godiya da zaɓin zafafa biyar????????????????????


     Har Nu'aymah ta cire kaya zata shiga bahon da Addah ke haɗa mata ruwan turare saita tuna da tabar wayarta a sashen Abbah, gashi Yah Ab yace mata zasuyi magana ta Cat. Towel ɗin wankanta babba ta cira daga ƴar durowar da suke sakawa, ta ɗaura sannan ta fito ɗakin ta ɗauki babban hijjabi dogo ta zumbula. Batace ma kowa komaiba ta fice daga ɗakin zuwa sashen Abbah.
   Sai da tai sallama a ƙofar ɗakin aka bata iznin shiga sannan ta shiga, Abbah ta iske shi da Abban Abuja suna shan shayi, ta gaida Abban Abuja kanta a ƙasa dan haka kawai yau kunyarsa takeji fiye da kullum shi Da Mamah. Shikam fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonta, “Mamana ai tun ɗazun nake baza idon ta ina zan ganki amma kin ɓoyemin gaba ɗaya”.. 
    “Lah Abba ba ɓoyewa nayiba, ALLAH bammasan ka iso ba”. Ƴar dariya yayi irin ta kamilan mutane, yace, “To shikenan na amince mamana, kina lafiya ko?”. “Eh Abba lafiya lau”. “To Alhmdllh Mamanmu”.
  Juyawa tai batare da tayi zancen wayarba, dan da anan ta barta tasan Abbah zaiyi magana. Tunanin zuwa inda suka zauna da Yah Ab tayi danta duba ko acan ta yadda bata saniba.
     Gidan yayi shiru, dan mafi yawan mutane ƴan biki sunyi barci kasancewar har 12 ta gota, sai ɗai-ɗaiku marasa barcin wuri. Duddubawa ta farayi kasancewar akwai wutar Gen da aka tada, kamar wasa saita jiyo ring ɗin wayar acan gaba da inda take. Cikin mamaki da kila wakala ta nufi inda takejin, sai dai a ranta tana son ƙin gaskata wayartace, tafi tunanin wanine mai irinsa dai.
 Tana tafiya Ring ɗin wayar na sake gaba, da kuma ya yanke zataji an sake kira, saita fara tunanin ko Yah Ab ne keta jera mata kiran? Ƙila ya hau online bai gantaba. To amma miyasa kamar ana tafiya da wayarne?. Babu mai bata amasa, ƙuruciyarta baisa ta fahimtar da ita akwai matsalaba kuma ta cigaba da bin sautin ring ɗin wayar har ta iso ƙaramar ƙofar da akai daga cikin gidan ta ɓulla massallacin ƙofar gidansu, inda su Abbah kebi da asuba yin sallar asuba dasu ma kansu idan suna buƙata ko zasu shiga islamiyya.
   Anan ne ta tsaya cak tana waige-waige. Sai kawai taji an jeho mata abu akan fuska. Saurin saka hannu tayi ta janye guntun handkerchief ɗin da aka jeho mata fari tas. Kafin ta samu damar yin wani tunani akan hakan ko neman taimako taji duk jikinta ya saki idanunta na wani lumshewa kamar wadda hankalinta ke neman gushewa daga gareta.
  Daga haka bata sake sanin mike faruwaba kuma...............✍

Tashin hankali, to wanene kuma ya da wannan aiki?????????????????????.

Amsarku na a Littafin SARAN ƁOYE dake cikin rukunin littatafai biyar na ZAFAFA 2021 da a yanzu haka sun fara zuwa muku da ɗumi-ɗuminsu, karku bari a baku labari guys, wannan tafiyar tanada banbanci sosai dana baya ina ƙara tabbatar muku????????????????????????????????????????.

       ZAFAFA BIYAR 2021
Read more: SARAN BOYE COMPLETE

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????

          *_SARAN ƁOYE!!_*


    *_Bilyn Abdull ce????????_*

Free page????.

No. 3

……………Sama-sama takejin motsin mutane na matsota, sai dai bata fahimtar maganar da sukeyi balle ta ɗauki muryar kowa. Ta dafe kanta dake tsananin juya mata tare da jingina jikinta da bangon daya raba gidan nasu da massallaci. A hakanma dai bata tsiraba, garin cigaba da mata hajijiya yakeyi. Tai ƙasa zata zame ta faɗi aka riƙota. Ƙoƙarin buɗe ido take taga wanene? amma ta kasa saboda nauyin da sukai mata, haka ta sake jiki ga koma wanene ya riƙeta sosai, kafin ya fara janta suna takawa a tare batare da tasan ina suka dosa ba.
Tabbas taji an sakata a mota an kwantar, amma daga haka bata sake sanin komai dake faruwaba a duniyar, dan barci mai nauyin gaske yayi awan gaba da ita…….

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button