Noor Albi

NOOR ALBI 48

Kokarin sake fahimtar da ita Zinat take cikin takaicinta na kasa tsayawa ta fahimta Amma Ms Na’ima Sam takasa yadda ma ta dauka zancen Dan bazai taba yiyuwaba,
Daga Turakin har Laylan sunsan halinta Babu Wanda zaiyi ko mafarkin aikata Mata hakan Dan walh ba qaramin yaqin duniya zaayiba sbd ko uban daya Haifa Laylan saita aika lahira harma da uwar riqonta ta farko Momy bazata ragawa,
Danginsu kaf saitaga bayansu.

Jin zancen Zinat din nason fara shiga Kanta yasata bude idanuwanta dasukai jajir ta kalli zinat tana kokarin calming kanta,hannuwanta duka biya akanta tana Dan yamutsawa sbd borin datakeji cikin Kan ya rage tace”

Zinat kinsan kaina bazai dauka wannan maganar dakike fadaba yanzu,
Komai zai iya faruwa idan nayi loosing control Dan Haka ki daina maimaita min zancen wata Abu tsakanin Turaki nawa da Laylah,

Ina buqatan tsayar da Laylah agabana nayi Mata kallon tsaf itada cikin jikinta,
da bakinta nakeson tafadamin waye yayi Mata ciki kafin komai sbd inason ta kalli fuskata lokacinda zata ban amsata,

Idan maganarki tazama gaskia ita da kanta tasani gwara ta dauki cikin shegu dari Akan cikin mijinta,
Shikuma Turakin Wlh akanta yagama Amfanuwa da kowace mace kuma…..Kai bama zai yiyuba Dan Haka Zinat daina fada kaina juyawa yakeyi…..

Bubbuga kanta tafara da qarfi tana cewa”

Inaaaa…bazai yiyuba wlh…..
Laylah da Turakin nawa…..

Yanda takeyine yasa Haj Zinat miqewa da sauri tana kwala Kiran siddika tazo ta Kama Mata ita
Ta bude jakarta da sauri ta dauko maganin Na’iman ta bude bakinta ta tura Mata tareda zuba Mata ruwa da sauri wasu Suka shiga wasu Suka dawo daqyar ta hadiye maganin kafin suka saketa jikinta na kakkarwa…

Kamata Haj Zinat tayi ta kaita dakinta ta kwantar Kan gado tana kallonta cikin sabon tashin hankali.

Allurar Jakarta da zata dauko saikuma ta fasa sbd Bata cikason yiwa Na’iman allauraba Idan abun ya taso Dan likita yabasu tabbacin tayi sabo da alluran idan abun yazo allurar kawai zata kwantar dashi.

Tana tsaye akanta har ta rufe idanuwanta dasukai jajir ahankali sai baccin wuyar wahala ya dauketa.

Ajiyar zuciya ta sauke sbd tasan kafin tasamu damar wani masifar tashin hankalin sai ankwana biyu
Dan Haka ita zatai amfani da wannan damar tasa siddika tasamo Mata tabbacin komai tunda siddikan tayi sabo da Laylan Sosai.

Fitowa Palo tayi ta zauna zuciyarsa na dugunzuma cikin zurfin tunani da rashin madafa,
Akaro na farko da mamakin duniya ya sakata kasa tunanin komai,
Tabbas wlh tanada babbacin Turaki nada alaqar da cikin,
Kuma alamun kuru kuru sun nuna shi da Anne sunsan da cikin Koda bana Turakin bane kuwa.

A gidan ta wuni sai dare ta wuce tabar Na’iman a kulawan siddika bayan tayiwa siddika bayanin abunda suke buqatan son sani game da komai na shaanin.

****Laylah kuwa tun bayan fitar mum Anne da kanta takaita har dakinta ta zaunar da ita tareda kwantar Mata da hankalinta dataga ya tashi kafin ta fito tabarta ta samu nutsuwa tukuna.

Ta Jima zaune tana kokarin nutsar da kanta din Amma takasa samun nutsuwar
Haka ta miqe jiki a mace ta Isa toilet tashige tayo alwala tafito tafara yin sallah.

Tanaji wayarta na ringing Amma takasa dagawa Dan tasan bazai wuce anty Sa’adah ko Abbanta ba kokuma Turakin sbd sune kawai masu numbern tunda sabuwace Abba ya siya Mata a Lagos.

Abinci Aka kawo Mata dakin aka jere Amma daqyar Anne tasata taci abincin kafin tafara Dan dawowa daidai.

Maganin ciwon Kai Tasha ta kwanta aka barta tayi bacci ko zata samu nutsuwa
Dan Haka tana kwantawa ta rufe Ido Amma Babu baccin dayakeda Shirin zuwar Mata Haka dai tayi lamo tunanin duniya suka rufo Mata har baccin dolen gaske ya dauketa.

Sai magriba ta farka ta tashi Ahankali ta nufi toilet tafarayin wanka da alwala ta fito tayi sallah ta Sanya farar doguwar free Riga Mai kyau Mara nauyi sai qaramar hula akanta red da slippers da Bata taba yawo ko cikin inane ba slippers ta fito tana sanyayyan qamshin turaren Creed.

Direct Palon Anne ta nufa tana kokarin kashe wayar dake hannunta data Gama magana da Anty Sa’adah.

Kai tsaye da siriyar sallama ta shiga palon batareda tayi tunanin samunsa acan din ba
Suna hada Ido ta dauke idonta ta nufi gurin Anne kanta aqasa ta gaidata tana kokarin juyawa ta koma Dan tanajin idanuwansa akanta gakuma Anne agurin.

MAMUH

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button