NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN

HAƘIN MALLAKA : QUEEN NASMERH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’

بِسم الله الرحمن الرحيم

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah me kowa me komai da ya bani ikon fara littafin nan me taken *NAWA* *ƁANGAREN*. Littafin da ya ƙunshi abun al'ajabi da ƙaddara wadda bawa baya wuce mata.
Wannan littafin ya ƙunshi wani darasi guda ɗaya wanda shi ya ja hankalina har na ji ina son in rubuta wannan littafi.
Littafin nan ƙirƙirarren labari ne, ban ce lallai duk abun ke ciki ya na faruwa ba. Na yi shi ne dan isar da wani saƙo guda ɗaya amma dunƙule_*Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka*_._Keep your face always toward the sunshine, and shadows will fall behind You HABEEB-ALBI_

_____________________€pisode 1................✍️"Kalmar soyayya ta daɗe da fita a cikin ƙundin kaddarata. Duk inda na ga ana tarairayarta rayuwata tana ɗugunzuma baƙin ciki ya maye gurbin farincikana na tsani ko waye ko da kuwa a nawa NAWA ƁANGAREN ne. A taƙaice na tsani 'Ya mace, tsana mafi muni. Da addinina ya halasta kisa a doron ƙasa jinsin mata yana sahun farko na waɗanda zan kawar ko da zan samu sa'ida. Ki hutar da kanki daga wahalar sona".Take idanuwanta suka canza launi zuwa tsanwa, ɗago da su tare da sanya su a na shi ido muryarta na rawa

Ta fara mayar da martani tana kallon wani makeken hoto da ke manne a bangon ɗakinta." Ina sonka Naheel! Wallahi idan ban same ka ba zan iya mutuwa. Rayuwata tana maƙale da wanzuwarka a cikinta. Me ya sa za ka tsane ni? Da ma so yana zama illah? Mine ne dalilinka na rashin yin soyayya ya kai masoyina Ɗan sarki?Murmushi wanda ke cikin hoton ya yi kana ya ce “Naheela ba huruminki ba ne". Kamar wata zakanya ta fara huci. Idanuwata suka ƙara fitowa waje kamar za su faɗo, fatar jikinta ta canza launi duk ta takure; kamar tsohuwar da ta shekera ɗari da saba'in a duniya. Ta durƙusa tana gunji da ƙarfi ta ce “Naheeeeeel!!"Akaifunta suka yi zago-zago komai nata ya sauya ba ta fasa kiran sunan “Yareemana!" Ɓat! Hoton Naheel ɓace bangon ya kasance tamkar wani abu bai taɓa zama wurin ba. Hawaye masu ɗumi suka ƙwaranyo mata a fuska tamkar idaniyar ruwa ta ce, “Ba ka da hurumin ƙin karɓar tayina, ba ka isa ka bar ni ba, Naheel Me ya sa zaka tafi bayan na wahala kafin na kawo ka nan? Ka sani ba ni da wani ɓangaren da ya wuce ka. Kai ne NAWA ƁANGAREN".Numfashi ta sauke kana ta cigaba“kai ne NAWA ƁANGAREN!"Ta nanata da ƙarfi, wanda ya sa wani iska me ƙarfi fito a bakinta iskan har wani kuka yake saboda tsabar ƙarfinsa nan take bangon ɗakin ya tsage har gida uku.Tashi ta yi ta nufi ɓangaren da bangon ya tsage ta kara tafin hannunta a gurin ta rufe idonta. Farin haske ya fara fitowa daga hannunta. Da ƙarfi ta ƙara tura hannunta a waje, sannan ta juyar da shi da ƙarfi ta buɗe idonta, ta ce “Zamzila ka nemo min NAHEEL! "Da ƙarfi take maganar idonta na fitar da wuta, wani ɗan ƙaramin maciji ya fito yana bin ƙasa da alama shi ne Zamzila. Ta kure sa da kallo iya hasken da za su fita iya ƙarfin ikon da za ta ba wa Zamzila domin ya nemo mata Naheel ɗan sarkin Aljanu...

______________________WURO BARKA........Damana uwar alheri! Idan sama ta guntso tabbas za ta fesar; ko da ba a inda ake tsammani ba ne. Iskan da ke kaɗawa a ko ina na unguwar ne zai tabbatar da cewa hadari ne mai tafe da iska da guguwa waɗanda ke majaujawa da ledodi suna yin sama. Al'umma suna ta rige-geniya neman mafaka suna kawar da ababen amfani sakamakon gabas da ta sha toka kan ka ce me! Aka kece da ruwa kamar a bakin ƙwarya

Daga can nesa wani saurayi ne da ba zai wuce shekara 27 a duniya ba, ya harɗe hannuwanshi wuri ɗaya yana kallon mutanen dake kai-kawo gurin shiga gida .Gashin kanshi baƙi ne wuluk, ya kwanta luf da shi, ba wata ƙiba gare shi ba, sannan dogo ne daidai misali. Fari ne sosai, irin farin nan mai kyau , sajenshi ma ya kwanta sosai ya bi fatar jikinshi, da ka gan shi ka ga Bafullatanin asali .Shaaaaaa! Ruwa suka cigaba da saukowa, amma duk da ruwan da ake bai motsa ba. Hankalinshi gabaɗaya ba ya jikinshi, wani ɗan ƙaramin yaro ya leƙo ta tagar da wannan saurayin yake tsaye ya ce “Bobbo ka shigo ciki ruwa yana jiƙa ka ".Firgigit! Maganar yaron ta dawo da shi daga tunanin da yake yi, ya ce ma yaron "Ga ni nan shigowa". Dayake gidajensu suna alaƙa da juna ba wata tazara, zagayawa ya yi ta ɓangarensu da sauri ya shige ɗaya daga cikin ɗakunan da suke kamar bukka.

Yara ne duk zaune sun kai su bakwai wani na bin wani, suna ganinshi ya shigo suka faɗa a tare “Bobbo sannu da zuwa ", matsakaiciyar matar da ke zaune sanye da wata riga ta Fulani, da zane, da alama matarshi ce, ta ce “sannu da zuwa me gida yau ba kwanana ba ne na Mairo ne", gaɗa kai yayi ya ce “na sani, zan ɗauki wani abu ne a nan ", ƙasan tabarma ya ɗaga ya ɗauki wata takarda sannan ya fita. Ɗayan ɓangaren ya shiga.

Kwance take a kan wata katifa daidai kwanciyar mutum biyu. Sanye take da kayanta na Fulani, rigar ta ɗan ɗage wanda ya ba tsohon cikinta damar fitowa da alama ita ce Mairo. Ganin bacci take yi ya sa ya ƙyale ta, bai tashe ta ba. Ya jawo kwanon da ke gefen katifar ya buɗe, fura ce wadda ta sha kindirmo, ta yi luƙui-luƙui da ita, ludayi ya ɗauka ya ƙara lunda furar sannan ya kafa kai ya fara sha, sai da ya ji cikinshi ya ɗauka sannan ya aje kwanon, ya ce “Alhamdulillah ". A hankali ta buɗe idonta ta sauke a kanshi kyakkyawa ce daidai misali, juyowa yayi ya kafe ta da ido, “Har ka shigo?" Ta faɗa."Ban daɗe da shigowa ba wataƙila ma baki san an fara ruwa ba ko?".Murmushi ta yi ta ce “Wallahi kuwa yau ba na jin daɗin jikina ne".A kasalance ya ce, "Ina yarana?""Suna gidan Arɗo tun safe".Gyaɗa kansa ya yi alamar ya gamsu.

Bobbo mutum ne, mai sauƙin hali, kaf cikin ƙauyensu (Mobu Ruru) ba ya da aboki ko ɗaya.Unguwarsu ma haka baya da aboki. A taƙaice Bobbo baya da aboki ko ɗaya, yana dai mutunci da kowa, amma ba za ka taɓa ganin Bobbo da wani sun keɓe yana magana da shi ba, idan ko ka ga haka to da Baffa ne ko Arɗo. Haka ya samu asali ne daga ra'ayinshi na rashin son an yi an ce, ya tsani duk wani dalili da za a ce “Bobbo ne ya ce kaza", ko “tare da Bobbo mu ka yi kaza". Ga shi mutum ne da baya son yawan magana ko kuma jan zance. Shiyasa komai na shi a taƙaice ya ke yinshi.Ta masu karatu a yau dai ni Queen Nasmah na zo muku da wani sabon salo na labari da ban taɓa ɗauko mu ku irinshi ba, bazan ce komai ba akan labarin ba, amma ƴar uwa wannan littafin na daban ne 


_MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU'A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE_ .LOVE U ALL FANS...................

*NASMAH LIMAN*

~*JIKAR-MAI-SHUKURA*~✍️

*09121873529*
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN* HAƘIN MALLAKA : QUEEN NASMERH

*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????**'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 

بِسم الله الرحمن الرحيم

~

Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka.
The bad news is time flies. The good news is you’re the pilot HABEEB ALBI.

€pisode 2…………….✍️

Da hanzari Macijin ya riƙa bin ƙasa, yayin da wutar da ke idon Naheela ta ci gaba da ruruwa, tana fitar da wani mashahurin zafi. Hannayenta duka suna a ware ta juyar da kowanne yana kallon wani ɓangare. Wani irin iska me matuƙar ƙarfi, ya riƙa fita daga tafin hannuwanra. Zamzila kuwa wani ƙarfi yake ji duk lokacin wannan iskan ya bugo sa, da ma ƙarfin iskan ke ƙara masa kuzari da karfin gudu kamar Ingarman doki. Shi kuma hasken wutar ke ƙara haskaka masa hanyar da zai bi, domin nemo Naheel, ba zato ba tsammani Zamzila yayi karo da wani ƙaton dutse.

“Ahhhhhhhhhh! “Ta saki wata mahaukaciyar ƙara wadda ta karaɗe ko ina na cikin dajin, sanadiyar Karo da zamzila ya yi da dutse. Jini ya kwaranyo daga cikin kanshi yana malala. Jinin da ke zuba a kan Zamzila ne ya janyo wa Naheela faɗuwa, guiwowinta suka lashi ƙasa. Tim! Ta durƙushe, kanta na kallon ƙasa, ta ɗauki kusan minti uku a haka. Daga baya ta ɗaga kanta sama, wani Koren haske ya fito cikin idonuwanta, wul-wul yana tsalle da sauka kamar ƙwallo. Sai da ta fitar da dunƙulen haske guda bakwai daga cikin idonta.

Kanta ta ɗaga tana kallon waɗannan ƙwallayen masu haske da ke zagaye Saman kanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana “Ku kai wa Zamzila ɗauki.” Ta ƙarasa maganar cikin rawar muryar.

Bat! Waɗannan Ƙwallayen suka ɓace, tare da lula a sararin samaniya, cikin ƴan daƙiƙu suka isa in da Zamzila yake. Daidai kanshi suka tsaya, sannan suka haɗe kansu wuri ɗaya suka saki wani ɗorowan haske ya dinga sauka kan Zamzila duk ƙarfin hasken nan bai sa ya motsa ba. Nan take suka ƙara warewa, suki doki juna ƙarar karon da suka yi ya assasa baƙin hayaƙi ya turnuƙe wurin, wani ƙarfi ya shiga Zamzila, ya tashi ya fara bin ƙasa amma yanzu ba kamar ɗazu ba sanadiyar buguwar da yayi. Zumbur Naheela ta tashi tsaye ta sake sakin wannan wutar kamar yadda ta yi ɗazu, wata mahaukaciyar dariya ta saki har tana wani duƙewa. Nan ta tsagaita tare da haɗe rai kamar ba ita ke dariya ba. Ganin yadda Zamzila ke tafiya cikin ƙasa baya sauri, ƙara ware idonta tayi ta ce “ Me na ci na Asham da zan yi ramuwar sallah, Zamzila gara ma kar ka sare dan faɗuwa ba tawa ba ce “.

Ta kai ƙarshen maganar tana fitar da baƙin hayaƙi a cikin bakinta.


FADAR ZAWATUNDUMA

Kowa ce halitta tana da nata muhalli, haka yake a garin Zuwatu. Garin Zuwatu gari ne da babu wani Ɗan’adam da yake da ƙarfin ikon takawa zuwa gurin. Gari ne da ba a ba wata halitta damar zuwa ba. A wannan garin akwai wata teku mai ɗimbin tarihi.

Wannan tekun ta girmi duk wani aljani da za ka gani a wurin, idan ka zaftare Mai Martaba ZAWATUNDUMA (wato sarkin aljanun teku).

Tun kafin Zuwata ya zama gari, Zawatunduma yake zaune a cikin wannan tekun, hakan yasa duk wanda ya zo, ya same shi a cikin a nan.

Wannan dalilin yasa Sarki Zawatunduma mulkin duk wani aljani da ke cikin tekun Zuwatu. Babu mai gida irin nashi, dutse aka sassaƙa ya zama muhallinshi. Sauran aljanun suna zama ne a cikin ruwa ba su da damar da za su gina gida wannan ƙarfin iko umurnin Mai martaba ne.

“Mai Martaba an samu labarin inda Gimbiya Naheela ta ke “. Ɗaya daga cikin Bafadenshi ya faɗa. Naheela kaɗai ce wadda ke wahalar da su idan ta ɓata duk dubararka sai ka wahala zaka gane inda take. Yau ma tun safe ake nemanta amma babu ta babu labarinta.

Da sauri Sarki ya miƙe a duniya babu abin sa yake so kamar Naheela ita kaɗai ce wadda ya mallaka madadin jininshi, a rayuwarshi bai taɓa aure ba. Ƙaddara ta haɗa shi da mahaifiyar Naheela wanda a yanzu bai san in da take ba.

” Tana ina? Ina Naheelar take ? “Ya tambaya cikin rawar murya. Bafaden ya ce “ A hasashenmu tana fadar Sarki Zimba, can ta ke zuwa wurin Yarima Naheel, kuma…”

“Dakata! Hasashe ne ma ashe! “Sarki ya faɗa a fusace.

“Yallaɓai mun haska abin duba, amma ƙarfin da Gimbiya Naheela ke aiki da shi ya mamaye duk wani kayan sihiri da muke da su. Ba zamu iya nemo ta da ƙarfinmu ba”.

Runtse ido Sarki ya yi , “kamin alƙwari ba za ka taɓa amfani da ƙarfinka ikonka a kaina ya kai Abbana” Maganar Gimbiya Naheela ta dawo mishi a kai.

Da sauri ya buɗe idonshi saboda tunawar da ya yi na ya ɗaukar mata alƙwari.

A hankali ya ce, “Yanzu miye mafita? Na yi wa Gimbiya alƙwarin ba zan yi amfani da sihirina kanta ba “.

Cikin jinjina al’amarin Bafaden ya ce “Babbar magana gawa ta riƙe mai wanka, yanzu ya za mu yi?”

Sarki ya ce “ Kira min Muƙanzimu ka ce ya zo da kayan aikin shi”.

“An gama Mai martaba”. Bafaden ya faɗa. Sannan ya tashi ya fita.


WURO BARKA

Yara ne sun kai su sha biyar, wasu duk tsararraki ne, babban cikinsu ba zai wuce Shekara 8 ba, zaune suke kan wundi (tabarmar kaba), an zuba musu abinci cikin wani ƙaton kwano, rinɗima-rinɗiman ƙwaryoyi ne cike da fura , har ƙwarya uku aje gefensu, da kuma wata ƙatuwar roba an cika ta da ruwa duk yaran kayan fulani ne a jikinsu, sai faman cin tuwo suke da madarar shanu, yayin da wasu mata guda uku suke sharar tsakar gidan.

Daga can ɗayan gefen kuma Arɗo ne da matarshi Asama zaune tana faman renon tsohon ciki, sai yaransu guda uku zaune suna shan fura. Mamma kuma mahaifiyarsu Bobbo na tsaye gaban turmi tana dakan fura, Bobbo ya shigo kanshi a ƙasa, yaran da ke zaune kan tabarmar kaba suka fara tsalle, suna murnar ganinshi, “Bobbo sannu da zuwa ” duk suka faɗa a tare. Sai da ya shafa kansu gaba ɗaya yana murmushi , sannan ya gaida Mamma, Mamma ta ce “Lafiya ƙalau Bobbonmu, kuma Bobbon yara ya kake?”Murmushi ya ɗan yi ya ce “Ina lafiya, bari na shiga daga ciki Mamma”.

Mamma ta ce,“Kai kullum ka kama ka ƙunshe kanka cikin ɗaki Bobbo, a ce kai ba za ka karɓi ƙaddara ba, jarabawa ce ubangiji ya riga ya jarabce ka da ita sai ka yi haƙuri da taka ƙaddarar”.

Murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kana ya gaida su Arɗo, ya tashi ya shige cikin ɗaki . Arɗo da Mamma suka hau mita,“ A ce mutum kullum da damuwa a ranshi, ya kasa bar wa Allah komai bari Baffanku ya dawo zan ƙara tuna mishi”. Mamma ta faɗa Arɗo ya ce “Wallahi ni ma Mamma abin nan yana matuƙar damuna, ɗazu nake wa Asama maganarshi”.

Nan dai su ka shiga mayar da zance. Asama ta ce “Ku yi haƙuri, irin yanayin nan bai da daɗi ko kaɗan, ku taya shi da addu’a “.

Mariya ɗaya daga cikin matan da ke shara ta aje tsintsiya tana karkaɗe farin zaninta ta ce “Bari na je gurinshi”, da yake yau kwananta ya shiga, ko da ta shiga ya cire kayanshi ya sa wata riga marar nauyi, ya zauna kan katifar dake shimfiɗe ɗakin. Ta ce “Mai gida na kawo maka ruwa?”.

Girgiza kai ya yi, sannan ya ce “Zauna magana nake son mu yi da ke “.

Samun wuri ta yi ta zauna jikinta duk ya yi sanyi dan ta san duk Bobbo ya ce zai yi magana da ke to ba lafiya ba.

Ido ya ƙura mata yana kallon yanayinta duk ta daburce, tausayinta ya kama shi, amma ba yadda ya iya, ya ce “Mariya bari na fara da cewa ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, don Allah ki yi haƙuri”.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button