NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai 

hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace “Barrister ka kunna 

plss…”

Lumshe ido Aliyu yayi jin sunan da ta kira lkci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya bude idanuwansa ya taka a hankali har ya isa gabanta, ja baya ta dinga yi 

xuwa lkcn ta daina kukan da take tsoro ne fal xuciyarta, ya xauna dab da ita har suna jiyo numfashin juna xata mike da sauri, yyi hanxarin rikota ta fashe 

da kuka jikinta na rawa, a hankali ya jawota jikinsa ya rungumeta lkci daya ta hadiye kukan da take, ya dinga jin yanda xuciyarta ke bugawa a kirjinsa kamar 

xai fito, lumshe ido yyi hawayen idanuwan sa suka xubo, cikin rawar murya tace “Barrister ka kunna wutan bana son duhun plss, switch the light on” Murya can 

kasa yace “Imannn” Ta fi second talatin muryar da taji na kai kawo a kanta, a hankali ta xame jikinta daga nasa tana kallon fuskarsa cikin duhun dakin kamar 

yanda shi ma yake kallonta a sanyaye, hannu ta kai fuskarsa tana masa wani kallo da kyar tayi gathering courage din cewa “Aliyu?” Rungume ta yayi kamar xai 

mayar da ita jikinsa cikin rawar murya yace “Yes Iman, I beg you… don’t say no to me plsss, this our fate… na sha wahala kan ki a rayuwa Iman, na sha 

wahala fiye da tunanin ki, kashe ni ne kadai son ki bai yi ba, for good six years bani da kwanciyar hankali bani da walwala, forgive and forget the past 

plss, Barrister Aliyu…” Kasa ci gaba yyi bayan wani lkci ya ci gaba voice dinsa na breaking “I owe him… he gave up for me…. Ya bar min ke Iman, don 

girman Allah ki ji tausayina kar ki bani wahala….” Kamar warce aka yi moulding haka khadijah tayi stiff jikinsa maganganunsa na mata yawo a kai, she’s 

still trying her best to apprehend all what he is saying, Jin tayi shiru ya dago kanta jikinsa na rawa, hawayen dake makale idonta suka xubo tana kallonsa, 

ta fashe da wani matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma wa da sakon mutuwa, sauka yyi saman gadon a rikice ya durkusa kan gwiwowinsa kusa da ita yace 

“Iman kiyi ma girman Allah kada ki wahal da ni, I have already had enough, don’t say no to this marriage, kar ki ce A’a Iman….” Kasa ci gaba yyi…. A 

hankali tayi baya ta fada saman gadon, ya mike da sauri ya riketa yana kiranta amma tuni idanuwanta suka rufe, ya dago ta ya rungume ta hawaye na sakko masa 

yace “Why Iman, kin yi saurin mance alkhairin da na maki a rayuwa, sharrin kawai kika bari a ranki, ba laifina bane, ba yin kai na bane, ni ba maxinaci 

bane, duk xaman ki gidanmu ban taba tunanin akwai ranan da xai xo in cuce ki ba….”  Kasa ci gaba yyi ya runtse ido yana rungume da ita har sannan. Sai 

kusan karfe hudu saura na asuba khadijah ta bude idanuwanta a hankali, Aliyu da ke xaune kan darduma ya mike da sauri ya iso kusa da ita yana kallonta da 

damuwa, mikewa take kokarin yi tana kallon jikinta, riga ce mara nauyi jikinta maimakon atamfar da ta sa tun a gida, Aliyu ya xauna gefen gadon a sanyaye 

yana kallonta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon yana son riketa amma yana tsoron abinda xai biyo baya, cike da karfin hali yace “Iman you are not 

strong ina xa ki, Wait…” Bai san lkcn da ya riketa ba ganin tayi baya xata fadi, xai kwantar da ita ta kwace kanta tace “Let me” Dafe kansa yyi, ganin 

xata sake tashi ya kara rikota, tura hannunsa tayi muryarta na rawa tace “Dole sai ka rike ni ne, nace bana so” ko saurarenta bai yi ba ya ki saketa, ta 

fashe da kuka tace “I want to use the restroom ka kyalenii….” Tashi tsaye yyi ya dagota ya nufi bayi da ita, suna isa bayin ta kwace kanta ta shiga ta 

rufe kofar, a hankali ya koma gefen gado ya xauna duk jikinsa a sanyaye, tana fitowa ta nufi kofar fita ya mike da sauri yace “Iman” ganin ko juyowa bata yi 

ba ya karasa da sauri kafin ta isa kofar ya rufe ya marairaice yana kallonta, Xaunawa tayi nan bakin kofar ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka 

xuciyarta yayi rauni ga wani xafi da yake mata, yanxu dama duk yaudararta Sudais yake, me yasa xai ci amanarta ya sa a aura mata Wai Aliyu?? Of all people 

why Aliyu? The beginning and end of her problem, the person that shattered her life, me yasa xai sa a aura mata shi, ta dinga kuka a raunane taji duk 

duniyar ya isheta, gaba daya ji tayi haushin kowa take har Umma don tasan ita ma ta sani amma ta boye mata, a hankali Aliyu ya sa key kofar ya cire a jiki, 

Jin haka ta mike a mugun fusace hawaye na sakko mata xuciyarta na bugawa tace “Malam ka bude min kofa in fita…. Bana son ganin ka, bana so….” Bai bari 

ta kai karshe ba ya jawota jikinsa ya rungume ta ya lumshe ido, duk iya kokuwan da ta dinga yi xata kwace kanta kasa wa tayi daga karshe ta hakura ta dinga 

kuka, a hankali murya can kasa yace “Plss, tell me how many days will it take you to finish this drama?” Dago kai tayi tana masa wani kallo xuciyarta na 

heaving, a sanyaye yace “I just want to get prepared… Just tell me for how long it will take you to finish it? And in sha Allah I will endure” fuskarta 

daure tace “Sake ni” a hankali ya saketa ta koma baya ta mika masa hannu tace “Bani makullin” ya mika mata makullin hannunsa, ta juya ta bude kofar ta fice 

tayi banging din kofar, Ya d’an tabe baki ya juya a hankali ya koma kan gado ya kwanta don har wani ciwo kansa ke yi masa baccin da bai yi ba, har aka kira 

Asuba bai bari bacci ya daukesa ba ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito don wucewa masallaci, kwance ya ganta kan 3 seater a parlor tana bacci ta 

dunkune waje daya saboda sanyin parlorn, ya kashe A.c sannan ya nufi kofa ya bude ya fita. Ko da ya dawo masallaci bai ganta parlorn ba kuma, ya wuce sama 

ya bude kofar dakinta a hankali yana leka ciki ya ga bata nan, juyawa yyi da sauri ya bude wani dakin, xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta jikin 

bango, tana ganinsa ta daure fuska ta cinno baki gaba, a hankali ya rufo mata kofar ya shiga nasa dakin ya kwanta, sai a sannan bacci ya daukesa. Sai da 

gari ya fara wayewa khadijah ta mike jiki ba kwari daga kan darduman da take xaune ta bude kofar dakin ta fito, dakinta ta bude a hankali tana kallon ciki, 

ganin babu kowa ta shiga ta rufe kofar, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito, bayan ta shirya ta kwanta saman gado jin kanta na ciwo sosai, bacci ne ya 

dauketa daga haka, Bata farka ba sai da aka danna bell a kasa, ta mike xaune da kyar tana kallon agogo, har sannan kanta ciwo yake ba kadan ba, karfe tara 

saura ta gani, ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta sa ta fita, a hankali ta bude kofar ta ga Baby tsaye rike da basket din abinci tana murmushi 

tana kallonta, khadijah ta hade rai sosai ta juya ta koma parlor, Baby da ta bi ta da kallo a xuciyarta tace kya yi ki gama ne ma, A nan parlor ta ajiye 

basket din ta juya xata fita khadijah ta bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar sai a sannan baby ta fara dariya kasa kasa, khadijah da ta bi ta da kallo 

ta xauna kujera lkci daya hawaye ya cika idonta ta ji kamar ta bi ta ta mata magana amma ta kasa tashi, wato dai ita ma tasan wanda aka aura mata amma bata 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button