NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

fada mata ba, tashi tayi ta wuce sama ta shiga daki ta fada kan gado tana kuka takaici, bayan wani lkci ta mike ta dauko wayarta ta shiga kiran Sudais, sau 

uku tana kira bai dauka ba, ta ajiye wayar tana share idonta ta kwanta xuciyarta ba dadi, ta jima kwance jin ciwon kai ya isheta tana son shan magani ta 

mike a hankali ta fito, downstairs ta sauka taga abincin da baby ta kawo na nan yanda ta ajiyesa, ta kalli agogo ta ga har sha daya ya kusa, sama ta kalla, 

ta fi minti biyar tsaye kafin ta nufi kofar da take xaton kitchen ne ta shiga ta dauko cup da spoon, shayi ta hada ta koma kujera ta xauna, kasa shan shayin 

tayi ta ajiye cup din hannunta a hankali ta wuce sama, dakin da take tunanin nasa ne ta bude a hankali, kwance ta gan sa kan gado idonsa a rufe, ta dinga 

kallonsa kafin ta karasa ciki kamar mai tsoron taka tiles din ta isa har kusa da shi ta duka, Bbu wanda ya fado mata a rai lkcn sai little Sudais, lkci daya 

taji jikinta yyi sanyi ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, lkci daya ya bude idanuwansa ta mike da sauri tana kalle kalle kamar mai neman abu duk ta 

daburce…..

Aliyu ya mike xaune yana kallonta yace “Did you come to check on me?” Ta tsuke fuska tace “Saboda kai Shureim ne?” Ya shafa kansa bai ce komai ba, ta juya 

da sauri ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice, sai a sannan ta ja tsaki taji haushin shiga dakin da tayi, parlor ta koma ta dau shayin da ta hada, da 

kyar take sha don gaba daya bakinta ba dadi, ji tayi kamar xata yi xaxxabi, ta mike ta dau sauran kayan kumallon ta kai dining ta ajiye ta wuce kitchen don 

wanke cup din shayin ganin baxata ta iya sha ba, xata ajiye bayan ta wanke taji kamar mutum bayanta ta juya da sauri suka kusa cin karo suna hada ido ta 

hade rai ta dauke kai, ya mika mata hannu a hankali yace “Bani cup din” tace “Saboda xaka amsa cup sai ka tsaya bayana toh” Bata jira me xai ce ba ta ajiye 

cup din ta fita kitchen din ya bi ta da ido. Har aka yi azahar bata kara fitowa daga dakinta ba, xuwa lkcn ta fara jin yunwa sosai amma ta kasa sakkowa, duk 

xaman dakin ya isheta, tana ta xuba ido taga kiran Umma amma shiru, ga kewar Shureim da ya cikata, duk abubuwan suka taru suka mata yawa, ta hade kai da 

pillow tana son yin kuka amma ta kasa. Aliyu na xaune parlor yana duba wasu articles bayan sun yi waya da Sudais yace masa suna hanya, saboda su ma ya dawo 

parlorn ya xauna, ajiye takardar hannunsa yyi ya dau pain reliever a center table for the second time in 2hrs ya balla biyu ya dau table water dake ajiye ya 

sha maganin ya mayar da ruwan ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, ya rasa me yasa bai samu relieve ba bayan wanda ya sha daxu, har ya 

fara bacci a haka ya ji an danna bell, ya bude ido ya mike ya isa kofar ya bude, Baby ce rike da lunch, ganinsa tayi murmushi tace “Yayanmu Ina yini?” Ya 

shafa kai a hankali yace “Lafiya lau” da damuwa tace “Are you sick?” Ya d’an bude ido yace “Me kika gani?” Tace “You look so” murmushi yayi yace “Am 

alright” Bata ce komai ba ta shigo parlorn cike da tausayinsa ta ajiye abincin hannunta ta juyo tana kallonsa tace “Ka ma yi breakfast kuwa yaya?” Yace 

“Nayi mana, ya su Mumy” Xaunawa tayi tace “Suna gaishe ku” ya xauna shi ma yace “Ki kai mata abincin sama” xaro ido baby tayi tace “Uhn ba ruwana, I don’t 

want to imagine me going to her now” Aliyu bai ce komai, tana kallonsa a hankali tace “You just have to be patient ya Aliyu, soon nasan xata hakura… Kar 

ka damu kaji yayana, I know it’s just for few days” Murmushi yayi yace “Toh Allah ya sa” cike da tausayin sa tace “Ameen” yace “Plss ki taho da Shureim idan 

xa ki xo anjima….” Tace “Ae yana can gidansu” yace “Ehh ki dauko sa can din, I am lonely…” Tace “Toh Yaya xan kawo sa” Wayarsa ne yayi ring ya dauka 

yaga Sudais ke kiransa, yyi pick din call din Sudais yace “Muna waje” Aliyu yace “Alryt ku shigo” Baby na kallonsa bayan ya katse wayar tace “waye yaya?” 

Yace “Barrister with Dr Ayman I guess” Baby tayi shiru bata ce komai ba, bude kofar parlorn aka yi khaleel ya fara shigowa kafin Sudais, Aliyu ya mike bayan 

sun gaisa gaba daya suka xauna, Baby na kallon Dr Ayman tace “Ina yini” yace “Lafiya lau ya kike?” Tace “Alhmdllh” kallon Barrister tayi dai dai lkcn da ya 

kallota shi ma, yace “Ina yini” xaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace “Ina yini” yace “Ohk I was thinking baxa ma ki gaisheni ba” Khaleel yayi murmushi 

yana kallonsa ta gefen ido bai dai ce komai ba, Aliyu ya kalli baby don tsoron xuwa daki gun khadijah yake yace “Baby talk to her tana daki” Mikewa baby 

tayi ba don tayi niyya ba  ta wuce dakin gabanta na faduwa, Khadijah dake kwance ta daga kai jin an bude kofa, ganin baby ce ta mike xaune tana kallonta, a 

sanyaye tace “Shine daxu baki min magana ba kika wuce ko Baby” Baby tace “Hmm tsoron ki nake ai ni Iman” Baby ta xauna kusa da ita, khadijah ta kamo 

hannunta a hankali tace “Amma baby kin san wanda aka aura min kika boye min, idan kowa ya boye min ke bai kamata ki min haka ba, Ni yanxu shkkn cikin kunci 

xan kare rayuwata, nobody is after my happiness….” Hawaye cike idonta ta kare maganar, a sanyaye Baby tace “Nan gaba xa ki gane ma’anar hakan da aka yi 

Iman, just give my brother a chance… Iman ki manta abinda ya faru a baya, ki kwantar da hankalin ki da Yaya Aliyu you won’t regret it am giving you my 

words….” khadijah ta dinga share hawayen dake sakko mata bata ce komai ba, tasan ita dai baxata taba kwantar da hankalin ta da wanda yyi disfiguring dinta 

heartlessly ba, cikin kwantar da murya Baby “Kiyi hakuri Iman, nima wllh ban san da yayanmu aka daura auren ba sai da muka tashi barin gida jiya da yamma 

kin dai ji na rantse maki” Har sannan khadijah bata iya ta ce komai ba sai goge idonta take, Baby tace “Ki sakko ki xo gu gaisa da su Barrister suna parlor” 

Kallonta khadijah tayi da sauri ta tsuke fuska tana girgixa kai tace “Am not going anywhere, they are nothing but group of deceivers…” duk yanda baby ta 

dinga lallabata Khadijah kin yarda ta fito tayi har da kukan ta, baby ta rasa yanda xata yi, mikewa tayi daga karshe ta dawo parlor, Aliyu na ganinta yasan 

kwanan xancen, Baby ta kirkiri murmushi tace “Tana fa bacci ne, Kuma bana son tada ta….” Murmushi Sudais yyi yana shafa beard dinsa a hankali yace “That’s 

nyc, thanks for covering up for her, but we are not strangers, kuma baxa mu ji haushi ba idan kin ce tace baxata fito ba, wataran xata fito mu ganta ai” 

Dariya khaleel yyi yana kallon baby da ta rikice sai rawar baki take, Aliyu yyi murmushi bai dai ce komai ba, Sudais na kallonta duk da dariyar da ta basa 

shi ma yace “Sorry, just relax Mami ni ban yi haka don ki rikice ba” Baby bata san lkcn da ta balla masa harara ba ta juya da sauri xata wuce tana murmushi, 

Aliyu yace “Kawo masu drink” kitchen ta wuce ta dauko masu drink din ta ajiye, Aliyu yace “Abinci fa?” Sudais yace “Nop Alhmdllh” mikewa baby tayi ta dau 

abincin ta wuce sama, Dakin khadijah ta shiga tana harararta ta ajiye abincin hannunta tace “thanks for making me look stupid downstairs, Kuma abincin ma na 

daina kawowa sai dai ku fita eatry da mijin naki” daga haka ta wuce, tana shiga parlor tace “Yaya ni xan koma, Mumy tace kar in dade” Yace “Alryt then, da 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button