NOOR ALHAYAT 81-90

driver ku ka xo?” Ta girgixa kai yace “Toh je sama ki dau transport” Khaleel yace “Xa mu wuce yanxu sai Barrister yyi dropping dinta tunda hanyar daya” Har
bakin mota Aliyu ya raka su bayan sun wuce ya dawo cikin gidan, sama ya wuce ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta. Har aka yi la’asar khadijah na daki, duk da
ta ji gidan shiru ta kasa fitowa ta dau plate ta debi abinci, Tana tunanin yanda xata fita aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo, sau daya ya kalleta ya mayar
da dubansa kan abincin da Baby ta ajiye dakin, ya isa gun abincin yace “Ain’t you eating the food?” Banxa tayi masa, ya duka ya bude warmer din yana kallon
abincin, dauka yayi ya juya ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo, ganin ya fita ta tashi da sauri ta bi bayansa har ya shiga dakinsa ta shiga ya juyo yana
kallonta, tace “Nace maka na ci abincin ne ni?” Kamar xata yi kuka tayi maganar, dariya ta basa, ya yi murmushi yace “You never told me” daga haka ya mika
mata ta karbe abincin ta juya ta fita, yana jin ta sauka don dauko plate a kitchen ta dawo ta shiga dakinta, sai a sannan ya sauka xuwa kitchen ya hada
shayi, duk da yunwan da khadijah take ji bata iya ta ci abincin me yawa ba, ta mike daga karshe ta fita, har xata kai abincin kasa sai kuma ta tsaya a
hankali ta bude dakinsa ta gansa xaune yana rike da cup din shayin, ta sauke kanta kasa ta shiga dakin ta ajiye masa warmer din ta juya ta fita ya bi ta da
ido. Karfe shidda saura baby ta dawo gidan tare da shureim, Sau uku tana danna bell, khadijah ta mike ta sauka bata san Aliyu ma ya fito bude mata ba, yana
bude kofar Shureim ya wara ido ganinsa cike da murna yace “Unclee” nufo sa yayi da nufin rungumesa ya hango khadijah, Wara ido ya kara yi yace “Anty….”
Murmushi ta sakar masa ta buda masa hannu, Har ya dau hanyar inda take sai kuma ya tsaya ya juyo yana kallon Aliyu dake kallonsu, dawowa yyi gun sa da gudu,
Aliyu ya daga sa sama ya rungume sa yana murmushi yayi Pecking cheek dinsa, Lkci daya murmushin fuskar khadijah yayi fading, Baby bata san lkcn da ta fashe
da dariya ba, Shureim ya xame daga jikin Aliyu ya nufi khadijah da gudu, wani kallo ta watsa masa tace “If I slap you” nan ya taka burki ya tsaya yana
kallonta, Ta turo baki ta juya ta wuce sama, Murmushi kawai Aliyu yayi ya nufi yaron ya daga sa sama yace “How are you sweetheart” yace “Am fine” Baby ta
ajiye abincin hannunta tace “Ina yini yayana” yace “Alhmdllh” tace “Driver na jira na waje, sai da safe” yace “Alright ki gaida mumy, tell her thank you”
tayi murmushi tace “Toh yaya” daga haka ta juya ta wuce tana daga ma Shureim hannun, yana rike da Shureim suka haura sama ya shiga dakin khadijah ajiye mata
shi yyi kusa da ita yace “Greet her now” a hankali Shureim yace “Anty good evening” dauke kai tayi ta hade rai tace “Evening” Daukansa Aliyu yayi suka fita
dakin ta bi sa da wani kallo, har karfe kusan tara na dare khadijah bata ji motsin su ba, ta yi wanka ta shirya cikin night wear, jin shirun yyi yawa ta sa
Hijab ta fita, ta fi minti biyu a tsaye, kafin ta tura kofar dakin a hankali, duhu ne dakin, ta laluba ta kunna switch, kwance taga Aliyu Shureim na kwance
kusa da shi duk sun yi bacci, kashe Ac dake aiki tayi ta kashe switch din ta fita dakin ta koma nata ta kwanta. Kasa bacci tayi sai juye juye take har kusan
sha biyu ta ji an bude kofa, sosai gabanta ya fadi ta kalli direction din kofar duk da wuta a kashe yake, rufe kofar yyi ba tare da ya kunna wutan ba ya iso
har inda take ya duka, mirginawa tayi da sauri daga wajen tace “Meye haka?” Yace “Na xo duba ki ne kamar yanda ke ma kika xo duba mu” Xaro ido tayi tana
kallonsa cikin duhun, yyi murmushi murya can kasa yace “Sweet dreams” daga haka ya fita ya kulle kofar dakin.
A hankali khadijah ta koma ta kwanta, bata kara minti biyar ba bacci ya dauketa. Da asuba tana jin fitansu tare da Shureim xa su masallaci, ita ma ta mike
ta shiga bayi, tana xaune kan darduma tana azkar taji shigowarsu gidan, bude kofar dakinta Aliyu yyi suka shigo tare da Shureim, kallo daya tayi masu ta
dauke kai, ya xauna gefen gado Shureim ya nufe ta ya durkusa gabanta yace “Anty ina kwana?” Tana kallonsa tace “How was ur nyt?” Ya wara ido yace “It was
cool Anty” Bata ce komai ba ta saci kallon Aliyu suka hada ido, d’an murmushi yayi a hankali yace “Good morning Iman” sunkuyar da kanta tayi bata ce komai
ba, ya mike ya nufi kofa Shureim ya bi bayansa da sauri ta bi su da ido har suka fita, ta fi minti ashirin xaune ganin gari ya fara washewa ta mike, tana
sane jiya babu abinda tayi a gidan, yau kam ta sauka parlor ta share ko ina ta goge, ta shiga kitchen ma ta gyara ta goge, tana kokarin sa turaren wuta a
burner aka danna bell, mikewa tayi tana kallon kofar, ta wuce sama da sauri don dauko hijab ta dawo ta bude, Baby ce tsaye da breakfast, Khadijah ta
langwabar da kai tace “Don Allah daga yanxu kar ki sake kawo abinci xan yi girki muna ba Mumy wahala…” Baby ta wara ido sai kuma tayi dariya tace “Xa dai
ki girka abinda xa ki ci, tunda nasan ba bama yayana xa ki yi ba, yaron ki kam nasan shi ma xa ki basa, Abbansa dai ne baxa a bai ma ba” tabe baki khadijah
tayi ta bata hanya ta shigo ta ajiye abincin nan parlor tace “Da fatan kun tashi lafiya, yau naga har da su gyare gyaren gida meye sirrin Iman?” Tana
murmushi da tsigar tsokana ta kare maganar, khadijah ta hade rai tace “Wani irin sirri?” yar dariya Baby tayi tace “Oho, ni dai xan wuce, a gaida min
yayana” Daga haka ta nufi kofa khadijah ta bi ta da kallo har ta fita sannan ta tabe baki, ta koma ta ci gaba da abinda take, dinning ta kai breakfast din
ta ajiye sannan ta wuce sama ta shiga daki, nan ma ta gyara gadonta tayi goge goge kafin ta shiga wanka, tana xaune gaban mirror bayan ta fito wanka tana
shafe shafe aka bude kofar bedroom din, xaro ido tayi tana gyara towel din jikinta, ganin Shureim ne ya shigo ta sauke ajiyar xuciya, ya iso kusa da ita
yace “Anty am hungry” tace “Me ya hana uncle din baka breakfast” Ya buda hannu yace “He told me I shud come to you ki bani” Tana shafa mai a kafarta tace
“Shi me yake yi?” Shureim ya matso cream din xai shafa mata ta 6alla masa harara tace “Ina wasa da kai koh?” Ya mike yace “Anty taya ki xan yi” toes dinta
ta mika masa tace “Toh shafa a nan” ya durkusa yana shafa mata tace “Tambayar ka nayi me uncle din yake?” Ya kalleta yace “He is lying down” shiru tayi bata
ce komai ba, a hankali yace “Anty yace min he is not feeling fine” Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “What’s wrong with him” Yace “I don’t know” Tace
“Je parlor ka jira ni in sa kaya sai in xo in baka breakfast” yace “Toh” sanann ya fita dakin, mikewa tayi ta dau atamfar da xata sa na riga da skirt, sosai
dinkin yayi mata kyau tayi simple dauri na dankwali ta sa eye pencil a idonta sai chapette ah two colored lips dinta, sosai tayi kyau, ta fesa turare daga
karshe ta fita dakin, har xata sauka stairs sai kuma ta tsaya, ta fi minti biyu tsaye kafin ta karasa kofar dakinsa a hankali ta bude, kwance ta gansa ya
rufa da duvet har kansa, ta sauke idonta kasa ta karasa dakin kamar mai counting steps dinta, tana ta tsaye kusa da gadon tana kallonsa, a hankali ta