NOOR ALHAYAT 81-90

durkusa dab da shi ta cire duvet din fuskarsa, idanuwansa a lumshe suke, ta kai hannu forehead dinsa, lkci daya ya bude idonsa tayi saurin dauke hannunta ta
koma baya, kasa tashi tayi kuma bata yarda sun kara hada ido ba ta fara kame kame, kallonta kawai yake, ta dago daga karshe tana kallonsa a hankali tace
“Are you sick?” Ya mike xaune yace “No…. am alright” shiru tayi tana kallonsa, ya sauka daga kan gadon ya nufi bayi ta bi sa da kallo don kana ganinsa
kasan karfin hali yake yi, Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita dakin, kwance ta ga Shureim ya kunna cartoon yana kallo parlorn yana ganin ta yyi
saurin kashe tvn da remote din hannunsa, ta tsaya tana kallonsa tace “Who asked you to switch on the tv?” Shiru yyi yana kallonta, ta wuce dining ta hada
masa shayi a cup ta debar masa dankali da kwai da plantain, sannan ta yankar masa bread karami ta daura gefen plate din Irish din, tace “Zo ka xauna nan
Shureim” ya taso ta ja masa kujerar dinning din ya xauna ta ajiye masa abincin a gabansa sannan ta koma kitchen ta dauko wani cup din ta dawo ta hada wani
shayin, ta debi Irish da kwai a plate, ta dauko wani bowl ta xuba pepper soup na kayan ciki, gaba daya ta daura su kan tray ta dauka ta wuce sama, a hankali
ta tura kofar dakin nasa, xaune ta gansa gefen gado ya rike kansa, jin an bude kofa ya dago yana kallonta, kanta a kasa ta iso har kusa da shi ta ajiye tray
din ba tare da ta kallesa ba ta mike ta fita dakin. Dining ta koma gun Shureim ta xauna kujerar kusa da na shi ita ma ta hada shayin, a hankali take sha har
ta gama, tuni Shureim ma ya gama ya mike pleadingly yace “Anty plss in kunna tv?” Kai ta gyada masa ya juya ya wuce parlor, ta kwashe duk abinda suka bata
ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito, sama ta wuce ta bude bedroom din Aliyu, kwance ta gansa ya kara rufa da duvet, ta karasa tana kallon breakfast da ta
ajiye masa, Bata san lkcn da ta xauna gefen gadon ta yaye duvet din tana kallonsa da damuwa tace “Baka yi breakfast din ba? What’s wrong with you?” Ganin
bai bude ido ba kuma bai ce komai ba ta kamo hannun sa da damuwa tace “Talk to me plss” bude ido yyi ya mike xaune, ta dauko cup din shayin da ta rufe ta
bude tana mika masa tace “Gashi ka sha sai ka sha magani” karba yyi xata dauko plate na irish ya dakatar da ita “Noo I will take this first” da kyar yyi
maganar, ta dago tana kallonsa ya kai shayin baki kamar wanda xai sha magani, kadan ya kurba ya cire a bakinsa, tace “Da zafi ne?” yana girgixa kai ya mika
mata, ta hade rai tace “Me xan yi da shi?” Xai ajiye kasa tayi saurin cewa “Kar ka ajiye shi, u better force ur self to drink it…” Bai saurareta ba ya
ajiye ya mike ya nufi bayi da sauri, a sanyaye ta mike bi sa da kallo, tana ta tsaye ita dai bata ji yana amai ba kamar ynda tayi tunani, can dai ta bi
bayansa, jingina tayi da kofa tana kallonsa ganin aman yyi har ya wanke wajen, ya juyo xai fita bayin ta rikesa a hankali tace “Let me make you water sai
kayi wanka” yana gyada kai yace “Finish first” daga haka ya fita, ta hada masa ruwan ta fito, kwance ta samesa ya kara rufe kansa, ta cire duvet din da
damuwa tace “Kayi wankan sae mu je asibiti” da kyar ta samu ya mike xaune, tana ta kallonsa ganin har rama yyi, sauka yyi daga kan gadon ya cire jallabiyar
jikinsa ta amsa ta ajiye sannan ya wuce bathroom, sai a sannan ta fita dakin a sanyaye. zaunawa tayi gefen gadonta tayi tagumi bayan kusan minti talatin ta
tashi ta koma dakinsa, dai dai lkcn ya fito wanka daure da towel, tayi saurin juyawa kamar mai neman abu sai kuma ta fita dakin, turo baki tayi ta sauka
downstairs ta tadda Shureim yana ta kallo ta xauna kusa da shi. Jin alamar Aliyu na sakkowa stairs ta kalli direction din, kananun kaya ne jikinsa yana rike
da makullin mota ya iso parlorn, ta mike tana kallonsa tace “Where are you going to?” Bai ce komai ba, ya nufi kofa, ta isa gabansa ta hade rai tace “Nace
ina xa ka?” Ya ki kallonta yace “To get drugs” kwace makullin hannunsa tayi tace “Let me do the driving” Daga haka ta nufi stairs ya bi ta da kallon gefen
ido, mayafi karami ta dauko a daki ta rataya a wuya ya dinga kallonta, ganin ta nufi kofa yace “Iman!!!” juyowa tayi tana kallonsa, yana nuna mayafin kanta
yace “Haka xa ki fita?” Kallon kanta tayi daga sama har kasa tana masa wani kallo tace “So?” Kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta hade rai ta dawo ta
damka masa makullinsa tace “Sai ka ja motar, ka tafi inda xaka” Komawa tayi ta xauna ya bi ta da kallo kafin ya fita parlorn, turo baki tayi jin yana
warming mota ta mike ta wuce sama ta dauko Hijab dinta ta sa ta sakko parlor, kashe tv tayi tana hararan Shureim da duk hankalinsa gaba daya na kan kallo as
if his life depend on it, ya mike da sauri yana kallonta yace “Anty ina xa ki je” Bata tanka sa ba ta nufi kofa ya bi bayanta, Tun daga nesa Aliyu ke
kallonsu daga cikin motarsa ko kiftawa babu har suka iso ya dauke kansa, Ta hade rai tace “Ka koma daya side din” D’an murmushi yayi ba tare da ya kalleta
ba ya fito ya koma daya bangaren Shureim na biye da shi a baya, yaron ya bude back seat ya shiga, shi kuma ya xauna front seat, ta shiga maxaunin driver,
sabon mai gadi dake bakin gate ya bude gate din ta fita da motar, a hankali take driving din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace “Wani
pharmacy?” Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira’ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace “Who taught you how to drive” Bata ce
komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace “A Good Samaritan taught me” Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta
bi sa da wani kallo, Shureim yace “Anty, Uncle ba shi da lafiya koh” Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya
shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace “Ina xa ki je?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Xan je gida in dauko ma Shureim wears
dinsa” “Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba” A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo
baki ta dau hanyar gida… Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da
ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta wuce kitchen, Cup din tea ta hada ta fito ta haura sama, bude kofar dakinsa tayi ta gansa xaune yana ballar drugs
shureim sai surutu yake masa, ta ajiye masa shayin gabansa ta fita, dakinta ta shiga ta kwanta, Bata san lkcn da bacci ya dauketa ba kawai taji hannu a
fuskarta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace “What?” yace “Kin yi baki downstairs” Ta d’an buda ido tace “Su
wa?” Ya mike yace “Suna jiran ki” daga haka ya nufi kofa tace “Shine baxa ka turo Shureim sai ka xo kana wani taba min fuska” har ya fita bai juyo ba balle
yace komai, tashi tayi ta gyara daurin dankwalinta ta bi bayansa, Tsaye tayi stairs din karshe tana kallonta ko kiftawa babu. Suka hada ido da Khaleel dake
jujjuya makullin motar hannunsa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ta karasa shigowa parlorn kanta a kasa, haka kawai taji wani mugun kunyarsa take ji, ta