NOOR ALHAYAT 81-90

juya ya fita, komawa tayi ta kwanta kan gado duk jikinta a sanyaye daga maganganun da Umma tayi mata, ta kusa minti talatin kwance Shureim ya shigo dakin da
sallama, tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon yana ta xuba kamshi, yana murmushi yace “Anty ina kwana” tace “How was ur night” yace “Alhmdllh” tace “wa
ya maka wanka?” Yace “Uncle, Anty we are going out yace in kin shirya ki fito, muna jiran ki” ta hade rai tace “Kayi breakfast ne?” Yace “Eh mun yi da
uncle” ta mike xaune tace “Toh ni ce baxan yi breakfast din ba xa ka wani ce kuna jirana” Tsayawa yyi yana kallonta, Aliyu ya bude kofar dakin, sanye yake
da shadda milk color, lkci daya kamshinsa ya cika ko ina na dakin, yana kallonta yace “Iman, ke nake jira” Ta kallesa tace “Ku kunyi breakfast ni kuma sai
in fita haka?” Ya daga kafada yace “Nobody stopped you from Breakfasting….” Tashi tayi tsaye ta nufi kofa kamar xata tashi ta bi gefensa ta fice dakin ya
bi ta da kallon gefen ido kafin yayi murmushi, Shureim yace “Uncle da mun kawo mata nata daki koh?” Karasowa yayi yana murmushi ya xauna gefen gadon ya dafa
kafadan yaron yace “Ko mun kawo mata cewa xata yi who sent us…” Shureim yayi dariya yace “Uncle but why is she even angry, ko bata son gidan nan ne, or
she don’t want you to leave with us?” Murmushi kawai Aliyu yayi yana shafa sajensa a hankali yace “I don’t know also, amma ka tambayeta” ya xaro ido yana
yar dariya yace “Xata doke ni ne” rungume sa Aliyu yyi a hankali yace “Not when am around darling” Suna ta xaune dakin har ta dawo, Bata yi xaton xata
samesu a ciki ba, Bata rufe kofar ba tace “Can you both excuse me” Ya kalli Shureim yace “Tafi downstairs gani nan xuwa nima” fita yaron yyi a dakin,
khadijah ta xaro ido tace “Cewa nayi both…” yana murmushi yace “Ni ba mijin ki bane xan yi excusing din ki?” ta daure fuska tace “Ni dai ka fita xan canxa
kaya” Yace “But am not stopping you Iman” ya kalli agogon wrist dinsa yace “Kina ta bata mana lokaci kuma da nisa xa mu je” Tace “Toh ka fita, ko kuma in
fasa xuwa” Yana kallonta kamar mai counting word din yace “I.. am.. going.. no where!” Wani kallo ta dinga masa, lkci daya ta nufi can karshen gado tayi
kwanciyar ta ta juya masa baya, murmushi yayi ya hau saman gadon tana ganin haka tun kan ya matso kusa da ita xata tashi yyi saurin cafkota, Kamar xata yi
kuka tace “Don Allah Aliyu ka bari, bana so, to nace ka fita in sa kaya ka ki fita, ya xanyi?” Sosai xuciyarta ke bugawa tana kallonsa, ya jawota jikinsa a
hankali ya kai bakinsa wuyanta murya can kasa yace “Me yasa xan fita, what is it that u are hiding” turasa tayi da karfi tace “Stop it Aliyu..” Ya dago yana
kallon idanuwanta yace “Really?” Jin yanda muryarsa ya canxa ta hadiye wani abu da kyar tace “Alryt, since you are not going na ji xa sa kayan haka, sake
ni” a hankali ya saketa yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ganin inda ta nufa da gudunta ya mike da sauri ya riga ta isa kofar ya sa makulli yana
kallonta, juyawa tayi kamar xata yi kuka tace “Me yasa kake min haka don Allah” ganin irin kallon da yake mata da lumsassun idonsa ta koma gun kayanta ta
fiddo wanda xata sa kamar xata yi kuka, bathroom ta nufa ya bi ta, ta tsaya bakin kofar pleadingly tace “Don girman Allah ka bar ni in sa kaya Aliyu, Kai fa
kace ina bata maku lokaci… ” bathroom din ya shiga ya jawota xata yi ihu ya sa makulli yace “Ki sa a nan tunda kina kunyar sa wa a cikin dakin” Bata fuska
tayi tace “Ni wllh bana son abinda kake min…” Ya amshi kayan ya daura kan washing machine yace “Let me help you” Bai jira cewarta ba ya jawota lkci daya
ya sauke doguwar rigar jikinta idonsa ya sauka kan tabon Cs dake cikinta, tayi kara a rikice ta durkushe wajen jikinta na rawa, dagota yayi yana kallonta a
sanyaye ko kiftawa babu, ta dinga nonnokewa tana cewa “Don girman Allah ka bari Aliyu, wlh kunya nake ji” a hankali ya saketa yace “Toh sa kayan ki” jikinta
na bari ta dau skirt din atamfar da sauri ta sa, sanann ta dau rigar ma ta saka, ya jawota jikinsa ya ja mata zip din rigar a hankali, ta kasa kallonsa,
dago kanta yayi a hankali, ta rufe idonta da sauri, yayi murmushi yyi mata light French kiss, a rude ta bude idonta ya saketa ya bude kofar ya fita bathroom
din, da kyar ta fito daga karshe duk jikinta ya mutu, Kasa shafa komai tayi a fuskarta ta sa turare da hijab kawai ta sakko downstairs, yana xaune parlorn
Shureim na kwance jikinsa, ta ki yarda ta dago kanta har ta iso ta tsaya daga bayan kujera, kallonta kawai yake ganin ta kasa dagowa yayi murmushi yace “Ko
d’an kwalliya baxa ki yi ba” Ta turo baki tace “Baxan yi ba” ya xaunar da Shureim yace “Toh mu je in fada maki me yasa xa ki yi” da sauri ta dago tana
kallonsa tace “A’a ni bana so…” Yace “Toh je ji gyara fuskar ki” juyawa tayi da sauri ta koma sama tana waigen ko ya biyota, tana shiga daki ta sa
makulli, eye pencil ta sa ta goga powder a fuskarta ta sa chappete, lokaci daya tayi wani sanyayyen kyau, ta maida hijab dinta ta sauko rike da flat shoe
dinta, kallonta kawai Aliyu yake ko kiftawa babu har ta shigo parlorn, ya mike yana kallon Shureim yace “Tafi daki ka dauko min makullin mota” tashi yyi ya
wuce sama, Aliyu ya mike ya nufo ta, tana ganin haka tace “Wayyo don Allah ka bari, Kar ka xo kusa da ni ka ga yanxu Shureim xai….” Toshe bakinta yyi
ganin ihu xata masa, yana kallon eye balls dinta yace “You… Are beautiful Iman” Tayi saurin sauke idonta gabanta na faduwa, ya xame hannunsa bakinta, Bata
ankara ba sai jin kiss tayi, duk sai da ya rabata da chappete din da tasa ta kasa kwakkwaran motsi wajen, ganin faduwa xata yi yayi saurin rikota tayi
regaining balance dinta, dai dai lkcn da Shureim ya bude kofa, Saketa Aliyu yyi ya fita parlorn da sauri, Shureim ya sakko yana kallon mum din tasa da tayi
stiff inda take yace “Anty what are you looking at” da sauri ta dawo ta fara kame kame, sai kuma tace “Toh ka kai masa makullin mana” waje ya tafi ta karaso
cikin parlor da kyar ta xauna, Tana jin ya gama warming mota don ma kar ya biyota ta mike ta fito da sauri, har lkcn xuciyarta bugawa yake, Sosai ta ji
dadin ganin Shureim xaune a gaba, ta bude back seat xata shiga Aliyu ya kalli Shureim yace “Kai koma baya sweetheart sai Anty ta xauna gaba” hade rai
khadijah tayi tana kallonsa, Shureim ya fito ya dawo baya, Tana masa wani kallo tace “Nima a bayan xan xauna” juyowa Aliyu yyi ya kafeta da idanuwansa,
sauke nata tayi da sauri, ta rufe motar ta xaga ta shiga gaba kamar xata yi kuka, har suka fita gidan bata yarda ta kallesa ba, sai bayan da suka hau titi
yace “Zaria xa mu je” ba tare da ta kallesa ba tace “To do what?” Yace “Xa mu je gaida Anty khadijah, daga can sai mu biya family house din su iklima tana
can” Lkci daya jikin khadijah yayi sanyi sosai, a hankali Aliyu yace “But idan baxa ki shiga ba sai ki tsaya a mota mu shiga ciki da Shureim” Ta girgixa kai
tace “A’a xan shiga” almost half of the journey surutun Shureim kadai ne ke tashi a motar, daga karshe khadijah da abun ya isheta ta juya tana masa mugun
kallo tace “You keep ur mouth shut…. ka dame ni” Aliyu ya bude ido sosai yace “Ni fa yake ba labari ba ke ba malama” Hararansa tayi tace “Ehh nace ya ishi