NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

kunne na, ya dakatar da labarinsa haka” Murmushi Aliyu yayi a hankali yace “Toh Anty…” Ganin sun kusa Zaria a hankali Khadijah tace “Toh baxa mu kai mata 

komai ba?” Aliyu ya d’an kalleta ya mayar da hankalinsa kan titi sannan yace “Like what?” Tace “Kamar fruits da dai abubuwan da marasa lafiya suke so” 

Murmushi yayi, bayan sun shiga Zaria yayi parking gun wasu masu siyar da kayan marmari, ya siya mai yawa, ya sa bayan mota ya dawo side din khadijah yace “I 

think fruits din ma sun isa” Khadijah tace “Toh iklima fah?” Yace “We will get her something idan mun fito” Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin 

driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya 

dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace “You need not to be afraid of anything 

Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito” Ta girgixa kai tace “A’a xan shiga” daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din 

shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da 

sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana 

xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga 

kallon Anty khadijah dake kan gado….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button