NOOR ALHAYAT 81-90

da Nanny ta daura ta juya tana kallon Shureim dake mika mata waya, ta hade rai tace “Waye yake kira yanxu kuma?” Yace “Doctor” tace “Nace kar ka sake kawowa
baka ji Koh” yace “Am sorry Anty” daga ya juya ya koma da wayar, Khaleel ne ke kiranta tun daxu ta ki daukar wayar, da ya kira sai Shureim ya kawo wayar don
yana hannunsa, Umma dake jin su a parlor tace “Wa ke kiran ki baxa ki dauka ba khadijah?” Turo baki tayi tana juya miyar tace “Umma number ne and I don’t
want to pick” Umma bata ce komai ba duk da taji san da Shureim yace doctor ne, khadijah ta sauke miyar ganin yayi ta hade plates xata wanke sai ga Shureim
ya dawo da waya yana mika mata, wani kallo tayi masa tace “Kana son duka koh?” Kamar xai yi kuka yace “Anty it’s a number, it’s not saved” karban wayar tayi
taga Aliyu ke kiranta, tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, a hankali yace “Iman ya kike?” Tace “Lafiya lau ya su Mumy?” Yace “They are fine, Ina
Shureim?” Tace “Gashi” yace “Ya jikin sa?” Tace “Ya ji sauki, only the cough” yace “Ohk basa wayar” Mika ma Shureim wayar tayi ta ci gaba da abinda take,
bayan wani lkci ya dawo mata da wayar, share hannunta tayi ta amsa ta kai kunne, Aliyu yace “Baby wai xata xo wajen ki, is that okay by you?” Khadijah tace
“Yaushe xata xo?” Yace “Anjima xan kawo ta” Khadijah taji dadi har ranta tace “Toh ina jiran ta sai ta xo” yace “Ohk” daga haka ya katse wayar. Bayan azahar
Umma na xaune parlor da Nanny suna llissafin abubuwan da xa a siyo a Dubai na kayan daki, ita dai khadijah tana kwance tana danna wayarta Kiran Aliyu ya
shigo wayar, Dagawa tayi ta kai kunne tana jin sa yace “Muna kofar gida Iman” khadijah ta mike xaune tace “Ohk ga ni fitowa” katse wayar tayi tana kallon
Umma tace “Umma ta iso bari in je in shigo da ita” Umma tace “Toh sai kin dawo” mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota
ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace “Khadijah…” Khadijah tayi murmushi tace “Baby ya su Mumy” Baby tace “Suna gida, sun ce a gaishe ku” Khadijah
tace “Ayya, Ina amsawa” Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace “Ina Shureim din?” Tace “Yana ciki” ta kama hannun Baby tace “Mu shiga ciki” Baby ta
kalli Aliyu tace “Toh yayanmu nagode sai anjima” khadijah kawai yake kallo yace “Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa” ba tare da ta juyo ba tace
“Toh” Da fara’a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace “Umma xai je su gaisa da
Mumy wai” Umma tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace “Gobe xan koma Iman” ta kallesa tace “Toh
Allah ya kai mu” yace “Ameen” har xata tafi ta juyo tace “Amma plss kwana baby xata yi koh?” Yace “Ban sani ba, ki tambayeta” tace “Tohm” daga haka ta wuce
ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da
irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da
tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace “Kuka Kuma baby, toh an gama labarin” baby na share
idonta a sanyaye tace “Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki…” Khadijah tayi murmushin karfin hali bata
ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace “Ki ci gaba plss Iman” a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai
baby take khadijah na kallonta, Baby tace “Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss” Khadijah tayi murmushi tace “Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa
tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings” A hankali baby tace “Allah saka ma barrister” shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi
murmushi a hankali tace “Ai shi xan aura baby” kallonta Baby take da mamaki tace “Yaushe?” Khadijah tace “In less then three weeks ne bikin” A sanyaye baby
tace “Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?” Khadijah tace “Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo
in kai ma Mumy kati” Baby tace “Ya Aliyu ya sani?” Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace “Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a
nan garin yake?” Khadijah tace “Ehh nan yake, ae kin san sa” Baby tace “A’a ban san sa ba” Khadijah tace “Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi”
Baby tace “Ai su biyu ne ranan” Khadijah tace “Ai anjima xai xo sai ku gaisa” Baby tace “Allah ya kawo sa” khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan
ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace “Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba” khadijah ta marairaice tace “Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely,
xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana” Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira
ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace “Toh yanxu Umma xata kirata” Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan
sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi
shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace “Am outside dear” murmushi tayi tace “Toh ae shigowa xaka yi”
Sudais yace “Uhm is it necessary?” Mikewa khadijah tayi ta dau mayafinta tace “Toh baxa ku gaisa da Umma ba?” Yace “Sai nayi shawara da ke? Even the day
before yesterday ai na xo, gaisheta tare ma muka je da Little Meerah” Murmushi khadijah tayi tace “Ohk then gani fitowa” daga haka ta katse wayar ta kalli
Baby tace “Baby mu je ki raka ni sai ku gaisa dama kin ce baki san sa ba” Baby tace “A’a je ki dawo ke dai, just extend my greetings” Khadijah ta bata fuska
tace “Don Allah ki taso mu je plss” Baby tayi yar dariya tace “Toh naji” tashi tayi ta dau gyalenta suka fita dakin, sai da Khadijah ta fara shiga dakin
Umma ta sanar mata xasu fita gun Sudais sannan suka fita, Yana tsaye jikin mota sanye cikin kananun kaya ya rungume hannunsa, tun da suka fito yake kallon
khadijah, Baby ce ta fara sallama tace “Ina yini?” Sai a sannan ya dubeta da murmushi ya amsa sallamarta yace “How are you?” Tace “Lafiya Alhmdllh, ya
aiki?” Yace “Mun gode Allah” daga haka ta juya tace “Toh Iman sai kin shigo” tana fadin haka ta shiga cikin gida, khadijah ta dawo gefensa ta tsaya tace
“Welcome My Barrister” ya wara ido a hankali yace “Really?” Boye fuskarta tayi tana yar dariya, yace “Kun xo lafiya dear?” Tana kallonsa tace “Alhmdllh”
yace “Ashe dama kina da kawaye?” Ta xaro ido tace “Uhm Baby ce fa kanwar Aliyu” Shiru yayi yana kallonta, can yace “Tana xuwa nan kenan?” Khadijah ta
girgixa kai tace “A’a tun bayan rasuwar takwaran ka sai yau ta sake dawowa” yace “How did she know u are back, ko kuna waya ne?” Tace “A’a fa, nasan Aliyu
ne xai ce mata mun dawo” yana kallonta a hankali yace “Ya aka yi Aliyu yasan kin dawo” shiru tayi ta kasa kallonsa, bayan few seconds ta dago kai tace