NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

gabansa ya mika masa hannu yana murmushi yyi masa sallama, Sudais ya basa hannun shi ma suka gaisa sannan ya kalli khadijah yace “Good evening” tace 

“Evening ya su Mumy?” Yace “Suna gaishe ki” kallon Shureim yayi yace “Go inside kace baby ta fito ina jiranta yanxu” Shureim ya shiga gidan Aliyu yayi ma 

Sudais sallama ya koma motarsa yana kallonsu ta ciki, Sudais bai sake cewa komai ba yana jingine da mota har baby ta fito, ta iso gun khadijah tana murmushi 

tace “Khadijah ni xan koma, ki taya ni yi ma Umma godiya idan kin koma ciki, nagode sosai” Khadijah tace “Toh nima nagode Baby ki gaida min mumy sai na kawo 

card din, and I will give you a call later” Baby tace “Alryt dear” sallama tayi ma Sudais ta wuce motar Aliyu ta shiga ya tada motar ya bar layin. Ranar 

Friday kamar yanda khadijah tace ma Baby misalin karfe sha daya ta shirya taje gidansu tare da Shureim don Sudais yace yana da wani case ranan. A hankali ta 

murda kofar parlorn ta ji a bude, ta shiga hade da sallama, Aliyu ne xaune parlorn tare da Salim yana operating laptop, ya daga kai yana kallonsu, ta sauke 

idonta ta karaso cikin parlorn, ta gaida Salim sannan ta kalli Aliyu tace “Ina kwana”  Yana xaunar da Shureim dake gaishesa kusa da shi yace “Lafiya lau ya 

gida” tace “Alhmdllh, Mumy fa?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Bata nan, ki jira ta xasu dawo yanxu” tace “Baby fa?” Yace “Tare suka fita” tace “Toh bari in 

baka sako ka ba Mumy” Ta bude jakarta ta fiddo IV din tana kallonsa ta mika masa, karba yayi idanuwansa a kan content din Invitation card din, a hankali ya 

dago yana kallonta ko kiftawa babu, bata sake yarda ta kallesa ba tace “You help me deliver it to her plss” daga haka ta sauko da Shureim dake xaune kusa da 

shi ta juya ta fita daga parlorn yana ce mata shi ta bar sa a gidan, ganin yanda Aliyu yyi still wajen, Salim ya karbi card din don ganin na menene. Gida 

khadijah ta koma tana ta ma Shureim dake mata kukan bata bar sa gidan ba masifa, tana sauka kan napep din tace “Don uwar ka ba sai ka koma ba tunda gidan 

dangin uwar ka ne can din” Ta bude jaka ta ba mai napep kudinsa ta wuce ciki abun ta, ya bi ta yana kuka kamar xai tsaga gidan, Ta fi seconds goma tana 

kallon takalman dake bakin kofar parlorn, can ta bude kofar ta shiga a hankali, Khaleel ta gani xaune parlorn Umma ma na xaune, ta wani hade rai bata sake 

kallon parlorn ba xata wuce daki Umma tace “Khadijah” tsayawa tayi ta ki juyowa, Jin Umma bata ce komai ba ta juyo a hankali tace “Na’am Umma” Hada ido suka 

yi da shi, ta sauke idonta tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau” Tana kallon Umma tace “Mun dawo Umma, ba mu sameta ba ma” Umma na kallon Shureim da ya makale 

bakin kofa yana kuka tace “Shi kuma me ya samesa?” Harara ta balla masa tace “Au kuka kake min har yanxu, nace ka koma gidan koh” a hankali yace “I don’t 

know the road” Umma tace “Me yasa baki bar sa ba” Tace “Mumy fa bata nan, Baby ma bata nan, to ina yake son in bar sa” yana kallonta yace “Wajen Uncle dina 

mana” Khaleel ya juya yana kallonsa yace “Come over dear” sai a sannan Shureim ya gansa ya taho gun sa da sauri yace “Uncle when did you come?” Khaleel ya 

xaunar da shi gefensa yace “Today” Murmushi yayi yace “Uncle kun xo da Anty na?” Khaleel ya shafa kansa yace “Sure” tabe baki khadijah tayi ta juya ta wuce 

daki abun ta, Tana xaune gefen gado tana danna wayarta Umma ta shigo dakin, ta xauna gefen gadon ita ma a hankali tace “Ashe abinda ya faru kenan Khadijah?” 

Kasa kallonta Khadijah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, sai a sannan ta dinga jin xafin maganganun da Jawahir tayi mata, maganganun suka dinga dawo 

mata sabo, Umma tace “Ni ban ce kiyi kuka ba, ki share idon ki kije ki samesa ki ji abinda xai gaya maki” cikin rawar murya tace “Ni baxan je ba Umma” Umma 

tace “Ban isa da ke ba kenan” goge idonta ta dinga yi a hankali ta mike ta dau gyalenta ta fita a sanyaye, tun da ta fito yake kallonta har ta karaso ta 

xauna kujera ba tare da ta yarda ta kallesa ba, a hankali taji yace “Khadijah” sai a sannan ta daga kai tana kallonsa.

✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨

 Kallon direction din daki yayi kafin ya kalli Shureim yace “Je ka dauko min wayar Anty a daki” yaron na wucewa  ya mike ya dawo gefenta ya xauna ta d’an 

matsa ta dauke kai, a hankali yana kallonta yace “Don Allah kiyi hakuri Khadijah, I wasn’t happy with what happened also, and… Plss forgive Jawahir for 

the sake of….” Katse sa tayi tace “Toh ni nace na riketa a rai ne? Not at all, don bata min komai ba” Ya lumshe ido ya bude yace “Don Allah kiyi hakuri 

Khadijah” tace “Wllh nayi, Kuma komai ya wuce a wajena, ita ma xan sameta idan na taba mata wani abun ta yafe min” Shiru yayi bai iya yace komai ba, mikewa 

tayi xai rikota tayi saurin barin wajen tana hararansa tace “Meye haka?” Kallonta kawai yake, ta tabe baki tace “Am coming now” daga haka ta wuce ciki sai 

ga ta ta fito da kati ta iso kusa da shi ta mika masa, Bai karba ba yace “Meye wannan?” Tace “Ka amsa ka duba mana” da kamar baxai karba ba sai kuma ya 

karba yana kallon katin, a hankali ya dago kai yana kallonta, ta rungume hannayenta tace “Xa ka samu xuwa kuwa duk da baka gayyaceni naka ba?” Ya sauke 

idonsa bayan few seconds yace “Why not” ta koma ta xauna a hankali tace “Toh nagode” Jujjuya card din kawai yake bai ce komai ba, can ya dago yana kallonta 

cikin sanyin murya yace “Ur happiness is mine khadijah, since this will make u happy, this is what u want for ur self, I am wishing you the best in it, 

Allah ya kai mu lokacin yasa ayi a sa’a” kasa cewa komai tayi tana kallonsa, yace “But I am happy for a reason, soon xan maki abinda xai sa ki farin ciki na 

har abada in sha Allah” daga haka ya mike yace “Kice ma Umma na tafi” har ya nufi kofa ya fita bata samu bakin magana ba, ta sauke idonta a hankali taji 

xuciyarta ya mata rauni. Tun ana biki saura kwana shidda Umma da Nanny suka fara shirye shirye ba ji ba gani, da kanta ta kai ma Kawun Khadijah katin bikin, 

kusan guda ashirin ta tafi da domin ya ba sauran yan uwansu can, Bata tsaya ta sauraresa ba balle matan sa da yanxu suka xama abun tausayi don miji ba shi 

da shi, ga yayansu duk aure ya mutu ana xaune gida, duk da bakaken maganganun da suka dinga jifanta da shi ita dai bata tanka su ba ta fita, wai don ma basu 

san da kaddarar da ta afka ma Khadijah ba kenan wannan, gidansu sadeeq ta shiga ta ba Mahaifiyarsa ma katin bikin sannan ta juyo xuwa kano. Tun da bikin ya 

gabato kullum sai baby ta xo gidan da close frnds dinta uku ganin da gaske khadijah bata da kawaye kamar yanda ta ce, tare suke shirin komai da xuwa kasuwa, 

babu wanda bai yaba kayan lefen da Sudais ya hada ma khadijah ba, as in abun ba a cewa komai, ya kashe mata kudi ba na wasa ba, Umma ta xuba kudi me yawa ta 

sa aka fara gyara khadijah, xuwa yanxu kam khadijah ta kara xama wani silent har da rama, hakan bai wani damu Umma ba sanin ko wace Amarya na experiencing 

haka, tun da bikin ya karato Sudais bai wani cika xuwa ba sai dai su yi waya, hakan yasa hankalin khadijah ya kwanta don ko ya xo bata jin ma xata iya fita 

gun sa. Mumy ta gama hada gudunmawarta gaba daya tana kallon Aliyu dake xaune yana danna waya dakin nata tace “Abuturrab ko kai xaka taimaka ka kai don 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button