NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

Allah” sai a sannan ya dago yana kallonta, Mumy ta xauna gefen gado tace “Na fa ce ka cire ma kanka damuwa Abuturrab, you are never destined to be married 

to khadijah, ba kadarraku ba kenan kuma baka isa ka ja da Allah ba, ga mijinta nan ka gani so plss take her off ur mind, ka samu mace kayi aure…” Ya sauke 

idonsa kasa cikin sanyin murya yace “But I have never for once complained Mum, kina gani har kiranta nayi na mata Allah ya sanya alkhairi” Mumy tace “You 

are not complaining but ur mind is, gashi nan duk ka fita hayyacin ka, ga shi nan kana neman jefa kanka cikin wani hali, dama mutum na auren matar da ba 

tasa ba Aliyu? Why not behave like a good Muslims and be happy with Allah’s plan?” Wani murmushi yayi yace “I am not complaining Mumy, am telling you the 

fact, but the thing is that don Allah ki taimaka ki mata magana ta bar min yaron, tayi hakuri ta bar sa gun ma, anytime she wants to see him xa a iya dinga 

kai mata shi, ko kuma yaje ya dinga hutu gunta, I know baxan iya rabata da Dan ta ba, but I just want to save him some humiliations, har duniya ta nade a 

gidan nan babu mai masa gori, babu mai masa kallon a child gotten out of wedlock, sannan babu mai takura masa, in da tayi aure fa, ko xai samu abubuwan da 

nayi mentioning a nan wllh it won’t be 100% don haka plss Mumy ki nusar da ita ta bar sa gidan nan” Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali ta kasa cewa 

komai. Duk yanda Mumy ta so fadi ma khadijah sakon Aliyu da taje gidan kasawa tayi saboda kunya, she don’t even know where to start from, haka ta koma gida 

daga karshe, da Aliyu ya bukaci feedback din khadijah, ta kwantar da murya tace “Abuturrab ka bari kawai bayan bikin, it will look as if we are not happy 

with her marriage, xa a ga kamar mun so kan mu da yawa, kaga bayan biki sai ayi masu bayani, Ina ga xai fi” yace “Toh shkkn mum, nagode” tace “Hope ka ci 

abinci” yace “Sure mum” daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo cike da tausayinsa har ya fita, she know he is just trying his best to be okay, 

Kuma taji dadin yanda yake harkokinsa duk da kana ganinsa kasan akwai damuwa sosai tattare da shi, addu’a tayi masa na cewar Allah ya fiddo masa da mace 

soon shi ma yayi auren nan. Ana gobe daurin aure aka xo har gida aka ma Khadijah gyaran gashi da lalle, all this while baby da kawayenta na tare da ita, 

Yanxu kam shirun nata ya fara isan Umma ga rashin cin abinci duk tayi mugun rama, Khadijah na son sanin ko Khaleel ya koma ko bai koma ba amma bata san ta 

ya ba, har lkcn maganar sa na karshe ya tsaya mata, Wai xai mata abinda xai sa ta farin ciki na har abada to meye wannan bayan xuwa gobe tana gidan Sudais, 

she will like talking to him before tomorrow amma ta kasa kiransa duk da ta ma kashe wayar kar Sudais ya kirata, a haka ta kwanta ranan cike da tunaninsa, 

tun daga ranan da ta fara ganinsa har xuwa yanxu, tayi wani murmushi ta gyara kwanciyar ta ta lumshe ido tana fatan bacci ya dauketa ko xata samu saukin 

ciwon kan da take ji.  Washegari tun da Sudais ya tashi yake ta kiran layin khadijah a kashe gashi ba shi da number baby, shi kuma baxai iya kiran Umma ba, 

yana xaune gefen gado misalin karfe takwas Jiddah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa tana murmushi tace “Happy married life in Advance 

Aliyu” ya dauke kai daga kallonta bai ce komai ba, wani murmushin ta kuma yi ta juya ta fita dakin, mikewa yayi ya fita parlor jin kamar kanninsa da few 

relatives da suka xo tun shekaranjiya sun fito parlorn, Kamar yanda yayi xata haka ne suna kitchen suna nema ma kansu abinda xa su ci don tun da suka xo ko 

ruwa jiddah bata taba debowa ta kawo masu ba, sai ma idan sun girka ta tafi ta diba ta ci, komawa daki yayi ya kwanta don sai bayan an sauko juma’ah daurin 

auren. Tun da khadijah ta tashi take kukan da bata san dalilinsa ba, baby tayi lallashin har ta gaji, Umma tun da ta tambayeta kukan me take taki bata amsa 

ta fita harkanta, gida ya cika fal da abokan arxikin Umma da yan uwanta da mutan garinsu, Babu Wanda xai ce ba ita ta haifi khadijah ba, yau dai Nanny har 

da yan uwanta a gidan, Mumy ma tun safe ta xo gidan da kawayenta biyu, Hajiyarsu Sadeeq ma da safe ta shigo gidan, da kyar khadijah ta mike ta shirya bayan 

Umma ta mata Jan ido taki ko da shafa kwalli a ido.  Karfe sha biyu wata kawar Umma ta fita bayan gidan kiran Umma, ba a dau lkci ba Umma ta shigo parlorn 

don ce mata tayi wasu baki sun shigo kuma cewa suka yi uwar amarya suke nema, kallon Jiddah da kawayenta su kusan biyar kawai Umma keyi don bata taba 

ganinsu ba, Jiddah na murmushi tace “Ke ce uwar Amaryar Mama” Umma tace “Nice daga Ina haka?” Jiddah tace “Kawayenta ne mu mun taba islamiyya daya mama” Da 

mamaki Umma ke kallonsu don Khadijah bata taba bata labarin tayi kawaye a islamiyya ba, sannan ga wani irin daurin dankwali na ture ka ga fitina da suka yi 

gaba daya, sun cakare cikin ankon super wax gaba daya, ita jiddah irin make up din da tayi sai ka rantse ita ce Amaryar, Umma tayi karfin halin cewa “Toh 

sannun ku da xuwa” Jiddah na murmushi har da ritsinawa tace “Mun gode mama, Toh ina amaryar take” Umma ta sa yar wata kawarta ta kai su dakin da su khadijah 

su ke, yarinyar na gaba suna biye da ita har suka shiga dakin, khadijah na xaune tare da Baby da kawayenta sai jujjuya wainar shinkafar da Mumy ta kawo mata 

ta ci ganin bata ci komai ba tun safe take, Su kuma su baby suna ta make up tunda ita har rantsuwa tayi baxa tayi ba, tun da su jiddah suka shigo Khadijah 

da su baby ke kallonsu, Jiddah na murmushi tana kallon baby tace “Amarya Sannu….” Baby na masu wani kallo ta nuna Khadijah tace “You are mistaken, ga 

amaryar can xaune” daga haka ta dauke kai ta ci gaba da shafa powder dinta don ko kadan ji tayi gaba daya jiddah da kawayen nata basu mata ba, Khadijah dai 

sai kallonsu take ko kiftawa babu, Jiddah ta iso kusa da ita tace “Ke ce Khadijah, Amira, Kuma Ummu Shureim koh?” Khadijah taji gabanta yayi mugun faduwa 

bata dai ce komai ba tana ta kallonta, Jiddah tayi wani dariya tana kallonta da kyau tace “Ke ce ke Shirin shigowa gidan Barrister a matsayin matarsa ta 

biyu Koh?” Khadijah ta hadiya abu da kyar still ta kasa ce mata komai, xuwa lkcn kam ta fara dago wacece ke tsaye gabanta ko tantama babu matar Barrister 

ce, Baby ta mike tace “Ke malama ance maki gidan radio ne nan wannan tambayoyin da kike jefo mata?” Jiddah ta mata wani matsiyacin kallo ta daga mata hannu 

tace “Dakata Hajiya ban yi da ke ba, ki xama yar kallo a nan, ja gefe ki tsaya kawai” daga haka ta mayar da dubanta kan Khadijah tana mata mugun kallo tace 

“Wato tsaurin idon ki yakai har ki rasa wanda xaki makale ma wa ya aure ki sai mijina Barrister Aliyu Sudais?” Tuni hawaye ya kawo idon Khadijah duk jikinta 

yayi sanyi, Jiddah ta fashe da dariya ta juya tana kallon kawayenta tana nuna Khadijah tace “Don Allah wacece xaune nan?” Kamar hadin baki suka ce “karuwa” 

Jiddah tace “Da ta yi me?” A tare suka kara cewa “Cikin shege….” Tuni duk mutanen dake parlor suka yo daki da sauri jin hayaniya a daki, Jiddah na kallon 

Khadijah da kyau tace “Toh don kaza kazan ki in har kin haifi cikin uwar ki da ubanki ki yi kuskuren shigowa gidan Aliyu yau, ke don fitsara ki gama yawan 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button