NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

karuwancin a gidan aiki ki haifi tagwaye sannan daga mijina ya taimake ki sai ki makale masa, daga taimako???? Har yana ikirarin tausayin ki da yake kadai 

yasa xai aure ki ba wani abu ba, kin xata badan uban tausayin da Allah ya xuba masa ba xai ce xai aure ki bayan yasan ke wacece? Toh bari ki ji, babu komai 

naki da ban sani ba, duk sirrin ki na tafin hannuna, babu abinda Aliyu ya boye min game da ke, tunda mijina ne shi din baya komai sai yayi shawara da ni, da 

farko na xata abun arxiki ne bayan ya bani labarin ki na amince ya aure ki don ya rufa ma ke da shegun ki asiri amma kawai daga baya tun baki shigo gidan ba 

na fara ganin canji, wato kin fara shanye min miji sai yanda kika yi da shi daga na amince masa ya aure ki ya rufa maki asiri koh? To wllh kinyi kadan, yau 

xan ga ta yanda xa ayi auren nan da kaxa kaxan ki sai dai ki koma ki ci gaba da karuwancin….” Baby bata san lkcn da ta mike ta cakumota ba ta makure 

ta….. Kan kace me fada ya kauraye tsakanin jiddah, baby, da kawayen jiddah, frnds din baby su ma suka shiga, da kyar mutanen da suka yi mutuwar tsaye 

parlorn suka raba fadan, Khadijah ta hade kai da gwiwa jin numfashinta na sama, ko kwakkwaran motsi ta kasa daga gun da take xaune, Jiddah ba irin xagi, cin 

mutunci da gorin da bata mata ba kawayenta na taya ta, har Umma sai da suka xaga, Baby ma bakinta bai mutu ba, da kyar aka fidda su dakin ana Allah wadaran 

Jiddah, sai a sannan hawaye ya dinga xubo ma baby taji tausayin Khadijah sosai duk jikinta yayi sanyi, Umma kam xaunawa tayi ita ma hawayen na sakko mata ta 

kasa cewa komai, Mumy kanta tsaye tayi ta rasa abin cewa duk jikinta yayi sanyi, Wata kawar Umma ta durkusa ta dago kan Khadijah a hankali cike da 

tausayinta, hawaye ne ke xuba idonta kamar an bude pampo, Baby ta durkusa kusa da ita ita ma hawayen na xubo mata ta rasa abinda xata ce mata, Khadijah ta 

kamo hannunta cikin rawar murya tace “is it my fault that I was raped baby? Is it my fault that I am an orphan, is it my fault that I had kids out of 

wedlock? Dama maraici….” kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai tana girgixa kai a raunane tace “Alhamdulillah for my fate… irin tawa kaddarar kenan 

kuma na amsa hannu bibbiyu, Amma me yasa mutane baxa su yi considering dina ba, ni ban so ma kai na haka ba, Allah ne ya kaddara min, but ya xan yi baby, 

dole in gode masa, ban taba karuwanci ba amma sun ce min karuwa, ban san Sudais baxai iya rike min sirrina ba he betrayed….” Mikewa Baby tayi ta dau wayar 

Khadijah ta fice daga dakin, Ta kunna ta shiga neman layin Sudais, Bata yi wahalan ganin number ba don Barrister tayi masa save as, tana dialing ba a dau 

lkci ba ya dauka cike da damuwa yace “Why did you switch off ur phone Amira…” Baby ta katse sa a xuciyarta na tafarfasa tace “Malam dama ka san baka iya 

rike sirri ba ka nace sai ka auri Khadijah??? dama kai din mijin ta ce ne sai yanda mahaukaciyar jahilar matar ka tayi da kai?” Kasa cewa komai Sudais yyi 

da farko don gaba daya he was lost, can cike da karfin hali yace “Wacece wannan?” A mugun fusace tace “Ba Lallai ka ji wacece ba, wllh ka ci amanar 

Khadijah, ka xalunce ta, and am advicing you ka janye batun auren ta kaje jahilar matar ka ta ishe ka, Kuma sai Allah ya saka mata” tana kai wa nan ta fashe 

da kuka sosai taci gaba “Naga ba ita ta ta xabar ma kanta wannan kaddarar ba har xaka xaunar da warce xa su xauna a matsayin kishiyoyi ka tsara mata komai 

na rayuwarta daga farko har karshe ta xo har gidan biki ta mata tonan silili ta gaya mata son ranta, tayi mata cin mutunci da cin fuska, tayi mata gori” 

katse wayar Sudais yyi kansa na juya masa ya mike daga xaunen da yake ya fito parlor, ya kusa minti sha biyar tsaye sai ga jiddah da kawayenta sun shigo 

parlorn, ya taka har gabanta ya sauke mata tagwayen mari, yana kallonta da jajayen idanuwansa yace “Na sake ki saki daya jiddah”

A hankali Khadijah ta bude idanuwanta ta sauke kan Khaleel dake xaune gefenta Aliyu na tsaye daga gefensa, Umma ta taho gunta da sauri ganin xata mike xaune 

ta riketa da damuwa tace “Sannu Khadijah, how are you feeling now?” Kirjinta kawai ta nuna ma Umma hawaye na xubo mata, Umma tayi kasa da murya a sanyaye 

tace “Xai daina in sha Allah, be strong daughter” Baby dake tsaye gefe daya ta karaso ta xauna kusa da ita tana kallonta ta kamo hannunta, rasa abinda xata 

ce mata tayi, lkci daya ita ma hawaye ya kawo idonta, Khaleel ya mike ya fita ward din sai gashi sun dawo tare da likita, Juyawa Aliyu yayi ya fita, likitan 

ya gama dubata suka fita tare da Khaleel xuwa office din sa. A sanyaye Umma tace “Kin dai ji abinda likitan ya ce maki, Kar ki sake kukan nan don Allah 

saboda lalurar ki” Khadijah bata ce komai ba ta kai hannu tana share hawayen idonta, bude kofar ward din aka yi Sudais ya shigo, tsaye yayi nan bakin kofar 

yana kallonta, A hankali Umma ta dauke kai kanta daga kallon da take masa, Baby ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Tun da Khadijah ta kallesa sau daya 

bata sake yarda ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, ya iso har kusa da ita, da kyar yayi gathering courage yace “Amira….” ta fashe da kuka sosai tace 

“Am begging you ka rabu da ni pls Aliyu ka tafi, My heart is aching at the sight of you, kayi hakuri ka wuce… let me rest plssss” cikin matsanancin kuka 

ta kare maganar, Yana mata wani kallo yace “Amma in har maganganun da Jiddah ta fadi maki sun yi tasiri xuciyar ki ba ki min adalci ba Amira, for good two 

years na boye ma mahaifiyata na ajiye ki gidana ko da kuskure ban taba sanar da ita ba ban taba tona maki asiri ba, hatta frnds dina ban da Yusuf babu wanda 

yasan labarin ki, sai a yanxu kike tunanin xan fallasa sirrinki, Kuma in rasa warce xan fada ma sai matata da ko kadan ba dadin xama da ita nake ba, am I 

that daftt??” Ya girgixa kai cikin bacin rai yace “I never expect such from you Amira, I thought ke me fadi ma wasu cewar makirci ta xo tayi displaying 

gidan ku….but I was mistaken” kasa ci gaba yyi ya juya ya fice daga ward din, Khadijah ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar an aikota, Baby dai ta kasa 

cewa komai duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon baby tace “Hope kin ji maganata ya fito ko, Ni nasan makirci ne kawai na 

mace, I know baxai taba yin haka ba, baxai xaunar da ita yayi mata tsarin da ta xo tayi ba, she set him up kawai saboda kishi….” Umma na magana tana goge 

hawayen dake xuba idonta, ta ji tausayin Sudais sosai, “Khadijah idan kika ce kin fasa aurensa kamar yanda kika yi ikirari before passing out kin yi 

butulci, baki kyauta masa ba, Kuma kin nuna ta ci nasara kenan matar tasa” Khadijah ta dago cikin kuka tace “Wayyo Umma kashe ni xata yi a gidan, baxan iya 

auren mata miji ba ni dai, ku rufa min asiri, Umma kin ji yanda xuciyata ke min ciwo, na hakura da auren gaba daya I prefer dying a spinster” Rungume ta 

Umma tayi tace “Ba abinda xa a fasa daughter, kuma tayi kadan ta kashe ki, we will prove her wrong, ta xo tayi masa sharri duk don kice kin fasa to xa a 

nuna mata iyakarta in sha Allah sai kin aure sa, sai in Allah yayi shi din ba mijin ki bane dama, Amma babu abinda xa a fasa” Tun da Sudais ya fita ward din 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button