NOOR ALHAYAT 81-90

I found out to be nothing but the truth, Aliyu shi ne kadai rufin asirin khadijah da yaron nan, toh amma ba lallai ta gane hakan ba, ban san ta ina xan fara
sanar mata ba” Baby ta sauke ajiyar xuciya, lkci daya jikinta yyi sanyi tace “Umma kar a gaya mata, she shud just see for her self, xasu sasanta kansu can
din” Umma tace “I thought as much… Haka yawanci kowa ke ce min” Tagumi baby tayi ta rasa wanne xata yi a ciki, farin ciki ko bakin ciki, Umma tace “Tashi
ki je ku gama shiryawa lkci na wucewa khadijah, har an gama kai kaya can gidan” Baby ta mike jiki ba kwari ta fita, tana komawa daki ta ci gaba da shirya ma
khadijah few abubuwan da tace mata, Shureim ne ya shigo dakin da shadda irin wanda Sudais yasa ranan da hularsa, sai sheki kayan suke sun masa kyau sosai,
tun wayewar gari sai sannan khadijah ta gansa, ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa a hankali tace “Where have you being today?” ya wara mata ido yace
“Uncle ne ya tafi dani since, mun dawo yanxu, Anty daxu Umma tace min baki da lafiya, me ya same ki” Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin yanda yake kallonta
ta rungumosa a hankali tace “Ae na samu lafiya yanxu” yace “Anty kinyi kyau sosai” Murmushi tayi ta ja hancin sa tace “Kai ma kayi kyau sosai, wa ya kawo
maka kayan nan” Yace “Uncle, shi ma ya sa irin nawa, na tambayesa Ina na Sudais yace ya ajiye masa nasa” Shiru khadijah tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta
yace “Anty what are they celebrating today?” Baby dake gefe sai kallonsu take ta dauke kanta a hankali, sai a sannan tayi mugun ganin dacewar abinda
Barrister Sudais yyi, shkkn sai su hadu su rungumi d’an su, khadijah ta sunkuyar da kanta tuna irin xagin da Jiddah tayi ma yaron daxu ta kirasa da shege
mara uba, hawaye ne ya kawo idonta sai dai bata bari ya gani ba, Jikin baby yayi sanyi don duk tana lura da ita, ta juya ta ci gaba da abinda take, Shureim
ya taho gunta yana gaisheta, ta rungume sa murmushi dauke fuskarta tace “Har kun dawo boy” ya gyada mata kai, shidda saura motocin tafiya da amarya suka iso
gidan, nasiha sosai Mum din sadeeq da wata frnd din Umma suka yi mata, Kanta a kasa take saurarensu hawaye na sakko mata, ita kam bata samu gatar nasihar
Uba ba, kalma daya Umma ta iya yi mata a lokacin bayan su Umman sadeeq sun gama “Allah maki albarka” hakan yasa khadijah taji dadi sosai, Shaheedah ta daga
ta suka nufi kofa baby da wata kawarta na biye da su a baya, banda kuka babu abinda khadijah take duk jikinta yayi sanyi, duk aka bi ta da kallo cike da
tausayinta, Baby da frnd dinta Hafsat sai mahaifiyar Shaheedah wato aminiyar Umma suka shiga mota daya da khadijah, sauran yan rakiyar Amarya suka shiga
sauran motocin, Jikin baby bai gama sanyi ba sai da taga sun iso gidan yayanta, duk tausayin khadijah ya cikata a xuciyarta ta dinga addu’ar Allah yasa
shock din ganin Aliyu as mijinta baxai yi affecting dinta sosai ba, dad’d’adan kamshin turaren wuta ke tashi ta ko wani angle a gidan, ga sanyin ac, parlorn
so chill, har lkcn kuma su Siyama da kawayensu da frnd din Mumy suna gidan suna jiran Amarya, Su Hajiya Sajeedah suka wuce da khadijah well furnished
bedroom dinta, ita dai har sannan fuskarta a rufe yake bata san kalan gidan ba gashi tun shigowar su gabanta ke faduwa ga hawaye ya ki tsaya mata duk
jikinta yayi sanyi, ana xaunar da ita gefen gado ta riko baby cikin rawar murya tace “Stay beside me plss don’t leave me” a sanyaye baby ta xauna kusa da
ita tana rike da hannunta, khadijah ta rike ta gam ta kwanta jikinta. Sai kusan bayan isha duk aka watse gidan har su Siyama suka wuce, sai da su Hajiya
Sajeedah suka kara mata nasiha kan xamantakewar aure kafin su wuce su ma, gidan ya rage daga ita sai baby da Hafsat, kuka kawai khadijah take don tana ganin
ko wani lkci jiddah xata iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d’an murmushi
tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru
ya d’an yi kafin yace “Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu” Tace “Toh” kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace “Waye ya kira
ki?” Baby ta sauke idonta tace “Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya” khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku, me
yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana” dariya ta ba baby amma bata yi ba tace “Gobe fa da safe xan xo Iman” cikin kuka
sosai Khadijah tace “Don Allah ki rufa min asiri ki kwana” Baby tace “In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika
ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya…” Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike
ta hade rai tace “Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya” Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na
biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta
yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace
“Ina yini yayanmu” yace “Lafiya lau” Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata
komai ba, Sudais yace “Alryt, sai da safe Dr” Aliyu ya kallesa a hankali yace “Baxa ka shiga ba?” Ya bude motarsa yana d’an murmushi yace “Gobe xan xo in
sha Allah” Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace “Ku shiga xai yi dropping din ku gida” Ta d’an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da
damuwa yace “Did she know….” Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby
yace “Don’t keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe” A hankali baby tace “Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya
I never knew makirci matarsa ta hada masa” Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace “Ki basa hakuri idan kin shiga motar” shiru
tayi, ya gyada mata kai yace “Yea, do that” a hankali tace “Toh sai da safe yayanmu” daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu
ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace “Good evening” sai a sannan ta kallesa
dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace “Ina yini” yace “Lafiya lau” a hankali tace “Am soo sorry for what I did daxu da safe
don Allah kayi hakuri” kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace “Wai dama ke kika kirani?” xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi
bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace “I bet da muna kusa har duka sai kin kai min” sauke kanta kasa tayi
bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar