NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 2) 1&2

     *_RAINA KAMA……_*
              _{Kaga gayya}_
               
      
             *_Bilyn Abdull Ce_*

~Book 2~ ????????1
    ………….Tunda mukayi maganar nan dashi banyi k’asa a gyuwa ba wajen dagewa da addu’oi wa mahaifinsa, ina buk’atar ruwan zam-zam, dan haka yau nashirya fad’a masa ya nemomin. tunda

safe ya fice, dan haka bamuga juna ba.

      Yauma dai haka Na tashi banida wata isashshiyar lafiya, Na tak’ark’ara nayi gyaran d’akin har zuwa falo, sannan Na had’a ruwa mai zafi nayi wanka dashi.
      Ina cikin shiri najiyo sallamar Samha a k’ofar falon, rigar dana fara sakawa Na k’arasa, sannan nace ta shigo.
        “humm Aunty gimbiya kina kallon kanki a mirror kuwa?”.
     Cikeda mamaki Na kalleta sannan Na kalli jikina, nace, “kamarya?”.
       Zama tayi a sofa tana ‘yar dariya, sannan tace, “wlhy kinyi k’iba, sati uku kacal da zuwanmu India kin koma wata madam”.
      Nad’an fiddo idanu waje, sannan Na harareta, “lallai Samha nagode da zagi to”.
       “tab wlhy babu wani zagi gaskiya Na fad’a, halan Uncle Sam bai ta6a fad’a mi ki ba……..”
     Ta k’arasa Maganarta da d’ai-d’ai saboda shigowarasa d’akin da sallama ciki-ciki.
        Suna had’a idanu ya watsa mata harara, hakan ya tabbatar mana da yaji maganar tata, da sauri tamik’e ta fita, Nikuma najawo gyalena na yafa sannan Na kallesa.
       Saman sofar ya zauna ya dafe kai, kallo d’aya zaka masa ka karanci damuwar dake shimfid’e bisa fuskarsa.
        “yalla6ai lafiya kuwa?”. ‘nafad’a cikin tausayawa’.
      Shiru bai amsaniba, banyi zuciyaba nataka a hankali zuwa gabansa, durk’usawa nayi a gaban nasa, a d’arare nasa hannu Na najanye nasa dayay tagumi dashi.
     Ya d’ago idanunsa da sukai jaa yana kallona. kasa jurar kallon cikin idonsa nayi, Na janye nawa gefe, cikin dakiyar zuciya nakuma fad’in “bakada lafiya yalla6ai?”.
      Yanda nayi maganar a marairaice saiyaji yakamata ya fad’amin, kodan nuna damuwar danayi akansa……
       Ganin yamin shiru nikuma saina yink’ura natashi ina fad’in “kayi hak’uri idan nashiga hurumin daba nawab……”
       Bankai k’arshen maganarba naji tattausan tafin hannunsa cikin nawa.
     Rintse idanuna nayi, saboda wani yarrr da tsigar jikina tayi, shima agaresa saiya lumshe idanu kawai. najuyo danufin zare hannun kawai ya fisgoni na fad’a saman kujerar, rabin jikinna duk yana a jikinsa, yayinda sauran rabin nake a kan kujera.
     Bansan nawani lumshe idanuba saboda daddad’an k’amshin turarensa d’aya ratsa hancina zuwa magudanar jinina. shikuma ya sauk’e 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
      Ya karkato da fuskarsa inda tawa take a gefen kafad’arsa har inajin saukar numfashinsa saman face d’ina, mayun idanun nan nasa suka kuma shiga cikin nawa, na janye da sauri, sannan nafara k’ok’arin cire kannawa daga kafad’arsa.
   Hannunsa na dama da nake jiki ya sak’alo ta bayana, ya maida kai na ya kwantar a kafad’ar tasa, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa tilas yace, “jikin Abie ne ya motsa, Ashe tun jiya basuyi barciba gaba d’aya, da safennan Akash yakirani yake sanarmin, nakasa kallon halin da mahaifina yake ciki Munaaya! Abie na yana cikin mawuyacin hali..” ‘yak’are maganar cikin zirarowar kwallar data cika masa idanu tunda yafara maganar’.
       Wani matsanancin tausayinsa ne ya ratsani, duk jarumtar Galadima kaga yana kuka ai kasan lamari ya 6aci gaskiya, nima hawayen suka fara gudun fanfalak’e a kumatuna, tashi nayi zaune sosai, cikin wata jarumtar da bansan inada itaba nasaka hannu Na kamo hannunsa cikin nawa. Sai kawai naga ya zame sosai ya kwantar da Kansa bisa cinyata, tareda hard’e hannayensa  a k’irji. duk da kujerar tama tsawonsa kad’an, dan ma Love’s chair ce.
        Kansa nafara shafawa a hankali, hawaye na zirara daga idona har yanzun.
       Shikam idanunsa a lumshe suke.
     Cikin tausasa harshe da tsantsar Nuna kulawa da tausayawa nace, “Yalla6ai kayi hak’uri, Abie d’inmu yana buk’ar addu’armu ne fiye da kukanmu, sannan itace jarabawarsa, wad’anda suka aikata masa hakan summa kansune, domin ALLAH bazai barsuba. idan ka amince akwai wasu addu’oi Dana Sani, Nina kakanmu ne yabama innarmu kafin yarasu, shine ta koya mana, mizai hana ka samo mana zam-zam muma mu farayima Abie su, Ubangiji gafurun rahimunne, babu abinda ya gagaresa, kuma shine yace mu rok’esa zai amsa mana”.
         Tunda nafara maganar bai bud’e idonsa ba, nikuma ban fasa shafa masa kaiba. Saida nakai k’arshen zancen sannan ya bud’e lumsassun idanunsa dasuka koma launin jaa a kaina. yamotsa baki kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru.
    Nima shirun nayi ban sake yink’urin yin magana ba, nadai cigaba da shafa kan nasa a hankali. ba akai 3minutes ba barci ya d’aukesa, sai numfashinsa danaji yakoma sauka a hankali.
    Ajiyar zuciya na sauke kawai, na tsurama fuskarsa ido, yaune ranar farko dana ta6a nutsuwa namasa kallon tsaff, sosai yake kamanni da dukkan iyayensa, Abie da Momma, amma yafi tsananin kama da Momma gsky, duniyar tunani nafad’a batare dana fargaba, tausayin Galadima da families nashi yana cukurkud’ar ruhina, insha ALLAH nayi alk’awarin bada gudun mawa a duniyarsu har zuwa lokacin da aurenmu zai k’are.
       kaina na jingina da jikin kujera, nima sai barcin ya kwasheni, dama bajin dad’in jikina nakeyiba.
********
         Bayan anma Abie allurar datake temaka masa yin barci mai nauyi idan jikinsa yamotsa irin haka su Momma suka sami nutsuwa, dan yayi barci.
     Sai alokacin hankalin Momma yadawo kan Neman Galadima, tabbas taga yafita hankali a tashe lokacin da Abie ke fidda numfashi a wahale, amma hankalinta bai koma kan  Galadiman ba.
       Aunty Mimi ta kalla tace, “Mimi ina d’an uwanki?”.
     Itama aunty Mimi sai yanzu hankalinta yadawo ta farga babu Galadima d’in, hankalinta a tashe tace, “Momma inagafa ya fita, bara na duba”.
    Bata jira cewar Momma ba tafito daga d’akin da sauri. ganin babu Galadima a wajen hankalinta yak’ara tashi, fitowa tayi harabar asibitin tana tambayar securitys d’in wajen.
    d’aya ya sanar mata ya fita a rikice gaskiya, dan suma sun nemi su taimaka masa amma baima tanka musuba.
   Innalillahi tashiga ambata. Bata koma wajen Momma ba tashiga mota tanufo gidan.
     Ta iske Samha a falo kwance, ko sauraren sannun datake mata batayiba tace, “k ina Uncle d’inku?”.
     Samha tace, “yana sama Mummy”.
     Da sassarfa ta haye step’s d’in, itadai Samha da mamaki taringa binta da kallo.
       Ko knocking bata tsaya musuba ta turo k’ofar ta shigo.
      Ajiyar zuciya ta sauke dan ganin Galadima kwance, kansa bisa cinyar Munaya, hannunta d’aya na bisa Kansa, yayinda shikuma yarik’o d’ayan hannun munaya ya had’e da nasa ya d’ora kan kirjinsa, suduka barci ya kwashesu a haka. cikin sand’a ta juya ta fita taja musu k’ofar tana share hawaye dayima ALLAH godiya d’aya bama d’an uwanta mace tagari wadda take kulawa dashi. inda dane kafin yayi aure shima sai ciwonsa yatashi saboda damuwar dazai saka Kansa akan motsawar jikin Abie, amma gashi yanzun yasamu mai kwantar masa da hankali, suma kuma nasu ya kwanta suji da Abie kawai.
      Momma ta kira ta fad’amawa dan hankalinta itama ya kwanta.
     Momma harda hawayen farinciki, tana godema ALLAH.
     Aunty Mimi bata zaunaba suka koma asibitin itada Samha da tace zata bita, itama sai yanzu takejin jikin Abie ya motsa.
*************
     A k’alla munyi barcin 47minute’s, Galadima ne yafara farkawa, ya bud’e idanunsa a hankali, hannuna dake rik’e a nasa yafara kallo, kafin yad’ago ido zuwa kaina, yamin kallo kusan na 2minutes sannan yad’an motsa da nufin gyara kwanciya, saina bud’e idona, ido muka had’a, kowa yay saurin janyewa cikin basarwa, hannuna dake kansa na cire, sannan nazame Wanda yarik’e d’in, dan wata matsananciyar kunya ce kuma takamani.
    Shima sai ya tashi zaune sosai, a hankali yacemin “thanks”.
      Daba kusa dashi nakeba ma bazanjiba. Bance komaiba, shima bai sake cewa komaiba yamik’e tsaye. takalmansa kawai yacire ya d’auki jallabiya a wardrobe d’insa yashige bayi.
      A hankali na sauke ajiyar zuciya, tareda janye idona daga k’ofar bayin, komai banceba nakuma zamewa saman kujerar na kwanta.
       Ya d’auki adadin wasu mintuna masu tsawo kafin yafito sanye da jallabiya ruwan toka, da alama wanka yayi, kallona yayi batareda yayi magana ba ya nunamin agogon dake ajiye a drowan gefen gadon alamar time d’in salla yayi.
     Kaina kawai na girgiza na mik’e, zuciya ta na mamakin hali irinna Galadima.
       Shikam turare kawai ya d’auka ya fesa yafice salla.
★★★  (())(())(())  ★★★
               A gidanmu kam hankalin mamansu yaa hameed da Zarah a tashe yake, dan babu Sa’eed babu labarinsa, kira Zarah tamasa yafi 50 amma yak’i d’agawa, ta tura massages babu reply, bata aikin komai sai kuka, ga ciki.
        Abbanmu kuma jin sanadin sawowar tata gida yace bazai kira Alhaji halliru ba har sai Zarah tafad’i ainahin gaskiya, danshi bai yarda ba itace ta d’auki kud’inba..
     Innarmu dai dasuke zagi suna kallonta mak’iyarsu batakai komaiba itace tashiga lalla6a Abba damasa magiya.
    Itama da farko buris yay da ita, saida yaga tanace sannan yace, “wai kekam Ai’sha miyasa kika damu kankine? kinbi kin damu da lamarin wad’anda basu damu dakeba, na tabbatar da Munaya ko Munubiya ke cikin wannan halin su murna zasuyi a gidannan”.
    Murmushi innarmu tayi, cikin kwantar da murya tace, “Alhaji ai daga Zarah harsu munubiya duk d’ayane a wajena, domin kaine mahaifin Zarah, dukkan abinda kuma yakasance naka ina kaunarsa fiye da zatonka, a duba lamarin yarinyar kodan abinda ke gabanta, ba’a son mace mai ciki da shiga tashin hankali, muyima tufk’ar hanci tun munada sauran dama, basai Abu yayi tsamariba kuma muce zamu nemo mafita, hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar alhaji, dan ALLAH kayi hak’uri kaji”.
         Jawota yayi jikinsa ya rungume yanamai saka mata albarka da aminta da buk’atarta na kiran senator halluru da safe insha ALLAH.
      Innarmu tamasa godiya itama.
**********
       “Babyna wai mike faruwane haka?”.
      Da gyar Munubiya ta d’ago ido daga kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar.
    Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne babu dad’i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”.
    Zama yay kusada ita, yad’ago kanta ya jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki mana?”.
       “a’a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa, kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d’in”.
        “Amma kuma k’ya zauna da ciwo, ki daure dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”.
       “babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na d’ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”.
      “Ana dai so aima Yaya wayo kawai”.
     Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,, takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon.
       Binta kawai yay da kallo yana murmushi, yana k’aunar matarsa kuma ‘Yar uwarsa, gaba d’aya Munubiya ta canjashi, dukda bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa, komai a d’auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da kawalwalniya a zuciyarsa.
     Mik’ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen d’in danya taimaka mata da aikin, dan yau d’in weekend ne baije aikiba. dan yayi resume tun last week.
(())*(())*(())*(())
            Tunda na idar da sallar nazame a wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad’i, jinake kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d’ago ido na kallesa, sannan na amsa ciki-ciki nima.
        Frigate ya bud’e ya d’auki ruwa yakoma saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad’a, saida ya shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na k’ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad’ago muka had’a idanu sannan nayi saurin yin k’asa da nawa.
      Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi muje hospital d’in, daga nan saimu samo zam-zam d’in”.
     Tunkan yakai k’arshen maganarma na mik’e tsaye, hijjab kawai nasaka nad’an gyara fuskata, shikuma ya d’auki kaya yashiga bayi ya canjo sannan muka fice.
      Jin gidan shiru yasashi d’aukar waya yakira sashen bayin gidan, babu dad’ewa saiga d’aya acikinsu tazo.
    Zubewa tayi tana gaishemu, ya d’aga mata hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”.
        “Ranka ya dad’e sunfita suda mummy”.
       Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi abaya.
     Sai da yasakama k’ofar security sannan muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d’aga musu muka shiga motar, suka bud’e mana gate d’in muka fice.
      Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk’insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d’in, tunda ba English baneba gaskiya.
       Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.
          Abinda ya kaimu muka shigayi, yad’ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad’in “saikuma mi?”?
     Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk’ara?, zuwa can nad’an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d’akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d’auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.
       Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.
     Mun k’arasa wajen biyan kud’i, bayan yabiya yaran shagon d’aya ya d’aukar mana zuwa mota.
     Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad’in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu’oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.
       Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d’in cikin k’oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal.
       Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.
     Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho.
    Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk’atar Abie ya kwana tare da ma’aikatansu.
          Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.
     A kunyace na mik’e domin cika umarninta.
     Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d’aura zani nasaka hijjab tareda d’aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa.
          Bai dad’eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.
      Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k’afafunsa na k’asa, ya tsurama rufin d’akin idanu alamar yatafi duniyar tunani.
        Nikam ruwa mai zafi na had’a nashiga koda zanji dad’in jikina, na dad’e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k’ofar bayin, Amma babuni babu dalilina.
      Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k’ofar cikeda basarwa.
   Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d’auki zani na d’ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa’i da wutiri, bayan na idar nad’akko roban zam-zam d’in d’aya na zauna nafara karatu Qur’an acikin ruwan zam-zam d’in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.
        Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik’ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa’i da witiri yay joining d’ina muka cigaba da karatun a tare.
   Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).
____((()))((*((()))*))((()))____
           
            Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d’aya xaka mata kagane abirkice take.
    Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d’in dad’i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d’inne.
        Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad’anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.
     Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa’eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.
      Hak’uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa’eed d’in zaizo ya d’auki matarsa.
      Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d’an uwansa hak’uri akan lamarin.
    Innarmu bata buk’atar jin k’arin bayani dantaji komai, takumaji dad’i sosai.
()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()
           Jikin Abie dai kam yayi tsanani a tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu’a, dan baisanma Wanda yake a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul’fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d’aukar kowa nasu, duk da d’ar-d’ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni, mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k’arema uwarsa tanadiba, ba kamarma mu ‘yan d’akinmu.
       hakama sarki jalalludden shida uwargidansa sunzo da mama Fulani.
     Ranar momma har tausayi tabani, kai mama Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid’a mulki a asibitin nan. Hummm????????.
     Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana ya dage ya ya6a mata bak’a shikuma.
      Ba gidan suka saukaba, a hotel suka sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.
        Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.
     Nima k’asa na durk’usa na gaidasu su dukansu har Momma da aunty Mimi.
        Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k’urillar da Mama Fulani kemin duk sai na takura.
       Tad’an ta6e baki sannan ta gyara zama idonta na kaina, tace “toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana? daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india”.
     Gaba nane yafad’i, dan nafahimci dani take, saina rasa amsar dazan bata..  
     ‘Yan d’akin kam kowa ido ya zuba ma mama Fulani har Galadima.
     Aunty Mimi ce tace, “Ranki yadad’e Kodai kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki?”.
        Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali, taji dad’in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad’an batason abinda zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a cikinsu………
       Wani munafukin murmushi mama Fulani tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga sama sukaji tace, “cikin namu wata nawane Galadima?”…………????
E me???????? mama Fulani mai gani har hanji????????.
*_ALLAH ya gafarta na iyayrnmu????????????_*
*_Typing????_*
    *_Haske writer’s asso…._*????
      
     *_RAINA KAMA……_*
              _{Kaga gayya}_
             *_Bilyn Abdull Ce_*????????
  ~Book 2~ ????????2
…………..Shiru Galadima ya mata,  da ace babu Momma daya ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.
     Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa kallona duk sukayi, nayi k’asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen tsohuwarnan yana son tsoratani.
        Shigowar Sarki Abdul’fatah (papi) da inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak’aita zancen. dan daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima, yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.
_____________________________
         Misalin 8:pm saiga Sa’eed yazo gidanmu, a time d’in gwaggon Haleematu da mamansu yaa Hameed suna ta hayaniyar fad’a, wai mamansu yaa Hameed ce takama gwaggon Haleematu tana kallon Zarah dake alwala a fanfo tana dariya.
    Shinefa mamansu yaa Hameed tace gwaggon Haleematu taci kanta tasha bak’in ruwa, karta lashe mata jika tun yana a ciki.
     Wannan kalma ta mamansu yaa Hameed itace tajawo fad’a, Dan gwaggon Haleematu tace mamansu yaa Hameed tace mata mayya bazata yardaba. Fad’a sosai sukeyi suna cin zarafin juna da gori, dama kowa kishi Na cinta a zuciya.
      Matan gidanmu duk sunyo waje anrasa masu dakatar dasu sai innarmu dake cewa suyi hak’uri Dan ALLAH, darene fa.
    Amma Sam sunk’i saurarenta.
      Innaro dataji hayaniyar tundaga gidanta yasata d’akko fayafi tafito, kamar anjehota haka tashigo gidan.
     Sa’eed da Sulaiman suna awaje a mota, duk badak’alar da akeyi daga cikin gidanmu suna jiyowa, har shigar innaro kuwa suna kallo. Dayake su Abbanmu suna masallaci.
      Innaro tanata magana sunk’i saurarenta, saiyi sukema kamar zasu fara danbe.
       Mamansu yaa Hameed Na k’ok’arin kwalama gwaggon Haleematu ludayin miya dake hannunta innaro takawo jiki zata kare sai a goshinta, jikake kwarrrr!.
     Tako dafe goshi tafasa k’ara..   
     Hakan kuma yay dai-dai da shigowar su Abba gidan, su duka ukun, tunkan sushigo sukejiyo hayaniyar dama, dukansu rai a 6ace suka shigo. Dan iskancin matan nasu ya ishesu hakanan, idonsu yarufe ko ganin motar su Sa’eed basuyiba.
        Ran Abba yakuma 6aci, Dan ganin duk matansa ne ma masu hayaniyar, ga abinda sukaima mahaifiyarsa akan idonsa. batareda yabi ba’asiba yace duk sufice su bar masa gida.
      Ananne kowa yay tsitt, yadaka musu tsawa yana fad’in wlhy idan basu fitaba zaisa a fiddasu, ko d’akunansu bai yarda wata takomaba kuma.
        Dole sai ‘ya’yansu suka d’akko musu hijjabai suna kuka da bama Abban hak’uri.
     Amma yak’i sauraren kowa, daddy da baba k’arami kuwa babu Wanda yay yunk’urin hanashi.
    Innarmu tamatsa kusadashi tana rok’onsa karyayi haka, yazauna ya sauraresu tukunna, Hararar daya zuba matace yasata jada baya tai 6am da bakinta.
        Innaro kuwa maman safara’u ce takamata ta zaunar, goshi harya fara kumbura????????.
                           
                     (((+)))***(((+)))***(((+)))
      Kafin mu baro asibitin nama manta da maganar mama Fulani, saboda murnar bud’e ido da Abie yayi ta d’aukema kowa hankali kuma, gaskiya ina tausayin bawan ALLAHn nan sosai.
     yauma bamuyi k’asa a guywa ba wajen cigaba da addu’oin damukeyi cikin zam-zam ni da Galadima, somuke muyi na 1week sannan afara bashi.
      Washe gari Alhmdllh jikin Abie yayi k’yau sosai, Dan inka gaidashi yakan maka murmushin sa Na dattako, hakan ya sanya su papi sukayi shirin tafiya da yamma.
      Ni da Galadima da Sauban muka musu rakkiya, sainaji tamkar nabisu. Harda ‘yar kwallata kuwa. Inno tanata tsokanata, Dan tsohuwar tashiga raina sosai.
        Tunda muka d’akko hanyar dawowa asibitin nakife kaina a cinya inata hawaye, sauban ne kawai ke tsokanata, amma Galadima tamkarma baya cikin motar. hakan saiya k’ara tunzura zuciyata, nakuma k’ara k’arfin kukan nawa.
     Sauban yasamu guri yay parking, da hannu Galadima yamasa alamar yaje.
     Fita yay yana k’uk’uni da k’umshe dariya, wai “su boss za’ayi lallashi shine aka koroni”. Saida yay nisa da motar sannan yasami damar dariyar, har yashiga wajensu Momma.
     Daga Momma har Aunty Mimi kalli
onsa sukeyi,, aunty Mimi tace, “Auta lafiyarka kuwa?”.
     Saida ya zauna sannan yashiga kora musu bayani, dariya kawai sukayi, sunsan Sauban babu sauk’i wajen taso mutum agaba.
         Tunda Sauban ya fita sai Galadima ya gyara zamansa kawai ya zubamin ido, mutum ne shi dabaya son shiga hak’in wani, ko kad’an baiso ace wane yana cikin damuwa ta dalilinsa……
      Wayarsa aka kira, ya kalli wayar kafin yakai hannu ya d’auka, salamar da akayi daga can ya amsa suka gaisa.
        Jin ya ambaci Nuren nagane da Wanda suka ta6a yin waya kwanakine, nad’an tsagaita da kukan ina sauraren mizasu tattauna. Galadima naji yace,
        “miya farune kakeson nazo Nigeria haka da gaggawa Nuren”.
       “no babu wani damuwa, driver da yarinyar nanfa suna hannu, so yakamata ka shigo muyi abinda yadace ko?”.
       “ok babu damuwa, insha ALLAH zuwa Wednesday idan jikin Abie ya kuma lafawa zan shigo”.
        “O right, ALLAH ya k’ara masa lafiya, a gaishesu”.
     “zasuji insha ALLAH, bye”.
      Wayar ya ajiye a tsakkiyarmu ya maida hankalinsa kaina.
    
     Cikin wani salo yace, “Munaaya!”.
        Wani Yarr naji a jikina, karo na biyu kenan danaji sunana a bakinsa, sainaji sunan nawa ya canja kamar ba shiba, danya iya sarrafa sunan a harshensa….. ganin ban d’agoba yakuma kiran sunan.
    Kasa jurewa nayi nad’ago idona na kallesa, ganin ya tsareni da idanu saina janye nawa. yad’an lumshe nasa ya bud’e a kaina ya furzar da huci “kina ganin haka abokai yakamata su kasance? ni friend nakine, miyasa bazaki iya fad’amin damuwarki ba? kiyi hak’uri nasan kina buk’atar zuwa gida, last week naso maidaki Nigeria, amma sai jikin Abie Daya motsa ya dakatar dani”.
       Tausayi yabani, nad’ago na kallesa, mutumne shi mai sauk’in kai, saidai idan baka fahimceshi ba zaka sameshi a amurd’e, domin yanada wahalar sha’ani, hawayen dasuka ziraromin na goge, muryata na rasa nace, “kayi hak’uri ina kewar su Munubiya ne, insha ALLAH bazan sake yin kukanba amma”.
       Murmushi yaymin yana jinjina kai, yad’an shafa girarsa zuwa kai sannan yace, “kinada tsiwa, amma wani time d’in kinada kirki”.
      Bansan lokaci da dariya tazominba, nad’an dara sannan nace kaima ai hakan kake, kanada tsauri kanada sauk’i”.
    Yawani k’ank’ance idanu cikin wani salon kallon yace, “really?”.
      Gira d’aya na d’aga masa nima nace, “yaah”.
     Murmushi mai k’ayatarwa yayi yakwashi wayoyinsa yabud’e motar yafita batare data sake cewa komaiba.
    Ganin haka nima saina fito fuskata washe da murmushi, kamar banice nagama kukan shagwa6a ba????.
           Tunda muka shigo aunty Mimi da Momma suka zubo mana ido, Sauban kam dariyar shak’iyanci yafara k’asa-k’asa.
    Momma tace, “ina kuka mak’ale haka?”.
       Murmushi yayi yana zama kujerar dake kusada Abie yace, “ba ko ina Momma”..
         Momma tayi ‘yar dariya tace, “shikenan tunda ba’aso muji”.
    Sauban da Aunty Mimi ma dariya sukayi, nikam kunya tasani k’asa da kaina inad’an murmushi.
__((*))__((*))__((*))__((*))__
               Abba dai bai yarda su maman yaa Hameed su kwana a gidanba, a daren kowacce tanufi gidansu, yayinda baba k’arami ya d’auki innaro zuwa asibiti.
        Su Sa’eed kam zare jiki sukai suka koma gida, zukatansu tab da mamakin wannan lamari.
     A ranar zarah sai sashenmu ta kwana a  tsohon d’akinmu ni da munubiya, saboda Aminu ya sanar mata yaga Sa’eed da mijin Siyama a k’ofar gidanmu.
       Gaba d’aya saitaji yau tanajin haushin mamansu, dan daba ta tanka dariyar da gwaggon Haleematu tamata ba ai dabasuyi rigima har Abba ya korasu gidaba, dayanzu gidanta zata kwana jikin mijinta itama, wane irin abin kunyane wannan kai kana gida uwarka na gidansu itama????????.
     %%%%%%%%%%%%%%%
     Dawowarmu kenan ni da Sauban da Samha daga zagaya gari, nagaji ovar, jikina sai ciwo yakemin, dama Yaya lafiyar giwa, saman sofa na zube Ina sauk’i numfashin wahala, wani zazza6ima nakejin yana neman rufeni, harna rufe idanu naji wayata na wringing, lalubowa nayi na duba mai kirana, nasan dai duk Wanda zai kirani to daga Nigeria ne, dan su Samha duk suna gida, Galadima kam bai ta6a kirana a wayaba, banmayi tunanin yanada number ba duk da shine ya sayi layin.
   Sunan munubiya dana gani yasani fad’ad’a murmushina, saida nabari ya katse sannan na kirata.
          Bugu biyu ta d’aga, jin muryarta can k’asa sai hankalina ya tashi, nashiga tambayarta ko lafiya.
       “sweetheart wlhy banajin dad’i, ko school nakai sati banjeba, ya kuke?”.
      “ayya sorry sweetheart, mike damunki?”.
     “wlhy zazza6i, kema naji muryarki wata iri ai?”.
       “nima lafiyar sai a slow wlhy, ina yaa marwan?”.
      “tofa, ciwo a time d’aya mu duka? ALLAH yabamu lafiya to, yaa marwan yafita gaida su mama, ya jikin Abie da Galadima?”.
        “everything Alhmdllh dear, jikin Abie ma yanata sauk’i, sun fara masa amfani da addu’oin, amma naji kamar doctors d’inshi suna complain wai abar shafa masa abinda ake shafa masa”.
      “karku wani sauraresu, Ku cigaba kawai, ALLAH yasa muji alkairi”.
       “insha ALLAH dear, dama haka Galadima yace shima”.
       “ALLAH ubangiji yabashi lafiya, bara na barki ki huta, a gaida minsu”.
      “ok sweetheart bye”.
        Ina ajiye wayar na mik’e, bayi nashiga nahad’a ruwa mai zafi nagasa jikina kozanji dad’i, haka nake kusan yini wanka da ruwan zafi, wai ko zan dainajin ciwon jiki, amma a banza, danayi wanka bana wuce mintuna talatin ciwon yake dawowa sabo.
     Wani ash d’in wando da Riga na jawo na saka, kayan basuda nauyi sosai, wandon kad’an yawuce guywata, rigar kam hannunta iya kafad’a ya tsaya, kamardai vest d’in maza take, saidai daga gaba tanada banbanci data maza. nasan Galadima bazai dawo gidan yanzuba saboda koya tashi aiki saiya biya ta asibiti kafin yazo gida, yanzu kuma akayi isha’i nasan sai zuwa irin 11, shiyyasa nayi tunanin sakasu ko zan ragema kaina nauyin jikin. komawa nayi saman sofa data zama gadona na kwanta, amma sai naji dukna takura, najujjuya naji babu dad’i kwanciyar, tsaki nayi namik’e nakoma saman gadon na kwanta, insha ALLAH kafin maishi yadawo dai natashi????.
     Banfi 5minutes ba da kwanciya barci ya d’aukeni.
*****
          Kansa daya fara matsa masa da ciwone yasashi tattara kayansa yabaro office, Dan yau sunyi overwork ne, suna shirin fidda laptop sabon k’ira, saida yashiga office d’in vijeey da Alexander yamusu sallama sannan yanufo gida, ko asibiti bai biyaba, Dan har wani jiri-jiri yake gani a idonsa, yasan barcin dabasa samun yine ya haddasa masa ciwon kan, bama kamarshi, Dan gara ni idan yafita nakan kwanta nayi barcin.
     Da k’yar ALLAH yabashi Damar isowa gidan. Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d’in yafara cire bottom d’in Indian suit d’in dake jikinsa white color, burinsa yana shiga d’akin yagansa a gado kawai.
     Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun mugun fito da surar jikina d’as, gashi sun bala’in min k’yau, yau da ace matar dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik’e, rigarma yakasa k’arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa.
    Jin jiri na neman zubdashi a k’asa yay saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi buk’atar kwanciyar haka ya daure yad’an watso ruwa, sannan yafito yasha magani, koma shafa’i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi.
      Abin dariya, saiya jawo dogayen filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k’arshe, shima babu dad’ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad’o babu ruwana fad’ama fans zanyi Galadima ya tik’o k’asa ehe????????????????)
    Can cikin barci Galadima yafara juye-juye, yasaba shi kad’ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya d’aukesu yayta wurgawa k’asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon.
       Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba.
     Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima masu jera fillos a jikin munaya????, d’umin jikinta yasashi kuma nanik’e mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta yamasa dad’i.
      Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda jin sanyi-sanyi da k’amshin turarensa kuma, sunbi sun k’adandane juna kaikace ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d’an uwansa.
Humm, bara na lek’o su innaro ‘yan Nigeria suma????, mai tuk’ulluma a goshi ba????????, ni nama godema mamansu yaa Hameed???? dama k’afar suka karya????.
_____________________________
        Anbama innaro magani a wani camix suka dawo gida, gidanta aka kaita, innarmu tad’an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka k’aramin towel danta gasa mata goshin koza’a samu yarage tukullumar dayayi.
     Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu tijara.
     Baba k’arami yay saurin tareta da fad’in “haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad’anda suka miki abunma ko kallo baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai’sha agarekine?”.
      Abbanmu da daddy suna zaune basuce uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k’arami kawai amma batace komaiba, itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata.
     Tanama innarmu masifa dai har akad’an gasa mata, aikam saigashi wajen yad’an saki, baba k’arami yamik’a mata kofin tea d’in da maman fauziyya ta had’a.
     Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta.
     Basu bar gidanba saida tasamu barci, da innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a’a tatashi suje gida tunda ga habiba d’iyar gwaggo safiyya dabata komaba.
      Badan innarmu tasoba tahak’ura, Dan aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad’an yake jira a ta6ashi ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma.
     
      Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi, innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d’akinta, abinda bayayi kenan, yakan shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d’akin.
     Tana yunk’urin tashi zaune zata tambayesa lafiya? ya d’aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka kwanta.
    Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru kawai kamar mai barci.
        Kamar yanda Abba bai isashen barciba hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu Sa’eed.
         Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon Haleematu basu rintsaba dasukaje gida.
      Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak’i cewa komai, yakuma k’i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa.
       Innaro harta fara samun sauk’i itama.
       Sa’eed kam dadynsa ya taso k’eyarsa washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad’i dukkan abinda zarah ke masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin iyayenmu ya harareta take shiru.
      Nandai aka musu fad’a bayan itaba dad d’insa yace tafad’i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita baya mata komai, wannan yasa aka musu fad’a da nasiha kawai akace yad’auki matarsa su tafi.
     Dad’i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu itama a dalilinta kuma?????).
     Washe garin rana ta uku tunda safe saiga mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai, komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud’inma dashi suke tak’ama yanzun, duk da mahaifinsu ya tara musu).
       Abba dai k’in saurarensa yayi, saida yaje ya kama k’afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin zuciyar ko nuna gazawa.
        Ansha fama akan Abba kafin ya sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k’uruciya har girma yafara kamasu sun k’asa canjawa, yabama kowaccensu damar k’arshe inhar suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma tatafi kenan har abada, Dan bazai duba ‘ya’yan dake tsakaninsuba ma.
       Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da Kansa koya turo anbasu hak’uri.
      Shikuma ya rantse saidai tayita zama inhar saiyaje bikonta.
       Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji, Dan baba k’arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad’in barin gidan gaduk wacce tasake fad’a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, ‘yan anguwa da makwafta sukaji kasiririt.
    Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun k’ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko ‘ya’yanta basuda farinjini wajen innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci????????).
***************
     Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti tana kukan batason zuwa, amma yak’i saurarenta.
      Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d’in samun rabo na wata d’aya kacal (yaa marwan sharpshooter????, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi????????).
         Wayyo zokuga murna wajen ogan miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai kunnenta.
      Harda kukan dad’i tayi, ikon ALLAH kenan, ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga Munubiya wata 1 da sati d’aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya, k’ila itama d’indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata complain batajin dad’i. haka innarmu taita murnarta a d’aki ita kad’ai, babu Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo gidan sagani.
       Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar laulayi haka yakeji, Dan tana d’an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata iyayi balle gyaran gida.
      Hakanne yasaka mama rabi’a cewa yadawo da Munubiya wajenta harta samu sauk’i.
      Saiya fara fushi da rok’on tabarta Dan ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita taimakawa Munubiya da aikin gidan.
     Mama Rabi’a tace a’a, Ayusher itake taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai????????, ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba????, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy????).
        Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari.
     Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama Rabi’a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya janyeta d’akinsa da wayo ya kashe arna????????.
    Mama Rabi’a duk tana kula da su, amma saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi yake????????.
    ????kai jama’a mu koma India.????????♀⛹????
…………………………………………….
______________________________
…………………………………………….
        Zafin jikinane yafara masa yawa, dan yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya rungume haka? jin kamar mutum yasashi k’ok’arin bud’e idonsa dasukai masa nauyi  saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar munaya, hardai yasamu nasarar bud’e idon gaba d’aya a kanta????……………..????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button