DARAJAR 'YA'YANA PART 1

DARAJAR ‘YA’YANA PART 1

DARAJAR ‘YA’YANA1-01
Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 08-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
__________________NA ___________HALIMA K/MASHI Cikin sauri sadiya take yin komai dan bata son mai gidanta ya dawo ya sameta ba yanda idonsa yake bukata ba.Tuwon (semo) tayi mashi miyar kubewa danya, sai farfesun kafar sa, sanan ta tanadifura da nono, tasa a cikin fridge don tana bukatar yayi sanyi.Ta share ko ina na gidan fes ta wada tashi da kamshi turare, taje ta fesa wanka sanan ta bata lokaci a gun

kwalliya.Kankwasa kofar da taji ne ta tuna da ‘yan yaranta, da sauri taje ta bude musu, kai tsaye ban daki tace su nufa.Wanka ta sake yi musu sanan ta shirya su cikin sababin kayansu masu kyau ta feshesu da turaruka.Ta dawo dakinta inda ta rasa wane kayane ma zata saka, a karshe ta yanke shawarar saka wani jan material riga da siket.Ta dubi kitsonta kanana da ta yarfa a madubi, sanan ta kashe daurin dan kwali.

Tasan yau zata burge mijinta, musanaman da ta kalli lallen hannunta na fulawa da aka zana mata.Ta kalli agogo karfe shida da kwata, wayarta wadda ta dauke saboda rashin chaji, ta jonata chaji.Ashe garin sauri bata sa dai dai ba, don haka bata samu chajin ba har aka dauke wuta. banda haka da taji yanzu mijinta yana dai dai ina?Kwnkwasa kofar ne ya dawo da ita daga haushin rashin cajin da wayarta bata da shi, ita da yaranta suka diba da gudu don taryo mijinta.Tana bude kofar shine tsaye, sanye cikin kayan yansanda,

daga ka ganshi kasan babban jami’ine, ta fada jikinshi tare da rumgume shi, amma me?Sai taga ya sabule tare da cewa sannu da gida.Cikin mamaki ta amshi ledar hannunsa tare da jakarshi, ya tsugunna yana sha kan yayan sa cikin jin dadi da kewa, sadiya ta tsaya cike da mamakin saboda al’amari da take gani a gurin me gidan nata.Abin da tasani a duk lokacin da ya dawo yakan iso ne a marmatse cike da kewarta, da ya

shigo burinsa kawai ya rungumeta tsam a jikinsa kafin yaran, amma yau sai taga ita ce ta rumgume shi har yana sabulewa, lallai wanan sabon al’amarine a gurinta.To ko dai gajiya ce take damunsa?Kokuma fushi yayi ya gaji da kiranta bai samu ba?Ta dubi kanta, kokuma kwaliyarta ce batayi ba?Ta sake wai wayawa ta kale su inda yake rungumarsu daya bayan daya.Da kausar ya soma, sanan Al’amen, sai mama ta tuno

yanda yake mata a duk juma’ar da yazo, ya kamata ya fi dokinta a wanan karon da ya hada saty biyu bai zoba.Abin duk ya dameta, tana tsoron kada wata masifa ko annoba ta ratso cikin kyakkawan zaman nasu, tana tuna da yadda take makale a gefen damansa sannan ya dauki mama da hannun hagunsa har cikin

falonsu.Yanxu dai ba zatace ganin yara bane, domintasan yaransu sun taso sun samesu cikin wata rayuwa da suka shinfida ta shakuwa da kaunar juna.Sun saba ganinsu rungume da juna, sun saba ita da yaran suyi ta kokuwa a jikinshi, basa yin wani abu da zai kawo matsala ga tarbiyar yaransu, amma sukan rungumi

junako yin falo da junan ana hira.Sun rigata shiga falo, ta shigo nan ma ta sake kallonshi, mamaki ganin ya zauna shi da ke zarcewa dakinsa, can suke zuwa ya basu tsarabarsu. Sanan ya basu ta iya ya ce su kai mata, sanan kada kudawo in na huta zanzo in gaidata, sai mu dawo tare.Su ce to Abba, su tafi suna

tsallensu.Shi kuwa suna fita wata ran ko wanka baya yi zai rungumota ya ce Dear my choice a matse nake.Ya wancin lokacin sai ya samu natsuwa kafin ya ci abincin ba yan yayi wanka.Dan Aliyu mutum ne mai matsanan ciyar bukata.Cikin damuwa ta isa kusa dashi.Yaya Ali yau kagaji sosai ko?Ya dubeta me kika gani?Ta ce, baka saba zama cikin falo ba.Ya miko hannu bani ledar nan in sallami yaran nan.

Ya fada ba tare da ya bata waccen amsar ba.Ta miko masa kanta daure ta nufi dakinsa da jakarsa, ya ba yaran tsarabarsu, kayan ciye ciye ne da na wasa, sanan ya mike ya nufi dakin sa.Kausar tace, abba yau ina tsarabar iya?Sadiya daga cikin dakinta ta kaso kunne taji amsar da zai ba da.Ba tare da ya waiwayo ya dubi kausar ba, yace kinga magariba ta kusa, bari in anyi sallah sai muje ko?Ya shiga daidai lokacin ta

shiga ban daki dan hada masa ruwan wanka.Ta fito yana zaune bakin gado yana kwance igiyar takalminsa ta iso gurin.Da sauri ta tsugunna tare da cewa abba kausar yau kuma harda aikina zaka shigar min?Ta ci gaba da kwance takalmi tana cewa, yau duk na ganka wani iri daban, ko duk gajiyar ce?Ya ce gajiya

saikace ba jami’in tsaro ba?Ta soma balle masa maballen riga, to baka jin dadin jikinka ne ko? Yaja tsaki, dan Allah ki bar ni da tambayoyinnan naki please, gabanta ya fadi, ta dubeshi da gaske yake yi fuskarshi daure.Jikinta yayi sanyi, ta gama balle botiran, ya mike ya nufi ban daki ta mike zata taimaka mashi kamar yadda ta saba, ya shiga sai ya banko kofar zata tura sai taji karar makulli yana kulle kofar.Cike da tsoro taje dakin tana kallon kanta a madubi, ko dai batayi kyau ba ne yau?Ta duba ba wata makusa, ta kara jan baki da turare sanan ta fito ta same shi yana shafa mai,ta isa gurinshi, ta ciro masa kaftani da wando na shadda mai ruwan sararin samaniya, ta ciro hular da zata dace da kayan ta ajeye masa, amma sai taga ya janyo jallabiya mai dogon hannu fara sol ya saka.Daga nan sai ta koma ta jingina da bango dan jiran ganin sarautar Allah.Ya fita, ta bishi ganin zai fita waje ta ce, tabban kausar abincin fa?A sanyaye tayi maganar.Ba tare da ya waiwayo ba ya ce, sallah zan yi tukunna.Kausar ta ce,Abba ina kayi sallar ka dawo kaje damu gidan iya, kada kaje daga can.Ya dubi yaran da murmushi zan zo muje kunji?Suka ce to Abban mu, bari

muyi muma sallar.Ko da tayi sallar sake zama tayi gaban madubi tayi sabuwar kwalliya sanan tayi canjin kaya daga jan yadin zuwa leshin ruwan dorawa mara nauyi .Ba kamar ko yaushe da yake kashe waya baina zasu ci abinci wayarshi kunne kuma jifa jifa yana amsa kira.Guri daya taji dadi ya zage ya kwashi abinci kamar yanda yake yi ko yaushe, haka nan haka nan ‘ya’yan shi yana ta surutu da su.Amma ita ya dauke wuta da lamarinta har ta kasa cin abincin ma, so take ta tuno kurun laifin da tayi masa dan kawai ta

bashi hakuri.Bata saba da wanan yanayin da suke ciki ba, zuciyarta ta ce ko ya ta kiran wayarki ne ba a ji?Da sauri ta dube shi.Abban kausar nasan kayi ta nema na layi naa kashe ko?Ya dubeta ban nemi layinki ba, ba wuta ne ta ce eh ba wuta.Kutashi muje gidan iya,suka mike cikin murna,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Kausar ta ce,Abba, momi bata dauko hijabinta
ba.Ya ce, bata son zuwa ne, tayi aiki ta
gaji.Wanan ya nuna mata ba a son zuwa da ita
tunda ba a tambayeta ba bare a ce ita ce tace ba
za ta je ba.Sun barta cikin tunani da jimami, ta


gyare gidan musanman gurin da suka ci abinci,
tayi ta jiransu tana zaune a falo tana kalon TV
amma inda zaka tambayeta abinda ake yi a TV
din ba zata fada maka ba.Ita burinta kawai ta
san laifinta, amma ina ta tuna da cewa anjima da
yazo dole zai sauke ko mai dan tasan cewa ba
zasu taba kasancewa gado daya da shi ba ya iya
kauda kai daga gare ta.Itama zata ja aji lokacin
har sai taji dalilinsa, ganin sun kai har sha daya
sai kurum ta cire tayi shirin bacci, kayan baccin
bakake masu matukar daukar hankali, ta dora
hijabi saboda da yara zai shigo.Kausar ce kurun
batayi bacci ba, Al-Amin yana sabe a kafadar
dama, mama a ta hagu, kausar din tana biye
dashi suka shigo.Kai tsaye dakinsu ya nufa da su,
tabi bayan su yana kwantar da su, ya fita ita
kuma ta gyara su, sanan tayi musu adu’a taja
musu kofa.Dai dai lokacin kausar tana cewa
momi sai da safe, sadiya tace, Allah ya kaimu
kausar.Dakinta ta nufa ta sake fesa turare, sanan
tanufi fridge don ta dauki furarshi wadda ta riga
ta dama.Shiru ta tsaya dan ya riga ya dauka, ta
nufi dakin shi.Yana zaune bakin gadonshi sanye
da kayan bacci, laptop ce a gabanshi kan dan
tebirin da ake ajeye mai fura.Kofin yana
hannunshi yana kurbar furar, idonsa sanye cikin
farin gilashi ta ce, tace ashe har ka dauko furar
ka?Ba tare da ya dubeta ba ya ce eh.Ta zauna
kusa da shi wai abban kausar nayi laifi ne da ake
ta share ni?

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Leave a Reply

Back to top button