RAYUWAR MACE 3
“Babe where are you?” Yace bayan an daga wayar
“Ok I’m on my way.” Ya kashe kiran ya mike yana kallon ta
“Ba zan yi tolerating kina hana min abinda yake nawa ba, ba zan sake dawowa ba idan an kawo ki gidan zaki ga yadda zanyi dake.”
Daga haka ya juya yana taku dai-dai yayi ficewar sa, be ko yi sallama da kowa ba ya kama gabansa sai gidan Fido, daga chan ya wuce wajen abokin sa ya karbi wasu kaya sannan ya wuce gida.
Tun ranar da ya tafi bata sake jin duriyar sa ba, Hajiya Mama dai tazo sau daya da maganar yadda bikin zai kasance tunda duk abu daya ne bangaren ta da na Abba, umma dai bata ce komai ba, duk abinda suka tsara suka yanke ita bata da ta cewa dan ko da tace din ma ba lallai suyi amfani dashi ba. Daga haka aka shiga satin bikin.
Ranar laraba aka je akayi kafi, gidan yayi kyau sosai sama da k’asa sai parking space, a jikin gidan Hajiya Maman yake dan katangar su daya, dama tace ko Adam zai yi aure yana tare da ita bata so yayi nisa ko kad’an, balle kuma da zai auri Asma’un sai take ganin ai shikenan ma dama Asma’un ikon ta ce itama. Alhamis aka shiga bikin gadangadan, gidajen biyu ko ina biki ya kankama Hajiya Mama dai saboda yawan mutanen wasu sai dan karamin hotel hotel din dake bayan gidan aka kama musu musamman abokan Adam din da sukayi karatu a turai tare suka zo daga wasu states din.
It’s better to marry late than to marry wrong! (Kamar haka dai bature yace, na manta dai.
Don’t marry out of desperation dan aure ya wuce duk tunanin me tunani!