Sai da ‘yan anguwarmu suka taba zane ni, sun zaci na haukace, mai sana’ar kyadin da ya zama miloniya a Legas


Wani dan Najeriya wanda ya zama miloniya da sana’ar kyadi ya ce ya fusakanci kalubale iri-iri da sana’ar ta shi, Legit.ng ta ruwaito.
A tattaunawar da Sojuloore TV ta yi da shi, ya bayyana cewa an tsane shi anguwar da ya ke zama ana kallon kamar ya haukace.
Azeez ya bayyana cewa akwai lokacin da aka lakada masa duka ba tare ya yi laifi ba har yana nuna tabon ciwon da aka ji masa.
Yadda ya fara sana’ar kyadi
A cewarsa bayan komawarsa Legas daga Abuja ne ya tambayi abinda ake yi da karafa bayan ya ga wasu suna tarawa.
Daga nan ne suka nuna masa kamfani da suke sayarwa shi ma ya fara harkar duk da dai mahaifinsa ba ya son sana’ar.
Ya bayyana yadda yana tsaka da sana’ar kamfanin ya dakatar da shi daga kai karafan amma ya ci gaba da tarawa.
Bayan wani lokaci kamfanin ya nemi karafan inda ya sayar ya samu makudan kudade har ya zama miloniya.
Mutumin ya shaida yadda ya ci gaba da tara karafan duk da kamfanin da ya ke kai mawa sun bukaci ya dakata. Ya tara karafa masu yawa.
Daga LabarunHausa
[ad_2]