WUTSIYAR RAKUMI 50

_NO. 50_*
……..Amaan ne ya fara farkawa, buɗe idanunsa yay a hankali bisa fuskar Ummukulsoom dake barcin wahala, hawaye duksun bushe mata a fuska, ya tsira mata ido yana ƙare mata kallo irin wanda bai taɓa mataba.
Komai nata abin birgewane, yanayin fuskarta irin na mutane ne masu karancin son hayaniya, sumbatar goshinta yayi yana sake cusata jikinsa, ji yake kamarma ya haɗiyeta shidai ya huta da zogin sonta dake ƙara faɗi kullum a zuciyarsa, shi kansa yasan ALLAH ya jarabcesa ne da son Ummu domin ya nuna masa iyakarsa shida mahaifiyarsa da ƴan uwansa, inda a labari akace akwai irin wannan soyayyar dake mamaye zuciya da jini da saiya ƙaryata, yama ce mai bada labarin mahaukaci ne, amma abin mamaki da al’ajab sai gashi shi ALLAH ya jarab cesa akan wadda yake ganin a baya bata kai ya sota ba.
Kuka Ummukulsoom data farka ta sakar masa jin ya matseta a jikinsa ko numfashinta da ƙyar yake fita, sassauta mata riƙon yayi yana maida dukkan hankalinsa a gareta.
Hawaye Ummu take wasu na korar wasu, dan ita kaɗai tasan irin azabar da takeji, har acikin barci a takure take. Amaan ya tashi zaune yana janye bargon da suke lulluɓe, bayi ya nufa ya haɗa mata ruwa mai ɗumi ya dawo. Har yanzu kukan take, bata taɓa sanin muguntar Amaan takai hakaba sai yau, da farkone ya bita a hankali, amma da labari yay nisa saiya manta da tausayin nata ya cigaba da binta da dukkan ƙarfinsa, a fili tace, “kai jama’a, ALLAH ya tsinema masu yin iskanci, banzaye duk wannan azabar da akesha haka suke kai kansu saboda ƙwaƙwalwar kifine dasu”.
Amaan daya duƙo zai tadata maganarta karaf a kunnensa, harga ALLAH ta bashi dariya, kasa daurewa yay sai da ya murmusa kuwa, sannan ya ɗora bakinsa saitin kunnenta yana mata raɗa, “Gaskiyarki Babiena ALLAH dai ya shiryi masu iskanci”.
Hannu tasa ta ture fuskarsa tana kuma sakin wasu hawayen masu ɗumi, gaba ɗaya haushinsa takeji wlhy.
Duk yanda yaso ta tashi ƙi tayi saboda babu kaya a jikinta, da bargon take ƙudundune, rigar wankan data fito da ita ya shiga lalube, ya jawota yana ƙoƙarin saka mata ba tare da yayi magana ba, sai lokacin ta yarda ta tashi, sai dai taƙi kallon koda sashen da yake sam, ga hawaye har yanzu tanayi wanda shi yama rasa na miye hakan? Taku biyu tayi ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka mai ban tausayi, wanda ya nema rikita lissafin Amaan gaba ɗaya, dan ya lura akwai matsala gaskiya. Komar da ita yay bakin gadon ya zaunar fuskarsa cike da matuƙar tausayinta.
“Miya farune?” ya faɗa a hankali.
“Wlhy zafi, bazan iya tafiya ba, nashiga uku Ummi ya kasheni”.
Tausayi ta bashi, duk jikinsa saiya kuma yin sanyi ƙalau, haka ya miƙe dukda ta masa nauyi ya ɗauketa zuwa bayi. Ummu taso tayi dauriya ganin yanda Amaan ya damu sosai, sai dai kuma ta kasa, dan ƙara mai ban tausayi ta saki lokacin daya sakata cikin ruwan ɗumin daya haɗa, ta ƙanƙamesa sosai tana sama da numfashi tamkar zata shiɗe.
Lallai akwai matsala da gaske kenan, rasa miya kamata yayi yay, dole ya haɗa musu ruwan wanka sukai na tsarki kawai ya ɗakkota suka fito, dan lokacin salla ya gota.
A daddafe Ummu tai salla, dama zazzaɓi mai zafine a jikinta, yanzu saiya ƙara turewa jikin yay ringis har haƙoranta na haɗuwa wajen rawar sanyi.
Rasa abinda zaiyi yayi, sai zanin gadon kawai daya canja ya maidata kan gadon ya lulluɓe da bargo, yanata safa da marwa tsakanin falo da ɗaki, rashin mafita ta sashi kiran Attahir, bawai ya sanar masa abinda ke faruwa bane, yadai ce masa Ummu ce bata da lafiya.
Sam Attahir bai kawo komai a ransa ba ya faɗama Ummi, dan suna zaune a falon Abba ne suna magana, aikin yamma ne da ita yau, ga ruwa kuma da aka tashi dashi, danma zuwa yanzu ya ɗauke sai yayyafi da akeyi kaɗan-kaɗan.
Cokali Ummi ta ajiye tana faɗin, “tofa, ALLAH yasa ba Thypoid ɗin tace ta motsa ba, bara naje na fara dubata saina wuce asibiti”.
Attahir yace, “Bara na kaiki to Ummi”.
“A’a kayi zamanka ka huta, kunga ga baƙi a gida bazasuji daɗi dukmu fice mu barsu ba, nima zuwa 9pm insha ALLAH zan dawo gida Dr Sarah saita karɓeni da wuri”.
Addu’ar dawowa lafiya sukai mata, sai dai kuma maman Ahmad tana zargin anya ba Amaan bane ya angwance? Badai ta furta ba tabar zancen a ƙasan zuciyarta ne kawai.
Momcy daketa kiran wayar Amaan ce yaƙi ɗagawa ta miƙe tana tunanin lafiya kuwa? Dan Dad ma ya kirasa bai ɗagaba, da farko tayi tunanin ko barci suke, amma ganin lokacin salla ya wuce tasan sun tashi sai itama ta kira, dan Dad soyake ya fita zaije sokoto, Amaan ɗin kuma yace masa gobe zasu wuce, bai zama lallai ya dawo ya samu basu wuceba.
Yana zaune a bakin gadon kan Ummukulsoom a saman cinyarsa yana shafawa, yayinda ya jingina jikinsa da gadon idanunsa a lumshe, zafin jikinta na ratsashi har cikin ƙashi. Sauraren isowar Attahir yake da yace zaizo da Doctor ta duba Ummukulsoom, shi sam bai kawo Ummi zatazo da kanta ba……..
Knocking ƙofa da yaji anayine ya sashi buɗe idanunsa ya tashi zaune sosai, a hankali ya zame kan Ummu a cinyarsa ya ɗora kan filo, barcin wuyane ya sake figar mutuniyar taku????????⛹????♀️.
Yana buɗe ƙofar falon sai yaci karo da Momcy, sam baiyi zatoba, ta kallesa sama da ƙasa tana mamakin ganinsa a sanyaye.
Matsa mata yay ta shigo ganin yayyafi na jiƙata, “Fodio baka da lafiya ne? Tun ɗazun muke kiran wayarka amma kaƙi ɗagawa?”.
Da ƙyar ya iya cewa, “A’a Momcy”. Shi saima yanzu ya tuna da anan falo yabar wayar, gashi a silent take.
Hannu ta ɗora a wuyansa sai taji jikinsa normal, ta sauke numfashi tana waige-waigen neman Ummukulsoom, “Ina yarinyata?” tai tambayar cikin kafesa da ido.
Da hannu ya nuna mata bedroom.
Zama tai a hannun kujera tana faɗin, “Jeka kiramin ita”.
Shiru yay bai motsaba, sai da ya zuƙi iska ya fesar kafin yace, “bata da lafiya”.
Bata gama saurarensa ba ta nufi ɗakin kai tsaye, binta yay shima, dan shikam bashida wata mafitar data wuce yabar Momcy ta taimaki Ummu, wlhy yarasa yaya zai mata, shi sam tunaninsa bai kawo ciwo tajiba ko wani abu, yafi ɗaukar abun matsayin bata saba ba daga shi har ita.
Hannu Momcy ta saka akan goshin Ummukulsoom, zafi rau har huci yake, ta rumtse idonta tana faɗin “Ya salam, fodio tana cikin wannan halin amma kai shiru ko asibiti bakai yunƙurin kaita ba?”.
“Bazata iya bane Mom, na kira Attahir zaizo da Doctor ”.
Jitai kamar ta makesa, kai itakam indai wannan miskilancin Fodio zaima Ummu tana tausayinta, yanda itama take shan wahalar zama da Dad ɗinsu tasan Ummu zata fuskanci ma fiye da hakan, sai dai kuma akwaisu da tattalin mace idan sun keɓe, dan a hakama da suka manyanta a kullum Dad cikin faɗaɗa soyayyarsu yake, sai dai idan ta bata masa raine kuma babu ragi babu ragowa.
“Kaga ɗauka key muje asibiti kawai” tai maganar tana yaye bargon da Ummu ke ciki, ALLAH ya sosa ya saka mata doguwar riga lokacin da zasuyi salla.
Buɗe ido Ummu tayi tana yamutsa fuska zata saka masa kuka, duk zatonta Amaan ne ya buɗeta. Ganin Momcy sai tai yunƙurin tashi da hanzari, wata azaba ce ta ratsata, babu shiri ta koma ta kwanta tana sakin kuka.
Runtse ido Amaan yayi saboda tausayinta, yarasa mike mata ciwo, gashi taƙi faɗa masa.
Shiru Momcy tai tana kallon Amaan ranta a ɓace, dan zuwa yanzu kam tagama fahimtar inda matsalar take.
Cike da basarwa ya janye idanunsa daga momcy yana tura dukkan hannayensa a aljihu, kafin ta samu damar masa magana akai knocking ƙofar falon. Dama hanyar kuɓuta yake nema daga tsatstsaresan da Momcy tayi da manyan idanun daya gada.
Duk tunaninsa Attahir ne, yana buɗe ƙofar yaci karo da Ummi aunty nurse na biye da ita, da alama dai can sashen ta fara zuwa aunty Nurse ta rakota nan.
Risinawa yay ya gaida Ummi kansa a sunkuye, dan harga ALLAH baisan tsiyar da Attahir ya shuka masaba kenan, kasa binsu yay ɗakin, ya kuma dakatar da aunty Nurse da ido alamar karta bita.
Tasan halin kayanta, dan haka ta dakata a ƙofar tana cema Ummi ta shiga ciki.
Momcy na zaune ta rungume Ummu jikinta tana lallashi, Ummi ta shigo.
Hannu biyu da mutuntawa Momcy ta amshi Ummi, to dama ƙawayen junane, danma Ummi ce bata cika sakema Momcy ba saboda batason wasu halayyarta musamman ƙyankyamin talaka.
“Tofa, kice tana nan tana miki shagwaɓa”.
Dariya Momcy tayi kawai, dan itakam tausayin Ummu take har cikin ranta, duk da kuwa bataga ɓarnar da ɗan nata ya aikata ba.
Fita Momcy tayi ta basu waje acewarta zata haɗoma Ummukulsoom abinda zataci, Ummi bata kawo komai a ranta ba takai hannu a wuyan Ummukulsoom tana kafeta da idanu dayin nazarinta, yanda idanun Ummu suka kumbura ne ya bata mamaki, da alama dai kuka tayi bana wasaba.
“Autana mike faruwa? Dan wannan zazzaɓin kukane ya kawoshi?”.
Langaɓewa Ummu tayi jikin Ummi tana kuma sakin kuka, “Nidai Ummi kije dani gida kawai”.
Tsura mata ido Ummi tayi ba tare da tace komaiba, tana son tabbatar da abinda take zargi, dan haka ta janye Ummukulsoom a jikinta tana miƙewa tare da miƙar da ita, Ummu taso ta daure yanzun ma dan kar Ummi ta gane, sai daifa ta gaza hakan, dan hawaye har rige-rigen zuba suke.
Ummi ta girgiza kai kawai danta gama fahimtar komai, maidata tayi ta zaunar zuciyarta na mamakin halin maza na yanzu, sam basama budurcin mace da sauƙi, a da idan aka kaima miji mata saiya haɗa wata yana lallaɓata kafin ma ya kai ga nemanta, sannan bazai taɓa zuwa mata a rana ɗaya ba, a hankali zaita binta harta buɗe, amma na yanzu tsabar mugunta da rawar kai zuwa ɗaya sukema yarinya, babu ruwansu da yanda zasu fatattaka ta balle ita yaya zataji, sun mata rai dai guda ɗayane, yanda za’a yankesu suji zafi haka itama macen kejin zafi koda a sannu aka bita tunda ba taɓa yi taiba. Koda yake wani lokacin harda laifin iyaye, maganin matannan da suke ɗurama yara ba ƙaramin jawo musu wahala sukeba, yarinyar ke dake a ɓame, batasan dawan garinba zaki bama maganin mata, tayaya kike tunanin namiji zai ɗaga mata ƙafa ya bita a hankali. Basu bama su Ummukulsoom komaiba sai tsumi, amma jiba yanda suka jigata, ita kanta Bily sai da akai mata ɗinki, toga Ummukulsoom ɗin nanma da alama sai anzo ga hakan, balle Amaan daba yaroba ma tsohon tuzuru……..
Da ƙyar Ummi ta yakice tunaninta ta maida hankalinta ga Ummukulsoom ranta duk a jagule, “Kin shiga ruwan zafine?” ta tambayeta.
Kan Ummu a ƙasa ta girgiza alamar A’a.
“Mi yasa?” cewar Ummi again.
“Ummi da zafi, jinake kamar zan mutu wlhy”.
Tasan ragwantakar Ummukulsoom batun yanzuba, har tunanin dama randa za’ace haihuwa tazo musu takeyi, cikin ɗan faɗa tace, “Wannan gangancine ai, dan ƙaniyarki ba dole kiji zafin da yafi na farkoba, dakinyi haƙuri kinɗan gasa wajen aida komai ya kuma zuwa da sauƙi, yanzu ko yariga ya tsuma ai”.
Ita dai Ummu kanta a ƙasa tana hawaye, cire gyale Ummi tayi taje ta kulle ɗakin ta shiga bathroom, da kanta ta haɗa ruwa mai ɗan zafi tazo ta kama Ummu suka tafi, iyakar wahala da azaba Ummu ta shashi kafin su isa bayin, ta haɗa zufa sharkaf tamkar ba sanyi ake ba.
Ummukulsoom na kuka da magiya Ummi bata saurareta ba saida ta dannata aruwan, tsawon minti goma sannan ta fiddota suka dawo ɗaki.
“Ki nutsu na duba, matsayin likita nake a gabanki yanzu ba uwa ba, inba hakaba kuma zan ɓata miki raine”.
Kai Ummu ta ɗagama Ummi, sai daifa har ga ALLAH tana matuƙar jin kunya, amma yaya zatayi, yanda Ummi taga wajen sosai tausayin Ummukhoolsum ya kamata. Dolene suje asibiti kam.
★★★★★
Babu wanda ya sani a gidan aka fita da Ummukulsoom asibiti, shima Amaan ɗin yana wajen Dad suna magana, Momcy ce kawai ta bisu tanata faɗa, sai Ummi ke bata haƙuri.
Babu bata lokaci suna isa Ummi tai mata allurar kashe raɗaɗi data barci, ahaka tai mata ɗinkin. Dukda bata cikin hayyacinta saida taji zafin kaɗan-ƙaɗan cikin barci.
Momcy kamar zata ari baki dan faɗa, ca take wannan rashin tausayine kawai, Ummi dai tanata lallashinta, tunda dai ta riga ta afku ai haƙuri shine magani kawai.
Amaan tare sukazo asibitin shi da Dad, amma ba a sanarma Dad gaskiyar zancenba, ca akai masa kawai zazzaɓine Thypoid ɗin Ummukulsoom ce ta motsa mata, ya tausaya mata tare da jero mata addu’oi kafin ya wuce.
Dad na fita Momcy ta hau kan Amaan da faɗa kamar zata mangaresa, shidai baice uffanba, tasan kuma bazaice ɗinba, kansa sunkuye a ƙasa yana kallon Ummukulsoom dake barci, shi sam baiyi zaton abin zaikai hakaba sam.
A gurguje Please????????
Dole a asibitin Ummukulsoom ta kwana, baba halima aka kawo ta kwana da ita, da Amaan ya kafe shi zai kwana, sai da Momcy tai masa wuju-wuju ne, Attahir yaja hannunsa yana dariya.
“Kai wlhy ka haƙura da kwanannan, inba hakaba Momcy zaneka zatai a sibitinnan, ka kira ruwafa da yawa Ajiwa”.
Idanunsa ya lumshe yana shafar girarsa, sai dai baicema Attahir komaiba, shi tausayin matarsa ma shine ya gallabi ransa, gashi taƙi yarda su haɗa ko ido, ko magana yay mata batason amsawa. Dole yabi Umarnin Momcy Attahir ya saukeshi a gida, ranar dai barcinsa ragaggene, ya kira wayarta kuma saiya ganta a ɗakin bata tafi da itaba a she, dole ya haƙura ya kwanta yanata juye-juye.
Washe gari koda yaje ma ƙin yarda tayi ta kalli sashen da yake, ta dai gaishesa, ya tambayeta jiki taƙi amsawa, zama yay a kujerar ya kama hannayenta duka cikin nasa, dan baba halima ta fita su kaɗaine a ɗakin.
“Bama za’a kalleni ba _Noorulain_?”.
Kanta ta sake sunkuyarwa tana kumbura baki, a ranta faɗi take “anki a kallekan, mutum sai baƙar mugunta da miskilancin tsiya”…..
Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta duk dan su haɗa ido, sai kawai ta lumshe idanun.
Guntun murmushin da bai niyyaba ya saki yana komawa bakin gadon kusa da ita, har yanzu hannunsa riƙe da haɓarta, bakinsa yakai gab da fuskarta ya ɗan sumbaci laɓanta.
Da sauri ta ture hannunsa tana janye fusmarta, “Ni fa ka tashi ka fita karma wani yazo ya ganka anan”.
“Aiba kwartanci nazoba ko?” yay maganar da fisgota ta dawo jikinsa. Haushinsa ya kuma kamata, ta dalla masa harar.
“Indai kinamin wannan harar ALLAH zakita shan wahala, dan kamar kina cewa Amaan zo ka ƙara yi ne ehe”.
Babu shiri Ummukulsoom ta waro idanu da mamakinsa.
Ya ɗaga kafaɗa da taɓe baki kaɗan, “Nifa abin da ke raina na faɗa miki”.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }()); Shiru tai masa, dan itakam lamarin Amaan yafi ƙarfinta, dama gaskene da mutane ke faɗin mutum mai shiru-shiru sai addu’a, itakam ta yarda da wannan magana.
Ƙin tashi yay daga jikinta har saida yasata taci abincin da baba halima ta zuba mata, ya bata magani tasha sannan ya tashi saboda shigowar Ummi.
A dai taƙaice ranar da daddare aka sallameta, bayan Amaan yasha gargaɗi wajen Momcy, shi harma dariya ta bashi, kodai giyar wake yasha ai bayace zai jema Ummukulsoom ba dama.
Gab da magriba suka shiga gidan, dan haka Amaan bai shiga cikiba ya juya tsaya suna gaisawa da Ameer, maman Ahmad ta rako Ummukulsoom sashenta, Momcy kuma ta wuce nasu sashen itama.
Maman Ahmad bata zauna ba ta fito dansu tafi, jirgin 8pm zasubi zuwa lagos yau, sallama taima Ummu dasake gargaɗarta akan abinda ya dace sannan ta fita.
Da to kawai Ummu ta bita, dama basu iske su Amaan a sashen ba, duk sai taji babu daɗi da maman Ahmad ta wuce, tashi tai jiki duk a sanyaye ta shiga bayi, danyin wanka, tana shiga babu jimawa Amaan ya shigo ɗakin, motsin ruwa da yajine ya tabbatar masa da tana wanka, ya zare hannayensa a aljihu yana zama bakin gadon tare da zamewa ya kwanta rigingine, sai da ya jawo ƙaramin filo ya ɗora kansa sannan ya lumshe idanunsa a hankali.
Kusan mintuna 30 da kwanciyarsa Ummukulsoom ta fito, dan saida tai gashi kamar yanda Ummi tace ta ringayi tsawon sati guda.
Ummu bata lura da shiba, sai dai taji ƙamshinsa, amma sai bata kawo a ranta yana ɗakinba.
motsinta da yajine ya sakashi buɗe idanunsa kaɗan, ganin bata lura da shiba sai abin yaso bashi dariya, da yanzu an fara kumbura masa baki.
“Mai makon a jirani nazo muyi wankan”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa.
A rikice Ummu ta juyo ta kallesa, jikinta har ƴar rawa yake wajen ƙoƙarin jan hijjab ta saka.
Baki ya taɓe kaɗan yana miƙewa zaune, idanunsa ƙyam a kanta, itako sai faman kumbura fuska take da ƙunƙuni.
Miƙewa yay ya taka zuwa inda take, sai ta matsa baya da faɗin, “Ana kiran salla kai kana nan ɗaukar magana”.
Ta bashi dariya, amma saiya haɗiye kayansa tare da shafa girarsa ya zagayeta ya wuce bayi ba tare da ya tanka ba.
Yana shigewa ta saki ajiyar zuciya tana lafewa a bango da rumtse ido, ALLAH da akwai yanda zatai jini yazo mata a yau da sai tayi, haka kawai take jin tsoron sake kwana dashi a ɗakin, dan ba ƙaramin wuju-wuju taji ba a shekaran jiya, Amaan jarumine, kuma gwarzo a zahirinsa da baɗini, inhar a haka za’a cigaba da tafiya lallai akwai sauran tsalle a gabanta harma da tsilge-tsilge.
Harya fito tana wajen tsaye, da alama alwala kawai yayo, jitai kawai an bata sumba a kumatu.
Tai saurin buɗe ido a kansa, ido yaɗan kanne mata ya wuce abinsa sam fuskar dai babu walwala.
Yanzunma ajiyar zuciyar ta sauke, tare da kai hannu ta shafi kuncinta da ya sumbata………………✍????