NOVELSUncategorized
NAJEEB 9

Mum kam ita duk wannan abunda sukeyi, ita bata ganin zata yarda, ” Ayi ma d’anta haka, “dan ita gaskiya bazata yarda a d’aura ma d’anta wa Innan matan ba, haba ai wannan ba adalci bane ko kad’an, “taya yaron daya taso a waje, yayi karatu a can, ace za’a aura Mai wa Innan matan,
gaskiya da sake, inshi Dad yayi shuru gaskiya ita bazata yarda a cuci d’anta ba, ‘In ma auren akeso yayi sai a Bari ya zaba da kanshi bawai a Kawo mishi wa Innan y’an kauyen ba, ai sai a matsa Mai ya kawo mata a aura Mai indai haka akeji.
Dad tashi yayi “yana fad’in saida safe Bari inje in huta.
Granny tace “Allah ya tashemu lafiya.
Ya amsa da Ameen sannan ya wuce “itama Mum ta tashi tabi bayanshi
Ibtisam da zarah da Granny suka rage “Granny ta kalli ibtisam “tace wai yaushe shima kabirun zai turo ne? “naji shuru ya kamata dai ya turo “musan halinda muke ciki.
Ibtisam tace “haba Granny aikya Bari in warke koh, “kuma Kinga ga yaya Najeeb baiyi aure ba, ya kamata injira in yayi nima sai inyi hakan zaifi.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Granny ta tsuke baki, “can tace ke nifa so nake a had’a bikin duka, dan ban son Ayi ta hidima kan hidima aita abu a rarrabe, gwara a had’a, zaifi, ” saiki fad’a ma Kabiru ya turo, inbai shirya ba mu sani. “kallon zarah tayi tace kema ya kamata in kina da manemi anayin nasu Kema kice ya turo, nida so samu ne duka basai a had’a ba.
Ibtisam tace ni saida safe tare da tashi tabar wajan.
Granny tace ” oh ni Amina yara basa son zancen aure, daka an fara saisu tashi, kaman masu iska, “Zarah Anya bakya tunanin suna da aljanu kuwa? Granny ta jefo ma Zarah wannan tambayan.
Zarah dariya tayi tare da biye ma Granny “tace ashe bani d’aya nake tunanin haka ba, “Granny tace haba ashe Kema kina tunani kai na shiga uku, “Kinga miskili shi tunda yaji zancen aure yabar gidan har yanzu bai dawo ba.
Zarah tace “Granny nifa ina tunanin wannan matan ne baya so, ” inda zaki canza mishi wasu da hakan yafi, ko kice ya kawo wanda yake so.
Granny tace “sam wannan ba abu mai yihuwa bane, “koso kike a maidani karamar mutum?
Zarah tace “kaman ya Granny?
Granny tace “inje in kwaso Mata har hud’u, sannan ace bai d’auki ko guda d’aya ba, “inna koma Mai zance ma iyayen yaran? “Kinga tashi kije ki kwanta, “Granny tashi tayi tana fad’in saida safe, “miskili d’an banza ya’ki dawowa.
Najeeb bai farka ba sai wajan d’ayan dare, “tashi yayi yaji gaba d’aya jikinshi yayi mishi nauyi Sosai, “Kai tsaye ya nufi toilet yayi wanka tare dayin alwala yazo yana rama bashin sallah, Allah dai ya kyauta, “bayan ya idar ya tashi ya d’auki key din motarshi yabar hotel din, ” Kai tsaye gida ya nufa inda yayi horn Mai security suka bud’e Mai kofar ya shiga part d’inshi ya nufa direct, “Bayan ya shiga gaba d’aya kayan jikinshi ya cire yasa jallabiya tare da kwanciya bai dad’e ba bacci yayi gaba dashi
Washe gari da safe tunda Granny tayi sallah asuba, ta fito falo ta zauna “wai miskili bai kwana a gida ba Tana jiran ya dawo taji gidan uban wa ya kwana, sai gyangyad’i takeyi, “amma ta’ki tashi tana nan zaune Wai tana jiran miskili, ” a haka bacci ya bingirar da ita a nan Hhhhh, “shi dama bacci barawo ne gashi ya sace granny.
Wajan karfe 10 mum ta fito falo “ganin Granny kwance akan kujera tana ta shakar bacci,abun yaba mum dariya, “tare da fad’in badai a nan ta kwana ba? Har zata tasheta ta fasa dan in Granny ce sai tace ta katse mata bacci, dan haka ta Fasa tare da wucewa kitchen taga mai masu aikinta suke dafa musu, “koda mum ta nufi kitchen “gaidata masu aikin suka farayi cikin girmama a harshen turanci ,”Mum tace an kammala komai kenan?
Suka amsa da yes ma
Fita Mum tayi ta koma falo inda ta Tarar da Granny zaune tana hamma “Mum tace ina kwana mama
Granny tace “lafiya an tashi lafiya?
Mum tace lafiya Alhmdlh.
Granny tace “Ina nan tun dazu ai ina jiran dawowan wannan Yaron, tun jiya bai shigo gida ba, saiya fad’amin inda ya kwana, kallon Mum tayi “tace Wlh kuna bani mamaki ace d’anki bai kwana a gida ba amma ku ko a jikinku, baku ma sani ba, kai Wlh wannan halin naku yana bani mamaki.
Mum dai shuru tayi dan bata da abun fad’a, inma tana dashi bazata iya jayya da Granny ba, tunda Uwar mijinta ce, dole itama ta d’auketa matsayin uwa, “Abu d’aya Mum take ganin za tayi jayayya da Granny shine ace Najeeb ya auri matan data kawo, sai dai in shine yace yana So, shine zanyi shuru.
Granny sai faman fad’a takeyi ta inda take shiga ba tanan take fita ba “ace yaro saurayi ya kwana a waje ba tare da saninku ba, wannan wace irin tarbiya ce? “Haya niyan Granny shine ya tashi Dad Wanda ya fito falon da sauri, ganinshi yasa Granny tace yauwa gwara da kazo
Yanzu d’anku ace ya kwana a waje, amma baku damu ba?
Dad yace mama kiyi hakuri Najeeb ba yaro bane, sannan shida yake wata k’asar da bama ganinshi ma, “Allah ne yake karewa n…..
Dakata dakata Granny ta katse shi da fad’in haka, sannan tace “can daban nan daban, Niko can Ameka din da yake aiki baso nake ba, andai fi karfina ne, saboda y’an Ameka basa ji wlh, suko kunyan taba junansu basayi, kai duniya ta lalace, ku ko tsoro bakwayi ya kwaso irin halin….. Shuru tayi na wani lokaci sannan taci gaba da fad’in “koda yake shi miskili bazai yi wannan iskancin ba, yaushe wannan miskilancin nashi zai Bari ya kula wasu, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya “koya yake k’arewa da abokan aikinsa oho? “Nifa ina ganin an canza shi a Ameka, Inba haka ba taya yaro zai’ki son aure? “daka maganan aure sai yabar gida tun jiya, ” na taba ji ance a Ameka suna canza ma mutum halitta koso kwashe jinin mutum susa Mai wani, Anya basu ma Najeebu haka ba kuwa?
Ba mum ba harta Dad saida maganan Granny ya basu dariya, “su Zarah da surutun Granny ya ishesu suma suka fito, gaida iyayen nasu sukayi “sannan zarah tace Granny Wlh kin hana mutane bacci,.
Granny tace “aikya fad’i haka, kina zaune a gida hankali kwance babu maganan aure, “wai kai audullahi baka ganin girman yaran nan ne, da suke gabanka?
Dad shuru yayi domin yasan abun Granny harda tsufa, koda yake tsufan ne ma, sai anyi hakuri, kwata kwata kwaya nawa Yaran suke? ” yaushe suka taso da Granny zata Fara maganan Ayi musu aure…..
Maganan Granny ne ya dawo da Dad daka duniyar tunanin daya fad’a “inda take cema ibtisam ya hannun?
Ibtisam tace Alhmdlh da sauk’i, “sai dai har yanzu ina jin zafi Sosai “Mum tace sannu yarinyata zai daina a hankali Kinji? Allah ya k’ara sauk’i my dear
Ibtisam ta amsa da Ameen mum, “shima Dad ya mata Allah k’ara sauk’i.
Granny tace ni yunwa nakeji wlh, “shi miskili zai dawo ya tarar dani, “ke Zarah jeki kira yaran da nazo dasu….. Fitowan Najeeb yasa Granny sakan ba’ki “lokaci d’aya kuma tace yaushe ka dawo?
Najeeb daba jin abunda tace yayi ba ya banka Mata harara, tare da gaida iyayenshi cikin harshen Hausa Wanda bai kware ba, “Ina kwanan ku ya furta a gajarce tare da nufa dinning dan yayi breakfast.
Granny tace miskili koda idonka zai fad’o k’asa harshen harara sai kayi aure ja’iri, ke Zarah jeki kira matan nan ya zaba a ciki “Zarah ta amsa da toh tare da tafiya kiransu
Shiko Najeeb abinci ya fara ci, ” Ibtisam dake tsaye ta kalleshi cikin ranta tace mugu azzalumi, wlh abunda kamin saina rama, Koba yanzu ba “shi Najeeb bai masan tana wajan ba dan bata su yake ba, so yake ya koma America danya gaji da wannan tsohuwar Sosai take takura mishi.
Granny nufanshi tayi tana fad’in ja’iri dama ka iya Hausa? “harda wani Ina kwanan ku. “toh Bari kaji Nasan kana jina Wlh ka zabi d’aya cikin matan dana kawo, “koka auresu duka.
Najeeb ko kallonta baiyi ba “ji yayi kaman ya bugeta dan haushi take bashi, shi yanzu a duniya ya yarda ta gama raina mishi wayau, “Toh Inba haka ba taya zata kawo mishi wa Innan Buran tace ya aura, ko Dad d’inshi da yake tsoho balarabiya ya aura, balle shi yaro dashi, wanda yasha nonon balarabiya saita kwaso mishi wa Innan masu Kama da Buran, munana y’an kauye kai wannan tsohuwar ta gama dani, amma zan koya Mata hankali wlh
Granny tace baka jina ne?
Tsaki yaja tare da banka Mata harara, cikin harshen turanci yace “Wlh Granny ki kama kanki da tsufanki tun Kafin inyi miki babu dad’i.
Dad yace kana da hankali kuwa Najeeb? Cikin harshen turanci yake Mai maganan, “yace Uwar tawa kake fad’ama haka?
Yace Dad nifa gaskiya na gaji da halin wannan tsohuwar haba, koku bakwamin abunda takemin haba, gaskiya na gaji, tana gab da kaini bango Wlh, ka Mata warning ta fita harka na, ko a kanta nake da zata takura min? Ta tashi ta kwaso Mata wai in zaba in Aura for god sake ance mata Ina bukata ne, ko me? Ya k’arasa maganan cikin zafin rai
Granny daba jin abunda suke fad’a tayi ba, “tace wai Mai kuke fad’a ne haka? Ku fad’amin inji.
Najeeb tsaki yaja tare da ture plate din dake gabanshi na chips din da yakeci tare da tashi yana k’okarin barin wajan
Cikin fushi Dad yace koma ka zauna, mutumin banza,”zama yayi rai a bace tare da tamke fuska
Granny tace ikon Allah, yau naga dan banzan yaro? Wai Mai yake nufi ne Toh haka?
Zarah ce ta fito,”matan na bayanta duk sun sha kwalliya da ba’kin kwalli, da Jan baki ja sai wani fari suke dan sun hango Najeeb din “ibtisam bata san lokacin data saki dariya ba, da sauri tasa hannu ta toshe bakinta, dan bata san dariyan zai fito ba.
Najeeb kam wani shegen kallo ya watsa ma ibtisam Mai nuna da zan hukunta ki, har yayi k’asa da kanshi ya d’ago da sauri ya kalleta Wanda yaga hannunta an d’aure alaman tayi karaya ko gocewan k’ashi , “har ya bud’e baki zaiyi magana idonshi na kanta lokaci d’aya kuma yayi shuru tare da kawar da kanshi daka kanta.
Granny tace yauwa y’an mata an fito? “Sannunku Sannunku “gaida su Granny y’an matan sukayi.
Dad kam da ranshi ke ce da Najeeb akan abunda yayi ma Granny, lokaci d’aya ya “d’aga kanshi ya kalli y’an matan, da sauri ya zare ido cikin mamakin badai su bane Granny ta Kawo ma Najeeb ba, Tashin hankali.
Granny ta kalli audullahi tace gasu nan saika fad’a mishi ya zaba d’aya.
Dad kam mamaki abun ya bashi, taya Granny zata kawo ma Najeeb wa Innan matan tace ya zaba d’aya daka cikin su… “koda yake may be Najeeb din akwai wacce yake so, domin shi so babu ruwanshi abincin wani guban wani
Kallon Najeeb yayi da fuska ke tamke kaman ba’kin kumurci, “yace Najeeb ga mata nan ka zabi d’aya.
Najeeb da sauri ya kalli dad din nashi, sannan yace “Dad babu wacce tamin a cikinsu, Dad taya kaima zaka biye mata? Gaskiya n…. “Dad ya d’aga mishi hannu alaman ya isa haka
Dad ya kalli Granny yace “mama yace babu wacce tayi mishi, “Granny ta saki tsaki tare da fad’in sauran matan su koma mai Yaron ta tsaya wacce Granny ta kira da Hanne, “Granny Jan hannun zarah tayi ta matsa kusa da Najeeb tana fad’in Zarah Bari inyi mishi magana ki dinga fad’a Mai Kinji? Inya fad’a nima saiki fad’amin mai yace
Ibtisam kam babu abunda take ro’ka sai “Allah yasa Granny tace dole saiya auri matan, tare dayin dariya k’asa k’asa ganin yanda Najeeb din ya tamke fuska rai bace, “tace ai yanzu ka Fara gani, “mara mutunci, mugu, wanda bashi da tausayi
Granny ta taba kafad’an Najeeb cikin sigar rarrashi ta Fara magana kaman haka “Haba Najeebu na Mai Sunan masoyi na, in wa incan basu maka ba, ina son kayi hakuri ka d’aure ka auri wannan Hanne kodan yaranta, mijinta ya rasu ya barta dashi, wlh Abun tausayi, gashi bata da uwa wajan matan babanta take ance tana musguna mata Sosai, ita da wannan marayan yaro abun tausayi, “Najeebu ka taimaka ka aureta ita, da nace duka hud’un zaka aura amma yanzu ka auri wannan kaji dan jika na.
Najeeb daba jinta yake ba, sai kallonta yake, “amma ya Lura tana mishi maganan cikin sigar rarrashi ne
“kallon zarah tayi tace fad’a mishi abunda nace Kinji.
Zarah fara fad’ama Najeeb abunda Granny tace tayi, “lokaci d’aya ya d’aga Kai ya kalli matar da Granny take cewa ya aura yayi,” fuskanta tasha kwalli tayi d’ige d’ige gata kana kallonta Kaga tsohuwa Hhhhh Allah sarki ba tsufa bane wahala ce kawai Najeeb, lokaci d’aya idonshi ya sauka akan yaron wanda akace ya zama babanshi, yaron ba’ki gashi gashi duk ya fige ya kanjame kaman Mai cuta, daka gani dai yaron bashi da wani jini Sosai yanda najeeb ya Lura, ansa mishi irin rigan Fulani duk ta kod’e tayi datti, ko wando babu a jikin yaron
Granny tace Zarah tambayeshi ya amince?
Zarah ta fad’ama Najeeb abunda Granny tace “kiran Dad akayi a waya yabar falon “Bayan Zarah ta fad’ama Najeeb abunda Granny tace
Tsaki yaja tare da tashi yana fad’in kice Mata ban amince ba, ai Tana da yara ta aura musu ita yana fad’in haka ya fita fuuuu “Mum na kiranshi amma bai tsaya ba……
*Gskya naji dad’in yanda kukai min sharhi jiya, one luv kuci gaba da yanda kukayi jiya, nima insha Allah zan dinga kokarin yi muku posting kullum koda ba yawa*
~MARYAM OBAM~