NOVELSUncategorized

SANADIN K’AWA 6

6
Fatima tace “Da gaske da shi xan je” Husnah tace “Ji walakanci, ban gane da shi xa ki je ba, ba ga kaya can na kece raini ba na aro mana” Fatima tace “Toh ni basu min ba tunda ba biki xan je ba, I prefer wearing my hijab” Husnah da ta saki baki tana kallonta tace “Tabdi, amma wllh baki da hankali Fatima….”
Fatima tace “Na ji” daga haka ta ta shiga gidansu Nafisa, Nafisa dake wanke wanke ta taso da sauri tace “Lah, Fatima kece gidanmu yau” Fatima tace “Eh mana tunda ke baxa ki xo ba” Nafisah tace “Allah sarki ba haka bane Fatima, har yanxu jikin Umma sai a hankali kinga ko islamiyya ma bana xuwa yanxu” Fatima tace “Ayya, wllh ban sani ba da na xo gaisheta, kuma ko shekaranjiya sai da Ammi ta tambayeni jikinta nace da sauki” Nafisa tace “Ai kam sai dai a gode Allah, daga ina ku ke haka” Fatima ta kalli Husnah da ta nemi kujerar tsugunne ta xauna tace “Daga gida mana” Nafisah ta kalli Husnah ita ma tace “Sannu Asma’u ya su inna” bbu yabo bbu fallasa tace “Alhmdllh” Fatima ba ta da kawar da ta wuce Nafisah a da, tun da suka hadu da Husnah a bikin wata kawarsu Husnah ta nace mata har suka fara kawance Wanda lkci daya Husnah tayi nasarar kusan raba ta da Nafisah don a dalilin Husnah sai da suka yi fada da Nafisah sbda yawan bata shawara da take kan tarayyarsu da Husnah ganin bata da kamun kai, Nafisah yarinya ce me hankali da natsuwa, sosai Ammi ke son alakarsu da Fatima, sai dai tunda Fatima suka hadu da Husnah kawancensu ya ja baya sosai da Nafisah a cewarta Husnah ta fita wayewa, Husnah da ta daure fuska ta mike tace “Kinga fa yamma nayi Fatima tunda ke baxa ki canxa kayan ba ni bari in canja mu wuce” Nafisah tace “Ina xa ku?” Da sauri Husnah ta karbe tace “Xumunci” Nafisah bata ce komai ba, Husnah ta shiga dakinsu Nafisar rike da ledan kayan da ta karba hannun Fatima, fatima ta mike ta bi ta ta shiga dakin shiga don kara gyara fuskarta, Tsaye Nafisah tayi bakin kofa tana ta kallon su ganin uban kwalliyar da Husnah take da shegen kayan da ta saka, tuni fatima ma ta gyara fuskarta ta xauna tana kallon Husnah har ta gama sannan suka fito tana kallon Nafisah da ta kasa daina kallonsu tace “Anguwa xa mu je sai mun dawo Nafee” Shiru Nafisah tayi, can ta ce “Ohk shigo mu d’an yi magana fatima” Husnah ta bi Nafisah da harara, Fatima ta bi Nafeesar suka koma dakinsu, Nafisah na kallonta da damuwa tace “Ina xa ku fatima?” Fatima ta yi dariya tace “Ke ba ko ina fa xa mu ba, gidan wata kawarta xa mu” Nafisah tayi shiru, can tace “Toh shkkn, amma ki dai kula pls kinji” Fatima tayi ‘yar dariya tace “Toh  Ammi” daga haka tayi ficewarta tana cewa “Sai mun yi waya” a bakin soro ta tarda Husnah tana cika tana batsewa, tana dariya ta ja ta suka bar gidan, masifa Husnah ta dinga yi tana xagin Nafeesah har suka isa bakin titi, a nan Fatima ta kira Elbash, ya katse ya kirata, tana dagawa ta sa a handsfree tace “Yanxu. xan fito” yace “Ohk don’t stress ur self send the address of where you want our driver to come and pick you” tace “Ohk” daga haka ta katse kiran, tana xaro ido tace “Ke ina na sani a Abuja da xan tsaya driver ya xo ya daukeni” Husnah ta kwace wayar tace “Bari in sa address din gidansu Sadiya” hakan tayi bayan ta tura suka hau mota xuwa cikin garin Abuja, tun basu karasa gun ba wani number ya Kirasu yace Elbash ne ya turo sa ya daukesu kuma ya kusa address din da ya basa, Fatima tace “Alryt sai ka iso” cikin sa’a suka isa dai dai gun kafin shi ya karaso, Husnah tace “Ke kirasa kice a bakin titi xai jira kar ya karaso nan ya gan mu a tsaye” da sauri Fatima ta kirasa ta sanar da shi abinda Husnah tace, yace “Ai ina bakin titin ma yanxu haka” tace “Toh jira yanxu xan taho” daga haka ta katse wayar, da kafa suka karasa har bakin titin, ta kuma kiransa yyi mata describing din irin motar da ya xo da shi, Fatima da ta hango mota irin Wanda yyi describing din mata ta katse wayar sannan ta nufi motar Husnah na biye da ita, kallon mutumin dake cikin motar kawai take tana mamakin wai driver cos he didn’t look like one, kallo daya yyi masu ya dauke kai tace “Da kai muka gama waya?” Ya kuma kallonsu yace “Eh ni ne Wanda Dr ya turo in yi picking din ki” Tace “Ohk” ya kalli Husnah yace “Wacece ma a cikin ku tukunna?” Tace “Ni ce” ya kalli Husnah da ke wani yauki yace “Ohk mutum daya yyi instructing dina in dauka so ban san ko ya xa ki da kawar nan ta ki ba” da sauri tace “Noo tare muke kuma rakani xata yi” ya girgixa kai yace “Kin taba ganin inda yaro ya tsallake maganar uban gidansa” Rasa abun cewa Fatima tayi mamaki ya cikata, can ta kalli Husnah da ta marairace, Husnah tace “Amma bawan Allah aminiyar ta ce ni fa, ka kirasa ka kara masa bayani rakata kawai xan yi ko da baxan shiga ciki ba” Yace “Ba umarnin da ya ban ba kenan, sai dai ta kirasa ita ta gaya masa” Fatima ta hade rai tayi dialing numbersa ya katse ya kirata, tana dagawa ta sa a handsfree tace “Hey, am coming over with my frnd fah, and….” Katse ta yyi saurin yi yace “Nop that was nt our deal, beside I didn’t tell my family u are coming with a frnd” kasa cewa komai tayi, Husnah da kiris ya rage hawaye ya xubo idonta tace “But I am her frnd fa wllh” yace “I didn’t announce she’s coming with a frnd to my mum with siblings” Fatima ta ja tsaki kafin tace komai ya katse wayarsa, Ta mayar da wayar jaka tana kallon Husnah tace “Mu wuce gida….” Da sauri Husnah tace “Gida kuma” Fatima tace “Yeah I am nt going anymore” Jan ta Husnah tayi da sauri xuwa gefe tace “Ka ji sha sha sha xata tona mana asiri, ke baki ga irin motar da aka xo daukar ki cikinsa ba, bbu xancen mu koma gida, kawai shiga ku wuce ni na hakura xan shiga gidansu Sadiya in jira ki, amma ki min alkawarin komai kika samo raba dai dai xa mu yi baxa ki boye min ba” Fatima tayi shiru tana kallon ta, Husnah ta kwantar da murya tace “Don’t say no plss besty this is d only opportunity we have wllh, in dai ni ne na hakura wllh kije” daga haka ta ja hannunta xuwa gun motar tana kallon Wanda ke xaune maxaunin driver tace “Toh shkkn Allah kiyaye hanya, she will go alone tunda bai son in bi ta” daga haka ta ja Fatima xuwa front seat ta bude mata ta sa ta shiga ta rufe motar tana kara lekan motar, Driver ya ja motar Husnah ta dinga daga ma Fatima hannu tana murmushi, Fatima dai bata ce komai ba amma banda faduwa bbu abinda gabanta ke yi har suka yi nisa daga inda Husnah take. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi Fatima ta kalli drivern a karo na farko tace “Wai ba mu isa gidan bane har yanxu?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Eh” wayar drivern ne yyi ring ya daga ya kai kunne, yes kadai ne abinda ya dinga cewa har ya katse wayar, ganin sun kara tafiyar kusan minti goma tace “Ka ga in har haka gidan yake da nisa naga yamma ya fara yi kawai drop me let me be going back home” yace “Mun kusa daga nan bai fi tafiyar minti biyar ba xuwa gidan” bata kuma cewa komai ba, sai bayan wani minti goman suka shiga wani layi, tun dai tana kirga kwanan da suke sha har ta gaji ta hakura, kana ganin anguwannin kai kasan sai wane da wane, ko ina tsit sai haushin karnuka a wasu gidajen, ta rasa me yasa xuciyarta ke bugawa gashi ta kasa tsayar da takamaiman addu’a a xuciyarta, gaban wani ubansun gida yyi horn bbu bata lkci aka bude katon gate din drivern ya ja motar bai xame ko ina ba sai parking space, ya bude motar bayan yyi parking ya fito, a hankali ita ma ta bude ta fito tana kare ma kantamemen gidan kallo, can ta kalli Wanda ya bude gate din, ko Kadan bai mata kama da mai gadi ba, Drivern yace “Mu je” bin bayansa tayi kamar me tsoron taka kasa har suka isa main parlor din gidan, bbu kowa parlorn sai sanyi Ac da karar sa hatta TV a kashe yake, cool scent ne ke tashi a parlorn, ya nuna mata kujera ya wuce sama, bayan wasu mintuna ya sakko kasa ya nufi kofa xai fita ta mike da sauri tace “Wait, am I to sit here all day?” Ba tare da ya juyo ba yace “They are coming” daga haka yyi ficewarsa ya ja kofar, kasa xama tayi duk gabanta ya ki daina bugawa, ta kalli agogo taga har karfe biyar, lkci daya kawai ta yanke shawarar ita ma ta fita kawai bata kai ga aikata hakan ba taji taku stairs ta juya da sauri, idonta ya sauka kan fararen kafafuwansa don da alamar 3qtr ne jikinsa, ta kasa daga kai ta kallesa tayi saurin dauke kai xuciyarta na mugun bugu, tuni kamshin turarensa ya gauraye ko ina na parlorn, duk yanda ta so juyowa ta direction dinsa kasawa tayi har lkcn kofa kawai take kallo, kawai ganinsa tayi tsaye gabanta suka yi ido hudu, kaii Ashe photo bai masa adalci ba don ba ainahin kyansa yake fitarwa ba, this is just d definition of Handsome keenly yake kallonta kamar me examining din abu a tare da ita, da sauri ta juya cikin sarkewar murya tace “Ur… family members?” Bata Ankara ba sai ji tayi ya juyo ta xaro ido a rikice tace “What???” Ya d’an cije lips dinsa yana mata wani kallo daga sama har kasa yace “Fatima Muhd, the daughter of the former minister of education right?” Ta hadiye wani abu da kyar ta girgixs masa kai ba tare da ta san tayi hakan ba tace “Nop, I lied about that” wara ido yyi yace “Really?” Ta gyada kai, wani murmushi yyi yace “Amazing” cikin rawar murya tace “Ur family members pls, I want to apologize and leave it’s getting 

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


late….” Juyawa taga yyi yana yar dariya, ji tayi komai nata ya tsaya, lkci daya taji sanyi na shigarta, bata yi wani tunani ba ta nufi kofa da sauri ta murda handle ta ji sa a rufe, still tayi a wajen ta juyo a hankali tana kallon sa xuciyarta na bugawa, murmushi taga yana yi yana kallonta, ta fara girgixa masa kai cikin tashin hankali, kamar an tuna mata wayar hannunta ta daga da sauri ta shiga kkrin dialing number, taku hudu ya iso inda take ya warce wayar tana kallo ya kashe sannan ya karasa kan kujera ya jefar, sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, na shiga uku don Allah don annabi ka rufa min asiri am begging u in d name of God” tana magana tana jijjiga handle din kofar, ji tayi ya fixgota har sai da suka yi karo tana jiyo saukar numfashinsa fuskarta, tsayar da kukan da take tayi lkci daya ta sauke masa mari fuskarta daure tana huci.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button