NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 22

???? *WA ZAI FURTA?*????
              2⃣2⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

????????????????????  *RUKAYYA  BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*????????????.


*Wannan page din na sadaukar dashi ga dukkan masoyan wazai furta*????????
Shi yasa yau na saki biyu don kuji dadi farincikin ku shine nawa wallahi.???????? Ina son ku???????????? kullum sai nayi kukan dadi.

        **************
*ABUJA NIGERIA*

…….. Ya tallabo bayanta ta dawo ta tsaya dai dai Amma ta kasa yarda su hada ido, *INA SON KI BILKISU* Yau na *FURTA* Abinda kike son ji….. Ta Kara kasa da Kai jikinta har lokacin bai daina kyarma ba….Wai mafarki takeyi ko kuwa da gaske ne?
   Ya rungumota ta sunne Kai jikinsa…. Ya Kara Rada Mata… *ina son ki* tsikar jikinta ta tashi Yarrrr….. Duk wannan haukan da Kika ga inayi sonki nakeyi, Shi yasa na kasa boye kishina gareki…… Nasan kin fahimta Yanzu Kuma kin Sami amsar fadawa su daddy ko?
 Ya dago fuskarta….ta koma da sauri…. Ya kyalkyace da dariya yau Kuma jikina ake son Hawa?
  Kin wahalar damu da yawa, kina kawo rigima kullum because you want me to say it…. Ni nasan kina Sona I knew it…Kuma ko Baki furta ba nasan kina Sona wallahi……. Ki daga ni na tafi… Ya fada Yana dariya.
  Kinga duk laifin ki ne, da kinsan zakiji kunya da hakuri kikayi muka tafi a Haka bakiji komai ba….. Ta zame a hankali ya mayar da ita da sauri, kafin ki gudu Dan Allah gobe kada ki Sanya mun hijab din nan kuma kiyi mun girki da kanki Zan zo around 10:00am kinji ko?
    Ki ce b lefe na kawo ba, hasafi ne saboda Ina son ki…. Ta zame yayi saurin rike hannun ta ki jira na Baki kudin dinki Mana ….. Ka barshi nidai… Bakya so?
Ta daga Kai….. Da gaske bakya so?
Um, tace a hankali.
Yayi Yar dariya kudin ke Baki so ko Ni?
Kudin ta fada tana sim sim da Kai.
Yayi murmushi Ni kina Sona Kenan?
Ta yi alamar fizge hannunta…. Ya rike gamm. Kice inji Mana kina Sona?
Ta yi kasa da Kai ji takeyi kamar ta bude kasa ta shige ta huta.. …ya Kara dariya sosai ohh ni Anwar Ashe akwai ranar da bakin nan zai mutu?
Ai Dana San wannan kalmar ce zata sa in Sami saukin tsiwa da tuni na Gaya Miki saboda na Dade Ina dakonta…….
   Idan daddy ya Baki zabin auren mu kice kinfi so ayi kafin mu Gama school……. Lokacin ne ta banka mishi harara da sauri ta kawar da Kai.
Ya Kama dariya ya figi hannunta zo kiyi mun rakiya naga alamar nema kikeyi ki gudu ciki ko?
Ta biyoshi a hankali yasa hannu ya fiddo rafar kudi ya ajiye hannun kujera idan kin shigo ki wuce dasu na dinki ne….na gode. Ta fada a hankali. Tayi murmushi ya ce my pleasure dear.
Ta Dan harareshi ya tuntsure da dariya shin na Riga na *FURTA* ai to boye boye name?.
   Suka fito tayi saurin fizge hannunta ya Kama murmushi Yana  fadin ke dai Yar kauye ce…… Allah yayi?
Sadeeq ya taresu.
  Allah yayi sadeeq yau kwana ta saka ni sai da na *FURTA* Ina son ta…… Sadeeq ya you firgigi ya ce waoooh *Anzo wurin kenan*…. Duk suka bushe da dariya ita ko sai murmushi takeyi kasa kasa…… Munafuki ai duk Kaine tun farko kayi ta wahalar da ita… Shin ai nadai FURTA gobe Zan dawo *Zance* ya bangajeta da kafada ko Bilkisu???
Ta galla mishi harara suka kwashe da dariya…..
   Kiyi mun tuwo goben…. Ya shiga mota tana tsaye har suka fice gate din….
      Wai da gaske ka furta kana sonta?
Wallahi kuwa, sadeeq rigimar Bilkisu bana iya daukar ta, ta tsareni lallai sai tasan wanene Ni…… Saboda me zaka boye Mata Wai?
Ai na fada…. Amma fadar sai ta tsorata Kuma. Na rasa me take so, Kuma Wai ita ya zata fada a gida wace amsa zata bawa su daddy….na ce kice *Ina son ki* saura kadan tayi penting …..suka bushe da dariya…… Amma ka Mata gatsal! To ya zanyi da ita? Kaga yanda ta nemi ta firgice mun?
   Banza finally ka furta dai.
Yayi dariya *Anwar ya furta* naji tsoro yarinyar Ina son ta saboda class wallahi…..gidan sa dake *Minister’s hill* suka nufa.
   Mommy….. Mommy ta Fara kwada Mata Kira tana Hawa sama.
  Tana faman shirya jaka ta shigo dakin, mommy Anwar fa ya kawo Kaya da yawa ….. Wane irin Kaya?
Ina daddy?
Sunje sallah kasa.
Wane irin Kaya ne ya kawo.
Jikunkuna ne set hudu…. Ta kalleta da sauri jakunkuna? Na menene????
Ta sunkuyar da Kai ta sunga Mata kudi Kinga Wai su Kuma nayi dinki…… Duk Akan me?
 Ta Kara kasa da Kai, ya ce tsaraba ce ya kawo mun…. Saboda???…… Ta Kara katseta da sauri.
  Ya ce Yana Sona ne???
    Muje naga kayan, bazaki ce mishi daddyn ki ya hana karbar kaya ba?
Wallahi duk abinda na kokari in sanar dashi bai yarda mommy.
   Wohohoho ta fada tare da rabka salati…… Amma kin San daddyn ki zaiyi fada ko?
Mommy Anwar Shi ne *Hamza bushara*….. Mun sani. Ta ce a takaice ta zaro ido Kun sani mommy?
Yes, ta fada tare da wucewa tana fadin jekiyi sallah nasan fada ne yau duk sai mun Sha ni da ke…..
    Ta falon ya shigo Yana ganin kayan ya kwala ma Bilkisu Kira.
Ta fito da gudu gudu…..

    Wadannan kayan fa? Ta sunkuyar da Kai, Anwar ne ya kawo  su daddy.
Na menene?
Ya ce tsaraba ce kada yazo hannu biyu….
Saboda me?
Tayi jimmmmm kafin ta ce *Wai Yana Sona ne* yanayin yanda ta Fadi maganar kamar Yar koyo mommy ta shigo ya kalleta Kinga Kaya?
Hada kudi….
Ya kalli Bilkisu ke kina sonsa?
Tayi shiruuuu kinji mamana kina son sa?
Tayi kasa da Kai kawai…. Yayi murmushi kina son sa kenan.
Ki mayar mishi da su kice bana karbar irin wannan kyautar idan har da gaske yakeyi ya turo iyayensa…. Ta dora hannu saman Kai…. Daddy bayar Dani zakayi haka da wuri ta kurma ihu tana kuka.
  Ya yi Yar dariya, to tunda kin Sami Wanda kike so me ake jira….. Nidai kada a turo…ke bama son rashin wayo.
Turowar an fada Miki Yana nufin za’ayi Aure?
  Hakan zai nuna idan da gaske yakeyi sai a ajiye magana.
Ta danyi shiru alamar ta gamsu.
     Ya wuce Yana girgiza Kai Yana  murmushi,
  Mommy ta kalleta tana hararar ta, wannan koke koken ba komai zai janyo Miki ba sai raini wurin Miji. Komai ke sai ki bare Baki saboda kina ruwa ruwa…. Mtsew ta ja tsoki.
   Wannan rawar Kan da Anwar keyi inba auren ba meye zai kamance ku?…. Mommy..
Yi min shiru, Ina ce Nan Kika diririce Kika firgice saboda yayi fushi da ke ko?
Ta zumburo Baki kaiii mommy……. Ke arrr kilibabba.
 Ta wuce , ta Mike ta bita da gudu mommy yace zai zo gobe by 10… Sai kije ki fadawa su Rahina don su shirya mishi kin dai San ba Mai sauko Dani da safe ko? 
  Mommy cewa yayi ni Zan girka baya son nashi…… Sai kawai tayi dariya tace yaron nan hooo.
To ya kyauta ma kansa sai kiyi asubanci saboda na sanki da shegiyar nawa da duminiya, Bilkisu za a Fara wa miji hidima….. Kai mommy ta bita tana shagwaba….
   Ta kyalkyace da dariya. Ai munji dadin zuwan sa saboda kullum daddynki cikin waya yakeyi Yana jiyo labarin badakalar ku…..kamar ya mommy??
Tayi Yar dariya akwai wadanda kebin movement dinku kullum…… Ta zaro ido yasan Anwar na zuwa gurina mommy???
Tayi murmushi har ciwon cikin da kikayi ya je har cikin dakin ki,sannan ya balla Miki kofa…. Ta zare ido na shiga uku na… Ke dakata, tunda bai nuna Miki ba wallahi kada ki nuna kin sani Babu ruwana…. Cikinta yayi kulululu ta hadiye miyau kut!.
   Mommy Dan Allah laifina ne? An fada mishi Nima bana son haka ko?
 Ina Jin abinda yayi saving din ki kenan….
Ta saki ajiyar zuciya kaiii Anwar case ne.
     Ko bude kayan basuyi ba yanda suka ajiye haka aka barsu a wurin.
   
*WASHE GARI*

   Karfe bakwai tana kitchen, daddy ya fito zai je office ya leka… Bilkisu a bani abinda ya sauka na jiyo kamshi ko Anwar din kawai keda shagalin?… Ya karasa maganar Yana murmushi.
Kaiii daddy ta fada cikin Jin kunya….
Har ciki ya shiga Rahina nata fere dankali, saratu na grating kwakwa, ya kallesu yau aiki ya karu ko?
  Iyye hada kaza haka?
 Ya bude oven…. Ta rufe fuska lallai yarinyar ashe catering school din bai tashi a banza ba…
   Menene can?
Wipping cream daddy… Zakiyi cake ne?
Na Gama gashi can ma…. Ya sa hannu ya dauki daya ya Kai Baki….. Um um..ya naji wannan kamar ba irin Wanda ake Mana ba?…… Kai daddy ta Kara fada yayi dariya….
  Mommy ta shigo ga break din can fa…. Zo kiga sonkai Bilkisu na hadawa Anwar gara ba irin ….. Kai daddy… Eh Mana.
 Ta matso iyyeh lallai Shi yasa baji gida ya Fara daukar harami…. Ta bude tukunya.. hada Kan rago?……
Kai Kai Kai daukon kwano Shi zata zuba mun ja’ira….. Duk suka kama dariya.
 Rayuwa irin ta gidan su Bilkisu tana da ban sha’awa……mommy ta kalli Rahina, yau taku ta sameku ko?…. Abinda na fada Yanzu kenan…. Daddy ku je falo Zan kawo muku nidai… Duk suka kwashe da dariya… Mommy tace komai Zaki debo Mana ko sai ankai wa Anwar din nazo na ce Zan Dauka….. Kaiii mommy Wai ya Zan ce baza ku ci ba ????
Suka fita suna dariya hannun daddy rike da cup cake Yana gutsira…
Ya kalli mommy in shaa Allah tarbiyyar da muka ba Bilkisu bazai taba Sanya muyi Dana sani ba…. In shaa Allah.
Ina ta fada akan catering school din nan Kika dage Kinga Yanzu amfanin yazo ko?
Ai na fada ma Kuma wallahi cewa yayi nata yakeso baya son na Yan aiki kaga Idan Bata iya ba zai aureta Yana sonta Amma can gaba matsalar dole ta taso…. Yaron Yana da rawar Kai akan Bilkisu hakan na bani tsoro, ya kasa danne feelings dinsa kin lura ko?
  Hada yarinta ke damunsa….. Yes da giyar kudi. 
Yama arzikin sa kankanta kawai hankali da natsuwa yaron ke bani sha’awa…da kunya Kuma….yes Yana da kunya of course.
   Bilkisu ta shiryo musu komai a tray ta kawo Yana Shan Lipton da biscuit….daddy biscuit Kuma???
 To wancen kwalayen biscuits idan bama ci ya zamuyi dashi na ce ku rabar Kun jibgesu…. Dasu mommy zata tafi sokoto ne na dibar Mana namu Yana store… Ohhh ban sani ba … Ta ajiye ta koma.
   Ya bita da ido, abinda ke tayar mun da hankali shine yanda yake son ringa nuna Mata komai da karfin tsiya….. Gaskiya fa.
  Yanzu idan ya turo iyayen zuwa taushe zaka ce su kawo kayan baiko?
  Eh, ki Bari zuwa dare zamu maganar kiji yanda na tsara lamarin…..
   Karfe takwas ya fita office mommy Kuma ta Haye sama domin komawa barci.
  Sauri sauri suka karasa aikin , goma saura kwata an shirya komai ta fada wanka.
  Ta fiddo Kaya sunfi ashirin ta rasa wane zata saka?
  Tabbas Bata son ta saka matsattsu tunda ya tilasta gyale zata saka.
  Da kyar ta dauko wata doguwar riga bubu na boyel peach an mishi kwalliya da *Stones* blue. Dinkin ya bude sosai, ta yi simple kwalliya ta shafa light pink na lipstick….. Rahina ta kwankwasa Mata kofa… Aunty kizo.
  Inji waye? Ta fada tana gyara lagen gyalen… Uncle Anwar ne gashi can na bude mishi falo…. Ki ce Ina zuwa..
   Ta Kara feffesa turaruka a jiki…. Ta juya ta Kara juyawa a madubi sai Kuma ta danji kunya tayi murmushi ta fita tana takawa dai dai cikin plat shoe light blue kalar gyalen.
  Tana bude kofa sai kawai ta kwashe da dariya ganin sa bisa dining table Ya Fara cin abinci…. Na shiga uku Kai baka bakunta ne Wai??????
   Ya kyalkyace da dariya inayi Mana gashi ni nake zubawa kaina? Idan bana bakunta ai zanje ciki na Kira ki zuban ….. Ta galla mishi harara Kai baka da aiki sai ci….. To ai yunwa ba kanwar ubana bace ko?
 Ta kyalkyace da dariya ya akayi Kika San Ina son kan rago?
Ta ce hmm, ya lunkuma harshe a Baki Yana um…um…um please budan can menene?
  …… Wai Kai baka ko irin Jan ajin Nan?
  Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Zaki Sanya na kware wallahi.
   Daukon lemu Mai sanyi ni bana Shan tea wannan sai ku Yan gayu….. Ta Kara hararar sa…. Ya kamata na Sanya wa hararar nan doka duk lokacin da kikayi ta ……
Ta Mike kawai ta Isa inda fridge ta bude wane kala Zan kawo maka?…. Peach daukon peach dinnan Amma fa roba biyu Ni daya bata Isa ta…. Ta Kara dariya ohh Allah gamu gareka….
   Ya Miko Mata chips da egg Fara ci Nim zanci irinsa….. Kana da cikin Zane ne?
Yayi murmushi Amma kajin nan dasu Zan tafi fa don sai dare Zan dawo…. Zaka dawo Ina?
Anan…. Ya fada Yana kallonta.. ke na dawo Abuja fa sai an koma school nida Kano……ta zaro ido duk kana me?
Ya nutsar da idonsa cikin nata yace duk Ina zuwa Ina ganin ki… Tayi kasa da Kai tana murmushi…..
 Kill babba abinda kike son ji kenan ko?
  Tun karfe nawa Kika tashi yau?
Ta Dan zumburo Baki ban koma barci ba tun asubah….. Nima haka ya fada Yana murmushi. Ta harareshi kana meye?
Ina kallon agogo na kagara 10 tayi kamar na Miki waya na ce na mayar dashi eight….. Ta yi Yar dariya yabi kuncinta da kallo….. Kinyi kyau sosai fa.
Ta ce hmmm.
Ni na yi kyau? Sabbin Kaya na dunka saboda zuwa Nan fa…. Ta kyalkyace da dariya Kai na bani yau to me nace?
Ya Dan Sha mur naga kamar Baki fahimci hakan ba…. mtsew ta ja guntun tsoki.
  Yayi Yar dariya ya Mike Yana goge baki da tissue taso idan bazakiji ba muyi magana ba dadewa zanyi ba Zan barki kiyi barci sai na dawo da dare ko? Ya na maganar Yana tafiya tare da janyo hannunta….. Ohh Shi baya Jin komai ya Kai hannu ya tabani ni Bilkisu??.
  Ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita…. Ya akayi Kika bar kayan can anan? Daddy yace ki mayar mun?
Ta daga Kai alamar eh,
 Kin fada mishi in sonki?
Nan ma ta daga Kai?
Duk da haka bai karbi kyautar ba?
Ta ce eh,
Sunyi yawa?
Eh,
Yayi murmushi to Yanzu me yace?
 Ta yi kasa da Kai yace ka turo iyayen ayi magana…. Ihu ya daka kawai sai ya Mike tsaye ya janyota ya Bata wani hot hug.
Ta zame ahankali ta zauna tana murmushi……. Dan Allah kizo na you hugging dinki…
 Ta galla mishi harara ya zauna Yana dariya *Amma fa nazo da sa’a* …….kawai ta jiyo motar daddy alamar ya dawo…. Gama daddy Nan ya dawo…. Gooood ya fada tashi kije kice Ina son magana dashi…..
 Ta zaro ido…. Meye zaka fada mishi?
Zan rokeshi yabar Miki kyautar nan bazan koma da ita ba…. Kai Anwar daddy fa baya son gardama…. Haba? 
  Allah.
Yayi murmushi jeki ce Ina magana…… Tashi kada ya shiga ciki please…. Ya mikar da ita…
  Yana kokarin shiga ta fito daddy ka Kuma dawo? ….. Bilkisu kice ma Anwar securities din nan ya Basu damar Zama Mana tsayuwa ai babu dadi ko?…… Shine yace Wai zaiyi magana da Kai…. Ya kalleta da sauri Yanzu?
Eh, okay Zan biyo ta Nan Ina sauri ne nayi mantuwa….. 
  Police din da suka rako Shi suka bude mishi kofa ya shiga ta dayar kofar.
  Ta dawo, yace na fito?
No. Zai biyo ta…. Ya banko kofa Anwar lafiya dai ko? Ana jirana office…. Da sauri ya sauka kujera ya zukunna…. Yayi saurin Mika mishi hannu taso inji menene???? Ya rike hannun sukayi hanyar fita…. Ya Kara kallonsa menene?
  Ya kasa magana kunya duk ta kamashi…. Ya tsaya chak ya fuskance Shi…Anwar!
Ya Dan rusuna daddy Dan Allah abar Mata kayan bana son na koma dasu….. Ya kura mishi ido… Amma kasan sunyi yawa ko?
  Ayi hakuri Zan kiyaye next time Amma now abar Mata don Allah.
  Ya Kara kallonsa sosai sai Kuma yayi murmushi… Shikenan Amma bana so ka daina kaji ko?
  Ya rusuna na gode Allah ya Kara lafiya da shekaru masu albarka…… Aminnnmm ya Rabbi.
Ta fada maka nace ka Aiko?
Ya Kara sunkuyar da Kai In shaa Allah zasu zo gobe… Yayi dariya
 gobe yayi sauri zuwa asabar dai ko?
 Ya noke Yana murmushi…. Shikenan sai na dawo ana jirana ……
      Ya dawo Yana murmushi tana zaune…..ya karasa Yana fadin yace ki dauki kayan shikenan ko?
 Ta kalleshi da sauri.
Yayi dariya rokonsa nayi, ya Kuma amince … Ta ce hmmm. 
Na ce mishi Zan turo gobe yace sai zuwa asabar….
Ta ce hmmm kawai… Yanzu Kinga Ina da hujjar cin uban Suleiman ko?
  Ta zaro ido…. Dan Allah ka bar maganar sa, Zan fada mishi an Mana baiko…… Ban yafe ba Kika Kuma magana dashi ….. Ta zaro ido..lallai idan aka koma school akwai chakwakiya.
  Ya Mike Zan tafi sai na dawo anjima kinji ko?
Ta ce toh itama ta mike, daukon kazar da wancen cake din dasu Zan tafi.
  Ta sungumo mishi suka jera ya fizge gyalen tare da shafa gashin ta yaja…. Nayi sa’a fa domin Ina son yalo yalon gashi….. Rufen gashi ko na saki kayan Nan su zube… Da kin sake wasu wallahi.
Ya Kara shafa gashin Yana murmushi sannan ya mayar Mata da gyalen… Ta banka mishi harara… Kana da matsala wallahi hakan haramun ne… Astagfirullah na daina.
 Ya fada Yana dariya…

      Yana tafiya ta saki ajiyar zuciya tace kaiii Anwar case ne.
  Ita da mommy suka bude jakunan….  Tsoro yasa suka mayar suka rufe….. Ta kalli Bilkisu yaron nan sai ya kusa haukata ki idan kukayi Aure…
   Tayi jimmm… Kawai.
Tare da Sadeeq ya dawo….. Tana shigowa yace koma ki sako hijab……..
Ikon Allah sadeeq ya fada tayi saurin juyawa…. Banza wallahi kwakwa ke kawo ka marar zuciya….. Naji kome zaka ce kai ne ka jawo ni dole na biyoka kuma na gama zaman zuruu…… Ya yi murmushi.
   Abinda Zan Rama?? Kai kishin naka ma da bashi da aji….. Ya Kara kyalkyace wa da dariya, kishin har akwai Mai aji?
Ya mishi banza…..
Ta dawo rike da mango juice a cups..
…. Bilkisu kinji sadeeq Wai kishina baida aji kin yarda?
  Ta ce hmm, kawai ya Miko Mata sim card ungo Ciro mun layinki…. Ta zaro ido…
Yasha mur yes dole ki canza layi ….. Dashi fa nake jin alert….wane bank ne?
Access bank. Ta fada cikin fushi.
 A nan Kika bude account din ko sokoto?
 Ta bishi da kallo…. Anan Abuja… Kawai ya dauki waya…hello , yes nine lafiya.
  Zan turo ma wani account number please ayi blocking din sa zamu bude sabo amayar da komai can…. I don’t know buh I’ll ask her…
Ya kashe meye account number din???
Sadeeq kaga rigimar da Anwar ya kunno ko?
Ya danyi murmushi zamanki lafiya ki canza don tabbas kishin wannan zai janyo ma bank din matsala….. Tayi zugummm….
  Ya figi wayar kawo na canza Miki….. Zan dauki no. Su Aisha…. Zan saka Miki duk no.s din kawayenki Mata Amma wallahi Kika yi saving maza sai……… Kana ganin Ina kula maza ne… Ta fada a hasale…. Ya dalla Mata harara su ai suna kulaki ko?
Ta Bata rai…. Sadeeq ya jiyo zaku Fara ko?
Hakuri zakiyi dashi fa halin sa ne ba yarda Kika iya… Ni bana son wannan zargin da yake mun… Na daina ya hakuri shikenan ko?
   Tayi shiru. I’m sorry please. Shikenan ta fada tana hararar sa.
 Yayi Yar dariya…..
Firar rigima rigima soyayya soyayya don ma sadeeq nasa Baki idan sun nemi rikicewa…..
  Ya ce zai tafi Kano gobe zai dawo asabar Amma sai dare zai shigo bayan Baki sun tafi.
  Ta masu rakiya ya hanata karasawa waje ya ce ta koma kawai….

   Daddy ya buga ma kanen sa sokoto cewar yazo don su tarbi Baki, ya Kira yayan mommy da aminan sa biyu ministers.
  An shirya gaggarumar tarba.
Misalin karfe Sha biyu suka karaso.
  Abin mamaki ba kudi kawai suka kawo na neman Aure ba hada halawa da goro da biscuits.
    Bayan an gama gaisawa aka ci abinci aka Kara gaggaisawa kowa ya gabatar da kansa, iyayen Anwar biyu ne daya kanen maman sa daya Kuma aminin mahaifinsa ne sai wasu dangin babansa daga kauye saboda baya son da yawa asan abinda yake ciki kamar yanda Hajiya ta gargadeshi.  Daddy na gefe kanin sa ya Fara magana….
  Alhamdulillah munji dadin kasancewa daku ayau ya Allah yasa wannan yaza alkhairi garemu Baki daya….
   Mune da jin dadi hakika Hamza ya kawo mu gida na mutunci masu karamci Alalh yasa wannan yarinya tayi Hali irin na iyayenta….duk aka amsa da aminnn.
  Ga Kaya mun kawo na neman Aure da kudi dubu dari biyu ya Allah yasa muga ranar da zamu taru haka da sunan dauruwar auren su, aka ce ammmmeeenn…… Alhamdulillah daddy ya katse Shi.
  Duk aka kalleshi… Da sauri.
Kamar yanda na yanke shawara nida mahaifiyar yarinyar Nan da dangin mu, Ina ga a wannan haduwar mun Isa mu shaida Aure saboda haka na yanke shawarar wadannan kudin zamu karbe su matsayin sadaki goron Kuma aba kowa ya shaida Amma bisa ga sharadi..

 Bana son yaran nan su San Haka har sai bayan sun kammala karatu tukun….
Masha Allah Masha Allah duk falon ya dauka nan da Nan aka  Fara Shirin daurin

 Aure kowa ya bada wakili….. Cikin mintuna da basufi ashirin ba aka ce faaaaatiiihaaaa…..????✍????

*Zainab Dahiru wowo*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button