GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
01&02
“Ranki ya dade, gimbiya Hakima, Fulani tayi aike, tace tana son magana dake, “Lantana aje ace mata yau bani san yin magana da kowa….
“Maryamu, yau gimbiya Hakima tace bata son yin magana da kowa,”wai Allah kice yau an tabo jaraba a cikin gidan nan? “Aiko dai, “Lantana! Lantana!! Lantana, “na bani Maryamu, gimbiya na kirana, ni yau na shiga ukku, yau buguna ne Kawai baza tayi ba…
“Allah ya kara maki lafiya, rain Gimbiya ya dade, ina neman sausaci rain Gimbiya ya dade, “Lantana, mai kika tsaya yi waje ina ta kiranki kin gyaleni?
“Ina neman afuwarki ya uwargijiyata, “yi man shiru ba wanann na tambaye ki, “nace uban me kika tsaya yi a waje? “Eh naje nakai sakonki ne, “wani sako? “Na baki san yin magana da kowa yau..
“Shine kika yi ma wannan uwar tsayuwar, ke Bilki, “Naam Allah ya da rainki ya dade gambiya,”wuce maza ki kiran man Sarkin bulala, yanzun nan, “to Gimbiya, “dan Allah Gimbiya ki man rai, ki duba tsufa na, kiyi hakuri, kuskurene nayi ina neman afuwa..
Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana cewa, “yi man shiru tsohuwar banza, tsohuwar wofi, ke har wani tsufa ne dake da za’a kalla aji tausayinki, to ni GIMBIYA HAKIMA, bani tausan Yaro balle tsoho…
Suna cikin wannan yanayi sai ga Sarkin bulala yazo, “Ran Gimbiya ya dade, gani na ansa kiranki, yake uwar Marayun masarautar kano…
“Sarkin bulala, ina son yanzun kayi ma Lantana bulala hamsin, indan ta sosa ta zube, ko kuma tayi kuka, itama ta zube, bayan ka gama, ka kai ta gida Maza, tayi sati biyu, ana yi mata horo mai tsanani….
“Angama uwargijiyata, Yanzun ko zani zartar da hukuncin da kika bani, nan Sarkin bulala ya fara zane Lantana, ko dogon tausayi babu a idonshi, sai da yayi ma Lantana tsinanan bugu, sannan aka dauke ta zuwa gidan Maza…
“Allah ya taimekike, “Maryamu, lafiya naga kin shigo haka, hankalinki tashe? “Allah ya taimakeki, Allah ya kara maki nisan kwana, da man Gimbiya Hakima ce tasa ake yi ma Lantana hukunci…
“Subuhanalillah, mai tayi mata? “Da man dan ta dade, da ta ce aso ace man nace maki yau bata son yin magana da kowa, shine tace ta dade, ta barta tana ta magana…
“Allah sarki, je ki kira man sarkin gida, “to Ranki ya dade, nan Maryamu ta wuce jiki na rawa ta taho da sarkin gida..
“An gaisheki, Amaryar sarki, daga ke ba kari, ” Sarkin gida, kai dai baka rabuwa da zolaya, kaje kace ma Hakima nace ta soke wannan hukuncin da tasa ayi ma Lantana, in ba haka ranta zai mumunan baci, kuma kace tasan tayi maza tazo kiran da nayi mata…
“To Ranki ya dade, nan Sarkin gida ya tafi, yana zullumin yanda zai hadu da Gimbiya Hakima, dan ya san lamarin ta ba mai sauki bane…
Nan Sarkin gida yana zuwa, ya aika ayi mashi neman iso,”Gimbiya Sarkin gida, yana son ganin ki, “Bilki kice mashi na ya san ida dare yayi mashi kafin raina ya baci…
“Allah ya taimaki Sarkin gida, Gimbiya tace yau bata son yin magana da kowa, “kije kice mata Fulani ta aiko ni, “Gimbiya yace sakone daga wajen Fulani, “kije kice ya shigo, ya jira ni gani nan zuwa….
Sai da Sarkin gida yayi awa daya zaune, yana jiran fitowar Gimbiya Hakima, amman shiru kake ji, ba bu alamunta..
“Bilkisu, dan Allah kije kice ma Gimbiya Hakima ina jiranta, “to sarkin gida, “gafara dai ran Gimbiya Hakima ya dade, nan Bilkisu tana shiga ta tadda Gimbiya Hakima tana chatting hankalinta kwace, “Ke lafiya kika yi man tsaya? “Allah ya huce zuciyarki yar sarki jikar sarki, da man sarkin gida yace yana jiranki, “je kice mashi ina zuwa, “to Gimbiya, sarkin gida tace tana zuwa…
Tafiya take cikin takama da jin kaika, tana tafiya tana harbin iska, tana busa hanci, “takawarki lafiya yar’masu gida, “yauwa sannunka Sarkin gida, lafiya kake nema, sai kace biyan bashi?
“Allah ya huci zuciyar Gimbiya da man Fulani ta bani sako, “wani kallar sako ne? Bana ce yau baniyin magana da kowa ba? “Allah ya huci zuciyarki, “naji mai tace maka? ka cika ni da surutun banza marar anfani, “da man tace ki maza ki soke hukuncin da kika yanke ma Lantana, tun ranku keda ita bai baci ba….
“Je kace mata naji, amman sai gobe zani sa a fiddo ta”godiya muke Gimbiya Hakima ikon Allah, nan gani nan bari, kinyi ma makiya nisa, “da kata sarkin gida, kana iya ta fiya dan ka matsa man da shirmainka
Nan sarkin gida ya tashi, jiki duk a sanyaye, yana mamakin yanda Gimbiya take gaya masu magana san yaranta, ko dan ta ganta ita yar sarki ce…
Ai a haife na haifi kamar Hakima sau ukku, amman dan ina karkashinta take zagina, baki daya bata biyo halin iyayenta ba, Allah dai ya shirya…
“Allah ya taimaki Fulani, “sarkin gida, ya kuka yi da ita? “Eh tace zata saketa amman sai gobe, kuma tana kan bakarta na yau bata son yin magana da kowa…
“Hmmm shikenan, sarkin gida, Allah ya shirya mana zuri’a, ka haifi da’ baka haifi halinshi ba…
Nan dai Fulani ta kama fada tana mamakin halin diyar tata, ta rasa inda ta gado wannan bakin halin na wulakanta tallaka, tana mamakin yanda Hakima bata son tallakawa ko daya…
A rayuwa kenna, haka dai fulani ta gama sannan ta wuce shashen Yakumbo…..
“Ranki ya dade Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Fulani, tana neman iso, “kuje kuce mata ta shigo,nan Gimbiya Fulani ta shigo ita da kuyunganta suna take mata baya…
“Sannu da hutawa Yaya, “yauwa sannu da zuwa Fulani, naji ance Hakima ta yanke ma baiwarta hukuncin sati biyu a gidan maza, “Hmmm hakane yaya, amman yanzun tace gobe zata sa a fiddo ta..
“Gaskiya Fulani, Hakima tana bukatar gyara, ban san ina ta samu wannan halin ba..
“Hmm wallahi nima Yaya wannan halin na Hakima yana da muna ban san ya zanyi da ita ba, kai haifi d’a baka haifi halinshi ba…
“To kuma naji ance tace yau bata san yin magana da kowa! “Eh hakane ai yanzun shashenta zan wuce dan ya zama dole ta tsaya ta saurare ni, tun kafin maimartaba yaji abunda tayi a yau..
“Gaskiya ya dace ai, “to ni na wuce Yaya…
“Nan Gimbiya Fulani ta tafi sheshen Gimbiya Hakima dan sunyi magana da ita..
“Ran ki ya dade ga mai girma Gimbiya Fulani a hanya, “to naji wace ki ban waje..
“Nan Bilkisu ta fita jiki duk a sanyaye, tana cewa haka dai zasu hakuri da uwargijiyar tasu..
“Fulani sannu da zuwa.
“Yauwa Hakima, ai ke keda sannu tunda kin nuna ban isa da ke ba, to ni gani na taso da kaina..
“Fulani zan fiddo Lantana gobe dan har umarni na bada na fiddo ta a gobe..
“Ni ba wannan ya kawo ni ba, inkin fiddo ta kanki inma baki fiddo ta ba shima kanki, tunda kinfi kowa anfana da Lantana..
“Nazo ne nayi maki bayanin addimission dinku a fito, dan haka Maimartaba yace ki fara shiri ko wani lokaci kina iya ta fiya makaranta..