SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Zahrah na zaune wata Aunty Ladi ƴar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin ɗakin babban mayafi me kyau ta ɗauka haɗe da rufe Zahrah dashi, miƙar da’ita tsaye tayi cikin farinciki tace
“Allah yayi yauzaki tafi ɗakinki amarya muje ɗakin Inna’n taki aimiki nasiha”
aitun kan aƙarasa ɗakin Inna Zahrah ta ɓarke da kuka wiwi, (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daɗin gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan ????????)
Nasiha Inna da sauran matan dake ɗakin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda ƙafa inayi bari na bari, komin ƙanƙantan ɓacin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taƙi ji tagani taƙi gani, takuma riƙi haƙuri don shine tubali kuma gini haka ƙinshiƙin zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a’a watarana dole sai kunɓatawa juna, dole sai kunyi haƙuri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daɗi, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har ƙasa ta duƙa tabasa haƙuri, domin kuwa har kullum shine sama da’ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiɗewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daɗi tafiyan Zahrah’n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol ????.
Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da’ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faɗa jikinsa haɗe da sake ƙara volume ɗin kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye, daƙyar ya’iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar ɗayace shine tabi mijinta sau da ƙafa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haƙuri akan dukkan komai, sannan kuma yaroƙi yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata????
Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za’a zo a ɗauketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin????…
Anasa amarya acikin mota sauran ƙawaye da ƴan uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa…
Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner…
Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaɗan bata nuna musu ɓacin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baƙaunarsu sukeyi ba, ɗaki guda aka warewa amarya, balaifi ɗakin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah, mintuna kaɗan da shigowansu ɗakin wasu ƴan mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor……
Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke ƙiran nata yasanya ta ɗaga wayar bawani ɓata lokaci
“Bestie’n mu how far?” abunda wanda yaƙirata acikin wayar yafaɗa kenan..
Dariyane yakamata amma saita taƙaita dariyan haɗe da cewa “I’am fine sai dai gaskiya na gaji”
Murmushi shima yayi haɗe da cewa “Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da’ita fa tun ranan alhamis” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa…
“Kamar kuwa kasan kainaketa so kaƙira, wallahi yau tun safe Zahrah taƙicin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature ɗinta ya hau sosai” Husnah tafaɗi haka ga Dr.Sadeeq.
“Subahannallah, keda su waye aɗakin?” Dr. yatambayi Husnah cike da zaƙuwa..
Kallon waƴanda ke cikin ɗakin Husnah tashiga yi kafun tace
“Gaskiya munada ɗan yawa”
“Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters kinji”
“To shikenan zan kawota insha Allah”
Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta’ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riƙeshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taɓaci da yaudara………
Inasonku masoyana na Wattpad irin sosai ɗinnan, ina yaba ƙoƙarin ku wajen min comment, Allah yabar ƙauna
Kuɗin ma ae nadabanne masoyana na Whatsapp inajin daɗinku sosai iya wuya muna jone Insha Allah
Comment
Share
and Voted please
Fatymasardauna
????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 90 to 91
Saida kusan gabaki ɗaya mutanen da suka kawo Zahrah suka soma watsewa zuwa wajen dinner, kafun Husnah ta matso kusa da amarya Zahrah wacce take aikin kuka. Hannayenta takamo haɗe da zama gaf da’ita.
“Please Zahrah kidaina wannan kukan, yanzu haka Doctor yace inkai masa ke yana boys guaters, kuma kinga babu amfanin kije wajensa kina kuka” Husnah tafaɗi haka ga cikin lallashi.
Zahrah dai bata kumace da’ita komai ba bata kuma daina kukan ba,, wayar Husnah ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Dr.Sadeeq ne keyawo akan screen ɗin wayar,, tana kara wayar akan kunnenta yace
“Yadai Husnah, najiku shiru”
Sake kallon mutanen da sukayi ragowa acikin ɗakin Husnah tayi.
“Gaskiya babu dama Doctor, saboda dazaran anga zamu fita za’ace ina zankaita” Husnah tafaɗi haka cikin ƙasa ƙasa da muryarta….
Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa
“Okay to bakomai zan san yanda za’ayi, ku shirya me meckup tana nan zuwa”
Cikin matsanancin ciwon kan dake ɗawainiya da’ita tashiga toilet ta ɗauro alwala, kan ƙaton darduman dake shimfuɗe a tsakiyar ɗakin ta hau ta kabbara sallah’n magriba,, tana idar da sallan meyi mata meckup ta ƙaraso, haka tanaji tana gani ta bada fuskarta aka zizara mata meckup wanda yaɗauki fuskarta sosai.. Yauma dai meyin meckup ɗinne ta shiryata tsab cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga (wedding gown) na wani tsadadden leshi me matuƙar kyaun gaske, riga ce doguwa har tana sharan ƙasa yayinda bayan rigar aka sanya wani haɗaɗɗen net me matuƙar kyaun gaske, sosai net ɗin da aka sanya abayan rigan yakuma ƙawata ɗinkin, lace ɗin yakasance light pink colour yayinda kayan ƙyale ƙyale najikinsa yakasance golding ash colour, sosai kayan yayiwa Zahrah kyau,,, haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali aka tsantsara mata akanta, take tasake yin kyau,,,, yau dai kwalliya da kuma kyawun da Zahrah tayi haryafi wanda tayi a ranan kamu, komai nata yau na musamman ne tasha kyau sosai, ga doguwar riganta me ɗaukar hankali, daddaɗan ƙamshi kawai take fitarwa ajikinta me sanya nutsuwa,, duk da irin wannan kyawun da tayi sai dai fuskarta babu wani wadataccen walwala domin kuwa idanunta sunyi luhu luhu dasu, cikinta kuwa banda kukan yunwa babu abun dayake yi mata, amma kuma saboda masifar taurin kai irin nata taƙi sanyawa cikin nata komai na abinci.. Husnah ma yau zama tayi akayi mata meckup nagani na faɗa, sosai itama tayi kyau, tasha adonta cikin wata doguwar riga na golding white lace, idan ka kalleta dole ka ƙara domin itama tayi kyau sosai dama kuma itaɗin ma ko babu meckup tana da kyau masha Allah….