NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Babban likitan dake kula da al’amuran Zaid ɗinne, ya rufe Dad da faɗa akan wai saboda me yasa aka faɗawa Zaid ɗin maganar da zata tada masa da hankali, haƙuri Dad yashiga bawa Doctor ɗin,   sharuɗa masu tsauri Doctor ya shumfuɗa musu, akan cewa lallai dole babu wanda zai sake ganawa da Zaid ɗin harsai bayan kwana uku, sannan kuma koda sunkoma gida yazama dole akiyaye shiga damuwa dakuma ɓacin ransa, saboda yanzu zuciyarsa tazama kamar wani ɗanyen ƙwai sai anayi ana lallaɓata, zuwa yanzu abu kaɗan ne zai sanya ta buga, wanda hakan kuwa dai dai yake da rasa rayuwar Zaid ɗin baki ɗaya


Bayan awanni 4

Shikaɗai yasan irin raɗaɗi dakuma ciwon dake kwance acikin zuciyarsa,  hawayene suke ta fita daga cikin idanunsa suna gangara akan ƙuncinsa,,   “Da gaskene Zahrah’n sa tayi aure? me yasa Zahrah zatayi masa haka? Bazai taɓa iya jurwa ba, lallai koda Zahrah tayi aure bazai taɓa daina sonta ba, kuma koda duka mutanen duniya zasu taru akansa bazai sanja ƙudurin dake zuciyarsa na auren Zahrah ba, zaiyi duk wani abu wanda yasan Zahrah zata dawo garesa koda kuwa hakan zaijawo sanadiyar rasa rayuka ne, ZAHRAH kawai yasani kuma itace cikar burinsa”….. (???? karya kasheni nima????‍♀????‍♀)

(Gobe Birthday na???????? zan baku updated insha Allah????????gobe akwai show agidan Doctor ???? )

        21/January/2020

         Fatymasardauna
????????????????????????????????????????  

      SHU’UMIN NAMIJI !!

     Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

              WATTPAD
        @fatymasardauna

Editing is not allowed????

        CHAPTER 94 to 95

NIGERIA

Tunda Doctor yafita baisake dawowa cikin gidanba harkuwa Zahrah ta ƙaraci zamanta acikin falon ta koma uwar ɗaka, sai dai kuma yayi mata waya yasanar mata cewa yana gidan Hajiyarsa wani uzuri ne ya riƙesa…


Idar da sallan isha ɗinta kenan ta miƙe haɗe da ƙarasawa gaban dressing mirror,  lotion ɗinta me ƙamshi ta shafa ajikinta,  powder kawai ta shafa akan fuskarta sai kuma man leɓe…   Wata rubber pencil gown maroon colour ta sanya ajikinta, rigace irin marar nauyi ɗinnan sannan kuma an cika gabanta da fararen duwatsu wato (stones)   wani maroon ɗin mayafi me ɗan kauri ta ɗauka haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalin nan na turban akanta,   sosai tayi kyau saikace wata balarabiya,  zama tayi akan gado haɗe da jawo wayarta, ajiyar zuciya ta sauƙe, har cikin ranta tana mamaki ƙwarai na rashin dawowan Dr.Sadeeq, tun safe daya fita haryanzu baidawo ba,,  tashi tayi ta rage gudun ac’n dake cikin ɗakin, haɗe da ɗaukar wayarta tafice zuwa falo,  hankalinta gaba ɗaya ta maida kan  tashan MBC Bollywood da suke haska film ɗin nan me suna SANAM TERI KASAM bata taɓa kallon film ɗin ba amma kuma tana da waƙoƙin film ɗin acikin wayarta saboda sosai waƙoƙin sukeyi mata daɗi,, ta shagala a kallon film ɗin har idanunta sunfara kawo ƙwalla saboda tausayi,  jitayi ansanya hanu anrufe idanunta , a razane ta ƙwalla ƙara domin kuwa sam bataji motsin shigowan  mutum cikin falon ba, da sauri tature wanda yarufe mata idanun gefe haɗe da tashi tsaye,,  ganin cewa shine yasanya tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai,, murmushi yasakamar mata haɗe da cewa

“Matsoraciya” 

Zama yayi akan kujera,, itama zama tayi tana me da numfashi sosai yatsorata ta donkuwa bata tsammata cewa shi bane sam ta manta ma da cewa babu mayafi ajikinta… Kafeta da’idanunsa yayi yana me ƙarewa kwalliyartata kallo,, sai alokacin ta ankara da irin kallon dayake jifanta dashi.

  “Sannu da dawowa!” tafaɗi haka cikin sassanyar murya.

“Yauwa, kimin afuwa najima da yawa” yafaɗi haka yana me sanya hanunsa ya kama kunnensa alamar yana neman afuwa,   murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa dakanta…

Miƙewa tsaye yayi haɗe da cewa “Bari naje nayi wanka, akwai kayan fruit acikin fridge please kiɗan yanka min kafun na fito”

“To” kawai tace dashi haɗe da tashi tanufi wajen fridge ɗin shikuma direct ya wuce ɗaki donyin wanka…

Tana kammala yanka fruit ɗin ta ɗauko wani plate me kyau tarufe yankakken fruit ɗin,  kan kujera ta koma ta zauna haɗe da sake maida hankalinta ga tv.. Sanye da tree guater jeans ajikinsa haɗi da wata farar t-shirt ya fito, ƙamshi kawai yake fitarwa, satan kallonsa Zahrah tayi haɗe da ɗan sakin murmushi, bata taɓa ganinsa acikin irin wannan shigar ba amma kuma yayi mata kyau sosai..   Akan lallausan carpet ɗin dake malale tsakiyar falon ya zauna haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa,    alama yayi mata da hanunsa cewa ta miƙo masa fruit ɗin, ɗaukan plate ɗin tayi taƙarasa gabansa, durƙusawa tayi har ƙasa kana ta aje plate ɗin,, “Miƙomin wancan ledan”  yafaɗi haka yana meyi mata nuni da leda wanda shiya shigo dashi sam ita batama lura ba,,  cike da nutsuwa taɗauko ledan kamar yanda ya umarceta ɗan duƙawa tayi  haɗe da miƙa masa ledan,,  amaimakon yakarɓi ledan sai taga ya jawota jikinsa,  zaunar da ita yayi acikin jikinsa  haɗe da sanya hanu ya zame ɗaurin turban ɗin dake kanta, take lallausan gashinta ya zubo harzuwa kan bayanta,   kansa ya cusa acikin gashin nata yana me shaƙan daddaɗan ƙamshin dake tashi ajikin gashin nata,,   “Kiyi mini afuwa my princess,  banƙi dawowa haka kawai ba!” yafaɗi haka yana me ƙara matseta acikin jikinsa.

“Ni bakayi mini laifi ba sam sam,  nasan ae bazaka ƙi dawowa haka kawai ba” tafaɗi haka cikin zazzaƙan muryarta..

“Yauwa my wife nasanki dama kina da haƙuri, natsaya a wajen ƴar uwarki Salima ne, ina fatan banyi laifi ba?”

Da sauri tajuyo da kanta tana kallonsa,  “Salima kuma? bakace tafasa aurenka ba” tatambayeshi fuskarta ɗauke da tsananin mamakin jin abundayace..

Dariya yayi ganin yanda tawani zaro idanu kishi ya bayyana akan fuskarta ƙarara daga ambatan sunan Salima.   

“Wasa fa nake miki Madam, miye na wani tsorita haka”  yafaɗi  haka yana me ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo..

Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da  ɓata fuska, ta juya da kanta batace dashi komai ba,, sarai ya lura taji haushi,,,  yankakken apple ya ɗauka haɗe da kaiwa kusa da bakinta..  ƙin buɗe bakinta tayi saima daɗa kauda kanta da takeyi jefa apple ɗin yayi cikin bakinsa, haɗe da sanya hanu ya juyo da kanta yazama tana fuskantarsa…

“Fushi kike da mijinki? kiyi haƙuri banfaɗi haka don ranki ya ɓaci ba, wasa nake miki kiyi mini murmushi kinji Zahrah na!”

Hakanan taji zuciyarta tayi sanyi harbatasan sanda tasaki murmushi ba..   Yankakken apple yakuma ɗaukowa  yakai bakinta babu musu ta buɗe bakinta yasanya mata… Tana zaune acikin jikinsa haka yaciyar da’ita domin kuwa atare sukasha fruit ɗin haɗe da ɗaura fresh milk akai.. Yana nan azaune ta tattare wajen takai kitchine haɗe da dawowa, miƙewa tsaye yayi haɗe da ƙarasawa gaban tv wanda yaketa ɓaɓatu shikaɗai ya kashe,  kallonta yayi kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, wutan falon ya kashe kana yakama hanunta suka nufi ɗaki,  hmmm tun ɗazu bata ji tsoro ba sai yanzu da ta gansu sun hallara acikin bedroom, janta yayi har cikin bathroom sukayi brush… Da kansa yaciro  wani ƴar fingilar rigan bacci wanda take shara shara kamar rariyan tata sai dai kuma tana da ado ata wajen wuyan..  Ganin yanufota kai tsaye ne yasanya tayi saurin saddakanta ƙasa, zuciyarta kuwa luguden duka tashiga yi mata, kamar anka mata tana sata, harga Allah ita tsoronshi take Allah yasa yauma karyayi mata komai.. Tunaninta ne ya katse sakamakon sauƙar hanunsa da taji abayanta,  matsowa yayi gaf da’ita harsuna iya jiyo hucin numfashin junansu,,  ahankali yayi ƙasa da zip ɗin rigar nata, lokaci guda yasanya hanu ya soma zame rigar daga kafaɗunta, rumtse idanunta tayi ƙam, haɗe da takure jikinta waje ɗaya,  bazata iya hanasa ba, amma kuma dazai barta yace ta cire rigan da kanta da hakan yafiye mata komai daɗi, saboda ko bakomai zatayi iyaka ƙoƙari wajen ganin ta kare ƙirjinta,  lokacin daya kawo ƙirjinta kasa jurewa tayi, dasauri ta duƙa ƙasa haɗe da cewa “Dan Allah kabarni naje toilet na cire da kaina”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button