SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????

MARUBUCIYAR

1 UWAR GIDA NA
3 AUREN DOLE
4 RUHI ƊAYA
5 FAROUK
6 INAYATULLAH
7 ASANADIN ABAYAR SALLAH
8 AKAN AIKINA
9 JAMILA
10 DR NAWWARA PAID BOOK
11 DARASI PAID BOOK
12 SILAR FYAƊE FREE BOOK

Bismillahir Rahmanir Rahim

       1????2

. . . .Kuka na ke kamar raina zai fita tsabar tashin hankali,wai yau ni ce agaban gawar mahaifiyata ina kallonta bata numfashi,wani irin ihu na sake sakawa ina girgiza Ummana cikin kuka na ke ce wa”Ummana don Allah ki tashi kada ki mutu,in dai da gaske ne kin mutu to nima tabbas mutuwa zanyi”.

“ke wai wacce irin mahaukaciya ce?saboda uwarki ta mutu sai ki saka mutane a gaba kina wani kukan banza?to wallahi ba a gidannan ba,banza karuwa wacce ta bawa wani ɗa namiji jikinta ya yi mata ciki,ai gashinan yanzu kin kashe uwarki da baƙin ciki kinzo kina wani kukan banza da wofi”.

Da sauri na jiyo da idanuwa na da sukayi jawur kamar wuta,tsabar tashin hankalin da na ke ciki bai saka na mayarwa da Maman Nusaiba amsa ba,sai ma ba da ƙaimi da na yi akan kukan da na ke yi,don dole suka fita suka ƙyeleni sai da na yi mai isata sannan na yi shiru,ɗan ciki na naji yana ta motsi kamar zai fito wanda tun da na samu cikin baiyi motsi mai ƙarfi haka ba.
Ina ji ina gani aka fita da gawar Mamana,a duk cikin mutanen da suka zo ta’aziyya babu mai rarrashi na, ni kaɗai na ke kuka na ina share hawaye ranar yini na yi banci ba bansha ba,ƴan uwan Mama na suka kawo abinci katan katan suna ta sha’aninsu ɗaura wannan ɗaura wancen,ni dai ina ɗaki ina tunanin rayuwa ta,a shekaruna da basu wuce 15 ba naga rayuwa kala kala.

Ina ɗaki naji Baba na yana ƙwala min kira,da sauri na fito jiki na sai kakkarwa ya ke saboda rashin cin abinci ga juna biyu a jiki na.

“Ke dan iskanci shine ki ka shige ɗaki ki ka ƙwanta uban waye zai yi miki duk wannan aikin da jama’a su ke maza fito ayi da ke,banza ballagaza kawai yaja wani dogon tsaki ya fita.
Ko da na fara aikin wani irin mugun jiri ne ya dinga ɗiba na ina daurewa don nasan halin Baba yanzu zai dawo,a haka har na gama tatar ƙullin kokon,ina tuno da mahaifiya ta ina ta kuka mai ciwo.

  • * *

“Girke2 ake a gidan kana shigowa zaka ji ƙamshi ta ko ina,masu aikin gidan kowa da aikinsa,gida ne ƙaton gida mai ƙyau d tsari kana ganin gidan kasan gida ne na masu kuƊi sosai.

A tsakiyar garden ɗin gidan an saka wata mat ƙatuwa doguwa wacce zata sada ka da cikin gidan mai ɗauke da sunan,WELCOME MY LOVELY SON.

Hajiya Barakat ce ta ke ta zagaya gidan tana ganin irin decoration ɗin da aka yiwa gidan,wanda ya yi tace ya yi wanda baiyi ba ta ce bai yi ba.

Da wuri ta saka ƴaƴanta a gaba ƴan mata guda uku masu suna,Zeenat,Rabiat,Aisha,Fatima.

Suka tafi taro babban yayan nasu sojan sojoji wato admiral Aliyu Muhammad,A.A M.

Miss green ce????????️
????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

   5????6

“Me Martaba dafatan mun sameku lafiya”?.inji Salimat ta faɗi hakan tana mai sunkuyar da kanta ƙasa alamar girmamawa.

Kallonta Me Martaba ya yi yana yaba hankalin ƴarsa tilo wato Salimat,da ƙer ya buɗe balinsa irin na ƴan sarauta ya ce”lfy ƙlau gimbiya Salima.”

shiru Salimat ta yi tana jin kunyar sanar da mahaifinta wannan maganar,gashi kuma babu wanda za ta faɗawa ya faɗa masa don ba ta da uwa araye yau shekarar mahaifiyarta huɗu da rasuwa.

Yasan halin Salimat da kunya saboda haka ya janyo abin rubutu ya miƙa mata ya ce”Gimbiya a rubuta mana anan komene ne?”.

cikin sanyi ta amsa ta rubuta abin cikin kunya ta miƙa masa, hannunta yana ta girgiɗi,sai da ta bawa mahaifinta me martaba sannan ta yi dana sanin miƙa masa wannan takaddar.

Mamaki sosai Me martaba ya yi,yana kallon Ƴar ta sa cikin nuna kulawa ya ce”a tashi a tafi zamu nemeki”.

Jiki babu ƙwari Salimat ta tashi kamar zata yi kuka,saboda yadda Me martaba ya yi magana don kana jin muryarsa kasan a fushi ya faɗe ta,don tasan abinda ta aikata laifi ne babba a cikin gidan sarauta,kuma gasu fulani kun san yaren fulanj aƘwai kunya,ita dai za ta ɗauki ƙaddarar soyayya don da alama ba tada dacen masoya,ayanzu gimbiya na da shekara 25 aduniya ta ga ƙalubalen soyayya kala2 har kawo i yanzu,saboda wasu don kuɗin mahaifinta suke sonta ba don Allah ba.
*** *** ***

Kuka sosai su afra suke kuka bayan sun dawo daga boarding skull don yanzu anyi hutu.

Ina cikin lallashinsu Khadija ta ce”wallahi Anty Rabiatu baki ƙyautawa rayuwarki ba,da ki ka bawa namiji jikinki ya yi miki ciki,yanzu gashinan kin kashe mana uwa da baƙin ciki”.

Salimat ma ta ɗora da cewa”Wallahi Anty Rabiatu na tsaneki tsana mafi muni a rayuwata don wallahi ba zamu yafe miki ba,kin kashe mana uwarmu da baƙin cikin ki.”ta faɗar hakan ta fita tana hawaye.

Afra ce kawai ta kalleni ta ce”Anty duk da a yanzu shekaru na basu wuce 15 ba amman nasan rayuwa sosai,duk da na girmi Khadija wacce a yanzu tana da sha uku da rabi 1/3,amman ta gane cewa baƙin cikinki ne ya kashe Umma, amman yana da ƙyau mu tsaya muyi miki adalci ke ma,ki faɗa mana abinda ya faru da rayuwarki don wallahi ba zamu yarda da duk wanda ya lala ta miki rayuwa ba”.

ƴar dariya kaɗan Rabiatu ta yi sannan ta ce”Afra kenan kina nan da halinki na ƴan jarida?Allah dai ya cika miki wannan burin na ki”.

ka saƙe Afra ta yi tana kallon yayar ta cikin tausayi ta ce”Antynmu na sanki da zurfin ciki don Allah ki faɗa min don nima in fita daga sarƙaƙiya please”.ta haɗa hannayenta alamar ban haƙuri.

Riƙe hannayen Afrah na yi a hankali na ce”zan faɗa miki Afrah,don hankalinki ya ƙwanta amman a rayuwata ba na son to na asirin kowa,amman ya zama dole shima asirinsa ya tonu”.

ina kaiwa nan na tashi na jingina da sip ɗin mahaifiyarmu na fara ba ta labarin.

Labarin ya ɗakko asali ne daga.. .v.

Miss green ce
????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????

Wattpad user name
Rabiatu33

   3????4

. . . . .Cikin ta kunsa mai kyau da tsari ya fara sakkowa a jirgin ,fari ne ƙal kamar zaka taɓa sa kaga jini tsabar farinsa,yana da jiki da kuma tsayi, ƙyaƙƙyawa ne shi ajin farko,yana sanye cikin wasu haɗaɗɗun ƙana nan kaya,waɗanda suka amsa sunansu ya cire cort ɗinsa ya riƙe a hannu yana gƴara necktail ɗinsa.

Ayshe ta fara hangosa ta ce”Hajiya ga yaya cen yana sakkowa,gaskiya yaya ya daɗa ƙyau wallahi gaskiya Hajiya yaya ya fimu Ƙyau”.

Rabiatu ta ce”ke kuma kina kishi ko?ke dai wallahi aisha kishi ne da ke wallahi,ke ce ki ka yo dangin Papa shuwa arab kishi ne dasu”.

Hajiya ta ce”kuyi wa mutane shiru zaku fara halin ko?”.suka ja bakinsu suka yi shiru ita daman Zeenat da Fatima miskilanci ne dasu irin Yayansu.

Zeenat tana da shekara 25,sai Fatima 22,sai Rabiatu shekara 19,sai Fatima auta mai shekara 17.

shi kuma babban gogan yana da shekara 35 a duniya,Har hajiya ta fitar da ran haihuwa sai kuma ta dawo ta haifi mata har huɗu.
Da sauri Hajiya ta ƙarasa ta rungume ɗanta cikin so da ƙaunarsa duk da sojojin da ke bayansa,shi kuwa jan zaki Aliyu Haidar kunya ce dashi sosai,don haka cikin kunya ya rungume ta,shi daman tun yana yaro kunya ce dashi,tun yana shekara 4 ya daina yadda mahaifiyarsa na yi masa wanka,sai dai ya rufe gabansa ta yi masa,haka har ya girma shi mai kunya ne.

Yana cikin cin abinci wayarsa ta kama ringing ɗin wayarsa,ya ƙi ɗauka Hajiya Barakat ta ce”haba son ka ɗauki wayar mana kaji ko menene?”.ta faɗi hakan cikin yaran yarbanci,shima cikin yaran ya ce “to momi”.

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button