SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

Wani irin faɗuwar gaba na ji idanuwa suka kawo ruwa daman ina da matuƙar saurin hawaye,Mama ta daka min tsawa ta ce”me ya faru da ke Rabia na shiga uku me zan gani a gidana?Rabia cikin shege a gidana,mari ta kaimin na kauce ina kuka Baba ya shigo don tambayar ba asi Mama ta hau nu na ni kamar ta ga abin tsoro.

“Ke me ki ka yi mata ta ke nuna ki”?.

ya faɗi hakan cikin tsawa da sauri na ce wai banyi period ba?,gumi ne ya fara tsastsafowa Baba ya ce”Maryam ki faɗa min gaskiya me ya faru da ƴarmu,cikin kuka Mama ta fara faɗa mai duk sauyin dana ke samu,Abba na ya katseta da cewa ta shi mu tafi asibiti zaman gida bai ka ma mu ba.

Test ɗin farko ya nuna ina da shigar ciki har na tsawan wata biyu.

Tun daga wannan ranar Mama ta faɗi jininta ya yi mummunan hawa sosai tun daga nan komai ya canza a gidanmu,idan ka shigo kamad gidan ma ko ki,daman daga ni sai Mama tunda su Afra suna makarantar boarding,yin duniya an tambayeni wanda ya yimin ciki amman naƙi ba da amsa sai kuka har suka gaji suka saka min idanu,ga shi cikin kamar ba na fari ba,don yadda ya ke da matuƙar girma na zama wata babbar mace ko ina ya ciko.

Tun daga ranar da Abba yasan ina da ciki ya daina yimin magana musamman da matarsa ta kamu da ciwo akaina don yana mayuƙar son Mama don yadda kasan layla majno haka suke.sannan Abba ya kori Salis bayan shima yasha tuhuma daga mahaifina don Abba na ƙin yarda ya yi shine ya yi min ciki don yadda muka shaƴu sosai dashi.

Tun daga nan Mama ta yi ta ciwo da ya ke ciwon ba na tashi bane Mama ta mutu,kuka sosai Rabiatu ta farayi don tunowa da mahaifiyarta Afra tana taya ta kukan haka sukayi ta yi babu mai taya su har sukayi shiru.

Cikin kuka Rabiatu tace”wannan shine gaskiyar labarin Afrah,a ina zanga wannan bawan Allah wanda rana ɗaya ya lala tamin rayuwa?da ma ace na ganshi yanzu”.sai ta fashe da kuka sosai ya yinda ɗan cikinta ya ke ta wutsil2 babu abinda ya shafe sa.

Miss green ce
????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

 11????12

. . . .haka muka yi ta kukanmu babu mai rarrashin mu tun daga ranar babu wanda ya Ƙara kukani,Salimat da khadija ko kallon inda na ke ba sayi,Afra ce kawai ke kulani don dama hutun sallah suka zo.

Bayan wata uku 3

Rannan ina ƙwance naji wani mugun ciwo baya ya kamani ga ciwon mara me tsanani ni kaɗai a cikin ɗaki ina ta kiran sunan Allah gwanin ban tausayi abin sai wanda ya gani,na haɗa wata uwar zufa sannu a hankali gumi ya ringa tsattsafomin ɗan cikina ya koma ƙasa baki ɗaya yana ta motsi kamar zai fito.

Afrah ta shigo kawomin abincin safe taga halin da nake ciki,da sauri ta je ta kirawo su Khadija sai da suka zo buɗe bakin Salimat ta ce”wallahi da ina da dama da sai na kashe Wannan cikin harda uwar ma,don sun jawo mana raini da cin fuska da zagi a gari,ta juya ta kalli Khadija ta ce to ni dai na tafi wajen Asil birthday ɗinshi idan kinga dama ki zauna wajen wannan akuyar idan kin ga dama ki taimake ta”.
tana faɗar hakan ta saka kanta gaba ta yi tafiyarta.

Khadija ma tafiyarta ta yi tana surutai,Afrah ta kalleni cikin tausayi ta ce”Anty jikin da sauƙi yanzu ko in aika akira abba a majalisa”.

Da sauri na girgiza mata hannu alamar kada ta kirasa,ni dai kawai kiran sunan Allah na ke asannu ,a sannu kan ɗa ya fara fitowa na ƙwanta a kan gado ba buɗe ƙafafuna Afra ta riƙe hannuna tana zubar da hawaye,kanta a sunkuye don ba ta son ganin tsiraicina,a haka na dinga faɗin sunan Allah har ɗa ya fito kyakkyawan yaro fari ƙal kamar ɗan larabawa.
Da gudu Afrah ta fita tana haɗa hanya ta shiga gidan Mmn Nusaiba don ta faɗa mata,ta kalli Afrah sheƙeƙe ta ce oh yau Allah ya yi an haifi shege ni da ina da iko da sai na kashe shegen banza”.
Tana faɗin hakan ta yi shigewarta ɗaki tana ta surutai.

Har ta fito daga gidan ta hango mmn junior kishiyar Maman Nusaiba,ta ce”a ah lfy Afrah me ya farunne?”.kunsan maganar gwarawa.

Nan Afrah ta faɗa mata a taƙaice,da sauri Mmn junior ta faɗa gidan tun kafin Afrah ta ƙarasa faɗa mata.

Tana shiga ɗakin ta jiyo nishin Rabiatu da sauri ta ƙarasa ciro mata ƴar budurw Ƙyaƙƙyawar gaske,wani gauran numfashi Rabiatu ta saki tana kiran sunan Allah.

Yaran mmn junior ta fara gyarawa tsaf,sai dai babu kayan saka musu da sauri ta tafi gida ta ɗebo kayan da ta fara tarawa saboda haihuwar da za tayi watan gobe, kala biyar ta ɗebo masu kyau ta sakawa yaran sukayi ƙyau gwanin sha’awa.

Sannan ta gyara Rabiatu tsaf ta gasata da ruwan zafi sannan ta riƙo ta kamar ƙaramar yarinya,ta saka Afrah ta dafa min ruwan tea da harda madarar ƴan boarding su Afrah.

wani kuka ne yazo min tuna maraici,idan banda maraici me zaisa har mace ta haihuwa a rasa me gyarata,duk da cikin shege ne amman da mahaifiyarta tana nan duk Ƙin da ta ke yiwa yaran za ta kulasu.

Asannan na tuno da AUNTY Rabiatu ƙanwar mahaifiyata wacce ta ke a merica da mijinta,wacce har yanzu bata san yayarta ta rasu ba,saboda sanin irin halin da zata shiga.
*** *** ***

wani mummunan faɗuwar gaba yaji a take ya zauna yana faɗin sunan Allah messenger ɗinsa ya shigo kawo mai saƙo,da hannu ya nuna mai ya ajje ya tafi,messenger ɗin ya kalli ogan nasa amman babu damar magana saboda halin da ya tsinci kansa alokaci ɗaya,ya shiga kiran sunan Allah har dai abin ya tsagaita masa,amman ranar babu damar aiki don haka ya nufi gida,don har yanzu zuciyarsa zafi ta ke masa.

*** *** ****

“Aliyu abinda ka ke ka yi gaggawar zuwa gida ina son yin magana da kai”.

“oky hjy gani nan zuwa”.

Hajiya Barakat ta zauna a ɗaki tana jiran zuwan Aliyu,Fatima tace”Hajiya kada ki faɗawa Bro wannan maganar ransa zai ɓaci wallahi”.cikin yaren yaroba ta faɗi hakan.

Hajiya Barakat ta daka mata harara ta cigaba da danna wayarta.

Miss green ce
https://arewabooks.com/chapter?id=62966a04b3924a9ab448be72

????SILAR FYEƊE????

NA????
UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

13????14

“Aliyu da ma jiya munyi magana da alajaa Hajara kan maganar aurenka da Ƴar wajenta Rasheeda shiyyasa na ce bari in faƊa maka idan yaso Sai Kaje ka ganta ku haƊa kanku.”

Tunda ta fara magana Aliyu yaji ransa lokaci Ɗaya ya tashi,a halin da ya ke ciki yanzu na busy shi bai ga abinda zaiyi da wata mace ba,kai idan ma ya ce zai auren ai cutar matar zaiyi,kuma bayan haka ko da auren ma zaiyi zai auri mace mai kunya ne ba Rasheeda mara kunya ba,yana cikin tunanin ya jiyo Hajiya na cewa”ka tashi ka tafi Allah ya yi maka albarka na ji da Ɗin wannan biyayyar da ka yi min kai ma Allah ya baka masu yi maka”.

shi dai admiral A.rasa me zai ce ya yi ya tashi ya tafi kansa na mai tsananin sara masa,ya shiga ban Ɗaki ya sakarwa jikinsa ruwa.

ya rasa me yasa ba ya son ko zancen aure?ya rasa abinda yasa kuma baya jin feeling a duk macen da ya kusanta,bai taɓa kuma son wata ɗiya mace ba tunda ya ke a rayuwarsa har kawo i yanzu da shekarunsa sun dushi 37.


Wani irin hamdala gimbiya Salimat ta yi sannan ta ce”ranka ya daɗe ina mai miƙa godiya ta a gareka abisa son dukkanin farin ciki na matuƙar alkhairi ne sai ka tabbatar da ka sama min farin ciki na.”

Ƴar fara’a nahaifin Salimat ya yi sannan ya ce”babu komai gimbiyar mata,ai abinda ki ka zo dashi ba abune wanda ya zama sabo ba,sunnah ce ki ke son yi don haka ina miki fatan alkhairi aduk inda ki ke gimbiya.

Cikin jin kunyar mahaifin na ta,ta tashi ta shige sashinta tana ji a zuciyarta kamar ta samu Admiral A. Ta samu.

Shu kuwa gogan Admiral A.ba ƙaramin kaɗuwa ya yi ba da ganin Mai martaba har cikin office ɗinsa,kuma ya nemi yardarsa wajen auren ƴarsa,kunya da kawaici sosai Admiral A. Yaji don haka cikin nutsuwa ya amsa masa zai auri Salimat ba bisa tursasawa ba,a zuciyarsa kuma yana mamakin irin mugun son da Mai martaba ya ke yiwa ƴarsa Salimat,mai makon namiji yaje neman aure amman sai aka ɓige da nemawa ƴa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button