SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

????BOOK 2

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.


SIRRINKI????????

ƳAR UWATA ANASO BAYAN KIN GAMA AL’ADA KIDINGA TSARKI DA GANYEN MAGARYA,YANA CIRE INFECTION DA SAURAN ƘARNIN JINI????????.

DAGA DR UMMU MAHER.
21????22

Yana kallon Rasheeda har ta shigo cikin kyakkyawan Ɗakin mijin na ta Babu ko gaisuwa ballantana sannu da zuwa ta ce”ashe ka dawo”?.

ta FaƊi hakan cikin yarensu na yoroba,banza ya yi mata ya tashi zaune sannan ya ce”kije ki kirawomin Salimat ku sameni a babban farlona”.

yana faƊar hakan ya yi waje ko ajikinsa don duk wani iyayin da Rasheeda ta ke ko kallonta bai yi ba,ballantana ma yaga wata ƙwalliyar da ta yi mai.

Haushi da kuma dana sanin zuwanta ɗakin admiral A. Ya kama ta sai zagin kanta ta ke don sam arayuwarta ta tsani wulaƙanci tana matuƙar son admiral A. Shiyyasa ma ta ke shanye duk wani shariyarsa.

Sanda ta isa mangaren gimbiya Salimat wani ƙamshi mai mugun daɗi ya ziyarci hancinta,wani malulun baƙin ciki ya dirar mata,bata ƙara jin wani haushin ba sai da ta saka ƙafafunta a wani lallausan kafet mai mugun laushi ta haƊiye wani mugun yawu na baƘin ciki ta Ƙara sa shiga babban farlon wanda ya gaji da haɗuwa,duk kyan kayan Rasheeda sai taga na Salimat ya ta ka na ta a kyau da kuma tsaruwa komai na farlon white ne da kuma pink ya yi matuƙar yin ƙyau.

Tana cikin kallon farlon ne,jakadiya ta ce”baiwar Allah lafiya?baki iya sallama bane?”duk alokaci ɗaya jakadiya ta yi wannan tambayar.

Wani banzan kallo Rashida ta yi mata sannan ta ce”ki gayawa ita uwar mulkin maigidan yana son ganinta”.

Da sauri Jakadiya ta ce”to bacci ta ke amman bari in tashi gimbiyar mata.”tana faɗin hakan ta yi hanyar ɗakin Salimat.

“Ke dai ta ke gimbiyarki amman ni ba gimbiya ta ce ba”.
Ado sosai Salimat ta yi da wata lifaya mai ƙyau fara ƙal sai ɗaukar ido ta ke,ta sha turaruka masu ƙamshi.

Sai da Rasheeda ta raina kanta ganin irin ƙwalliyar da Salimat ta yi.

Sallama ta yi sannan ta gaishesa,yaji daɗin gaisuwar da Salimat ta yi masa don ko babu komai ta girmama sa.

Rasheeda taji haushin abinda ya yi na amsa gaisuwar Salimat da ya yi ai kuwa ta cukule fuskarta tamau.

Abin yaso ya bawa Aliyu dariya amman sai ya basar da hakan,nasiha ya yi musu mai ratsa jiki sannan ya tabbatar musu da cewa Salimat ce uwargidansa tunda aurenta aka fara ɗaurawa.

Ai kuwa Rasheeda taji haushi sosai cikin yaran yoruba ta ce”gaskiya tun a yanzu ma nasan ba adalci za ayi ba”.

ko kallonta baiyi ba don yasan abinda ta ce,sannan ya ce su tsara kwanakin da yafi yi musu,Rasheeda ta yi banza Salimat kuwa ta ce kwana biyu ya yi.

Tana faɗar hakan Rasheeda ta ce baiyi mata ba Aliyu ya ɗaga mata hannu sannan ya ce duk wacce ta nemi ta yar masa da hankali to fa zai yi displing ɗinta yadda ya kamata.

A take ta yi shiru don tasan waye Aliyu.

A ranar ya kamata Salimat ta amshi ƙwananta amman har dare ta rasa yadda za ayi taje wajensa don wata kunya da girman kai ta keji.

Kuyi haƙuri na yi typing kaɗan ayi manage.

Miss green ce
????SILAR FYAƊE????

????BOOK 2

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


SIRRINKI????????

ƳAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIƊANU.

23????24

. . .. Har Ɗaki jakadiya Binta tabi Gimbiya Salimat don tasan tau ya kamata Salimat ta ƙwana a ɗakin mijinta Admiral A.tunda itace uwargidansa don aurenta aka fara ɗaurawa.

Tana zaune ta yi ta gumi ta sameta,Jakadiya ta samu waje ta zauna a ƙasa ta ce”uwar ɗakina idan babu damuwa aƙwai maganar da na ke so muyi da ke”.
Salimat tasan maganar don haka bata ce komai ba ta tashi ta shiga bathroom Ɗin da ke manne ajikin Ƙaton ɗakin na ta,ɗan murmushi Jakadiya ta yi tana mamakin hali irin na Salimat kamar ba ita bace ta ke kukan son Aliyu ba,yanzu kuma ta sameshi sai ta yi wasarere dashi,ta yi wa mahaifiyar Salimat alƙawari tun kafin ta rasu za ta kula da Salimat kamar ita ta haifeta.
Kafin ta fito da sauri ta fita daga ɗakin taje ta ɗauko mata wani magani na sirri da ta aika aka kawo mata tun daga garinsu don ta yi dabarar sakawa Salimat a cikin madara don tasan ta da shan madara,shi wannan sirrin na dabanne wanda ke saka mace ta mallake mijinta ta hanyar shimfiɗarta.


babu abinda zance da zamana agidan ƙanwar mahaifiyata don babu abinda na nema na rasa,twins sun ƙara yin wani ƙyau da kuma ƙiba don suna samun abinci mai gina jiki,nima jikina ya ƙara ƙyau ni daman ya ya lafiyar kura don jikina jikin manyan mata ne na ƙara cika da ƙiba.

Ɗakina ma kaɗai abin kallo ne saboda yadda aka ƙawata shi gwanin sha’awa ga kuma suturu sai wanda na ke son zaɓa don wadrope ɗina cike ya ke da kaya masu ƙyau.

Rannan da yamma muna zaune a farlon Anty Rabi Layla ta ce”Sister don Allah inason ki rakani super marker in ɗanyo shopping”.

ɗan murmushi na yi sannan na ce “babu komai Allah ya kaimu”.

Idris ƙanin Layla ya ce”gaskiya ba za’aje da twins ba a barmin su muyi wasa.”Dariya na yi na tashi na ce”ai ni daman yanzu na barmaka twins”dariya ya yi tayi yana murna wai na bar masa twins.

Ƴaƴan Anty Rabi huɗu ne uku maza mace ɗaya,maza biyun suna Germany acen suke karatu.


Ƙwalliya Salimat ta yi cikin wasu kayan bacci masu matuƙar ɗaukar hankali,sannan ta feshe jikinta da turaruka kala2,Sallama Jakadiya ta yi sannan ta ce”uwar ɗakina ga madara mai sanyi nasan kina so”.

amsa Salimat ta yi tasha tana mai jin daɗin madarar,ta saka lifayarta mai ƙyau ta yi hanyar ɗakin oga Admiral A.

Ta saman bene Rasheeda ta hango Salimat za ta je ɓangaren mijinsu,wani irin malolon baƙin ciki ne ya ɗarsu a zuciyarta ta saka a zuciyarta matuƙar tana numfashi sai ta tarwatsa fadar Salimat,don ta yi alƙawarin sai ta wargaza fadar Salimat awajen Aliyu don ta lura tun yanzu fadarta mai yawa ce awajensa.

Kuyi haƙuri matsalar charge na ke da ita.

Miss green ce
????SILAR FYAƊE????

????BOOK 2

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

addu’ar samun lfy ga ko wani irin ciwo

an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu’ar kamar haka;

“bismillahir turbati ardina biriqati ba’dina yashfa Taqimuna bi’izni rabbina”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button