SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

“Haba A/D ka tausayamin ka dinga ɗaga waya ta,kasan dai babu ƙyau wulaƙanta ɗan adam, please ka yadda ina sonka tsakani da Allah”.

“oky”.

kawai ya ce mata ya kashe wayar.

Salimat ta goge hawayen da suka zubo mata don matuƙar ba ta auri admiral ba komai zai iya faruwa,ya zamar mata dole Ƙara Ƙaimi wajen yin addu’ah don komai yazo da sauƙi,tana cikin wannan tunanin ta tashi ta shiga bathroom ta ɗauro alwala ta fara yin sallah tana kai kukanta ga mahaliccinmu subhanahu wata ala.

*** *** ***

yau aka yi 7 ɗin mahaifiyata dangi duk sun fara tafiya,har yanzu mutuwar mahaifiyata tana cikin ƙoƙon zuciyata,na share wata ƙwallar da ta cukomin ƙwarmin idanuna,na gogesu ina cigaba da ƙara tsanar wannan bawan Allahn da ya yi sanadin rugujewar rayuwar a halin gidanmu.

Ƙannena uku ne duk suna bording skull,Salimat,Afra,khadija.

Har lokacin kuma ba a gaya musu rasuwar mahaifiyarmu ba,ko ya ya zasuji idan suka ji mahaifiyarmu ta cika oho?.

ina cikin wannan tunanin naji an watsomin ruwan kanzo mai sanyi,don alokacin safiya ce,na waiga don ganin maiyi min wannan izayar,mmn nusaiba ce da kuma Hafsatu,wacce ta kasance ƙanwa awajen mahaifina.

Suna ta kumfar baki wai na iya munafunci na shiga ɗaki na ƙi fitowa don nasan na yi abin kunya.

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara fitomin a ƙwarmin idanuwa na,na gogesu na fita don yin aikin da suka ce zuciyata tana yimin ƙuna.

miss green ce
????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

         7????8

“Wata rana Umma ta aiki ni gidan Baba Na sidi sai akai rashin sa a ranar anyi ruwa kamar da bakin Ƙwarya,har Mama Khaltum tace in ƙwana na ce mata ai ban tambayi Mama ba,babu yadda bata yi dani ba nace ni tafiya zanyi haka na biyo hanya ga dare ga komai haka na fito ina ta tsare motoci amman babu wacce ta tsaya.

Na yi tagumi kamar zanyi kuka wata ƙyaƙyawar mota ce naga ta shawo ƙwanar titin,banji tsoro ba haka na tashi naje tsakiyar titi,ina tsayar da motar da hannuna,baiyi niyyar tsayawa ba amman sai da na tsayar dashi,sauke glass ɗin ya yi,kansa a ƙasa bai kalleni ba ya ce”come in”.

da sauri na shiga ina ta raba idanuwa,ban kalli mai motar ba shima bai kalleni ba,da alama bashi da lafiya don naji yana ta numfarfashi ni kuwa tsoro na ya ƙara ƙaruwa sosai jin wani baƙon al’amari yana ta ziyarta ta,shima a nashi ɓangaren haka wannan abin ya dinga faruwa.

In ta ƙaice miki a wannan dare ne abubuwa da dama suka dinga faruwa,na samu kaina a mai ƙin hanashi duk abinda ya ke son faruwa,tun abin yana tafiya gentle gentle har dai ya yi tsanani,ban san me ya faru dani ba?ban taɓa jin tsananin feelings ba sai aranar,a wannan dare komai ya faru kuka na ya tsananta sosai.

Shima hankalinsa ya tashi sosai da sosai,don ina jin gunjin kukan da ya ke yana cewa Allah ka sani ban taɓa zina ba,ban taɓa kusantar ta ba sai yau ya Allah idan mafarki na ke ka farkar dani ya Allah.

A matuƙar hargitse na fito daga cikin motar ina ji yana ta yimin magana don shima har fitowa ya yi,amman na fizge hannunsa na tsayar da wata adaidaita kamar ƴan party ya ɗebo,akayi sa a unguwarmu ɗaya don haka muka tafi.

Ina dawowa Baba yana kiciniyar kulle gida don sun san tunda na kai yanzu to sai gobe zan dawo,mamaki Baba ya yi na ganina amman bai ce komai ba ya matsamin na wuce,kai tsaye ban ɗaki na wuce ina kuka haka na cire sutura ta,kamar a mafarki haka na ke ganin komai yana dawomin,to me ya faru dani haka na bada kaina ga wani wanin ma ban sanshi ba.

Kaca kaca siket ɗina ya yi da jini ina kallonsa na saka wani ihu a banɗaki,Baba da ya ke a tsakar gida hankalinsa ya tashi yana tambaya ta lafiya,shiru na yi ina rufe baki nan ina kuka don tabbas na cigaba da kukan to kaina xan tonawa asiri.

Don wannan abin ba dole ya yi min ba,ban san me ya shiga brain ɗina ba,Rabiatu me addini me kishin musulunci,me girman kai awajen wasu saboda kamun kai to me ya sakani aikata haka kuma?.

Ina fitowa ina ɗingishi na hango Baba da Mama suna tsaye cirko2 suna kallo na na sunkuyar da kaina zan shige ɗaki,Mama ta daka min tsawa ta ce”aiken ne sai yanzu?Kuma me ya samu ƙafarki ki ke ɗingishi”?.

wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riskeni,gaba na yana dukan uku uku na buɗe bakina daƙer na ce faɗuwa na yi Mama,ba tare da ta ƙara cewa koma ba ta shiga ɗaki ita da Baba.cen kuma ta fito a lokacin ina zaune na yi tagumi da hannu bibbiyu ga ƙasa na kamar zai tsage saboda tsananin zafi.

“Rabiatu ina saƙo na”?.

sai alokacin na hau dube dube don sai yanzu na tuno na barshi a motar wannan azzalumin mutumin.

Anan zan tsaya saboda matsalar chagi.

Miss green ce????
????SILAR FYAƊE????
Free Book

      NA????

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

   9????10

. . .. .kuka na fara yi wa Mama ina bata haƙuri,cikin faɗa ta ce”to yanzu ina saƙo na ki ka fara kuka?ko dukanki na yi?”,cikin kukan na ce”wallahi Mama saƙon ya faɗi ki yi haƙuri don Allah”.

ta fa hannu ta fara yi tana salati ta ce”yanzu Rabi’a yarmin da kuɗin adashin ki ka yi kuɗi dubu hamsin da ɗoriya?amman kin cuce ni Rabi’a yanzu me zance da masu bina bashi”?.

Har yanzu kuka na ke Baba na ya shigo ya ce wa Mama ta yi haƙuri idan ya ɗauki salary zai bata dubu talatin ta rage asara.

Da safe da ƙer na tashi na tafi makaranta gashi muna jarrabawar waec da Neco munyi waec saura Neco,ban rubuta wani abin azo a gani ba,shiru kawai na yi dana shiga ɗakin exam ɗin,na yi ta gumi ina tunanin rayuwa ta,yanzu shikkenan wani cen ya ɓatar min da tantanin budurci na?me zance wa mijin da zan aura?alokaci ɗaya na tuno da Salis gumi ya shiga tsatstsafomin,don tuno da yadda ya ke ƙwatantamin daren farkonmu,to ni ta ina zan nishaɗantar dashi alhali kuma ina on-virgin.

Dukan tebir ɗin dana ke kai wani invigilator ya yi sannan ya ce”lfy me ya faru?can i help u?”.

duk lokaci ɗaya ya yi min wannan tambayar yana yimin wani irin kallo,sai a sannan na gane shi malamin daya na ce min sosai kamar wani cingum,na ɗanyi tsaki kaɗan yadda ba zai ji ba,na turo ɗan ƙaramin baki na gwanin sha’awa.
Lumshe idanu jibril ya yi yana tasbihi a cikin zuciyarsa,don matuƙar ya kalli Rabi’at yana tsintar kansa a cikin wani hali ya juya yana kallonta sosai yarinya kyakkyawa da ita,wato Rabi’at ita ba doguwa ba ita ba gajeriya ba,tsaka tsakiya ta ke,tana da yalwar mazaunai sosai don shiyyasa ma bata saka mayafi kullum sai hijabi,choco colour ce tana da siririn hanci da ɗan ƙaramin bakinta dai dai gwargwado,tana da idanuwa masha Allah waɗanda suka yalwatu da siraran eyelashes masu ɗaukar hankali,pinck lips ɗinta mai matuƙar ɗaukar hankali,tana da gashin jiki wanda ya ƙwanta luf gwanin sha’awa.

To wannan kenan.

Tunda wannan abu ya faru a rayuwata sai na zama so silent wani lokacin sai dai in shiga ɗaki inyi kuka in share hawaye na,abin dai yana matuƙar damuna,Mama tayi2 in faɗa mata abinda ya ke da muna amman abu ya gagara.

Cikin wannan halin ne na yi wani irin fari sosai na ɗashe sosai idanuna sukayi fari ƙal kamar madara,mama na suka ciko sukayi Ɓam dasu,tun abin baya damun mama har ya fara damunta ta shiga bincika ta don yadda na ke matuƘar Ƙellin goshi abin sai wanda ya gani,daman mazaunai ba a maganar su.

On serious Mama ta kafe ni da idanu ta ce”Rabi’atu yaushe rabonki da period?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button