SILAR FYADE HAUSA NOVEL

Kan Aliyu gaba ki ɗaya ya kulle ya rasa me zaiyi taka mai mai ga Hajiya ta saka shi a gaba akan Rasheeda,ga Mai martaba shima da ya sako shi a gaba akan Salimat kuma Mai martaban ya ce baya son bikin ya wuce wata ɗaya,haka zalika itama Hajiya ta ce ba ta son ya wuce wata 1.
to wa zai aura a cikinsu yabar wata?ana nufin sai dai ya haɗa su rana ɗaya ne ko kuwa?shi kansa gaba ki ɗaya ya kulle gashi yanzu wani irin tulo masa aiki a keyi a office.Ga ba ki ɗaya kansa ya yi mugun kullewa.
A hankali na ke rainon ƴan biyu na,kyawawa dasu kamar ka sacesu ka gudu saboda tsabar ƙyau da ƙwarjininsu,Abba na kuwa kullum cikin hantara ta ya ke yi dani da ƴan biyu na,ko laifin me su kuma sukayi oho.
Daman bai taɓa ɗaukarsu tun suna tsummansu har yanzu da suke wajen wata na uku.
Mmn junior ita ke kula da komai nawa hatta wankan jarirai ita ce ta yi min har nima kaina ita ta yi min,kaya kuwa kullum cikin aiko min dasu ta ke masu kyau.
Dangin Abba na dana Mama na babu wanda yazo don ya dubani ko yaga halin da na ke ciki.
Busy????
Miss green ce
https://arewabooks.com/chapter?id=6297ab36c8d26a9288bb4632
.????SILAR FYAƊE????
NA????
UMMU MAHER(MISS GREEN????)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
15????16
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya,yau saura sati guda auren Admiral A.da zanka zankaɗan matansa Salimat da kuma Rasheeda.
A ɓangaren ango dai babu wani shiri da ya ke,tunda aka fara shirin bikinma sai yau ya dawo daga tafiyarsa zuwa Holland,ya fito daga banɗaki kenan daga shi sai boxer yana goge jikinsa da tawul ɗin daya riƙo a hannunsa,gashin jikinsa ya ƙwanta luf luf,kawai ji ya yi an buɗe ɗakinsa an shigo babu ko sallama,da sauri ya juyo don ganin me yi masa wannan aika aikar don ya tabbata Hajiya ba za ta taɓa yi masa haka ba,su ma su Fatima ba za suyi haka ba don suna matuƙar jin tsoronsa.
Rasheeda ya gani a tsaye akansa kamar wata doki,babu tsayuwa ma irin ta mata a ah yadda kasan namiji haka ta ke,bata iya action irin na mata ba.
Wani banzan kallo ya yi mata sannan ya ce”ke! lfy zaki Shigo min ɗaki ba tare da sallama ba,haka aka koya miki rashin respect”.
ya faɗi hakan ya haɗe girar sama da ta ƙasa gashi ƴar wannan maganar da ya yi har ya fara haki don bai saba doguwar magana ba.
“Ai daman dole ka tambayeni me ya faru?ashe daman kai macuci ne maci amana,daman ba ni kaɗai zaka aura ba,to wallahi baka isa ka haɗa ni da kowacce mace ba don ni kaɗai aka halicce ka,don duk macen da ta raɓe ka ta raɓi mutuwarta”.
Kallonta kawai Admiral ya ke yana mamakin tsiwa da rashin tarbiyya irin na Rasheeda,ya rasa me ma zai ce mata duk shiru shirunsa ya ga alamar Rasheeda ƴar zafin kai ce kawai so take ta ɗora mai hawan jini.
Wata uwar tsawa ya daka mata sannan ya nuna mata hanyar fita ba tare da ya kalleta ba,da gudu ta arta ana kare gabanta yana mugun faɗuwa don ba ƙaramar dauriya ta yi wajen tsayawa ta yi mishi wannan tsiwar ba,tana fita ya riƙe kansa da ya ke sara masa don matuƙar ya yi magana da ƙarfi sai yaji kansa yana masa ciwo.
Da kuka ta samu Hajiya tana faɗa mata wai Aliyu ya zage ta,kallonta Hajiya Batakat ta yi sannan ta ce”ke fa Rasheeda ba ƙya bin komai a hankali,na gaya miki halin Aliyu yana da zuciya kuma mutunne mara son haya niya,kinga kuwa dole idan kina son kama mijinki a hannu sai kin iya makirci da sauransu sannan zaki mallekishi,kuma ko baki da haƙuri sai kin koya don Aliyu yana matuƙar son mai haƙuri,kinga wannan yarinyar ƴar sarkinnan tana da matuƙar haƙuri sosai shiyyasa har Aliyu ya yadda da aurenta saboda haƙurinta da kawar da kai,don haka kema ya kamata ki zama mai haƙuri sai kiga kin zama tauraruwa.”
Mahaifin Aliyu Shima haka ya ke da zuciya Allah yajiƙansa da rahama.
to da wannan shawarwarin yasa Rasheeda yin shiru sannan tana ayyana wa acikin zuciyarta ko ta halin ƙa-ƙa sai ta zama sarauniya a idon Aliyu.
Kuɗi sosai Aliyu ya ware ya bawa Hajiya Barakat na kayan lefe,da kanta taje dubai da wata ƙawarta suka siyo kayan lefe na gani na faɗa,ko wacce a cikinsu dozin biyu aka yi mata masu ƙyau da tsari,amman ba kala ɗaya bane don sai da aka tambayi kowaccensu ta faɗi kalar da take so.
Dinner kala biyu aka shirya ta farko Salimat ce ta shirya kayarta,a wani babban hall wanda ya gaji da haɗuwa,da ƙer Aliyu yaje don har kuka Salimat sai da tayi rannan sannan yazo sunyi matuƙar ƙyau,kayan da suka saka white ne ita ta saka gown fara ƙal sai net mai ɗaukar hankali,shi kuwa gogan farar shadda ya saka wacce taji aiki tana ɗaukar ido.
Ranar hauka ne kawai Rasheeda ba ta yi ba,saboda yadda wajen partyn ya haɗu sosai sannan su fatima duk sunje,ƙannen ango da amarya sun saka skye blue ɗin gown wadda ta yi matuƙar yi musu ƙyau.
Ana ta watsa musu sky ɗin rose flowers,abin sai wanda ya gani,hatta cake ɗin su ma sky ne.
Rasheeda ma ta yi na ta Dinner ɗin sai dai ko kusa bai kai na Salimat ba,Kuma gashi babu ango don tafiya ta tasowa Aliyu zuwa Germany don haka ya yi tafiyarsa don gaba ki ɗaya Nigeria ɗin ta ishe sa.
Ƙarshe har aka ɗaura aure baya nan don yana sane ya damƙa komai a hannun Amininsa Sooraj har haɗaɗɗen gidan da zai zauna da ke Abuja huse road,mai part huɗu wanda ya gaji da haɗuwa.
Haka nan aka fara ɗaura auren Salimat sannan na Rasheeda,wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ran Rasheeda ya yi ba har ma da Hajiya Barakat ta ji haushi,sai dai ba tada bakin magana don ƴan uwan mahaifin Aliyu ne suka tsara komai,don mahaifinsu Aliyu Bafula tani ne shi,kun san Fulani kuma da haɗin kai.
*** *** ****
Rabiatu tana ƙwance tana yiwa Afrah wanka ƴan biyunta kenan don Ammar da Afrah sunan yaran,hannunta har kakkarwa ya ke saboda wata muguwar yunwar da ta ke ji,a yanzu Ƙanwarta Afra ta koma makaranta,Khadija da Salimat ne a gida saboda sun zana jarrabawar waec da neco shiyyasa ma basu koma ba.
Ƙwata2 sun daina bawa Rabiatu abinci tana ji tana gani suke rabewa tsakaninsu su cinye,sai dai idan sun bar ɗan ƙanzo ta tattare taci a haka.
Don ma ƴan biyu suna da kufan jiki don ko a yanzu yadda kasan wasu ƴaƴan commisioner haka suke.
Bani da mai taya ni hira idan ba ƴan biyu na ba,sai Mmn junior amman su Salimat ko kallon inda na ke ba sa yi.
Wani lokacin idan na kalli Twins sai na fashe da kuka idan suka girma suka tambayeni ina mahaifinsu me zance musu?sai wani kuka yaci ƙarfi na yaci ƙarfina in ɗaga hannuna sama ina kuka ina roƙon Allah ya ya buɗe min wannan lulluɓin zanin in gane waye ubansu Afrah.
Ina cikin wannan tunanin naji gidan ana ta koke koke ban san ko meye ba,jiki na yana rawa na fito tsakar gidan don jirin da na keji,Afrah tana ta kuka don cire mata Mama da na yi a bakinta.
Miss green ce
????SILAR FYAƊE????
NA????
UMMU MAHER(MISS GREEN????)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
17????18
Wani tsalle na yi na rungume Anty Rabi ƙanwar mahaifiyata wacce naci sunanta,kuka sosai mukayi a ranar tuno da Mama,sannan Anty Rabi ta ce”babu abinda ban sani ba taƙwara na sanki tun kina ƙaramarki nasan abinda zaki aikata nasan wanda ba zaki aikata ba,amman ina mamakin yadda hakan ta faru”.
Kuka ne ya ɓalle min ina cewa”Anty Rabi wallahi ba laifina bane ban san sanda abinnan ya faru ba,na rasa yadda zan fassara abin,na rasa wa zai bani shawara”.sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.