SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

Wani kallon rainin hankali su Khadija suke min don gani suke kawai raina wa mutane wayo na ke amman nasan komai,a ganinsu ta ya ya mace za tayi cikin shege sannan wai ta ce bata san wanda ya yi mata ba?.

A hankali na bawa Anty Rabi labarin komai ina kuka kamar raina zai fita.

Shiru ta yi tana ɗan nazari na sannan ta ce”babu komai Rabi atu Allah n daya ɗora miki shine zai warware komai da yardarsa,abinda na keso da ke ki cire wannan tunanin a ranki ki cigaba da addu’ah Allah ya bayyana komai”.

Ƙwananta ɗaya ta ce za taje rijiyar zaki gidan kakaninmu sannan za ta dawo mu tafi Abuja tare da ita don zamana anan ba zai yiyu ba.

naji daɗi ta wani ɓangaren don nasan can babu mai zagi na ballan tana hantara,kuma ga su Laila ƴarta kusan sa a ta ce nasan zan samu nutsuwa.

Amman idan na tuno da barin gidanmu sai naji wani kuka ya kufcemin,ina tuno irin rayuwar da su Salimat zasuyi,don tun yanzu Salimat idan ta fita tun safe sai yamma ta ke dawowa,don tun safe idan Abbanmu ya fita sai dare ya ke dawowa,babu yadda ba ayi da Abbanmu ba akan ya yi aure amman ya yi banza da al’amarin.
da wuri na haɗa kaya na,na shirya twins cikin kayan sanyinsu wanda ya ƙarɓesu sosai gwanin sha’awa ɗaya daga cikin wanda Anty Rabi ta kawo mana jiya da tazo.

Har gida naje na yiwa Mmn junior Sallama tana ta kuka,Mmn nusaiba kuwa cewa ta yi Allah ya raka ta ki gona,daga nan ma in huce birnin sin.

Da wuri Anty Rabi ta dawo alokacin Abbanmu yana shirin fita ta ke sanar dashi hukuncin da ta yanke,magana ɗaya ya faɗa wacce sai da na zubar da hawaye ya ce”Allah ya tsare hanya idan taje ma kada ta ƙara tunawa cewa ni ne ubanta”.

abin y ƙular da Anty Rabi sosai amman ba tace komai ba har ya tafi,su kuwa ƙannena su Khadija kallona kawai suke yi amman sun kasa cewa komai har muka rabu.

Idanuwa suna zubar da ƙwallar rabuwa da gida shekara 17 kenan da aka haifeni a wannan gida ban taɓa ƙwana awani waje ba idan ba gidanmu ba tunda ba a saba mana da ƙwanan wani waje ba,ko da kuwa Rijiyar zaki ne unguwar iyayen su Mamanmu.

Tun da na ke a rayuwata yau ne rana ta farko dana hau jirgi sai tsoro ya kamani Anty Rabi ta amshi Ammar ni kuma ina riƙe da Afrah.

Cikin lokaci ƙanƙani muka sauka A Abuja,masha Allah kawai na ke faɗa saboda yadda garin ya ke gwanin sha’awa ga shi luf luf da ya ke lokacin sanyi ne.

Ban ƙara mamaki ba sai da muka shigo unguwarsu Anty Rabi ko wani gida da sunan mai gidan,duk gidan da ka gani sai ka ƙara kallonshi saboda ƙyau da tsaruwarsa.

Gidansu Anty Rabi ma gida ne mai ƙyau ga shi ƙato gwanin sha’awa sanyi da Ƙanshin flowers suna ta yi maka barka da zuwa,ji na yi kawai an rungume ni Laila na gani a gaba na tana ta dariya ta amshi Afrah a hannuna ni kuwa sai kallonta na ke yadda ta ƙara fari ƙal ga wata uwar ƙiba da ta yi,acikin lokaci ɗaya na tuno da yadda na ke ada.
*** *** ****

Motoci ne sun kai goma suka shigo ƙyaƙyawar unguwar a cikin ta tsakiya ne na hango Admiral A.yana zaune da system ɗinsa a hannu,yana ɗan wani nazari bisa wani bincike da ya ke.

Wayar sa ce ta ɗauki ƙara ganin mai kiran ya sa ya ɗauka a hankali,cikin girmamawa ya ke gaishe da mahaifiyar ta sa cikin yaren yoruba.

Ta ke tambayarsa ya iso Nigeria ne? ya ce mata eh ya shigo?nan ta ƙara yi masa nasiha akan ya kula da matansa musamman ma Rasheeda don ita ce ƴar uwarsa,to kawai ya ce mata sannan sukayi sallama.

A cen ɓangaren su Rasheeda da kuma Salimat kowaccensu taci ƙwalliya ta alfarma don taron miji musamman ma da yau suka cika ƙwana biyar a ɗakinsa ba tare da sun saka shi a idanuwansu ba.

Ummu Maher ce
????SILAR FYAƊE????

NA????
UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

19⬜20

Kai tsaye ɓangarensa ya nufa bai nemi kowaccensu ba,Rasheeda kuwa ta kafa ta tsare tana jikin windon ɗakinta ta saman bene tana hango Admiral A.sanda ya shigo don haka har komawa ɗaki ta yi ta ƙara shafa hoda da janbaki tare da ɗakko wani turarenta mai mugun ƙarfi ta shafa.

Ita kuwa Gimbiya Salimat tana kan sallaya ta ɗaga hannuwanta biyu tana roƙon Allah akan Allah ya mallaka mata ziciyar Sojanta.

Tana cikin wannan addu’ar jakadiyarta ta shigo tana neman iso,tana shigowa ta ce”uwar ɗaki na kuma uwar gida a wajen angonta Admiral A.Yanzu naga motocin Admiral sun shigo gidannan, don haka na garzayo don inzo in gaya miki wannan albishir.
Ɗan murmushi Salimat ta yi sannan ta ce”nima ina yi mishi barka da dawowa Allah ya tsare mana shi a duk inda ya saka ƙafafunsa,amman bazan je ɓangarensa ba don a yanzu hutu ya ke buƙata don haka nasan da kansa zaizo”.

kallonta Jakadiyarta ta yi sannan ta ce”haba uwar gijiyata kin fa san ba ke kaɗai ce matarsa ba yana da wata,ba kya tsoron ita yanzu taje ke baki je ba.”

“Hmm Yaya na fuskanci abinda ki ke nufi amman nasan kinfi kowa sanin ƴaƴan sarauta da kuma yadda suke gudanar da sha’aninsu na sarauta,don haka ba zan iya zuwa wajensa ba saboda kada ajina ya zube”.

Jakadiyarta dariya ta yi tana ganin wauta da kuma ƙuruciya ce ta ke damun Salimat don haka bata ƙara cewa komai ba ta fita daga ɗakin don tasan halin ƴaƴan sarauta akwaisu da kafiya.

Tun rana Aliyu ya dawo amman ko nan da cen baije ba,don yana shiga ɗakinsa da ya yi wanka yabi lafiyar gado ya ƙwanta don baya son hayaniya.

Rasheeda kuwa tana cen hankalinta a tashe don tana saka ran dawowar miji amman kuma taji shiru,don haka da kanta da daddare ta shirya cikin wasu arnan kayan bacci wanda sunansu sabon salon fanɗarinka a waje.

Sannan ta ɗakko wani turarenta wanda Hajiyar Aliyu tayo mata oder ɗinsa tun daga Sudan,matuƙar namiji ya shaƙesa to fa ya gama aiki.

A hankali ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,shi kuwa Aliyu ya zata mai kawo mishi abinci ne ya ce”come in”.

Babu wani jan aji Rasheeda ta shigo tana wani takunta kamar wata munafuka,tana shigowa ta cire hijabinta kai tsaye ta yi wajen Aliyu.

Miss green ce

Kuyi min afuwa rashin charge ne????????

Na gama littafin darasi free page,don haka idan mutum yana da buƙata ya tintibeni ta wannan no ɗin.

Ga ɗanɗano da ga littafin darasi na payments.

DARASI!DARASI!!DARASI!!!

Alokacin General A.ya shigo da muƙarabansa waɗanda suka rakosa motoci sunfi goma sha,tun daga nesa ya ke kallon kyakkyawar halittar Fahima ga gashinta sai ɗagawa ya ke kamar wara ba indiya ko balarabiya,ya yi tsaye yana kallonta yana mamakin a ina aka samo wannan kyakkyawar yarinyar?.

Dai dai lokacin aka tsuge da ruwan sama mai tattare da ni’ima da ƙanshin ƙasa haɗi dana flowers ɗin gidan,ga wata iska mai daɗi.

Tsalle Fahima ta ke tana wasa da ruwan kana ganinta ka ga yarinya,a hankali Ammar ya biyo ta bayanta ya cire rigar sanyin da ya saka ta sojoji ya lulluɓawa Fahima,da sauri ta juyo cikin tsoro,aka yi rashin sa a ta zame ta faɗo ƙirjin Ammar yadda kasan awani indian film haka abin ya faru,daga shi sai singlet,gashin ƙirjinsa ya ƙwanta kamar wani gashin jariri.

Kallon ƙuda suka shiga yi babu ko ƙiftawa zuciyoyinsu sai bugawa suke kowannensu zai iya juyo ta ɗan uwansa.

A dai dai wannan lokacin kuma hancin motar Hajiya Sakinat ta shigo,bata kula da abin da ke faruwa ba sai da ta fito sai da ta da fa murfin motarta sannan ta iya tsayawa da ƙafafunta,idanunta sunyi jawur kamar gauta wata wutar jaraba da wutar kishi Sakinat taji a ƙirjinta,cikin wani irin mahaukacin sauri ta tunkaro inda su Ammar da Fahima suke.
????SILAR FYAƊE????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button