SILAR FYADE HAUSA NOVEL

SILAR FYADE HAUSA NOVEL

25/26

Da sallamarta ta shiga ɗakin hankalinsa na kan system ɗinsa ya ɗukufa da aiki ya amsa mata ya ɗan kalleta kaɗan sannan ya cigaba da aikinsa,waje ta samu aɗan kaɗan da nesa dashi ta ce”ina wuni”a hankali shima ya ce “lafiya”sannan ya kashe system ɗin ya ce mata yana zuwa.

Bai daɗe ba sai gashi ya shigo da wata ƙatuwar farar leda sannan ya ajje ya shiga bayinsa ya yi wanka da ɗaura alwala a inda ya barta anan ya dawo ya sameta ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafin lifayar ta ta,ya ce”tashi ki ɗauro alwala zamuyi sallah”.a hankali ta tashi ta shiga banɗakin alwala tayo ta fito banɗakin nasa ya ƙawatu sosai wanda har sai da ya burge ta banɗakin kamar na mace komai fes dashi yana daga cikin abinda yasa ta ke matuƙar son Aliyu kenan aƙwai tsafta sosai.

Tana fitowa har ya tada sallah ta bishi suka yi har suka idar,a hankali ya ɗaga hannuwansa sama yana addu’ah tana amsawa da amin har suka gama tana jin ninkin ba ninkin ɗin son aliyu don bata Ƙara gasgata ilimin da ya ke dashi ba sai yanzu.

Ya kama goshinta ya shiga karanto mata addu’ar nan da manzon Allah(S.A.W) ya mana”alluhuma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wamin sharri ma jabaltaha washarri ma jabaltaha alaihi”.

Kaza ce ƙatuwa mai girman gaske sai fresh milk ƙaton ƙwali uku mai sanyi sai shawarma wacce tun kafin a buɗeta ƙamshinta ya cika hancin mutum.

Tura mata kazar ya yi dukkanta sannan ya tsiyaya madarar yasha ya buɗe swan yasha sannan ya Ƙwanta ya ce”sai da safe”.

wata ƙwallace ta biyo ta kuncin salimat ta kula kara kawai ya ke mata don kada ta fuskanci ba ya sonta,har cikin zuciyarta taji abin ya yi mata zafi amman yanzu ta wacce hanya ya kamata ta janyo hankalin aliyu don ya sota?babu mai bata amsa don haka ta Ƙwashe kayan ta kai fridge sannan ta Ƙudunduna a Ƙasan kafet ta Ƙwanta,aliyu yana kallonta sai da ya bari tayi bacci sannan ya sungumeta ya Ɗorata akan gadon sannan shi ya sakko Ƙasan ya Ƙwanta.


Da wuri na shirya na fito ina yiwa twins dariya don da sunga naci ado sai suyi ta maƘale min wai zamu tafi unguwa,yanzun ma haka ne ya faru suna hannun mama suka miƘomin hannu dariya mama ta yi sannan ta ce ai kuwz baza a tafi daku ba in rasa Ɗan hira”.

ƴar dariya na yi sannan laila tace”ai kuwa ba zamu tafi dasu ba sun saka ayi ta ganin mamansu matar aure gwara mutafi siƘau Ɗin Mu”.

har muka fito daga supet market na duba hannuna sannan na ce”ai kuwa laila na yi mantuwa”tsayawa ta yi a waje ni kuma na shiga don Ɗauko abinda na manta Ɗin wani anu naji na buge dashi kamar mutum don haka na juyo,,wata irin muguwar faƊuwar gaba naji tun daga kaina har Ƙasa na”.

ina godiya sosai fans ɗina na darasi da sauran littattafaina ina godiya sosai akan nuna kulawar da kuka nuna min alokacin da na yi rashin lafiya,lol saƙo har yanzu sunyi min yawa,don Allah waɗanda ban duba nasu ba suyi min uzuri ina godiya.????????????

miss green
????SILAR FYAƊE????

????BOOK 2

UMMU MAHER(MISS GREEN????)

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

27????28

Sosai gabana ya faɗi don ganin wanda na gani,bansanshi ba?ban san daga inda ya ke ba?amman kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba matuƙar ka kalli twins ɗina zakaga babu abinda ya banbanta su kawai abinda ya banbantasu shi babba su kuma yara.

Kasa barin wajen na yi shi kuwa yana ta siyayyarsa ya fito ta hanyar da na ke,wani glass ne na ɗora hannuna akai ban sani ba ina kallonsa kawai sai naji ya faɗi ƙasa ya tarwatse baki ɗaya,nan ta ke hankalin kowa yayo kaina,nima cikin tsoron na kalli glass ɗin.

Aliyu ma kallo inda yaji ƙarar glass ɗin ya yi sojoji biyu ne a tare dashi,kallona ya shigayi sosai ammanfa bani ɗin ya ke kallo ba hannuna ya ke kallo wanda ya yanke har yana fidda jini amman ni ban san yana fidda jinin ba saboda tsoro da firgici.

A hankali yazo inda na ke nima a lokacin kallon nasa na ke kawai don har yanzu mamakin kamannin na ke.

“Baiwar Allah kina bleeding baki sani ba”.da sauri na kalli hannun wanda sai a yanzu naji zafin hannun,alokacin securities ɗin wajen sunzo suna ƙwashe glass ɗin da ya fashe.

Alokacin Layla ta shigo hankalinta a tashe tayo kaina don ganin hannuna yana fidda jini tana tambaya ta me ya faru?amman ban ba ta amsa ba baki na yana rawa na ke nuna mata Aliyu,kallon inda hannuna yabi ta ke yi,a ta ke itama tayo waje da idanuwanta tana kallon inda na ke kallo.

Aliyu mamaki ne ya kamashi ganin suna ta nuna sa alhali basu sanshi ba,ganin shima mamakin ya ke yasa Layla ta buɗe wayarsa ta tako a hankali wajen Aliyu ta buɗe mishi hoton twins.

Shima waro idanu waje ya yi ganin waɗannan yaran masu mugun kama dashi ya yi imanin cewa ko da ƴaƴansa ne da ƙer zasu yi irin wannan kamar.
Da sauri ya ce”baiwar Allah wannan yaran yaranki ne?”.

A hankali Layla ta juya ta kalli Rabiatu sanman ta nuna ta da ɗan yatsa,kallon Rabiatu ya yi sosai ganin wai wannan ƴar yarinyar ce mahaifiyar yaran wacce ko a fuskarta bata nuna alamar ta taɓa haihuwa ba a ƙiyasce ma bata fi shekara 18 ba.

A hankali Aliyu ya ta ka ya i’sa wajen da Rabiatu ta ke wacce har a lokacin kallon Aliyu ta ke,a hankali ya ce “baiwar Allah biyo ni waje muɗanyi magana”.

Cikin wata iriyar muryar da Rabiatu bata san tana da ita ba tace”in biyo ka kace fa?ka ɗauka zaka ƙara yaudarata yadda ka yaudareni a baya,ka lalata min rayuwata ka cutar dani da gurɓatattun ƴaƴan da ka yi min fyaɗe na haifa maka”.

da sauri Aliyu ya juyo jin furucinta fuskarsa ta yi wani irin jajir jijiyoyin kansa suka tashi,da alamar allurar nan ta sojoji za ta tashi,da wani irin sauri ya fita don barin wajen don gani ya ke kamar a mafarki wai yau wata ce ta ke ce masa wai ya yiwa mata ciki.

Da sauri Layla ta kamo hannun Rabiatu don subar wajen don har mutane sun fara taruwa.

Muna fitowa muka iskesa a waje na ta ka a hankali naje inda ya ke,kallonsa na ke gabana yana mugun faɗuwa don ba ko wacce mace ce zata iya kallon Aliyu ta yi masa furucin da na yi masa ba na ce”Bawan Allah idan har kana ja inja akan ba kaine uban waɗannan yaran dana haifa ba muje ayi gwaji hakan shine zai ƙara tabbatar min da zargina don wallahi ko rantsuwa bana yi kaine uban twins.

Da sauri Ola wato sojan dake hannun daman Aliyu zai dakatar dani akan maganar da na kewa ogansu,shima Aliyu da sauri ya ɗaga hannu ya dakatar dashi don ko babu komai wannan yarinyar macece.

Aliyu baice komai ba ya ce”bayin Allah muje asibiti sannan ku ɗauko yaran?don gaskiya ni nasan ban taɓa auren wacce mace na saki ba,ballan tana ace ma wai harni Aliyu inyiwa wacce mace ciki amman ni nasan Allah yana nan.

Motar Aliyu daban tasu Haidar wato Aliyu daban.

Sai da suka shigo layin sannan yaga ashe layin da ya ke ne amman bai ce komai ba.

Atare suka fito harda Mama da kuma su Twins,Mama ma mamaki sosai ta ke na ganin Aliyu don babu abinda zaisa kaƙi cewa shine babansu Twins,shima Aliyu sai yanzu ya ke ganin wata muguwar kamar da sukayi da yaran kallonsu kawai ya ke yana kabbara har a fili.

Wani private hospital suka je aka yi sa a suna zuwa suka shigar da ƙorafinsu aka ɗauki jininsu dukka,shi kuwa Aliyu mamaki kawai ya ke wai yau shine a asibiti ana gwada jininsa wai ana zarginsa da yiwa mace ciki.

Suna zaune wata nurse ta fito ta ce”wai ku shigo dukkanku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Leave a Reply

Back to top button