NOVELSUncategorized

SOORAJ 13

????????????????????????????????????????

           *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

             *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance


            *Chapter 13*

Wani numfashi mai ɗumi ya fesar daga bakinsa, haɗe da maida idanunsa ya rufe,  kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin kunnuwansa, ji yayi tsikar jikinsa na tashi, hakanne ma yasa ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne.

Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana.   Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan,  sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba,  “To kenan ya akayi ta koma kan gado?” tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta.   Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi.  Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar.  Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi.    “Ya jikinna ka dai?” Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba.

Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaɗo ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta.

“Da sauƙi!” Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin.

“Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?” Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa.

“Babu” ya bashi amsa ataƙaice.

“Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!” 

Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo.

Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.     “Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya”  

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta.   Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa,  kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa,  tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban,  tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake.

Muryarta na rawa tace “YAH…YAH!!”   ita kanta batasan ya akayi ta ƙirasa da wannan sunan ba.

Cak ya tsaya daga murza hanunnasa da ya keyi  haɗe da buɗe idanunsa da suka zama jajur dasu,  ɗago da kansa yayi ya kalleta.

Sai da taji gabanta ya faɗi alokacin da  idanunsa suka sauƙa acikin nata idanun,  bakomai ya tsorata ta ba kamar yanda taga idanunsa sun rikiɗe daga farare zuwa jajaye. 

Ko second biyu bai ɗauka ya na kallonta ba ya sauƙe idanunsa ƙasa.

Ƙwalla ne suka cika idanunta, murya araunane tace “Dama…. dama.. Bansani ba ne ko kanajin yunwa”  tafaɗi haka tana mai murza ƴan yatsun hanunta.

“Miƙomin rigana”  yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ko ya tanka mata maganan da takeyi ba, babu musu ta ɗauko rigan nasa tazo ta miƙa masa, tashi tsaye yayi daga kan gadon haɗe da sanya rigarsa,  Kallon ƙafansa ƴayi yaga ko takalmi baida shi.  Hanu yasa ya dafe goshinsa.

  “Ina wayata?”
 yayi mata tambayar yana mai tsareta da idanunsa.

“Wayanka?” tafaɗa tana mai rarraba idanunta.

Yanayin yanda tayi maganar ne yasashi ƙanƙance idanunsa haɗe da ware su alokaci guda.

   “Wa ya kowani nan?” ya tambayeta yana mai ƙoƙarin maƙala aninayen dake gaban rigarsa.

“Ni da Kamalu driver ne” tabashi amsa tana mai wasa da ƴan yatsun hanunta. 

Ɗauke kansa kawai yayi daga kallonta, dai dai lokacin Dr.Haisam yashigo cikin ɗakin.

Sooraj na ganinsa yace “Ko zan iya samun aron waya?” 

Murmushi Dr.Haisam yayi haɗe da cewa “Eh” ciro wayarsa yayi ya miƙawa Sooraj ɗin.

Number’n Khalid yasanya acikin wayan Dr.Haisam haɗe dayin dialing.     Ringing biyu Khalid yaɗauki ƙiran,    “Ina Mahfuz Specialist  Hospital, kazo kayi dropping ɗina a gida”   Baijira mai Khalid ɗin zaice ba ya kashe wayan, miƙawa Dr.Haisam wayar yayi.  Takardan sallamansa Dr.Haisam ya miƙa masa. 

Mintuna kaɗan Khalid ya iso cikin asibitin.    Yana shigowa ɗakin, cikin tashin hankali ya kalli Sooraj cike da kulawa yace “Raj maiyasa meka haka, harda zuwa asibiti?” 

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa ” stress ne kawai, muje ko”  yaƙare maganar cikin yanayi na ƙosawa.

Motar Khalid suka shiga, suna zaune agaba ita kuma tana zaune agidan baya,     Khalid ne ke ta tambayar Sooraj jikin nasa cike da kulawa, amma kuma shi Sooraj ɗin cikin halin ƙosawa yake mayar masa da amsa.

Suna isowa gida Khaleed yayi musu sallama ya koma, dama aiki yabari a office ɗinsa ya zo.

Wanka yayi haɗe dayin brush sai alokacin yaji wani ɗan iskan yunwa na ƙwaƙulan cikinsa,   dogon wando yasanya da wata riga marar nauyi, kana ya zura slippers ɗinsa ya fita zuwa falo. 

Direct kitchine ya wuce, ruwan zafi ya tafasa haɗe da juyewa acikin flask.  Cup ya ɗauka ya haɗa tea, hannayensa ya sanya akan waist ɗinsa, yana ƙarewa kitchine ɗin kallo.   itace ta faɗo masa arai, yasan gaba ɗaya zaman yunwa tayi acikin  a asibitin.

Ruwan zafi ya ɗaura akan gas, mintuna ƙalilan ruwan ya tafasa  indomie ya jefa acikin ruwan haɗe da sanya spiece.  yana tsaye acikin kitchine ɗin, har Indomie ɗin ya nuna, acikin wani plate na tangaran mai kyau ya juye indomie’n.  hanunsa riƙe da plate da kuma cup ɗin tea ɗin ya fita zuwa falo.

Zaune  take akan gado, tayi jigum fitowanta daga wanka kenan, ta sanya wani riga da sket ƴan kanti.  Zuwa yanzu idanunta har sun soma rufewa sbd yunwa, gaba ɗaya ƙarfin jikinta ya gudu, duk da zama da yunwa ba sabon abu bane a wajenta.. 
 Wani irin murɗawa taji cikinta nayi.   Hanu yasa ajikin ƙofar ya ƙwanƙwasa, batare daya jira anbuɗe ƙofar ba ya juya ya koma cikin falon. Zama yayi akan kujera haɗe da ɗaukan cup ɗin tea ɗinsa ya soma sipping da kaɗan kaɗan.

Cikin rashin ƙarfi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, ganinsa zaune a falon yasa ta nufo cikin falon.

Durƙusawa tayi agabansa, kafun tace wani abu, ya turo mata plate ɗin imdomie ɗin gabanta.

Ɗago da kanta tayi ta kallesa, gani tayi kwata kwata idanunsa ba’akanta suke ba.  Ɗaukan plate ɗin tayi ta ɗaura akan cinyarta, loman farko da tayi ta lumshe idanunta, wanda suke cike da gajiya da kuma bacci,  sosai takecin indomie’n harta manta ma da cewa agabansa take.
Duk abun da takeyi yana lure da ita, duk wani motsin da tayi yana kallonta ta gefen idanunsa.    Bata gama cin indomie’n  ba har ya kammala shan tea ɗinsa yatashi yabar wajen, tana kammala cin indomie ɗin taji wata nutsuwa ta sauƙar mata, ɗaki ta koma tana kwanciya bacci yaɗauketa.

*** *** ***

Tun tashinta yau ta riga da ta gyara ɗakin da take kwana tsab, hakanan taji sha’awar shiga kitchine ɗin gidan, gani take kamar wahala take bashi don kullum saiya saya mata abun da zata ci, duk da cewa baya wuni agidan amma yana turowa ana kawo mata. Yanzu rabonma da ta sanya shi acikin idanunta kusan kwana biyu kenan.

Tsayawa tayi a kitchine ɗin tana ƙarewa ko ina da ina kallo, ita sam bata wani iya girkin zamani ba, shinƙafa kawai ta iya dafawa,   wata drawer dake cikin kitchine  ɗin ta buɗe, kayan abinci ta gani shaƙe acikin drawer’n,   ruwa ta ɗaura akan gas, wanda da ƙyar ta iya kunnasa, saura ma kaɗan wuta ya kama hanunta.   neman inda zata samu kayan miya tashiga yi, saidai neman duniya tayi bataga wani abu mai kama da kayan miya a kitchine ɗin ba, dolenta haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kitchine ɗin.

Fitowarta yayi daidai da shigowarsa cikin falon. Sanye yake da suit coffee colour, ya yinda ƴar cikin rigan ta kasance milk colour, Sosai yayi kyau. Har batasan sanda tasake baki tana kallonsa ba.

Kallonta yayi tare da kawar da kansa gefe.  “Ɗauko mayafinki” yace da ita ataƙaice.

Babu musu ta koma ɗaki ta ɗauko mayafinta.

Tafiya suke kowannensu da abun dayake saƙawa acikin zuciyarsa.  Gaban wani tangamemen gate taga sun tsaya yayinda yasoma danna horn ɗin motar. Wangale musu gate ɗin akayi ya tura hancin motar ciki.      adai dai wani ƙaton parking space ya yi parking motar.    “Muje” yafaɗa yana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar,  yana gaba tana biye dashi abaya, gaba ɗaya hankalinta naga tsirarun mutanen da tagani suna shawagi a tafkeken farfajiyan wajen, daga mata har mazan dake wajen sanye suke da uniform maroon and milk colour.     Direct office ɗin Mr. Isyaka Nuhu suka nufa, har cikin office ɗin akayi musu iso.   Cike da mutuntawa Sooraj yabawa  Mr. Isyaka Nuhu hanu suka gaisa.  Fuska cike da fari’a Mr.Isyaka Nuhu ya dubi  Ziyada haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj.   “Wannan itace yarinyar?” Ya tambaya.

“Eh” Sooraj yabasa amsa.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da danna ƙiran wata number,  yanajin an ɗaga ƙiran yace “Kasameni a office ɗina” yana aje wayar bawani jimawa saiga wani mutumi yashigo cikin office ɗin. 

Kallonsa Mr.Isyaka Nuhu yayi haɗe da cewa. 

  “Kuje da yarinyarnan kayi mata interview” 

“Okay Sir!” mutumin daya shigo ya faɗi haka haɗe da kallon Ziyada yace “Muje ko” 

Kallon Sooraj tayi saidai kuma taga sam idanunsa ba akanta yake ba, wayarsace ma ahanunsa yana dannawa..


(manage)


*Vote me on Wattpad*
    @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button