NOVELSUncategorized

SOORAJ 12

????????????????????????????????????????

            *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna#romance


      *Chapter 12*

Arazane ta tashi daga zaunen da take haɗe da waro manya manyan idanunta.   Lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa,  ƙafafunta na rawa haka ta nufi inda yake a yashe baya numfashi.

Hanunta dake rawa ta ɗaga haɗe da kaiwa kan fuskarsa, hanunta tasa adai dai saitin hancinsa, saidai bataji abun da takeson jiba, wato numfashi.

Tsorone yasake kamata, hanunta ta ɗaura akan kafaɗunsa ta shiga jijjigasa, cikin wata irin murya mai ɗauke da tsantsar tsoro haɗe da ruɗewa tace.   “Katashi ka buɗe idanunka Don Allah!”        wasu hawaye masu zafi ne suka soma sulalowa daga cikin idanunta suna sauƙa akan fuskarta.     Ganin jijjigashi da takeyi bazai kawo mata wata mafita ba, yasa aguje ta fice daga cikin falon,  wajen mutumin dake zaune a bakin tankamemen gate ɗin gidan ta nufa.  Yanayin yanda yaganta abirkice har yaso yaɗan tsoratashi.    Kafun yace wani abu ta rigashi cikin haki tasoma cewa….     “Baya numfashi kataimakeni kada ya mutu!”   

 Zaro idanunsa waje Sammani mai gadi yayi cike da tsoro. Yana ƙoƙarin tambayarta meke faruwa, yaga ta sake rugawa aguje ta koma ciki.  Cikin hanzari shima ya rufa mata baya.

Sake zube guiwowinta tayi  a ƙasa haɗe da cigaba da jijjigashi,   Dai dai lokacin Sammani mai gadi ya shigo,   ganin Ogan sa kwance aƙasa baya motsi yasanyashi ƙarasowa cikin falon da sauri har yana jin tuntuɓe.

“Meke faruwa mekikayi masa?” Sammani dake a ruɗe ya tambayi Ziyada wacce gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska.

Cikin tsoro tashiga girgiza kanta cikin sarƙewar murya tace.

“Wallahi banyi masa komai ba, bani bace, kawai nima gani nayi ya faɗi, Allah banyi masa komai ba!” Taƙare maganar tana mai fashewa da wani irin kuka mai sauti.

Da gudu Sammani yafita daga cikin falon, Kamalu driver yaje ya ƙira suka dawo falon a tare, hankalinsu amatuƙar tashe.

Da ƙƴar Kamalu driver da Sammani suka iya ɗaga Sooraj suka yi waje dashi, ganin haka yasa itama ta rufa musu baya, mota Kamalu ya buɗe suka sanyashi agidan baya. 

“Kajira gidan, mu zamu kaishi asibiti” Kamalu driver yace da Sammani mai gadi.   Kallon Ziyada da har yanzu idanunta ke fitar da ƙwalla yayi.   “Muje” yace da ita yana mai buɗe mata murfin motar,  da saurinta ta faɗa cikin motar shima Kamalun yashiga.  Sammani ya buɗe musu gate suka fice daga cikin gidan, gudu sosai Kamalu keyi hakan yasa basu wani jima ba suka isa asibitin da yasan Sooraj ɗin nazuwa. 

Da taimakon wasu likitoti aka ɗaura Sooraj akan wani gado mai ƙafafun taya, sannan aka gungurasa zuwa Emergency Room.. 

Kai Ziyada ta cusa acikin cinyoyinta, haɗe da sakin wani sabon kuka,   addu’a take aranta Allah Yasa ba mutuwa yayi ba, hakanan takejinsa acikin wani ɓangare na jikinta, ko ba komai yayi mata hallacci, ya killace rayuwarta daga gurɓacewa, bazata taɓa son wani abu ya sameshi ba.    

A Emergency Room kuwa sosai likitoti suka duƙufa akansa wajen basa taimakon gaggawa,  da ƙyar suka samu suka shawo kan al’amuran, alokacin da suka gano matsalar kuwa baƙaramin mamaki sukayi ba, domin sun gano cewa allura akai masa ko yayiwa kansa, wacce take da mugun haɗari sannan tana da ƙarfin gaske, aƙalla idan a kayiwa mutum ita zai iya kaiwa sati ɗaya batare daya san inda hankalinsa yake ba, koda kuwa ya farfaɗo ba zai dawo cikin hayyacinsa da wuri ba, sai dai ma shi Sooraj ɗin yaci sa’a jininsa na da ƙarfi sosai,  amma duk da haka ƙarfin alluran yayi tasiri acikin jikinsa.     Drip suka ɗaura masa sannan suka wuce dashi wani ɗaki na musamman, kasancewar kusan duka likitotin asibitin sun sansa, don yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana dubawa koda akwai waƴanda suke da buƙatar taimako shi yakan zuba dukiyarsa ya taimaka musu. 

Dr.Haisam wanda yake ɗaya daga cikin manya manyan likitotin asibitin  ya kalli Kamalu driver,  dawo da kallonsa ya kuma yi ga Ziyada wacce har yanzu kuka take….   

“Tare kuke ne?” Dr.Haisam ya tambayi Kamalu yana maiyi masa nuni da gefen da Ziyada’n ke zaune.

“Eh ƙanwar Oga ce” Kamalu driver yafaɗi haka, don ya rasa ma mai zai ce.

Kai Dr.Haisam yajinjina alaman gamsuwa,   kallon Ziyada ya kumayi wanda itama a yanzu kallonsa takeyi.

  “Biyoni Office”  yace da ita yana mai nufar hanyar office ɗinsa. 

Kallon Kamalu driver Ziyada tayi,  kansa ya jinjina mata alamar ta bi Dr. Haisam ɗin, jiki a sanyaye tabi bayanshi.

Zama Dr.Haisam yayi akan kujera haɗe da yi mata nuni da wata kujera dage aje gabansa yace “Ta zauna”  

A ɗaɗare ta zauna akan kujeran tana mai murje ƴan yatsun hanunta.

“Ya Sunanki?” Dr.Haisam ya tambayeta.

Murya araunane tace “ZIYADA”

Kansa yajinjina haɗe da maimaita sunan ZIYADA acikin ransa.

“Ki kwantar da hankalinki Ziyada, ki daina kuka kinji, yayanki zai warke insha Allah, Ina iyayenku suke? don yana da kyau na tattauna matsalan dake damunsa dasu”  

Ɗago jajayen idanunta tayi ta kallesa,  murya asanyaye tace.
“Basanan sunyi tafiya!”   ita kanta batasan ya akayi taji ta furta wannan ƙaryan ba, sai dai kuma bata da wani abun da zata ce masa ne wanda ya wuce hakan.

Ajiyar zuciya Dr.Haisam yayi haɗe da cewa.

“Shikenan ba damuwa, amma a wannan yanayin yayanki yana tsananin buƙatar kulawarki, bazance miki zai farfaɗo a yau ko gobe ba, wannan na Allah Ne, amma ki zauna atare dashi ki basa kulawa har zuwa farfaɗowansa,  idan drip ɗin da aka sanya masa ya ƙare kizo ki ƙirani saina cire masa ko” 

Kanta kawai ta kaɗa masa alamar    “To”

“Tashi kije”  yace da ita yana mai ƙoƙarin haɗa wasu takardun dake kan table ɗin gabansa.

Tana fitowa Kamalu driver ya tambayeta wai me Dr.Haisam ɗin yace mata.

“Babu”    kawai ta basa amsa ataƙaice, wata Nurse ce tazo garesu, kallon Kamalu driver tayi haɗe da cewa “Oga yace katafi ƙanwartasa sai ta kula dashi”   kai Kamalu driver ya jinjina alaman gansuwa, sannan nurse ɗin ta wuce gaba Ziyada ta rufa mata baya. 

Nurse ɗin na nuna mata ɗakin da yake kwance ta juya tayi tafiyarta.  Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga.

Yana kwance akan gadon asibitin, kansa da jikinsa duk suna fuskantar sama, yayinda idanunsa kuwa suke a rufe ruf, wata na’ura ne mai kamar computer agefensa,  yayinda aka saƙala masa wata ƴar waya da tafito daga jikin na’urar a ƙirjinsa.   Wasu hawayene taji sun taru sun cika idanunta, wani irin tausayinsa ne mai ƙarfi ya ɗarsu acikin zuciyarta.

Ahankali ta taka har zuwa jikin gadon,  kan kujeran dake kusa da gadonnasa ta zauna, a kusa da inda hanunsa yake ta ƙifa kanta.  Kusan 30 minute ta ɗauka tana zaune a wajen,  a hankali ta ɗago kanta haɗe da duban ledan ruwan da aka ɗaura masa, gani tayi saura kaɗan ruwan ya ƙare.   Dawo da kallonta tayi zuwa jikinta,  kwata kwata ta manta da shigan dake jikinta, baƙar doguwar riga ce  ajikinta mai dogon hannu, sai kuma mayafin rigan dake ɗaure akanta,  warware mayafin rigan tayi da yake yana da girma ta rufe jikinta dashi,  fita daga cikin ɗakin tayi, da ƙyar ta iya gane office ɗin Dr.Haisam, yana zaune tashigo tasanar masa cewa ruwan yakusa ƙarewa..

Cire masa ledan ruwan Dr.Haisam yayi kana ya barsa sai zuwa anjima asake sa wani.

Dr. Haisam na fita daga cikin ɗakin tasoma jin ƙiran sallan Magriba, wanda yake fitowa daga cikin masallacin dake gefen asibitin. 

Kallon ƙofar da Dr.Haisam yace mata nanne banɗaki tayi,  ahankali tatura ƙofar tashiga, banɗaki ne mai kyau da tsafta,  gaban sink taje ta ɗauro alwala sannan ta fito. 

Tsayawa tayi tana nazarin yanda za’ayi tayi sallah babu sallaya, duk da cewa rayuwar rashin ƴanci da kuma ƙauyanci tayi, hakan baisa ta zamo mace mai wasa da sallah ba, duk da bawani ilimi take dashi akan addini ba, amma tana kyautata zaton wajen bazaiyi sallah ba idan har ba a shumfuɗa sallaya ba,   kallonsa tayi yananan dai a yanda yake, ahankali ta ƙarasa jikin gadon, aƙalla ta ɗauki sama da 7 minute tana kallonsa, jitayi duk ƙwalla suncika idanunta,   buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fice.   Tana fita daga ɗakin taga wata nurse zata wuce, da sauri ta ƙarasa gareta haɗe da gaisheta. 

Amsa mata gaisuwar nurse ɗin tayi tana mai ƙare mata kallo.

“dama Sallah zanyi shine kuma banda sallaya ko zaki ɗan aramin” Ziyada ta tambayi nurse ɗin tana mai sanya mata fuskar tausayi.

“Biyoni muje ki amsa” nurse ɗin tafaɗi haka tana mai ci gaba da tafiyarta.   Sallaya hadda Hijab nurse ɗin ta bata, ta kumace ta riƙe a wajenta zuwa gobe,  godia Ziyada tayi mata sannan tadawo ɗaki, shumfuɗa sallayan tayi  haɗe da tada Sallah.   Sosai ta jima a sujjadanta na raka’an ƙarshe, addu’a tayi sosai akan Allah yabawa Mai taimakonta lafiya.   “Mai Taimako” shine sunan da Ziyada ta raɗawa Sooraj acikin zuciyarta.  Tananan zaune akan sallayan har aka ƙira sallan Isha..   Shima a sujjadan ƙarshe saida tajima tana addu’a kafun ta ɗago.  Shiru haka ta zauna akan sallayan haɗe da jingina bayanta ajikin bango.  Har ƙarfe 9 Ziyada na zaune agefen gadon,  sannu ahankali yunwa ke ƙwaƙulan cikinta,  gyan gyaɗi ta fara mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa.  Cikin dare     Sanyin AC ya dameta, tashi tayi ta lulluɓe jikinta sannan ta koma bacci. 

Washe Gari.

Tunda ta tashi da asuba tayi sallah, wani bacci yasake ɗaukanta, ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe 8 na safiya. Ban ɗaki ta wuce taje  ta wanko fuskarta, tana zama akan kujera Dr.Haisam ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, gaishesa tayi cike da girmamaw,   fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata.

Checking ɗin Sooraj ya sakeyi, yaji daɗin ganin komai Normal kuma zai iya farfaɗowa ako wani lokaci.

Hannayenta ta ɗaura akan kumatun ta haɗe da kafesa da manyan manyan idanunta, kyakkyawar fuskarsa take kallo, babu wani abu dayafi saurin ɗaukar hankali akan fuskarsa kamar yalwataccen sajen sa, wanda yake baƙi siɗik, ga zara zaran eye lashes ɗinsa da suke a mimmiƙe, sosai suka ƙarawa fuskartasa kyau, hakan yasa bata taɓa gajiyawa da kallonsa…

Wasa Wasa har ƙarfe 5 na yamma Sooraj bai farfaɗo ba, haka Ziyada ke zaune awajensa, batare da ta ci wani abu wai sunansa abinci ba, ruwa kawai take ta zubawa cikinta.  Tun yunwar na damunta har tazo ta daina ji, yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Taimakonta ya buɗe idanunsa.

9:30 pm  Babbar yatsan ƙafarsa ta dama ne ta soma motsawa  sai kuma yatsun hanunsa,   sannu sannu bugun zuciyarsa ta dai dai ta, yayinda cikin sakannin da basu wuce huɗu ba brain ɗinsa ta soma aikin. 

Ahankali ya soma buɗe idanunsa,  da kaɗan kaɗan yake ware idanun nasa hakan yasa ya soma ganin komai dishi dishi. Sannu ahankali idanun nasa suka washe, kallon saman ɗakin daya gansa aciki ya soma yi.  Sake ɗan lumshe idanunsa yayi, komai daya faru ya dawo cikin kansa,  ɗan yunƙurawa yayi ya tashi zaune haɗe da jingina bayansa da pillow,    juyo da kansa yayi zuwa gefen damansa,  idanunsa suka sauƙa akanta, tana zaune akan sallaya ta jingina bayanta da kanta a  jikin gadon da yake, bacci takeyi cikin yanayi na takura, da dukkan alamu bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, domin kuwa hadda goran ruwa riƙe ahanunta, ƙurawa fuskarta idanu yayi,  hango wasu  zanen busassun  hawaye  yayi  kwance akan fuskarta,   kallon yanda ɗan ƙaramin bakinta ke ɗan buɗe yayi.  Janye idanunsa yayi daga kanta, haɗe da ɗan tattaro ragowan ƙarfin daya rage masa ya sauƙo daga kan gadon. 

Ƙofar da yake tunanin nanne toilet ya nufa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa.  Kunna shower yayi ya tsaya ruwa ya dake shi sosai.   Dogon wandonsa kawai ya maida batare da ya sanya rigar shi ba ya fito daga cikin toilet ɗin. 

Zama yayi abakin gadon haɗe da sanya hanu ya dafe kanshi dake yi masa ciwo sosai, hakanan yakejin shi  wani iri,  gaba ɗaya babu wani isashshen kuzari ajikinsa, yasan hakan kuma duk yana daga cikin sharrin Alluran da yayiwa kan shi ne. 

Kallon shi  ya kuma maidawa zuwa gareta, har yanzu tananan tana wahalallen baccin daya ɗauketa,  gaba ɗaya jikinta a tukuikuye yake da Hijab,  tashi yayi ya ƙarasa jikin window’n ɗakin, hanu yasa yaɗan buɗe labulen window’n kaɗan, gani yayi gaba ɗaya duhu ya mamaye sararin samaniya,  hanu yakai yashafi aljihun wandon dake jikin shi,  atunanin shi wayar shi na tare da shi.  sai dai kuma saɓanin haka yaji shi  wayam, ɗan kalle kalle yasomayi acikin ɗakin ko zai hangota amma baiganta ba,  komawa yayi ya zauna akan gadon yana mai lumshe idanunsa, saboda wani juwa da yaji yana neman ka da shi.   Aƙalla yakusan mintuna goma idanunshi suna  lumshe, jin da yayi juwan yasoma lafawa ne yasanya ya tashi tsaye, inda take zaune ya nufa, tsayawa yayi akanta ya kasa ta ɓuka komai.  Ɗan ranƙwafowa yayi ya ɗagota caɗak,  kan gadon da aka ajiye musamman don taya majinyaci kwana ya ɗaurata,   a hankali ya zare hijab ɗin dake jikinta ya ajiye mata shi agefe.  Ziyada da baccinta yayi nisa sam batasan meke faruwa ba, saima ƙara gyara kwanciarta  da tayi, sakamakon jin ta samu sauyin makwanci.     Komawa kan nashi gadon yayi ya kwanta,  lumshe idanunsa yayi bawai kuma don yanajin bacci ba saidan kawai babu wadataccen ƙarfi ajikinshi..

Yatsun ƙafanta ya ƙurawa ido, azahirin gaskiya yatsunnata yake kallo, amma kuma hankali da tunaninsa ba agareta suke ba, yayi nisa acikin wani tunanin daban, baiso ace ya biyewa zuciyarsa ba, baiso ace ya kasa haƙurin ɗaukar ƙaddaransa ba,  duk da cewa shiɗin mai raunine amma yana fatan dacewa anan gaba, saidai aduk sanda yayi wannan tunanin sai wata zuciyar ta gargaɗesa da kada ya yaudari kansa, dolensa haka yake haƙura  ya watsar da tunnin acikin ransa. 

Buɗe gajiyayyun idanunta tayi, ganin haske tarwal acikin ɗakin yasa ta tashi aɗan zabure, kallonta takai wajen window gani tayi har hasken rana yasoma bayyana ta jikin window’n.  Da sauri ta zuro ƙafafunta daga kan gadon,   dai dai lokacinne kuma idanunta suka sauƙa akansa, yana kwance ya bata baya.

Sake waro idanunta tayi haɗe da mutsutstsukasu  atunaninta ko gigin bacci takeyi ganinsa da tayi babu riga, bayan koda zata kwanta tabarshine sanye da riga ajikinsa.        “Kodai likita ne yazo ya cire masa riga’n tana bacci bata sani ba?” tambayar da tayiwa kanta kenan. 

Ahankali ta sauƙo daga kan gadon, cikin sanɗa tataka harzuwa inda yake kwance.

Kanta ta ɗaura ajin gadonnasa, lokaci guda idanunta suka kawo hawaye murya araunane tace.

“Mai Taimakona Allah yabaka lafiya, tausayinka nakeji sosai, banso wani abu ya sameka!” taƙare maganar daidai lokacin da hawayen dake cikin idanunta suka samu daman gangaro zuwa kan fuskarta,  daidai lokacinne kuma shima da tun tashinta zuwa yanzu yanajin abun da takeyi ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan….

     *Vote Me On Wattpad*
        @fatymasardauna  

#love
#fantasy

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button