NOVELSUncategorized

SOORAJ 14

????????????????????????????????????????

          *SOORAJ !!!*

    *Written by*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*


           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

#romance

         *Chapter 14*

Basu wani jima ba suka fito daga ɗakin da akeyiwa duk wani ɗalibi da yakasance sabon zuwa interview.  Direct office ɗin principal ɗin suka koma zuciyar Ziyada cike take da farinciki da kuma jin daɗi, addu’anta ɗaya Allah yasa hasashen da takeyi yazamanto gaskia.

“Har kun gama interview ɗin?” Mr. Isyaka Nuhu ya tambayi Sir. Yusuf wanda shine ke yiwa duk wani sabon ɗalibi dazai shigo makarantar interview.

“A’a Sir ai ma bata taɓa zuwa makaranta ba, inaga kawai sai dai afarayi mata lesson”
Sir.Yusuf yafaɗi haka cikin siga irinta bada shawara. 

Jinjina kai Mr. Isyaka Nuhu yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj wanda har yanzu wayarsace riƙe ahanunsa yana latsawa. 

“To kaji abun da yace, ya kagani ko za’a fara yi mata lesson ɗin, idan ta ɗan soma iya wasu abubuwan sai abata ko s.s.one ne”

Sai alokacin ya ɗago kansa, wannan murmushin nasa da baya wuce kan laɓɓansa yayi haɗe da cewa. 
“Bakomai hakan yayi, yaushe za’a fara lesson ɗin?”

“Ai tunda kusan munkammala komai ko yau ma idan kun shirya sai afara yi mata” Inji cewar Mr. Isyaka Nubu (Principal).

“Okay ba damuwa, ni zan wuce”  Sooraj yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, hanu yabawa Principal ɗin sukayi musabaha, kana yabawa Sir. Yusuf ma suka gaisa,  ko kallon gefen da take baiyiba ya fice daga cikin office ɗin.

Principal ne yace da Sir.Yusuf  suje ya samo mata malamin lesson su fara tun yau, hakan kuwa akayi,   Wani Teacher Abdallah Sir.Yusuf ya samo mata, wanda shine zaina koyar da ita lesson everyday, hatta ranan saturday da sunday zai na zuwa koya mata gida, domin biyanshi za’ana yi.

abubuwa masu sauƙi Teacher Abdallah yafara koya mata, sam babu wani abu da ta fahimta tana dai jinsane kawai, duk kuwa yanda taso ta fahimci abubuwan sam ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka.
***
Zaune yake atamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan parking shirt dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin, turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba, yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take jin son sa acikin ranta, komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa, uwa uba kuma kyau da kwarjininsa dake tafiya da imanin duk wata mace da zatayi tozali dashi,  cikin takunta nason ɗaukar hankalinsa tasoma takowa zuwa cikin office ɗin.   Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi wacce ta shigo cikin office ɗin nasa,  jiyayi wani abu ya toshe masa maƙoshi,  sam yatsani ganinta ko kaɗan bayaso tana raɓarsa, baisan ita wace irin mace bace wacce bata da zuciya ko kaɗan.    Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba,  cikin muryar shagwaɓa tace. 

  “Barka da hutawa ranka ya daɗe”

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita,  bakinta da yaji pink lips stick taturo gaba.   “Maiyasa kakemin hakane wai Raj? at least dai ko kallona yakamata ace kayi wajenka fa nazo” taƙare maganar tana ɗan bubbuga ƙafafunta, alaman shagwaɓa.

Sai alokacin Sooraj ya ya ɗago kansa, saidai bai kalli inda take ba.    “Kina da buƙatar wani abu ne?” yatambayeta ata ƙaice.

“Kainake da buƙata Raj, wallahi kainake da buƙata, kafi kowa sanin yanda na damu dakai, maiyasa kake min haka ne? kadubeni Raj nacika mace irin wanda take girgiza zuciyoyin maza amma maiyasa bazaka dubeni ba? na amince ma kayi duk wani abun da kakeso dani amma maiyasa bazaka amince min ba!” taƙare maganar kamar zatayi kuka.

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da tashi ya ƙarasa gaban fridge, buɗewa yayi ya ɗauko ruwa mai sanyi, saida yasha sosai kafun  ya sauƙe goran ƙasa,  inda suit ɗinsa ke aje ya nufa, ɗaukan suit ɗin yayi ya saƙala ahanunsa,  touch watch ɗin dake hanunsa ya duba,  gani yayi akwai sauran time sosai kafun lokacin tashinsa ya cika, amma a yanda  Aneesa tashigo masa  office baya jin zai ƙara mintuna biyu acikin office ɗin.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da rufe laptop ɗinsa,   juyawa yayi ya nufi ƙofar fita yana mai karkaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa.

Da sauri Aneesa tasha gabansa, idanunta cike da ƙwalla tace “Please Raj ka tsaya atare dani, kasani kaine burina da kuma fatana, maiyasa kakemin haka ne?”   hawayene suka gangaro daga cikin idanunta.

Sai alokacin Sooraj ya ɗaura idanunsa akanta, kallonta yayi tun daga samanta har zuwa ƙasa. sannan yasaki wani killer smile. 

   “Bani hanya na wuce”  ya faɗa mata haka cikin halin ko inkula.

“Bazan baka hanya ba Raj, harsai kamin abinda nakeso, please Raj kasani akullum da buƙatarka nake kwana, please kabani dama ko sau ɗaya ne.”  

Ƙanƙance idanunsa yayi haɗe da tamke fuskarsa alokaci guda, cikin takaici yasanya hanunsa ya turata gefe, harsai da kanta ya bugu da bango, ƙofar office ɗin ya buɗe ya fice abunsa.

Kuka Aneesa tasanya mai ɗauke da tsananin ɓakin ciki da takaici,  takardun dake kan table ɗin office ɗin ta soma watsarwa a ƙasa tana kuka, ta tsani wannan banzan halin na Sooraj,  a kullum baida wani buri da ya wuce ya wulaƙantata, mai tarasa wanda har zai tsaneta haka? alƙawari tayiwa kanta matuƙar ta rasa Sooraj to kowacce mace aduniya ma tarasashi domin bazata taɓa ɓari ya auri wata mace ba idan ba ita ba.

Yana fita ya wuce wajen da yayi parking motarsa, sama sama yake amsa gaisuwar  ma’aikatan dake gaidasa.  Yana shiga cikin motar yayi mata key haɗe da ficewa daga cikin bank ɗin, direct wani hotel ya nufa……

Sosai Teacher Abdallah ya dage ya zuba mata lesson,  lokacin da aka kaɗa ƙararrawan tashi ga duka ƴan makarantan dai dai lokacin shima ya dakata daga koyar da ita english lesson ɗin da ya keyi.    Tana fitowa ƙofar ajin taga cincirondon ɗalibai maza da mata kowa na ƙoƙarin kama gabansa, ko ta ina acikin makarantar ɗalibaine, yayinda parking space ɗin makarantar kuwa ke cike da tarin motoci, har waje motoci ne a fake, duk wani ɗan makarantan dazaka kalla, kallo ɗaya zakayi masa ka hango alamun zaman naira ajikinsa, domin daga mata har mazan gaba ɗayansu ƴan gayu ne, da alama kuma kowa yanaji da kansa.

Kamalu driver ta hango ya nufo inda take, wata ajiyar zuciya ta sauƙe, domin kuwa da har tafara tunanin yanda za ayi ta koma gida ita kaɗai. 

Gaba ɗaya yau tsananin farincikinta ya kasa ɓoyuwa, jinta take cikin farinciki. Haka ta koma gida zuciarta cike da jin daɗi.  Wunin ranan gaba ɗaya haka tayishi cikin jin daɗi, duk yanda taso ganinsa tayi masa godiya abun yaci tura, domin kuwa ko motsinsa bata jiba

*** *** ***

Kullum sai Ziyada taje Lesson Kamalu driver ne ke kaita shine kuma ke dawo da ita, sosai ta kejin daɗin lesson ɗin nata, yanayin yanda ta dage tasanya son karatun acikin ranta shi ya ƙara sanya teacher Abdallah dagewa wajen ganin ya koyar da ita yanda zata fahimta,  zuwa yanzu dai tana ɗan fahimtan abubuwa da kaɗan kaɗan, musamman ma wajen karatun Hausa da kuma rubuta shi,  ta ɗan ƙware ta wajen wannan fanni, har ma idan taga abu zata iya karantashi, English ɗinne dai sai a hankali. 

Tun ɗazu aka tashe su saidai ga mamakinta yau Kamalu driver baizo ɗaukanta ba, gashi ɗaliban da suka rage acikin makarantar basu wuce ƴan tsiraru ba sam basu da wani yawa.   Kalle kalle take tayi ko zata hango Kamalu driver amma babu shi babu alamarsa.  Tsaye take a harabar makarantar, sanye take da doguwar riga da kuma Hijab, hannayenta nannaɗe suke akan ƙirjinta.  

Tun daga nesa yayi parking ɗin motar, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, ahankali ya ware idanunsa haɗe da sauƙesu akanta,   hakanan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akanta, kusan 2 minute ya ɗauka yana kallonta, mai da idanunsa yayi ya rufe,  wani irin gajiya haɗe da kasala ne yaji sun sauƙar masa alokaci guda.  Buɗe murfin motar yayi haɗe da zuro ƙafafunsa waje.  Tun fitowarsa daga cikin motar idanun ɗaliban da ke wajen ya dawo kansa.  Yanayin yanda yake taku cike da nutsuwa shine abun daya burgeta, har batasan sanda ta saki wani murmushi ba.  Yana ƙarasowa inda take yace.

 “Kijirani a mota” baijirayi mai zata ce ba, yayi gaba abunsa, tana kallonsa ya shige cikin office ɗin principal.  Juyawa ita tayi ta nufi inda ya aje motar tasa, jingina tayi da jikin motar tana jiran zuwansa. Baiwani jima ba ya dawo hanunsa riƙe da wata leda.

Tunda suka ɗauki hanya babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu kowa da irin tunanin da yake saƙawa acikin zuciyarsa,  yarda da abun da zuciarta ke gaya mata da tayi yasanya ta gyara zama cikin wata murya mai sanyi tace. “Nagode Yaya”

Bai kalli inda take ba, bai kuma tanka mata ba,  jin yayi shiru bai ce da ita komai ba yasa taji jikinta yayi sanyi.  Saidai kuma kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa. .  

“Waye yayan naki?”  yafaɗa cikin tsare gida, batare daya kula sashin da take ba. 

Jin tambayar nasa yasa ta ɗago da kanta ta kallesa, tsintar kanta tayi da kasa ɗauke idanunta akansa, musamman ma data ga hankali da idanunshi ba akanta suke ba.

“Kallon kuma fa?” yafaɗa adaidai sanda yake shiga wata kwana, da zata sadasu da gida.  

Da sauri ta janye idanunta daga kan nasa azuciyarta tanajin wani iri…..


Monday.

Yau ne zata fara shiga Class itama tayi karatu kamar yadda  ko wanni ɗalibi keyi.  Fitowarta daga wanka kenan. Ledan daya bata jiya da dare ta ɗauko, kayan shafa ne aciki sai kuma uniform da takalman makarantar ta. gefe kuwa wasu biscuit ne manya manya.  

Sama sama ta shafa mai ajikinta, babu powder bare wata uwa kwalli haka tabar fuskarta,  uniform ɗinta wanda suke riga da wando ta sanya, wandon irin mai tsukakken ƙafannan ne amma ba har canba, yayinda tsawon rigan ta kasance har zuwa guiwarta,  rigan milk colour ce, wandon kuwa shike da kalan maroon.   Warware hijab ɗin makarantar tayi tana ƙare masa kallo, bashi da wani girma da kaɗan tsawonsa ya wuce cikinta.  Tana sanya hijabin taje gaban makeken mirror’n dake ɗakin ta tsaya tana mai kallon kanta aciki, duk da cewa uniform ne amma sosai tayi kyau, white skin ɗinta yasake fitowa acikin maroon colour hijab ɗin,   jinta tayi awani ta kure, sam batajin zata iya sakewa acikin mutane da irin wannan shigartata,  sam bata saba ba,hakan yasa take ganinta wata daban.  Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan safanta ta sanya, tana kammala sa safa ta zura takalminta me kama da toms, sosai takalmin yayi mata kyau gashi milk colour kalan riganta.     Tunowa da maganan teacher Abdallah tayi inda yake ce mata “tazo da wuri kada ta sake ta makara”  tashi tayi da sauri tafice daga cikin ɗakin.

Tana fitowa falo daddaɗan ƙamshin turarensa da daɗinsa ke sanya taji wani bacci ya daki hancinta, hakan ya tabbatar mata da cewa bai jima da fita daga falon ba.  Da saurinta itama ta fita daga cikin falon, tana fita ta hango ficewar motarsa daga gidan.  Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da nufan inda Kamalu ke tsaye, ba wani ɓata lokaci ta shiga suka ɗauki hanyar makarantar…

Suna zuwa direct office ɗin teacher Abdallah ta nufa, don dama anan yace ta sameshi.

Teacher Abdallah yana ganinta yasaki murmushi..
 “Student!” yace da ita yana mai faɗaɗa fari’arsa. Murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa da kanta. Yana kammala abubuwan da yakeyi ya ce suje ya nuna mata ajin da zata zauna,  yana gaba tana biye dashi a baya. 

S.S 1 A  shine abun da aka rubuta asaman ajin daɗan manyan baƙi,   ɗalibaine  waƴanda aƙalla zasu kai su 25 acikin ajin maza da mata, wasu suna zazzaune, yayinda wasu kuwa ke tsaye, wasu kamma akan desk suke zaune,   suna ganin shigowar Teacher Abdallah ko wanne daga cikinsu ya shiga cikin nutsuwarsa, cike da girmamawa suka tashi  tsaye dukansu suka gaidashi, amsa musu yayi haɗe da basu izinin zama.    Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da  cewa 

“Ga sabuwar ɗaliba nan nakawo muku, ina fata zaku karɓeta hanu bibbiyu, sannan idan bata gane abuba, inaso kuyi mata ƙarin haske” cikin harshen turanci yake maganan.   Kallon Ziyada dake tsaye tama kasa ɗago kai ta kalli mutanen ajin yayi.

“Ga wajen zamanki nan daga yau” yafaɗi haka yana maiyi mata nuni da wata kujera wacce take tsakiyan wasu ƴan mata…


(Kuɗan ƙara haƙuri show ɗin yana gaba.)


   *Vote Me On Wattpad*
       @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button