NOVELSUncategorized

SOORAJ 15

????????????????????????????????????????

               *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*
{United we stand and succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
*https://ww.facebook.com/kainuwawritersassociation*


            
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance

            *Chapter 15*

Cikin sanyinta ta nufi inda teacher Abdallah ya nuna mata.  Ɗaya daga cikin ƴan matanne ta bita da wani irin kallo.  teacher Abdallah yana ganin ta zauna ya fice daga cikin class ɗin bayan ya bata jakar makarantarta mai kyau.

Gaba ɗaya jinta take atakure, kasancewar kusan gaba ɗaya rabin ƴan ajin idanunsu na kanta. 

“Sannu!” matashiyar budurwan dake gefenta ta faɗa, wacce aƙalla bazata wuce sa’an Ziyada’n ba.

Sai alokacin Ziyada ta ɗago da kanta ta kalli wacce tayi mata maganan.  murmushi tayi mata haɗe da cewa  “Yauwa!” 

Murmushi itama yarinyar tayi tare da sake cewa.
“Sunana Nasmah, kefa?”

“Sunana Ziyada”  Ziyada ta bata amsa tana mai ɗan faɗaɗa fari’an dake kan fuskarta.

“Nice name!”  Nasmah tafaɗa tana mai ɗaukan wani text book dake gabanta.

Ɗan satan kallonta Ziyada tayi haɗe da yin murmushi, duk da cewa bata fahimci me Nasmah’n take nufi ba. 

Shiru Ziyada tayi bata sake cewa komai ba,  yayinda suma ƴan matan sukayi shiru, Nasmah gaba ɗaya hankalinta nakan littafin dake hanunta, yayinda wacce ke gefen Ziyada ta ɓangaren damanta kuwa ko ƙala bata ce ba, sai dai time to time tana yawan kallon Ziyadan, maganane abakinta amma saboda halin jin kai irin na Shukhra ta kasa cewa komai.

Wani malami ne ya shigo cikin ajin, dukansu ɗaliban suka tashi tsaye haɗe da gaidashi, sai da ya ɗan yi rubutu kaɗan akan white board ɗin da ke cikin ajin sannan ya basu izinin zama.

Darasin Maths yake koyar musu cike da ƙwarewa, yayinda gaba ɗaya ƴan ajin suka bada attention ɗinsu gareshi, ciki kuwa hadda Ziyada, wacce  ɗigo ɗaya na daga cikin abun da yake koyarwa bata fahimta ba,  jinsa kawai take, tana kuma kallon yanda yake solving guestions.   Tambaya yayi da sauri wacce ke gefen hagunta, wato Shukhra kenan ta ɗaga hanu, ya ta da ita ta bashi amsa, ƴan ajine suka hau yi mata tafi.   Haka dai ya gama yi musu karatun ya fita abunsa.  Yana fita baifi da mintuna 5 ba wani Malamin Biology ya kuma shigowa.   Tunda malamin yafara darasi’n ta kafe allon da idanu, turanci yakeyi musu cike da ƙwarewa, sannan gaba ɗaya explanation ɗin da yayi musu da turanci yayi su, tunda ya shigo babu wani wanda yayi Hausa haka kuma shima ko A akalmar hausa bai ambata ba, kamar dai yanda wancan malamin maths ɗin yayi haka shima wannan ɗin,    hakanne ma yasa sam bata fahimtan komai, domin kuwa turanci zalla suke basa ko ɗan surkawa da yaren da zata gane wato Hausa, lokacin da taga kowa ya ciro littafinsa yana rubutu itama sai ta buɗe jakarta wanda Teacher Abdallah ya bata,  bayan littatafai dake cikin jakan hadda wasu tarin kayan snacks.  Wani littafi ta ciro haɗe da pen.  Dayake Teacher Abdallah ya ɗan koya mata rubutu a lesson ɗin da sukayi, hakan yasa rubutun bai wani bata wahala ba, sai dai kuma bata wani ƙware sosai ba.  Gani tayi shima kafun ya fita saida yayiwa ƴan ajin tambayoyi, amma inda Allah Ya taimaketa ita bai tambayeta ba, kuma ko dama ya tambayeta saidai ta bashi amsar shiru.   Yana fita wani malamin yakuma shigowa shima dai yaɗan jima yana musu darasi kafun ya fita.  Yana fita aka buga ƙararrawan fita break, gani tayi da ɗai ɗai  ɗaliban ajin ke  ficewa zuwa waje,    Shukra ce ta miƙe tafice daga cikin ajin.

“Bazaki fita break bane?”  Nasmah dake ƙoƙarin tashi tsaye ta tambayeta.

Samun kanta tayi dayin murmushi haɗe da cewa.

“Zan fita” 

Ganin kowa yana fita da jakarsa rataye akafaɗarsa ne, yasa itama ta ɗauki ƙatuwar jakarta ta rataya akafaɗanta,  sai da ajin ya zama babu kowa acikinsa sannan ta miƙe ta nufi hanyar fita,  awani babban barandan dake gaban ajin ta tsaya tana mai bin ɗaliban dake ta hada hadarsu a harabar makarantar da ido, kowani ɗalibi ka gani yana tare da abokinsa, yayinda wasu kuwa sukaiwa kansu mazauni akan kujerun da akayi da siminti wanda ke ƙarƙashin wasu bishiyoyi dake harabar makarantar,   zama tayi akan makeken dakalin dake ƙofar ajinsu, yayinda ta zuro da ƙafafunta ƙasa,  aranta wani daɗi takeji wai yau itace acikin makaranta makarantar ma ta boko,   yunwa takeji na ƙwaƙulan cikinta don haka ta buɗe zip ɗin jakarta, wani cake dake cikin wani haɗaɗɗen leda ta ciro, tare da fito da goran peach ɗin dake cikin jakar,   ɓare ledan cake ɗin tayi ta soma gutsura ahankali, gani take kamar idanun gaba ɗaya ƴan makarantar akanta suke, musamman ma da taga duk wanda yazo gilmawa ta inda take sai ya kalleta,  tana cikin cin cake ɗinne, ta hango Nasmah da Shukrah na tahowa zasu dawo aji.  Suna ƙarasowa gareta Shukra ta wuce yayinda Nasmah ta tsaya akusa da ita,  cike da kulawa tace.
“Me kikeyi ke ɗaya anan?”

“Babu” Ziyada ta bata amsa tana karkaɗe Hijabinta da burbuɗin cake ya ɗan zuba akai.

“Tashi muje Class, ko kin gane lecture’s ɗin da akayi mana yau?” inji cewar Nasmah.

Ɗago kanta tayi ta kalli Nasmah’n,  samun kanta kawai tayi da girgiza mata kai alaman “A’a”

“Okay to muje Class” Nasmah tafaɗa tana mai ƙoƙarin haura dakalin ƙofar ajin nasu.

Tare suka shigo ajin ita da Nasmah,  Nasmah  ne ta ciro littafin Maths ɗinta, ahankali ta shiga yiwa Ziyada bayani dalla dalla da Hausa yanda zata fahimta, abun mamaki kuma sai gashi ta ɗan gane wasu abubuwan,  tana kammala koya mata Maths ɗin ta ɗauko Biology shima ta koya mata, aikuwa harma tafi gane Biology’n akan Maths ɗin, kasancewar shi baida  lissafi, bakamar Maths ba, har subject ɗin da akayi musu na ƙarshe kafun break wato Agric science saida Nasmah ta koyawa Ziyada, Alhamdulillah kuma ta fahimta sosai, akuma ɗan lokaci ƙanƙani wata ƴar shaƙuwa ta shigo tsakaninsu da  Nasmah, duk abun da sukeyi Shukrah na jinsu, amma ƙala bata ce musu ba, saima wata fakekiyar wayarta data ciro ta soma latsawa.  Suna kammala karatun aka dawo break.

Sosai suke shan karatu basu suka samu kansu ba sai  ƙarfe 1 na rana nan ma sallah aka fito dasu.  Nasmah ne ta jata suka nufi masallacin dake cikin school ɗin, Nasmah saida ta jirata tayi alwala sannan itama tayi, atare suka shiga cikin masallacin nan suka iske Shukrah tana sallah, gefe suma suka samu suka tada nasu sallan, suna idarwa Nasmah ta sake kama hanun Ziyada suka fito daga cikin masallacin.   Aji suka koma kowa yaciro abincinsa yafara ci,  ita dai da bata da wani abinci sai snacks shi ta ciro ta ɗanci kaɗan, Nasmah ce tayi mata tayi’n  soyayyen doya da naman kaza wanda tazo da shi, amma sam taƙi ci babu yanda Nasmah batayiba akan taci amma taƙi dolenta ta haƙura. 

5:00  pm daidai shine lokacin tashinsu akowacce rana, yauma biyar na cika dai dai aka kaɗa ƙararrawan tashi.  Tare da Nasmah suka fito tana fitowa ta hango Kamalu driver tsaye ajikin mota, sallama tayiwa Nasmah da Shukrah sannan tanufi inda yake tsaye. 
Tana shiga yaja motar suka bar haraban makarantar.

Tana shiga cikin falon, daddaɗan ƙamshin turare ya daki hancinta, ko ina na falon a gyare yake tsab.  Ƙofar ɗakinsa ta kalla, sannan ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta soma cire kayan uniform ɗinta,  ban ɗaki ta shiga ta yi wanka, yanzu babu abun da bata iya amfani dashi ba na cikin banɗakin.

Tana fitowa awanka ta sanya kaya haɗe da faɗawa kan gado, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, wani irin gajiya haɗi da bacci takeji, basaban ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani ƙaton akwati dake aje cikin ɗakin. Tashi tayi ta nufi inda akwatin yake tana buɗewa taga kayane shaƙe acikin akwatin, kama daga kan dogin riguna riga da sket ƴan kanti, da kuma dogin wanduna,  murmushi tayi haɗe da lumshe idanunta, batasan da wani baki zata gode masa ba, amma tabbas Ya Zama MADUBI acikin rayuwarta, da sannu itama zata haskaka ta zama kamar wata TAURARUWA. Komawa tayi ta kwanta cike da ɗokin sababbin kayan da tayi masu yawa.   Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasa tatashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala bata tashi akan sallayan ba saida ta yi sallan Isha, tana gama naɗe sallayan da tayi sallah akai, ta faɗa kan gado, wani irin baccine ke fusganta,  tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauketa ko lufayan dake jikinta bata cire ba.

Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa abun yaci tura, kwance yake akan makeken Royal bed ɗinsa wanda yaji lallausan bedsheet.  Idanunsa dake alumshe ya buɗe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa dake wani irin sara masa kamar zai faɗo ƙasa haka yakeji.  Gaba ɗaya duniyar bata yi mashi daɗi, ƙuna yakeji acikin zuciyarsa abubuwa da yawa ne suka haɗe masa,  hanunsa na dama ya sanya akan cikinsa wanda ke ɗauke da manya manyan 6 packs,  ahankali ya ke murza fatan cikinsa,  idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jajur dasu.  Cigaba yayi da murza fatar cikinsa da ɗan ƙarfi haɗe da cije laɓɓansa.  “Sai yaushe ne zai zama mutum me cikakken lafiya? sai yaushene zai san cewa shima Namiji ne? yaushe ne damuwarsa zata gushe? yaushe ne zaiyi bacci acikin farinciki da nishaɗi? yaushene zaiji abun da yake buri da fatan ji watarana? Abun tambayar aransa shine yaushe ne yazama haka? yaushe ne kuma zaici wannan jarabawar tasa mai wahala?”  waƴannan tambayoyin su yakeyiwa kansa akullum, sau tari yakan cire rai amma yasan Allah na sane dashi idan yana darai watarana zai dace,  amma kuma yaushene wannan ranan zata zo? shine abun da baisani ba,    tashi yayi ya zauna still hanunsa nakan fatar cikinsa yana murzawa. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon,   gaban window ɗinsa ya nufa, tsayawa yayi ajikin window’n haɗe da sanya hanu ya yaye labulen window’n, buɗe glass ɗin window’n yayi  take wata iska mai daɗi ta bugi fuskarsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, ɗaga kansa yayi yana kallon sararin samaniya, farin wata ne ya haske ko ina da ina.  Ahankali ya kejin nutsuwa na sauƙar masa, sosai yakejin daɗin ni’imar dake hurawa, yajima tsaye ajikin window’n kafun ya dawo cikin ɗakin.  Kwanciya yayi akan gado yayinda ƙafafunsa ke ƙasa, ahaka wani bacci ya ɗaukesa, dagani kasan bajin daɗin baccin yake ba.

** ** 

Tun 7 ta kammala duk wani shirinta,  saboda ta fahimci ba aso azo late a makarantar, duk yanda ta buga sammako wajen fita, amma bata iske shi afalo ba, saidai ta iske daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, haka tashiga mota Kamalu driver yaja motar suka tafi batare da tayi tozali dashi ba.

Kamalu driver na tsaida motar ta  ɗauki jakanta haɗe da soma ƙoƙarin buɗe murfin motar.     “Ga wannan Oga yace abaki” Kamalu driver ya tsaidata tahanyar faɗan haka, yana mai ciro kuɗi acikin aljihunsa.

Kallon kuɗin tayi sannan ta kalli Kamalu driver.  “Ni kuma mai zanyi dasu to?” ta tambaya cike da mamaki.

“Haka dai yace abaki, hala ko kuɗin taran ki ne” Kamalu driver yafaɗi haka yana me ƙara miƙo mata kuɗin.

Cikin sanyin jiki tasa hannu ta amshi kuɗin, sannan tafice daga cikin motar aranta tana mai cewa da zaran takoma gida zata tambayeshi, hala ko wani abu ya keso tasayomasa da kuɗin.  

Yau ta riga Shukra da Nasmah zuwa saboda haka ita kaɗai ta zauna tayi jigum,  ba wani jimawa sosai sai gasu sunzo atare, ga mamakinta yau fuskar Shukra asake take babu tsumewa kamar na jiya,  Nasmah na ganinta ta saki murmushi haɗe da ƙarasowa ta zauna akusa da ita.   “Yau munyi late kin rigamu zuwa” Inji cewar Nasmah dake ƙoƙarin sauƙe jakarta dake kafaɗarta.

Ta buɗe baki zatayiwa Nasmah magana kenan malami ya shigo ajin. Sai bayan yafita ne suka ɗanyi taɗi da Nasmah.. Yau dai sosai Nasmah tasake jawota jikinta ko ina zasu tare suke zuwa kuma Shukra na biye dasu saidai bata cika yawan magana ba. Hatta sallah yau atare sukayi su duka ukun.   Ko da suka idar da sallan ma tare sukaci abinci wanda Shukrah ce tazo musu da jallop rice wacce taji ɗanyen kifi.

Yauma agajiye ta dawo daga school ɗin tana idar da sallah ta soma bacci. 

*** ***
Yau kimanin sati guda kenan tana zuwa makaranta, Alhamdulillah yanzu kam tana ɗan fahimtan wasu abubuwa musamman da Nasmah ta dage da koya mata,  acikin waƴannan kwanaki tayi sabo da Nasmah sosai, duk da cewa Shukra na shiga sha’aninta yanzu amma sunfi sabo da Nasmah,  aduk tsawon kwanakinnan bata taɓa ganinsa ba koda sau ɗaya ne,  saidai idan ta fito falo tana samun tsaraban ƙamshinsa dayake barmata akowacce rana.


(Wallahi yau ina busy sosai, tun jiya nagama typing amma bansamu daman yin update ba sai yanzu, . please kuyi manage da wannan banyi editing ba. Love you all and Son So.
Ku ƙaramin yawan Vote na ƙara muku yawan typing????)


     *Vote Me On Wattpad*
         @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button