NOVELSUncategorized

SOORAJ 16

????????????????????????????????????????
   
          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 16*


Saturday!

Kamar dai yanda kowa ya sani saturday ranar hutuce ga yawancin ɗaliban makarantar boko.   To haka ranar yau ta kasance saturday wato (Asabar).  Zaune take aƙasa ta tanƙwashe ƙafafunta, jakar makarantarta ne agabanta, sai kuma wani littafin English ɗin dake riƙe a hanunta,  lecture’n da akayi musu jiya take dubawa, so take karatun ya zauna akanta sosai, don taji malamin nacewa wani sati zai basu Assignment.  Tunda tayi sallah ta ke riƙe da littafi, gaba ɗaya hankali da nutsuwarta naga littafinta so take ta iya duk wani abu da aka koya musu,  a yanda ta ba da himma ne yasa ta fahimci wasu abubuwa da dama, wato shi karatu ɗan naci ne idan kanace masa da yardan Allah Zaka iya,  sannan zaka gane komai sannu ahankali, yarda da wannan da tayi ne yasa abubuwa da yawa dake cikin karatun da take suka zauna akanta.    Yunwar da ta soma ƙwaƙulan cikinta ne yasa ta aje littafin haɗe da jingina bayanta da jikin gado, ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci, kasancewar daren jiya bata wani samu isashshen bacci ba, domin kuwa jiya ba tayi bacci da wuri ba, har sai wajen ƙarfe 12:30  na dare sannan ta kwanta, karatu tayi sosai, sannan gashi kuma yau tayi tashin sassafe sakamakon wani irin zazzaɓi dake ta sanɗanta tun jiya da rana, amma dayake zazzaɓin baiyi ƙarfi ajikinta ba hakan yasa bata jikkata ba. 
***
Duk da cewa yau Asabar amma bayajin zai iya zaman gida, shi kansa yasan yana da buƙatar hutu amma kuma yasan ko ya zauna agida hutun nasa bazai samu yanda yakeso ba.  Fitowarsa awanka kenan yana ɗaure da towel a ƙugunsa, sannan kuma ga wani ɗan ƙaramin towel still dake riƙe a hanunsa, yana tsane ruwan dake kansa.   Yana gamawa ya ɗauko handryer, da shi yayi amfani wajen busar da gashin kansa, mayinsa mai ƙamshi ya shafa, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar dake kansa, mayukan gashi har kala uku ya shafawa kansa, take gashin kannasa ya ƙara  bayyana sheƙi da kuma walwali.   Dogon wandon jeans wanda ke ɗauke da zane irin na kayan sojoji ya sanya, wandon irin mai yawan aljihunnan ne sannan ƙasan wandon atsuke yake da rubber,  wata farar t-shirt ya sanya ajikinsa,  take kyawunsa ya sake bayyana sosai kayan suka amshi jikinshi, kasancewarsa namiji mai murɗaɗɗiyar surar jiki,  gun ƴar ƙaramar drawer’n da yake aje drugs ɗinsa ya nufa, wani magani dake cikin sachet ya ciro,  tare da ɓallan guda biyu ya watsa abakinsa, sannan yakora da ruwan swan. Hanunsa riƙe da goran swan ɗin ya nufi falo.

Yana shiga cikin falon ya soma bin ko ina dake cikin falon da kallo, ko alaman datti babu acikin falon, hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas gyara falon akayi, duk da cewa dama babu wani datti acikin falon, amma dai kallo ɗaya zakayi kasan an gyara falon.

Kitchine ya wuce ya tafasa ruwan zafi acikin heater cup, yana gamawa ya juye a flask.   Zama yayi akan dinning tare da haɗa tea ɗinsa.  Sanya kofin tea ɗin yayi agaba ya kasa koda  ɗauka ne yakai bakinsa, sai jujjuya spoon ɗin dake  hanunsa yake acikin cup ɗin, yanayin yanda ya nutsu yayi shiru shine abun da zai baka tabbacin cewa tunani yakeyi.   Tabbas kuwa tunanin yake, maganganun da mahaifinshi yayi mishi masu tsauri su suke damunshi, bai ɗauka fushin da mahaifannashi keyi dashi har yakai haka ba, bai taɓa tunanin suma zasuƙi fahimtarshi ba,  maganan da Abbanshi yayi mishi akan cewa  wai ya nemo matar aure ya aura, acikin ƴan ƙanƙanin lokaci idan ba haka ba kuma kada ya sake ƙiran wayanshi shine abun dake damunsa, tabbas hukuncin da Abbansa yayi mishi yayi tsauri da yawa, koda wasa baitaɓa tunanin zasu sake kawo mishi maganar aure nan kusa ba,  ya ɗauka zasu fahimceshi a wuce wannan stage ɗin,  ashe abun ba haka yake ba.  Wayarsa dake gefensa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira,  jikinsa a sanyaye ya ɗaga ƙiran tare da kara wayar akan kunnensa.  

Mas’oud dake zaune acikin motarsa yace
 “Gaye na shigo Abuja fa yanzu”

Cike da ɗan mamaki Sooraj yace 

“Da gaske?”

“Bakayarda ba?”  murayar dake cikin wayar Sooraj ne ta bayyana raɗau acikin falon, da sauri Sooraj dake zaune akan dinning ya kalli ƙofar falon.

Mas’oud yagani yana murmushi.

Murmushin da iya kansa leɓe Sooraj yayi tare da kashe wayarsa.  
“Kai ɗan rainin hankaline Mas’oud” Sooraj yafaɗi haka yana me kallon Mas’oud dake takowa zuwa garesa.

“Ni ne ɗan rainin hankali, ko kuma nida kai ne dukanmu ƴan rainin hankali?” Mas’oud ya faɗi haka yana mai ƙoƙarin jawo wata kujera dake fuskantar wacce Sooraj ke kai ya zauna.

Still ɗan guntun murmushinsa yayi,  haɗe da ɗaukan kofin  tea ɗinsa ya ɗanyi sipping kaɗan. 

 “Sauƙar yaushe?” 
ya tambayi Mas’oud.

“Banwuce 30 minute da sauƙa ba”  Mas’oud yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin ɗaukan wani cup zai haɗawa kanshi tea, duk da cewa bawani damuwa da tea din yayiba kawai don yanajin yunwa ne ya sanya zai sha. 

Ɗan sipping tea ɗin kaɗan yayi, tare da kallon Sooraj da yaketa aikin juya tea da spoon ɗin dake hanunsa,  ya ɗan karanci damuwa akan fuskar Sooraj ɗin, amma da yake yasan kwanan zancen sai kawai ya share haɗe da cewa..
  “Ya maganan waƴannan kayanne? kasanfa yanzu babu kaya aƙasa” 

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe haɗe da cewa “Next week zanje USA zan taho dasu” 

Kai Mas’oud  ya jinjina cike da gamsuwa sannan yace.
 “Amma baka karɓi ribanka na wannan month ɗin bafa”

Shiru yayi baice komai ba, aƙalla yaɗauki kusan 4 minute bai tankawa Mas’oud ba, ganin haka yasa Mas’oud yin murmushi kawai  ya cigaba da shan tea ɗinsa. 

Ganin bazai iya shan tea din bane yasanya shi miƙewa tsaye,  yana ƙoƙarin barin wajen Mas’oud yace.
 “Inason muyi magana dakai” 

Komawa yayi ya zauna tare da ɗaukan wayarsa ya soma latsawa   “Inaji!” yace ataƙaice.

“Aure nakeso nayi” Mas’oud yafaɗi haka yana wata ƴar dariya.

Ajiye wayan Sooraj yayi tare da dawo da duk wani attention ɗinsa ga Mas’oud.   

“Aure kuma?” ya tambaya da ɗan mamaki.

“Eh Aure mana, gaskia Raj na gaji, shekaru 29 fa ba wasa ba, ko so kake na zauna sha’awa ta kasheni bansamu na kawar da ita ba?” Mas’oud yafaɗi haka yana mai kafe Sooraj din da idanu.

Sunkuyar da kai ƙasa Sooraj yayi tare da cije laɓɓansa, wani irin abu mai ƙuna yaji acikin ƙirjinsa, ahankali ya ɗago kansa ya kalli Mas’oud ɗin cikin wata irin murya kamar mai koyon magana yace.    “Sha’awa!”

“Eh sha’awa, banason na faɗa halaka Raj, amma seriously ina da buƙatar mace akusa dani, ina da buƙatar zama cikakken mutum nima, inaga kawai zan tura su Baba gidansu Aisha, su tambayomin izinin aurenta, inaga hakan shine mafita, amma kai maikagani?”   Mas’oud ya tambayi Sooraj.

Wani murmushi Sooraj yayi, wanda shi kaɗai yasan menene meaning ɗin murmushin nasa,  leɓensa na ƙasa ya sake ɗan ciza, tare da fesar da iska ta bakinsa.  

“Allah Ya sanya Alkhairi!”  yafaɗa ataƙaice.

“Ameen” Mas’oud ya amsa yana maison karantar yanayin da Sooraj ɗin ke ciki, sai dai kuma sam ya kasa gano wani irin yanayi Sooraj ɗin ke ciki, saboda  Sooraj murɗaɗɗen mutum ne, zai maka wahala gane gabansa da bayansa. 

“Abba ya faɗamin yanda kukayi dashi,  ina fata dai zakayi abun da ya keso?” Mas’oud ya tambayi Sooraj.

Miƙewa Sooraj yayi daga kan dinning ɗin, tare da  ɗaukar wayarsa ya bar wajen.  Da kallo Mas’oud ya bisa har ya shige ɗakinsa,  kai kawai  Mas’oud ya girgiza, sannan yadawo cikin falon ya zauna.

Yana shiga cikin ɗakinsa ya rufo ƙofar gam, jingina bayanshi yayi da jikin ƙofar tare da lumshe idanunshi,  wani iri ya keji acikin jikinsa, baijin ayau zai iya ɓoye rauninsa.  “Inama da ace zai iyayin kuka, inama da ace akwai wani wanda zaiyi sharing ɗin damuwarsa dashi, inama da ace zaiji abun da Mas’oud ya keji.”   Abun da yake faɗa acikin ransa kenan.   Hanu yasa ya dafe saitin ƙirjinsa da keyi masa zafi.  Aƙalla ya ɗau kusan sama da mintuna 10 tsaye ahaka, da ƙyar ya iya jan ƙafafunsa ya zauna akan gado, har yanzu idanunsa a rufe suke,  jin kansa yake nayi masa ciwo, kwanciya yayi akan  gadon tare da buɗe idanunsa, numfashi yake fitarwa a hankali…. Saida yaji yaɗan dawo normal sannan yatashi ya fita falo, can ya samu Mas’oud, sake ɗan tattaunawa sukayi kafun daga bisani suka bar gidan baki ɗaya.

Gumi ne keta fitowa daga jikinta, zaune take agefen gado ta takure jikinta waje ɗaya, wani irin ciwo mararta da cikinta keyi mata, sake matse ƙafafunta tayi, laɓɓanta kuwa sai rawa suke kamar wata wacce  take jin sanyi,   ahankali sautin kukanta ke tashi acikin ɗakin,  jin mararta take kamar zata ɓalle ga zazzaɓi mai zafin gaske da ya rufeta.    Jin bazata iya daure ciwon ita kaɗai bane, yasa ta tashi a daddafe ta nufi falo.   Tana kaiwa tsakiyan falon ta faɗi a wajen tare da sakin wani ƙara, ciwonne ya ta so mata gadan gadan, kwanciya tayi aƙasa tanata mutsu mutsu da ƙafafunta yayinda ciwon ke ci gaba da nuƙurƙusanta.  Kuka take sosai hatta numfashinta saida ya soma seizing. 

Dawowarsu kenan daga Sheraton  hotel inda sukaje suka gudanar da wani business ɗinsu, atare suka shigo cikin falon. Akuma daidai lokacinne kukanta ya dira acikin kunnuwansu, a ɗan razane Mas’oud ya kalli Sooraj, shima kallonsa yayi amma sai ya share ya ƙarasa cikin falon,  idanunsa yaɗan waro ganin yanda take yashe aƙasa gaba ɗaya ta fita acikin hayyacinta, ɗan kwalin dake kanta ya zame gefe yayinda gashin kanta ya watse akan carpet ɗin dake malale a tsakiyar falon,  yanayin yanda yaga takeyi shine abun daya ɗan tsoratashi, domin kuwa ta shiɗe sosai da alama ma bata cikin hayyacinta,  amatuƙar tsorace Mas’oud ke kallon Yarinyar yana kuma kallon Sooraj, koda wasa bai taɓa tunanin Sooraj yana tare da yarinyar ba, a iya tunaninsa Sooraj yajima da sallamanta ta kama gabanta,  wani irin bahagon tunani ne ya ɗarsu acikin ran Mas’oud, bakinsa cike suke da tarin tambayoyi amma dole ya adana tambayoyinsa.

Ƙarasawa inda take yayi haɗe da ɗan durƙusawa hanunsa yakai yaɗan bugi fuskanta  “Ke!” ya faɗa yana mai sake ɗan tattaɓa fuskarta.  

Wani irin nishi tayi take kuma gaba ɗaya jikinta ya sake komai nata ya daina motsi.  Ya ɗan razana kaɗan da al’amarin nata, ɗaukarta yayi caɗak ajikinsa ya nufi ƙofar fita daga falon.  Tsananin mamaki shiya hana Mas’oud rufa musu baya, tsayawa yayi ya kasayin komai kamar wani statue,  ganin tsayuwar baza ta kai mishi ba, yasanya shima ya rufa musu baya, lokacin da ya fita waje har Sooraj ya sanyata acikin mota yana ƙoƙarin shiga gidan driver, da sauri Mas’oud yaje ya shiga motar ɓangaren mai zaman banza.     Gudu sosai Sooraj keyi akan titi mintuna kaɗan suka isa asibiti, likitoti ne suka karɓeta sukayi ciki da ita.

Zama yayi akan wata kujera tare da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa da tafukan hannunsa.  Agefen Sooraj Mas’oud shima ya zauna, shiru yayi ko wanne daga cikinsu da irin nazarin da yakeyi acikin ransa,   tambayoyi ne cike azuciyar Mas’oud, shi kuwa Sooraj ya marasa wani tunani zaiyi, abubuwa sunyi masa yawa,   ahankali idanunsa suka kaɗa sukayi jajur dasu, tananne kawai zaka iya fahimtar tarin damuwan da yake ciki.   Wani likita ne ya fito daga cikin ɗakin da aka kwantar da Ziyada, ce wa yayi su Sooraj ɗin su sameshi a office ɗinsa, babu musu suka tashi suka rufa masa baya.

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe abayyane tare dayin ƙasa da kansa.
Mas’oud ne yayi ƙarfin halin cewa “Yanzu likita wani hali take ciki?”

Gyara zama Likitan yayi tare da cewa.
 “Kamar yanda na faɗa muku a farko, ba wani babban matsala bane, yawancin mata sukan samun irin wannan matsalolin idan zasu fara period, to itama tana ɗaya daga cikin irin waƴannan matan, amma babu wani damuwa zata warke insha Allah, Yanzu haka ta samu bacci, da ta farka kuma zamu baku Sallama, ga wannan saiku sayo shine magungunan da za tana sha”  likitan ya faɗi haka yana me miƙowa Mas’oud wata ƴar farar takarda da yayi rubutu ajiki, amsa Mas’oud yayi tare da ɗan satan kallon Sooraj wanda har yanzu kansa ke ƙasa bai ɗago ba.    Hanu dukansu suka miƙawa likitan suka sakeyin musabaha daga haka suka fice daga cikin office ɗin, direct wajen da ake biyan kuɗi Sooraj ya nufa,  kuɗin gadon da aka kwantar da ita ya biya, sannan suka nufi pharmacy. Bayan sun karɓi maganin Sooraj ya sake biyan kuɗi,  direct motarsa ya nufa,  ganin haka yasa Mas’oud ya bi bayansa. Ƙoƙarin buɗe murfin motar yake, muryar Mas’oud ta dakatar dashi.  ɗan tsayawa da abun da yakeyi yayi tare da juyowa ya fuskanci Mas’oud ɗin. 

Shima Mas’oud fuskantar Sooraj ɗin yayi haɗeme da cewa..  “Wacece ita awajenka? Sannan mai yasa ka ajiyeta agidanka? Me wannan rayuwar da kukeyi take nufi SOORAJ ?”  Mas’oud yayi masa duka waƴannan tambayoyin alokaci ɗaya.


(Sorry kwana biu bana baku update da wuri????????   Fans ɗina na Facebook ina gaisuwa)


     *Vote Me On Wattpad*
         @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button