Labarai

Suna Ce Masa Dan Ruwa,Amma Dana Ba Dan Ruwa Bane Shima Mutum Ne Kamar Kowa

Labarin wani jaririn yaro da aka haifa a kasar Tanzania, Mahaifiyar shi ta shaidawa “yan jarida tun bayan data haifi yaron take fama da shan tsangwama daga wajen abokan zamanta da kuma ‘,yan uwa da abokanan arziki.

Hatta mahaifin yaron sai barinta yayi bayan da yayi ikirarin kawai ta wullar dashi su huta da kuda,sai dai batayi hakan daya bukata ba,daga karshe sai rabuwa sukayi dashi ta koma kauyen su da zama.

Haka zalika anan dinma dai bata tsira ba domin mutane suna kiran dan nata Dan Ruwa (Aljanin Ruwa) kuma suna nuna mata kyama da tsana.

Haka dai taci gaba da rayuwa da yaron nata,daga karshe yan jaridar da sukayi hira da ita ne suka samar mata da dauki ta gidauniyar su,yanzu haka an dauki nauyin fita da yaron kasar India domin ayi mishi magani.

Zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa.
Related Articles

Leave a Reply

Back to top button