NOVELSTA DALILIN SO

TA DALILIN SO 1&2

malama miye kikazo kimun ad’aki kina Ahaka?”wane irin mayune ku keda y’ar uwarki(feenah)?”wlh koki ficemun dg d’aki kona miki mugun duka”niba y’ar iska bace irinku”jikinki dana kallah kuma Allah ya isa”

Shiru biba tayi tana bin husnah da wani irin mayen kallo na sha’awa”ta mik’e tsaye tabar d’akin batare data ce komai ba.

Husnah ta fashe da kuka tana maimaita kalmar hasbinallahu wani’imal wakeel

yah Allah ka kamun mafita”wace irin masiface wannan?”nayi gudun gara na fad’a gidan zago”

tafad’a tana d’akko wayarta iphone 7 + ta shiga kira”
Ashraf
shine sunan data saka ma kira”

gab dazata tsinke yad’aga da sallama cikin muryar bacci”ya ake ciki Ashraf baka kirani ba d’azun??”tafad’a cikin siririyar muryarta”Ashraf yalumshe ido yace”.gobe insha Allah sunday zamuje dake FUDMA!*federal university dutsamma)”d’azun nadawo agajiye ne dg fudmar”sun amince kizama d’aliba acan”gobe zan amso takardar transfer d’in sai muje tare dake Ayi komai”monday ki fara d’aukar lactures ko?”ajiyar zuciya tasaki tace”. Allah yakaimu nagode sosai Ashraf”

yana k’ok’arin mgn murmushi shimfid’e afuskarsa husnah takashe wayar…..

Ahankali ta ajiye wayar tace”.dana zauna awannan mugun gidan ina ganin bak’in ciki da b’acin rai gara na canza skul nakoma hostel da zama yafimun….

tana k’ok’arin kwanciya taji gurnani da nishin mahaifinta da matarsa ta window”

Rintse to tayi cikin takaici da bak’in ciki ta tashi tasakawa k’ofar d’akin key”

tazo ta kwanta kan k’aramin bed d’in”saidai tasha alwashin duk rintsi saita raba Abbanta da Amaryarsa hjy Asiya (mommy)

“washe gari husnah na idar da sallah tayi wanka ta shirya”doguwar riga purple colour abaya tasaka”bakaramin kyau tayiba”ta fito a chacoolet colour d’inta”ga k’amshin turarenta mai dad’i natashi ajikinta”komai nata ta had’a acikin troleys guda 2″cikin hand bag nata tasaka wayarta”ta jawo troleys d’in takai bakin get”

dawowa main parlour d’in tayi”bbu kowa”hakan yasa ta nufi upstairs”

D’akin da shine na mahifinta agidan matarsa tasa ta tura k’ofar”

da sallama ta shiga ta sameshi kwance kan 3 seeter yana bacci”sbd adaren jiya tun 11 pm suke abu guda shida hjy Asiya “sai kusan 3 nadare tabarshi ya runtsa”kuma sunayin asuba aka cigaba.

Abba ! Abba!! bud’e idanuwansa da sukayi jaa yayi yana kallonta”

k’asa kan carpet ta zauna tana yiwa mahaifin nata kallon tausayi”

Ina kwana Abba?”lafiya qlau”ina zakije haka da safe?”

Ashraf k’arfe 9 zaizo muje yakaini skul d’in”

gara kije husnah”nima hankalina zaifi kwanciya ban amince da tarbiyyar su habiba da nafeesa ba”

Duk k’arshen wata zanzo na dubaki”kiyi hak’uri da rayuwa ki rik’e mutuncinki”kiyi abinda yakaiki”insha Allah Abba ta fad’a cikin tausayinsa.

Inada kud’i bara naka miki dubu50 kiyi shopping”sannan abinda yasamu zan miki transfer idan an kwan 2 ta acc naki”

kimun addua ASAMA’U!nikaina bansan meyasa na auri wannan matar ba?”sam bata dace dani ba”Allah yajik’an ummanki macen k’warai!share kwallarta husnah tayi tace”.insha Allah Abba”

tashi tsaye yyi ya wuce bed room d’in”bbu jumawa yafito da kud’in yamik’a mata”ta amsa tana masa godiya ta saka a hand bag nata”

zama Abba yayi yana k’ok’arin mgn hjy Asiya ta shigo da wani shegen d’amemmen siket iya gwiwa ajikinta”

da wata y’ar ficikar riga ajikinta” da rabin mamanta awaje”

Kallo d’aya husnah ta mata ta d’auke kanta”

babu kunya ta zauna gefen Abba har jikinsu na gugar juna”

sweet heart ina zataje da safe haka?”tafad’a tana kallon husnah”

makaranta zata koma”yafad’a cikin jin nauyin abinda tayi agaban y’ar sa”

Ina kwana mommy?”lafiya qlau”dg haka husnah ta mik’e ta fita dg parlourn.

wayarta ta zaro ta kira salaha k’awarta dake FUDMA!

tana tafiya wayar kare akunne”murmushi tayi tana amsa sallamar salaha kafin tace”.yanzun insha Allah ina hanya”wlh da gske nake”ai dama nace miki anan zan koma na Ida karatuna bazan iya zama a kano ba wlh”saidai na iso insha Allah”dg haka ta kashe wayar”

Tana k’ok’arin kiran Ashraf kiransa yashigo wayar”badan tasoba ta d’aga”sbd ita harga Allah Ashraf baya acikin tsarin mazan datakeso”

takuma sanar masa tun last 2 month da had’uwarsu”yayi hak’uri ita ba yanzun zata fara soyayya ba.

tana d’aga kiran ta masa sallama anutse cikin zazzak’ar muryarta”ya amsa had’e da fad’in ina waje”kashe wayar tayi ta nufi get”me gadi ya kwaso mata kayanta yasaka mata a boot”

Asharaf na a mota yanata kallonta”k’anwarsa taslim na back sit”shine yace tazo suje”sbd yasan halin husnah sarai zatace ita bazata tafi tare dashiba sukad’ai….

front sit ta bud’e ta shiga”kawai ta ayyana aranta”idan sunje skul d’in sun fita cikin gari itada salaha tayi siyayyar komai kawai”tunda saliha dadynta yakama mata d’aki guda anan wani gida gab da skul d’in.

Ranki yadad’e”hmm!ina kwana?”cewar husnah”lafiya qlau”hankali ya kwanta zaki koma FUDMA ko?”hmmm”ina kwana antynmu?”cewar taslim dake back sit”

husnah na murmushi ta amsa”Ashraf yaja motar bbu me mgn”sai jefi jefi husna ke mgn idan ashraf yyi mgn sau 10″

gaba d’aya haushi yake bata”ko kad’an bata wani sonsa takuma sanar masa amma yanace”

ko komawarta ayanzun skul d’in shine yace yaji yagani”shida wani abokinsa dake lacturing acan sukayi hidimar komai….

Tafiyar kusan awa 3 sukayi da wasu mintina”

kai tsaye skul d’in suka wuce”duk abinda yadace Ashraf saida yayi wa husnah”dama first smister ake”aji ukku aka bata dama kuma aji ukku zata shiga(lavel 3 )”

sosai husnah ta yaba da tsarin makarantar ga d’alibai wasu nata dawowa sbd befi 5 days kenan da dawowa hutu ba”

Kiran salaha tayi ta waya tasanar mata suna bakin get itada wanda yakawota”

Babu jumawa saiga salaha tazo suka gaisa da Ashraf ta kwashe kayan husnah ta nufi gidan datake haya”kasancewar bbu nisa da skul d’in”

Husnah kuwa da k’yar tasamu ta zame agun Ashraf sukayi sallama ta wuce hanyar dataga salaha tayi.

sosai gaban Ashraf ke fad’uwa fatansa Allah yasa”yadda husnah keda kyau na fitar hankali kar wani ya amshe masa ita acikin samarin jami’a.

Ahanya husnah suka had’u da salaha”suka koma gidan atare”

gidane mai kyau madaidai d’aki 5 ne akwai toilet acikin kowane d’aki”kowane d’aki mutum2 ne aciki”amma ita saliha ita kad’ai mahaifinta yakama mata”

zama sukayi suka gaisa”salaha ta zuba mata abinci mai rai da lafiya”ko ina d’akin k’al yake”sbd salaha akwai tsabta”

Abinci husnah taci ta k’oshi tayi wanka”sallar azahar tayi”ta kwanta baccin gajiyar hanya”

bata farkaba sai gab da sallar la’asar”sai asannan takoma yin wanka da alwalah tayi sallah”sannan salaha tasamu husnah namata mgn”tasan halin husnah miskilace ta k’arshe.

gsky k’awata Ashraf naki nada kirki”tab’e baki husnah tayi tace”.nikuma haushi yake bani”neman hanyar rabuwa dashi kawai nakeyi wlh”kumafa na fad’a masa yayi hak’uri ba soyayya bace agabana”

Amma sbd naci da rashin zuciya yayi wani k’ato k’ato yana manne mun”salaha na murmushin tace”.wlh bakida dama k’awata”nikaina gsky naga baku daceba”saidai nasan wlh yadda kike da aji zaki tafi da imanin samarin jami’ar nan”danma bakyayin make up”

Hmmm!nifa yanzun bata soyayya nakeba”asalima duk masu cewa” suna sona bbu wanda yamun”ta karatu nakeyi ba soyayya ba.

Kinga dalilin muntasir na gidan baba mu’azu(yayan Abban ta) nabaro gidansu”nadawo gun amaryar Abba”sai naga gara ma gidan baba mu’azu da gun amaryar”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button