NOVELSTA DALILIN SO

TA DALILIN SO 3&4

🅿️free page 3&4

“Cikin tsananin k’unar rai da fusata AL-HUSSAIN yace”.ina macen take anan?”niban gantaba”nine nan najefeki! in akwai matakin dazaki iya d’auka” ko akwai abinda zaki iya yi kiyi kawai”yafad’a cikin cool voice yana d’age kafad’a”alamar ko ajikinsa”

Tsaki husnah taja tana matsawa baya tace”.ai bansan muna maza bane yajefeni dabazan kulaka bama”sbd banga aji ko matsayin dazan iya mgn dakaiba kana kucaki…..hahahahaha!!wasu maza da mata suka yi dariya dazasu wuce”sbd husnah ba k’aramin burgesu tayiba”sbd bbu wacce zata iya gaya masa mgn a skul d’in haka…salaha takama hannun ta tana janta”

Cikin b’acin rai Al-hussain yatunkarota zai daketa sbd ganin yadda tafara k’ok’arin yarfashi cikin jama’a”

Abdallah da ibbi suka rik’esa yana fisgewa yana binta da wani irin mugun kallo”zan nuna miki ke k’aramar marar kunyace”

Kaine dai marar kunya da sanin yaka mata”kuma wlh mu zuba nida kai”dallah malamai ku cikasa inya cika namiji yazo yamun abinda yaga zai iya.husnah ta fad’a cikin masifa da hargowa….

gaba d’aya hankalin jama’a yadawo kansu”an rirrik’e Al-hussain shi adole saiya daketa”

salaha kuwa hankalinta yatashi tanata jan hannun husnah sbd su wuce amma tak’i binta tanata masifa itada Al-hussain”

Abdallahi da ibbi (manyan abokansa)kallon husnah sukayi suna tunanin sabuwar zuwace sbd basu santaba”saidai sun tabbatar itama tanada gadara kamar Al-hussain”

da k’yar su Abdallah suka janye Al-hussain dayyi mugun hawa dokin zuciya”

kai tsaye hostel suka wuce dashi”yana matuk’ar jin haushinsu dasuka hanashi yakoyawa wannan banzar yarinyar hankali”saidai yasha alwashin bazai hak’ura ba tamasa rashin kunya”

sai jan tsaki yakeyi ya kwanta kan bed nasa”

Abdallah yace”.my man gsky bakada kirki laifinkane fa”kaine kafara tak’alarta wlh”cewar ibbi”

Tsaki Al-hussain yaja yace”kunga bazai yuyuba yarinya tanemi tagayan mgn ta tsinkani ace nabarta”

na jefeta kuma acikin ku wani yad’auki mataki mana”naga ta tsaya tana wani iyayi shiyasa na jefeta”

dariya Abdallah yayi yace”.kodai tamaka ne?”

wata uwar harara Al-hussain ya banko masa yana shafa sumar kansa dake salk’i bak’i k’irin da ita”

kaga kayi hak’uri kabarta kawai”ba ajinka bane fad’a da mace”ina zaton sabuwar zuwace ma gsky”

Banza yamusu beyi mgn ba ya lumshe firgitattun idanuwansa yana tsotsar lip d’insa na k’asa”

shiru sukayi sbd sun san halinsa in y’an miskilancin suka motsa”

WANENE AL-HUSSAIN?
Al-hussain kabeer muhd!shine sunansa”d’an asalin garin Kano ne”iyayensa na zaune a anguwar nassarawa”

Twins ne shida abokin tagwaicinsa Al’hassan”sun shak’u da juna sosai suke son junansu.

Hjy rabi(mamy)itace mahaifiyarsu tunda ta haifesu bata koma haihuwa ba”

suna son mamy da daddyn nasu sosai”sannan suna kama da juna”Al-hussain wankan tarwad’a ne”dogo kyakykyawan gske”yanada Kiran ingarman namiji”miskiline shi sosai”becika yawan mgn ba”akwai aji da wayewa atare da guy d’in”uwa uba kuma gifted ne yanada k’ok’ari sosai”hakan yasa kansa ke fasuwa a skul d’in”baya tsoro baya shakka”be d’aukar raini ko kad’an….saidai wasu dg cikin mutane suna masa shaidar yana sallah cikin lokaci”(yanada ruk’o da ibada)sannan ba mutumin banzane ba”in aka cire wannan to mutane namasa kallon marar kirki me girman kai da fariya….
kusan halinsu guda da abokin tagwaicinsa”wato Al’hassan”

Al’hassan shi bak’i ne dogo”beda jiki tsayinsu d’aya da Al-hussain”
shekarunsu 28 aduniya”

Al’hassan yafi buk’atar yayi karatunsa akusa da gida”yyinda Al-hussain beda wannan tsarin…

mamy akwai yarinyar datake ruk’o y’ar k’anin daddy ce” da suke uwa d’aya uba d’aya wato HAFSAT!

mahaifiyar hafsat ta rasu tun hafsat nada 2 yrs”daddy ya amsheta yamaidota gun mamy”dama kuma mamy nason y’a mace”

Abban hafsat babu jumawa yayi aurensa”ya auri matarsa mai suna zaliha”ayanzun sunada yara 3 da ita”zaliha bata k’aunar hafsat ko kad’an”

Mamy nada kanwa anty dije wacce anty dijen keson y’arta bilkisu ta auri Al-hussain”

Hafsat ba wata babba bace tana 14 yrs yanzun”js3 take”saidai hafsat batajin mgn”akwaita da rashin ji da fad’a”kullum sai anzo kawo k’arar ta”sbd ita Al’hassan yazauna anan yana karatunsa”kusan kullum saiya daketa ko yasakata punishment”

Abaya hafsat ta shak’u da Al’hassan”amma sbd rashin jinta yasaka suka b’ata”

Daddy babban mutum ne mai arzik’i”sbd za’a iya lissafashi acikin masu kud’in kano”

Babban d’an kasuwane”yanada super market da compony na buga gadaje”

yanada shaguna a kwari na atamfofi da laces”

Al-hussain be tab’a soyayya ba”aganinsa bbu macen datayi ajin dazaiyi soyayya da ita a skul d’in”

yamafi so yagama degree nasa sannan yafara soyayya”

Duk y’an matan dake skul d’in sunsan da Al-hussain”wasuma sun rok’esa ko friending suyi amma ya yarfasu”

Akwai wata yarinya sunanta suwaiba”ajinta 3 amma ba course d’aya suke da Al-hussain ba”sosai yake disgata amma sbd rashin zuciya tana manne masa.

Idan akace ankusa fara exams ko CA text”haka zakiga anata bin kan Al-hussain yakoya musu abinda basu ganeba ko suka mance”

shikuwa yayita jan aji kenan da cewa sai anjima ko kaza yakeyi”amma kuma duk rashin fahimtar mutum idan yakoyar dakai karatu saika gane”

Al-hussain be k’arya yakuma tsani mak’aryaci”betaba nuna shi d’an wanine ba a skul d’in”dukda yanayin dressing nashi na nuna ba dg k’aramin gida yafito ba”sannan kuma mutum ne shi dabaida ruk’o ko kad’an.

wannan kenan anan gaba zakuji komai….


su husnah kuwa da k’yar salaha tajata suka tafi gida tana bata hak’uri”

tashiga sanar mata halayensa dakuma ai ajinsa 3 shima”

tab’e baki husnah tayi tace”.damuwarsace”wanda yadamu dashi shine zai tura kansa agunsa”aikin banza kawai”wlh nidashi muzuba”murmushi kawai salaha tayi batace komaiba….

washe gari tun k’arfe 9:30 am suka gama shirinsu”doguwar riga salaha tasaka ta yane kanta”husnah kuwa riga da siket na atamfa ta saka da hijab kalar atamfar iya gwiwa”

kasancewar ba course d’aya suke ba kowa yayi Inda zashi”k’arfe 10 su husnah zasu fara lactures”

fuskarta tayi fiyau gwanin sha’awa bbu make up afuskarta”amma haka be hana kyawunta fitowa ba”

ajin da aka nuna mata jiya”anan ta nufa”kasancewar ba raini husnah ke d’auka ba”sai ta shiga fuskarta ad’aure…

gabanta yafad’i sbd hango Al-hussain datayi zaune atsakkiyar su ibbi da Abdallah”

bata tankawa kowaba ta zauna a sit na gaba”kowa yanata harkan gabansa”gara mazan sunfi yawa hausawa”amma matan biyune kawai tagani musulmai amma duk yarene(arna).

sarai Al-hussain yaganta”aransa yace”.wato anan ajin wannan gadararriyar yarinyar take”be gama mgn baaransa, lucturer d’in yashigo duk sukayi shiru”

bayan yagama musu lacturing d'in"yakalli husnah sbd ganin ta bak'uwar fuska"

Hii wacece ke?”yaushe kika zo?”duk yatambaya cikin harshen turanci”

gaba d’aya ajin aka bita da kallo”husnah tawani d’aure fuska tak’i mgn”

Al-hussain yasaki shu’umin murmushin da, da wahala aga yayi irinsa”aransa yace”.brain nata bbu komai kenan sai isgili ko?”begama mgn azuciba”zazzak’ar muryarta ta daki dodon kunnansa”tana introducing d’in kanta”da sanar musu ita dg wata makaranta tazo anan….duk tafad’a cikin harshen turanci kanta ak’asa kirjinta nata bugawa sbd idanuwan jama’a….

tab’e baki Al-hussain yayi”sai kuma lacturer d’in yajeho wasu tambayoyi guda 2 zafafa” bayan yabawa husnah damar ta zauna data gama gabatar da kanta.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button