TA DALILIN SO 1&2
salaha tace”. Allah dai yabaki miji na k’warai”dakin gama karatu kiyi aure ki huta”
Ameen muduka k’awata”hakane gsky”yanzun kitashi muje mu zagaya skul d’in na nuna miki Inda baki sani ba”dg nan kiduba y’an ajinku k’arfe nawa suke da lactures?”
dato husnah ta amsa”ta canza kaya zuwa dogowar riga da lace fari ta zumbula hijab har k’asa ta d’aure kanta da mad’aurin hijab d’in”
Kallonta kawai salaha keyi tana yaba kyawunta aranta”
bayan sun shiga ciki”ta nunawa husnah ko ina”husnah dai aranta ta yaba da skul d’in”
Can wani fili Inda d’alibai ke zama wayayyu masu aji anan salaha tajata suka tafi.
kowa nata harkan gabansa”can kaga grp d’in maza ko mata”ko kuwa kaga mazan da matan wasu na assignment”
kinga ga wani block can muje mu zauna”cewar salaha tana nuna block d’in da hannu”
husnah na k’ok’arin mgn taji anwurgo mata wani abu afuska…dg husna har salaha kallon kwalin ziza milk da aka wurgoma husna sukayi”
Duk ziza milk d’in ta b’ata mata fuska da gaban hijab”cikin zafin rai husna da salaha suka kalli gefen da aka wurgo kwalin”
matasan samarine su 3 ajere suna tafiya hankali kwance”na tsakkiyar yana sanye da eye glass bak’i”da k’ananun kaya ajikinsa”yawani d’aure fuska”saidai guy d’in yahad’u k’arshe….wanene cikinsu yajefeni”?”cewar husna tana bin salaha da kallo”atake salaha ta fahimci AL-HUSSAIN ne yayi wannan aiki”sbd tasan gadararrene na k’arshe”shine mata kebi yana yarfasu”bbu wani namiji me aji da kyawu da k’ok’arin dayakai AL-HUSSAIN a skul d’in”kuma shima ajinsa 3″
Husnah na ganin zasu wuce kawai da sauri tasha gabansu”dukda salaha na tsaidata sbd tasan halin AL-HUSSAIN tsab zai yarfata.
Husnah tana binsu da wani banzan kallo tace”.wane marar tarbiyyar ne yaje feni?”da alama koma wanene besan darajar da Allah yayiwa mace ba”idanma bada gangan bane saiku bada hak’uri ko?”tafad’a cikin masifa tana harararsu….hakan kuma yayi daidai da isowar salaha agurin”
Cikin tsananin k’aunar rai da fusata AL-HUSSAIN yace”.✍️
Commented kawai guys😁😊
Abi Ahankali yazo da sabon salo ab’angare 2 na masoya labarin zai kama”yi k’ok’arin biya ki mallaki naki cikin kwanciyar hankali……