Labaran Kannywood

Tallar fim din Hausa da ake koya yadda ake Jima’i (Saduwa) ya bar baya da kura

Ba dan mutanen Kano na shirya fim ɗin Makaranta ba — Darakta

Daraktan fim din nan da ake ta yin tallansa mai suna ‘Makaranta’ ya ce bai damu da barazanar da hukumar tace fina-finan Jihar Kano ta yi na kama shi ba.

Fim ɗin Makaranta wani shiri ne da ya haifar da cece-kuce a ƴan kwanakin nan bayan da a ka saki tallansa a kafafen sadarwa.

Shi dai fim ɗin an yi shi ne domin koya jima’i tsakanin matasa, inda a ka yi amfani da kalaman batsa da sauran rashin tarbiyya a cikin sa har ya sanya Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta shiga farautar Daraktan.

Hukumar tana neman Daraktan, mai suna Aminu Umar Mukhtar ne ruwa a jallo, inda take zargin sa da lalata tarbiyya da kuma rashin bin ka’ida yayin fitar da tallan fim din.

Fim din ‘Makaranta’ ya nuna abubuwa da dama da mutane da dama suke ganin ba su dace a yi fim a kansu ba, wadanda suka hada da madigo da batsa da makamatansu.

Hakan ne ya sa shugaban hukumar tace fina-finan ta Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa sun aika wa daraktan takardar gayyata a watan jiya domin ya je gabansu ya yi musu bayani na dalilan da suka sa ya soma tallan fim din ba tare da samun izininsu ba.

A cewarsa, Aminu Umar Mukhtar ya shaida musu cewa zai zo gabansu idan aka shiga sabuwar shekara amma bai je ba, lamarin da ya sa suka fara nemansa ruwa a jallo.

Afakallah ya kara da cewa za su tuhumi daraktan fim din bisa laifukan da suke ganin ya aikata.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC Hausa, Aminu ya kare kansa bisa fitar da tallan fim din, yana mai cewa bai damu da neman da hukumar tace fina-finan Kano ke yi masa ba.

“Na samu labarin cewa hukumar tace fina-finan Kano tana nema na. Ban yi ko gezau ba domin kuwa ban aikata wani laifi ba,” in ji shi.

“Fim din da na yi ba a kan mutanen Kano ko Hausawa na yi ba, na yi amfani da harsuna 17 a cikinsa. Kuma ba a Kano aka dauki fim din ba, don haka ban san dalilin da ya sa ya zama abin ce-ce-ku-ce ba.

“Fim dina ba kawai yana magana ba ne game da ilimin jima’i ba, yana kuma nuna illolin kaciyar mata da wayar da kai kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin Hausawa da ma wasu al’ummomi.”

BBC Hausa ta rawaito Daraktan fim din na ‘Makaranta’ ya musanta cewa wasu ne suke daukar nauyin sa domin ya bata tarbiyyar mutane.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button