NOVELSUncategorized

TUNTUBEN HARSHE 2

*♡TUNTUBEN HARSHE????*
 _Voyage within the hearts!_         *WATTPAD*
  *@SURAYYAHMS*

 TH on Wattpad      https://my.w.tt/14DDAx4gW 


 _Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ 


 _2…our nigeria_Ni’imar dake tattare da shigowa sabuwar kasa dana sabon gidan mu s daban take kullum sai na tsaya akan balcony ina nazari

Wato ta kasar Nigeria wata shaharrariyar kasa ce a nahiyar Africa wanda zanso ince Allah ya riga ya Albarkace ta da komai da komai na arziki kasancewar in za’a bude tarin niimar dake kewaya da ita dan adam bazai gushe a dakika bai godewa ba.

Duk da kalubale da fadi tashi irin tamu ta dan adam Nigeria har wa yau tana amsa sunan ta Kasa Kimsatsiya kuma muhimmiya a duniya wadda ta kafa dumbin tarihi a ko wani fanni na rayuwar dan adam iyakar in da dan adam zai iyayin jigila da nisan tunanin sa

A kasar nigeria,Anfi sanin kabilar hausa a arewa,yoruba da kabilar igbo achan  ta kudu gabas da kuma yamma dumbin Rabe raben al’adu da kabilu yasa bambacin halayya da gogayyar yan nigeria ya rabu ta siga daban daban

Misali,karatun Allo ko ince arabi kusan wani jigo ne a rayuwar dan bahaushe,almost free and fully accepted,a kasar hausa shi cikakken bahaushe da chan ba’a san shi da tsanan ta neman ilimin kimiyya da fasaha ba,mafi akasari yaro a arewancin nigeria yakan taso ne yay gadon sana’an hannu awajen iyayen sa da kakkanin sa.

Hakan yasa Bahaushen mutum ya dawwama wajen neman nakan shi tare da karancin wayewa,bagidadanci da kauyanci,bai  damu da abunda ba nashi ba hakama a wajen bayyana halayya dan bahaushe ya fi nuna alakar sa da tarbiya daya samo asali daga addinin sa,daga bisani kuma bahaushe yakan kafa jigo da girman iyayen sa.

 bahaushen mutum ya kasance mai killataccen hali sabida tsarin addinin sa dake sakaye da al’ada da mu’amlayyar sa. 
Hakan yasa dan Bahaushe ya gaji akida,shugabanci، zumuncin sa da karar sa ya sa yake da madogara.

Shikuma bayarben mutum ya nemi ilimi,kuma ya samu.

Ko da shike turawar falar hula anan wajen su suka fi zakewa shiyasa ko a cigaba ne bayarben mutum shine agaba wajen kawo tsare tsare wajen hamayya da neman kawo cigaba ma kasa.

Sai dai shi kabilar bayarbe mafi akasari ya kan bautawa al’adan sa ne fiye da addinin sa ko kuma ya cakuda su waje guda,babu ruwan shi da kyashi su basu da bakin ciki musamnan in akan abun da zai amfane dan adam ne hakan yasa suke da shugabaci ilimi kara da karfin hamayya mai muhimanci a  tarihin nigeria

Sai inyamurin mutum,Shi dai iyamurin mutum  ya kasance ne mai ra’ayi,tsassauran ra’ayi,ya yarda da cewa duk abunda ka same a duniya to iya karfin ka ne da zafin neman ka ya samo maka ba Allah ba.

Hakan ne ya sa inyamurin mutum ya xamto mai son kai da son xuciya, akan neman nakan sa ya kan aje addini tarbiya da al’adan sa ya kulla alaka da iya abun da zai ficce shi,walau mai kyau walau marau kyau

 awajen iyamuri komi halal ne in har shi ya samu kowa ya mutu be damu ba,and this selfish attribute has only make them so infamous in nigeria till date.

Iyamurai sune mafi kankantar kabila amma bambacin halayyar su da saura jiga jigan kabilu biyu yasa suka fito daban.

Zafin nemansu shiya  ya kasa su cikin ko wata jaha a kasar nigeria,lungu da sako zaka gansu da iyalan su ko su kadai suna halattaccen aiki ko akasin haka.

Iyamuri koda ya samu arziki baxaka banbanta shi da mai nema ba domin shi san bai san ya ishesa ba sabida har yau yay amanna da akidar sa na cewa xafin nema shike kawo samo and there is more to his sweat in har yana numfashi.

Shi inyamuri Baida addini,bawai nace da su kafirai ba,sai dai dan su addinin bata hana su ko sa su yin komi sabanin kabilar hausa da yoruba da suke iya barin halak ko dan kunya..

Haka ma fannin shugaban ci,bahaushe da bayarbe sune agaba anma a wajen iyamuri shugabanci shine ka nemi arziki ka ciyar da kan ka da famlyn ka duk sauran kuma kowa tasa ta ficce shi

Girman kai da jin cewa komi sakamkon zufar sa ne,samun sa’ar sa da nacin sa yasa yake da Taurin kai da taurararren zuciya awajen sa ramin kura sai yayan ta This make him very selfish greedy and self centered.

Tun daga Yara har kakakani kusan haka luggar kowani kabila take tafiya har yau kuma bata sauya ba hala har karshen rayuwar mu. 

But We are still one nigeria,kamar yadda   mutanen cikin ta sukan maimaita ma juna kawu ma yace nan ne asalin tushen mu.

Gwamusa da hammaya wajen neman kudi ilimi da mulki ya sa aka saje da juna Zaman wata rana da dadi wani bin har akan zubar da jini in son kan yy yawa ko ince in hakuri ya gaza.

Kamar yadda abun yake,in ka ga kabilar da banaka a inda kake kana sa ran akwai abunda ya jawo shi,Walau neman ilimi,suna siyasa mulki ko dukiya 

Kano state nigeria itama babbar jigo ce arewacin kasar nig
Musamman awajen kabilar hausawa

Anayi mata ikirari da kano tumbin giwa koda mai kazo an fika dan haka kar kasha mamakin in nace kabilar inyamurai ma ba barsu abaya awannan jaha ba

Cikin wata anguwa ce mai shiru da tsafta inda ko da motaxe ya wulfa sai dai kaji wlhawar tashin tsunsaye 

Tsaka tsakiyar ba can ciki sosai ba Wani tanfasesen gida ne kirar ginin masu saka guntun wando da hular malfa babu ko fenti aciki,transitional multi billion dolla mansion ce mai dauke both modern and tradituinal onarments

Kangon gidan da tsawo ance kafin ka yi toxali  da asalin muhallin sai ka shirya,shirgegen bakar drag gate ne ya katange shi mai gaba daya akai an an rubuta 
_rsd oo7 CAMPBELLS OBASI_ 
a shiny gold plate

 Babu wani mahauki dake wulgawa tanan wajen kasancewa anguwa ne ko ince layi ne da masu kudin jerin top list na forbes.

Bisa doka da tsari kusan komi a kiyasce yake a rayuwan su dana yayan su,zumunci yarda da gogayyar sunka mai dashi abun gujewa domin kare darajar arzikin su da sunan su

Iya zagawar ka anan Ba kowani gida zaka iya cin karo da motsawar kofar ta.

A dalilin wani shaharriyar bikin da aka yi yasa masana suka iya dauko rahoton me ke cikin campbells obasi mansion.

Mr obasi campbells 
Shi ba sarki bane ba kuma dan sarauta bane Hakimtaccem iyamuri ne daya matukar tara dukiya

Ya bar amunze local gvnt dake chan anambara south tun yana shekara 12 yazo arewa naman duniya,mr campbells yana da tsananin zafin nema dan haka lokaci guda ya samo arziki yay family Allah kadai yasan source din kudin shi

dan da arzikin nasa ya bunkasa achan kauye ance uwar sa da ubansa duka suka mutu amma har yau dai baije ba

Matar sa MRS michelle campbells fara ce yar duma duma kyakwa suna da yara yan mata guda uku anma ba namiji ko daya

Meghan,carmilla,
Sai kate wacce suka kwallafa ta arai amma sai aka ga bata yi tsawon rai ba shekarun ta bakwai a duniya ta mutu.

Mr campbells is an ambituious and sturbon igbo man,very strict shiyasa Babu ruwan shi da komi inba cigaba zai kawo masa ba.

Akan dukiya da mukamin rayuwar sa bai aje ran dan adam akan kome ba

Kuma komin munin harka in har na karuwar sa ce yana kan gaba He is so selfish to the mantle,sune hausawa yan makarabta allo ke ce musu summun bukmun umyum fahum la yarju’un

Baji ba gani duniya ina ka fito duniya ina zaka je

He trade his time his word
Numfashin sa ma ji yake ina ma zai iy kiyasartawa su amfanar da shi dan ya samu dunia da tuni yyi

Shiyasa kusan komin sa akan tsarin magada  masu irin dukiyar  dayaso ya mallaka

Asalin sunan uban sa obasi chinedu attah amma dan yay dai dai da masu arziki yay legalizin
Family name dinsa ya dawo campbells
Irin na turawa masu kudi kamar bill gate,zuckerbeg and co

Yaransa da shika Allah bai bashi namiji ba suma ya sa musu inkiyar sunayen the great duchessess of the world  wato princess Meghan mikel,princess kate and princess carmilla..

Kafin mutuwa Mahaifiyar sa ce daga kauye tanace akan ko da bata raye ya sakaya ma yayan sa sunan yare

Ssi meghan campbells
Aka sa mata Adaobi
 carmila aka saka mata Adaora da shike Duk ta fisu kyau da tsari,Kate kuma an saka mata adamma duk dama she is no more.

Ba laifi duka sun dai sun biyo tsananin kyaun mahaifiyar su ne and of course hkan ma wani babbn hannun jari ne awajen mr obasi da harkokinsa

Kowacce cikin su ya tsara iriin dukiyar da zai samu akan ta tun ranar da aka haifo ta,sosai Yake ji da yayan sa kuma yake basu tsaro,ilimi gata kudi tsari da komai na duniya ya kan dora su akai

Carmila da meghan yan biyu ne amma ba masu kama da juna ba.Hasalima baxaka gane ba sai sun fada da kansu.

Duka suna da tsananin farin fata da kyau da dirin jiki na asalin lafiyayyr fatar jikin iyamurai kansu a shake yake da bakar suma siffar su mai cika da tsayi.wani bin kyaun halittar su shi yake  azama su wajen kara aza himma akan burrikan iyayen su musamman ita meghan da tafi kowa zakewa.

Uban ta yakan mata ikirrari da mace mai kamar maza dan bata taba saba mashi ba sai dai ma tayi abinda zai sha mamaki

Aganin shi kazar kazar da saurin dora burin ta akan komai irin nashi ta gado

Ita ce  ta samu miji
Irin wayan da mr obasi ya kayyade musu Wato ryan white

He is A son of a drug lord in cambordia saida cocaine weed da bindigogi shine harkan familyn sa

A auren sun ne aka sha shagali duk dama Ba’ayi white weding ba

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button