NOVELSUncategorized

TUNTUBEN HARSHE 4

*♡TUNTUBEN HARSHE????*
 _Voyage within the hearts!_

 _Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_ 

 _Toast:be bold u might not live long but u will die a hero,be brave and live to conquer!!_ 


 _4…what makes the storm_
Bayan ficewar kawu Muma muka tashi muka nufi hanyar daki,mita Asad yake shikadai bance da shi uffan ba har sanda na bude kofata na shige ciki,daga shiga tan ko zama banyi ba najiyo kamar inuwar mutum abaya na gaba na ne yay mumunan fadi hade da roling hazel eyes dina nayi saurin juyowa wani durus nagan shi a tsaye ya zuba min idanu
Na dafe goshi”oh god Asad?Nayi rau da ido Nace menene?yy shiru ko ajikinsa ya tsaya kyam agaban door cikin dage girar sa shima yamin alaman irin what?dauke kai nayi cikin fargaba na soma tahowa”..why r u here?Tun ma kan na kara magana ya nuna ni da yar yatsa
“yace hey stop there,karma kice min komai dan duk ke kika jawo min,na ware idanuna cikin mamaki nace ni?yace yes dana san silar kirar kenan dabanje ba”i just hate this place,..ya dan shafo gashin kansa yana yarfa hannu cikin sigar isknci harda wani lumshe idonsa,galala na tsaya ina kallon shi baki na a bude ina kan jinshi,”.
Wallhy wnan nigeriar bata da dadi,shikenan kullum mutum agida kamar wata mace?,this nigeria is fucking disqusting and soooooo boring.

A hankli Nayi tsaki nace shirme،toh cahn ta matse maka ai kai ka nace wa dakin so kai kaga dama…
Yace oh yeah,taking things and feelin ma self?ai daki yayi arayuwa…daga nan wani dan iskan pose yy yana mimiciking yadda yake shan taba da hannun sa dan inji haushi

“Ure so disquisting” na furta cikin harara idanuna tamkat xasu fado kasa ban iya daurewa ba na juya masa baya

 queit serious na shiga mita nace Abun nan da kake sha cuta ne kuma ka sani but ka nace mishi, look am tired of u asad,kaje ni bana bukatar me shan taba a daki na ma..

Dagowa yyi Cikin neman tsokana ya zaburo ta gabana a fitgit sanda na matsa a tsomare ina neman dafe bango

Wani yelwataccen murmushin shi mai narkarwa ke kan fuskan shi kuma yana mai cigaba da murmusawan ya dora yatsan sa akan karar hanci na ya lakata still looking cute to the moon,yace”u aint tired yet kinban abinci ne?sai ya dage min girar sa bansan sanda na dafe goshi na ba..”im hungry pulchritude..this time cikin sanyin murya ya furta cikin marairacewa har yana make kafadun shi abun tausayi kamar dan karamin yaro

Shiru nayi bance uffan ba dan har tsakar idanu na yake kallo…”ni wallhy yunwa nakeji kije ki kawo min abinci dabance uffan din ba ai kuwa  yay wata kasalliyar super akan gado na ya bararraje
.
Da Kallo na bishi a Dan dole nayi hkri na fita,spaghetii jolof ne da meat balls a ktchen sai nayi warming i have to take ma time dan  ko akan yawan shan taban nan Asad xai bukaci shan fresh juice na yayan itacuwa,so i used only apple dan na masa plain juice,dana kammala ice cube na zuba akai na saka straw da abincin akan tray duka na kawo masa daki,A hnkli Na turo kofar na shigo sai naga wayam babu shi da har zan juyo in duba sai naji motsin kofar bathrum dina.

Baki wangale na tsaya cikin kasa je tray din,Asad ne ya fito sanye da dogon wandon sa kirjin sa babu ko riga sai famar tsantsane kansa yakeyi nace
“O my god asad?me nake gani haka whats wrong with u?

Yyi saurin cewa excuse me?ke wanka nayi ya wani hade rai..mamaki ya cika ni nace this is a girl’s bathrum lapyar ka kuwa?wani kallon yamin harda dora hannu akan kirjin sa yace ke din da kike shige min nawa are u a boy?
‘Share shi nayi nace nidai bana wanka a dakin ka kuma kar ka sake yi a daki na..
Wucewa yy kamar bada shi nake ba,idanun sa na sauka akan tray din
wani sautin ahh ya sake ya taho da sauri zai xauna abakin gado dan ma ya nuna min ya matsu yaci abincin har saura kadan ya tureni,sai na dago muka hade ido kan nace uffan yace toh kiyi hakri, i said soryy… ke sai ata baki hakuri bazaki amsa ba i dont like it y wani hade rai yana shan qamshi
Kula shi ma baxai kara min komi ba so bance mashi cikan ka ba na aje mashi abincin na juya abuna,chan nesa da shi na zauna zan kunna system sai naga yana bubude abincin yana ta kallon su ‘….natty girl…nayi kamar banji ba yace nadra zo nan ki gamin wani abu,he has neva sound serious for ages sai kawai na tashi da guntun mita na taho ta gabansa aikuwa ko snds banyi ba charaf sai naji ya cafko ni a hankli ua jawo ni jikin sa ya matse ni akan cinyar sa

“Asad?Asssad
Asssad…yace meyey?raina a dan bace Nace bana so,to har na gama kokawar zamewar baice uffan ba haka kuma fir yaki ya barni sai shushhshh yake min da sautin muryan sa alaman na masa shiru da kyar har na hakura na xauna din.

A takure kuma Ban sake fuskata ba cos I hate when he behave this way with me,nayi kifi kifi da ido kamat mai shirin yin kuka,sai ya kalle ni as close as he can cikin jan shauki mai tsuma rai wani irin lumshe ido yayi  sannan yakai loma daya na abincin abakin sa yana kallon idanuna yana taunawa
Dada sauke kai na kasa nayi yace hmmm
“Tunda an hanani yawo da fita party ai sai kitaxama akan cinya na ko? Na dago na kai masa wani irin mutsine a kirjin sa very funy ya zaburo dani kadan y dafe wajen yace'”ouch ouccch oucch sai ya kashe mun ido cikin yar karamar dariya,”

 wani shagwabben muryan nasa cikin bori nace asad pls dan Allah ka sauke ni..ni wllhy banson haka…kuma mama zata iya shigowa fa yace toh sai me?na turo baki nace pls get out…batare da ya nuna kulawa ba yace mun I cant babe..,pls…dan Allah..sai na dada sauke muryata ina bin kyakwarar fuskan sa da ido babu kigtawa jim kadan duk sai naji jiki na na neman mutuwa.”..shima kallo na yakeyi but dan kar na gane sirrin zuciyar sa sai yayi fari da ido ya shiga kwakwalo tarin karya yana tayi har yana rike chest dinshi,tabe baki nayi na mika hannu da sauri na dauko juice nasa mashi abaki ba wani sha yake ba amma ya rike mun hannu ahaka sanda muka dau lokaci har sanda ya zuke tass sannan ya sake ni

Cike da sauke sautin lalatun ajiyan xuciya nace Asad yayi U need to go?

Wani luiii yayi da idanun sa aransa yana sallamewa my pouts is freezing him again?cikin kwayar ido na ya sauke nashi cikin kasala yace in fita?na dada sakalcewa nace right now?wani aje spoon din yayi kamar maraya
,”korata ma kikeyi ko? nidai tunda muka zo nigeria kika tsane ni ke baxaki barni nayi abunda nake so ba and u alwys hate me,kin hade ido dashi nyi sigar mamki nace ni?sai ya waro min idanun shi baice uffan ba,”nace kaine kake min wulkanci u keep provockng me evrytime even today..kuma ka shirya kula da dakan ka dakan ka i wont eva go there,neva neva eva 

Wani Jingina kanshi yay Da alaman Yadda nake maganan na shigar sa tun ban karasa ba naji ya dora min yatsan sa a bakina,sauri nayi na runtse ido bansan meyaji shima ya cire da sauri ba,daga nan bawanda ya sake cewa uffan acikin mu qamshin abincin naji dede setin baikina naga har ya debo a fork yana min alaman wai na bude baki shi zai bani

Bnyi musu ba Ba laifi na karba naci,2 more spoon sai na girgixa mai kai, karbe spoon din nima nayi cikin shiru na shiga debowa ina bashi abakin sa yana ci yana ta kallo na.

Har ya koshi na bashi ruwa a hannun sa yasha nima yasani dole nasha,..ina aje cup naji yace Alhamdullh niko inata Allah Allah ya sauke ni,dan harga Allah dauriya kawai nakeyi,ban gama saka hakan araina ba kawai sai naji ya kwanta da baya tare da ni a hannun sa

Mimmikewa na shiga yi ya riko ni dam,a yanayin na gaji nace Ohhhh Pls let go,Asad kaje dakin ka mana
tsaban a tsorace nake murya na sanda tayi rawa,dada tallafo ni yy 2mint yana kallo na tun ina ki ina kaucewa har muka lume cikin idanun juna har sanda na samu nitsuwa Chn kafin ya dan sake ni 

wani kau da kai nayi cike da shaukin jin bana son in hade ido dashi still sai Ya shafo goshi na”cahn cikin wata yanayin muryan kasala ya furta..”hey that pulchritude,’…shiru nyi dan tun muna kanana in yasan yamun ba dede ba sai ya furta hakan ban taba tambayarsa ba amma kuma yasan nasani cewa its a dictionary word meaning”Hey that physical beuty”. Tun banson pulchritude din nan har na saba dashi abakin asad,ya make murya yace hey am soryy’fushi be maiki kyau..ki dena fushi dani,kema kinsan an hanani jin dadin rywata neko?yadda ya sauke kai sai naji tuni hankali na yadan kwanta na turo baki nace toh kadena shan tabar toh…baice min kala ba ya tabe baki,nace asad pls,yace hmm da kyar ma yayi mika sai ya sauke ni akan jikin san nayi saurin mikewa a tsaye,mika min hannun shi yay still alaman na tallafa masa ya tashi shima,aikuwa ina mika masa naji ya wani jawo ni daf da karfi na fado jikin sa saura kadan bakina ya shige cikin nasa,rudewa nayi dana ji lips dinsa yayi brushin nawa hawayen birkita dana sake ya sa shi yayi saurin sakeni ya mike tsaye yana kallo na..cikin sauri ya matso fuskata yake son shafawa na buge hannun sa axafafe aikuwa be fitan ba sanda ya dora min kiss agefe da gefen kunci na,nikuwa hawaye kawai nake sakewa ido na a lumshe na turo baki, har ya gaji ya fice yana mai rufe min kofar ban  sani ba,a sulale nabi lafiyar gado na na jawo pillow kirji na cikin wani yanayi 

da ga nan idanuna fixed akan kofar a hankli naji ina wani irin tsuma ba abunda ke subucewa abakina sai murmushi wanda ko ni bazan iya fassara shi ba…..

Tun Daga ranar rayuwar ya kasance min haka,a dadi babu dadi we remain so conected da Asad,cikin raina sosai son asad ya same mafaka ya tike ni..

Tafiyar kawu da mukayi zaton bazai dade ba sai gashi yau ana neman sati uku bai dawo ba.

“A gida yanxu Daga ni sai asad sai mama,samowar sabuwar me aikin mu zulaiha agidan yasa na samu daman sa asad cin abincin a dining dan dole.. Quiet intresting ayi ta hira da shi in ya fito don wani bin har yana bamu da dariya gashi dama bakaramin damun mama ya iya ba”.. 
Toh Daga tace mashi bazai taba girma ba”shikenan tayi magananin sa kenan,yace wa mama shi be yarda zulaiha ta masa komi ba,da mama ta dauka ko iskancin ne irin nasa dake yana yawan cewa bayason nigeria,but a kasan zuciyar sa yasan yana furta hakan ne sabida ni,ko da muke egypt yafi sakewa in har nice akan abun cin sa ko da kuwa kushewa xaiyi he knws in yace bacin na mai aiki zaiyi ba dole nice zan dafa masa,so i still cook for him kuma mama tana sane da komi

Yawanci sai inga tana kallon mu a sace tana murmushi amma bata taba cewa komai ba

Aranta itakam ta qamsu cewa muna soyayya ne,awaje na is true but wajen asad he has neva take it a serious a shasahnce dai ake tafiya da shi kullum.

Sati na gaba ne muka fara fita muna sada zumunci da yan uwa,hkan be zame ma asad matsala ba sabida harkan yawo ne,so in yana tuki he make sure ya zaga garin kano da mu.

“Mama tayi ta masifa tana cewa yaushe xaka kaimu gida ne”sai yce mata yanzu,chan in taga ji sai ta dada cewa..nan inane asad?sai yace kwana kawai zamuyi mama،sai ta yi shiru amma anjima sai taga ba kwanan aka sha ba,duk dramar su nidai ina shiru amma asad ko ajikin sa shidai zaiyi ta waina mota sai yaga ya kare ma ko ina kallo sannan ya zago ya aje mu 

Shiyasa Duk sanda muka fita sai na lura da hnklin mama kamar ba a jikin ta yake ba,ita Duk da kawu baya nan anma hanklin ta be kwanciya in har bata yi abu akan tsarin sa ba,sabida yawon da asad keyi damu sai yasa ta ma dena fita ziyaran damu kwata kwata 

Ko ajikin sa cos shi din mai kwakwalwa ne im not surpised in yace ya rike sunayen wajeje da location dinsu a garin kano.

Shikuwa Tunda yaga gari shikenan

So iya yawan fitar mama anguwa iya ficewar asad yawo,wani bin harma ya dau lokaci mai tsawo awaje be dawo ba nikuma tsoro ya hanani sakat sai inyi ta jeka ka dawo a gida.

sau daya mama ta dawo baiya nan kuma nace mata yana sama dakin shi,duk dama nasaba karyan anma sai bana jin dadi sosai araina.

this is nigeria right?ance ba abun da ba’ayi anan kasar and who knows wani halin asad zaije ya sake yayumowa,kamar nice na tsuguna na haife shi haka nake kwana da fargaban haka,baki na kullum cikin adduar kada Allah ya hada shi da abokan banza ko harkan banza nake.

I know for sure my Asad bei bin mata,although in ya ga mace ta burge shi baya iiya rife bakin sa,but a fannin yin abokai till now asaad be yarda da kowa ba sai identical twin dinsa azaad.

Ranar 6am ina zaune kan sallaya ina early morning azhkr ashe wayata taci ringing banma lura ba,dama sabida shi nakan sa a vibe kar wata rana mama ta gane yana fita a sace,wani karar fasssss naji a glasss din window wanda yasa ni tashi a mugun hargutse na nayi tsaye da ido na kifi kifi,cillowar dutsin nagani sai na daure na isa bakin wajen,lekawar da zanyi ke da wuya nagan sa yana ta tsalle yana rarraba ido alaman yana so naji shi..”da muka hade ido sai yamin hannu ban bata lokaci ba na bude masa yayi tsalle ya kama raft din ya drko ta ciki,hummm hunnnm ya ke sake nishi na kare masa kallo bance mashi komai ba,he look so weird and weary,riped jeans din daya sa adan sake take and is so crazy dat zaka dauka mutum a cikin senses dinsa in ya dauka jean din sai dai ya yar a bola matsayin yagaggen wando,ko ina a barke take but da shike kalar me kyau ce ana gani an ansan swag ne,rigar sa ma farace sol tun kan na kare mata kallo ya yaye ta daga cikin sa ya bar kansa da farar singlet ..”cikin hamma yace natty girl bazaki ce mun sannu da dawowa bane? Ke bansan rashin da’a fa,”sai na daure dai na kalle shi cikin son in tabbatar ahankl na furta”dama ka fita har ka kwana wani wajen shine bazaka fadamin ba?ba yabo na fallasa yay min shiru duk idon sa yay lui alaman da gajiya sosai ajikin sa”i know he went for midnight clubing”dan ko a egypt ne yafi kaunar sha’anin da za’a fara shi cikin dare irin 123 haka kofa na nufa kamar kurma
Na ce toh xoka ka fita u have ur room pls go out..wani share ni yy har na gaji nayi shiru sai ya tabe bakin sa kawai ya jawo pllow ya kwanta akan gado na,”.

Zanyi magana  da wuri ya mike ya xauna har yana haki’yace dan Allah ki dakata wai Ke kullum sai anbaki hakuri?..toh jiyan kasa bacci nayi so i have to go out and party,”Nace a karfe dayan daren? tsaban kana nemana da magana shine harda kwana?..wani hamman ya doka yana rufe bakin sa silenty supplicating “toh ki saba da haka dan i realy enjoyed it,..nace ohh i see,komawa yay ya kwanta sai na juya na fice na bar mashi dakin daga kan step inajin shi yana ta kwala min kira
“nadrah…nadra tsaya kiji ko kulashi banyi ba na sauka,ina tsayuwa bakin kitchen island naji zut a wayata dagowa nayi on duba sai naga sakon wai inyi masa mint tea na kawo masa,tsaki naja na share tashar sa na cigaba da abunda ya kawo ni har zulai ta shigo ta mana breakfast ina de xaune tana dan min hira.

After 2 hours Mama ne ta sauko dan muyo break fast,da shike jiyan ya fara kwana awaje anan nigeria ashe itama jiyan hankalin ta sam be wani kwanta ba,i noticed her ina gama gaishe ta sai tace ina asaad din?maza jeki ki cemishi ya sauko ina san ganin sa,na ce to na mike daki na nufa straght inda na bar shi dazun,wani sautin nunfashin gajiya da kwarrr kwarr ya cika waje,ya baje sosai sai minshari yake kamar wani bugagge,Nace hmm “oh god wato da ban kawo mint tea bane ya bingire da bacci?

A Hkli Sai Na fara duba tun daga kan tsiraran yatsun kafar sa da shike ajere suke kuma a wanke tas siffar sa sai ya baka sha’awar kallo,kalar fatar sa mai kyau ce is matte nd caramel like da ke fidda wani irin haske da walkiya har zuwa kan kyafaffen sajen sa,idanun sa sunfi komi tsari bisa dai dai misali cikakken brow dinsa shi ya tafiyar da shape din tsiriyar hanci,he looks innocent while he sleep,dirty pink lips dinsa har mai mai tayi masha Allah,tare da sauke ajiyar zuciya na sauke wani huumm sai na juya kawai na bar dakin batare da na tashe shin ba,dana fada yana bacci wajen mama da kyar naga sakewar fuska duk dama itama baso take atadashi in baccin yakeyi ba.

Mama tace min sunyi waya da kawu yace yana daf da dawowa be dai fadi rana ba,naji dadin hakan sosai araina atleast xamu na fita schl nima na huta cos i cant keep risking it  in asad ya cigaba da zuwa midnith clubs a nigeria..

Daya tashin already Na masa mint tea din,karba yyi yasha har yana zufa baice min komai ba nima sanda na barshi yaje dakinsa yyi wanka yayi refreshing wajen cin abinci sai na fara masa ‘nasiha,he dint object me today,har nagama bayyana masa yadda natsani karerayin dana keyi ma mama akan sa
Na kuma gaya masa cewa kawu na daf da dawowa mama ce tacemin haka..

Banyi xato ba abu Kamar da wasa sai naga kamar magana ta tayi tasiri kwana biyu sai Asad sai baije ko ina ba amma dai be dena shan tabar ba,bansan ko dan ni bane ko kuma dan nace abban shin zai iya dawowa anytime.

I dont know what he is plannning dai but for sure nasan shirun dayayi kwana biyu akwai sakamakon sa…….
#surayyahms…share and share ur views pls.


Tallah.

_”uhm uhm ina yan mata da uwaye  masu bukatar karanta littafi domin samun karin ilimin sanin  istimna’i wato(masturbation )?nau’oinsa,illarsa na fili dana boye?…labarin kudi kumbar susa ya kafa jigo ne da hikiman Allah,zamantakewar Aure,yarda da qaddara da abunda ya shafi sihiri da son duniya’kks littafi ne mai tsada badon kudin da za’a saka mashi sai dan darasun da zaizo da shi wanda suka fiye faruwa agaske shin ko kina so ayi budirin nan dake?TOH????????.._

 _MAZA GARZAYA KI NEMI KUJERAN ZAMAN KI A KKS PAID GRP,domin kuwa labarin Kudi… kumbar susa zai fara zuwa ne a ranar Ashirin da shida ga watan mayu 26/5/2020 AMMA Kofa a bude take ga duk mai bukatar biyan kudin labarin iyanzu”.FARASHIN SA #300ne kacal,zaka iya biya direct ta ACCT  0152983148  @surayyah muhammad suleh GTB ko VTU transfer ko mtn digits ta wannan number 08060712446 sai ka tura shaidar biyar ta 08036651119 domin Asanya ka a grop din!..hey masoya  abun alfahari inbada kaina a sare domin ku inje gida ince ya fadi????kuyi kokri ku shigo adama daku don tsabar kauna da nake muku yasa bazan so ace wannan labari ya wuce masoyi na ko daya ba????ITS GONNA be WORTH..insha Allah!_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button