RAUDHA Page 1 to 10

Cikin siririyan muryan ta me sanyi tace “ga ninan zuwa”.
“Ok sai kin zo”. Cewar Ramcy tana katse kiran
Ajiye wayan kawai tayi taƙara speed, tana tuƙin ne cike da gwaninta har Allah yasa takawo ƙofar gidan su Ramcy ƙawarta, Ramcy dake bakin ƙofar gidan su a tsaye tanufo motan tabuɗe tashige, ita kuma taja sukaci gaba da tafiya, kallon ta Ramcy tayi tana murmushi tace
“Kinyi kyau Babe”.
“Thanks”. Ta’amsa mata ataƙaice
Daga haka basu sake magana ba har suka iso gaban wani kyakkyawan Club, fitowa sukayi cikin motan bayan tayi parcking motan aciki, atare suka jera sukayi cikin Club ɗin
Sosai ciki yacika da mutane maza da mata kowa na harkan gaban shi, an saka music wasu na ta faman cashewa, suna shiga Direct RAUDHA wajen masu rawa tanufa tashige cikin su tasoma kaɗa jiki tana rawa me ban sha’awa, dama abinda ke kawo ta Club kenan RAWA, tana ƙaunar rawa a rayuwan ta, koda tana cikin damuwa ne idan har zataji kiɗa na tashi to fa sai zuciyarta tayi mata sanyi, haka tayi ta cashewa tana rausaya jiki kamar zata karye, dama ba wani auki ne da ita ba, ita kuwa Ramcy ba gwanar rawan bace, zuwa tayi tazauna cikin wasu maza tasoma kora sheesha tana yi tana kaɗa kai
RAUDHA rawa yayi rawa sai zuba ihu take yi tana dariya tana tiƙan rawa, sai da tagaji sosai kafin tayo wajen Ramcy tazauna tana waftan Sheeshan hannun ta tasoma sha tana fesarwa ta hanci ta baki cike da ƙwarewa, mazan wajen duk kallon ta suke yi suna dariya, yayinda ɗaya daga ciki yasoma mata kirari yana faman koɗa mata kai, ita kuwa sai faman bankan sheesha take yi tanayi tana shaƙan Coken, Ramcy tashi tayi tanufi wajen wani saurayi dake can zaune tare da ƴan mata, magana sukayi sannan yamiƙo mata wasu ƙwayoyi da bansan ko menene ba, amsa tayi tanufi wajen Receptionist tayi odan Juice tadawo, kallon ta kawai RAUDHA take yi har tazauna kana tamiƙa mata hannu, ita kuma tabata Cup ɗaya bayan da tasaka mata ƙwayoyin ciki, amsa kawai tayi tasoma korawa tana jin ta asama, zuwa lokacin tasoma kai ƙololuwan bugawa, don daƙyar take iya buɗe kyawawan idanuwanta tana kallon mutane, sai da tashanye gaba ɗaya tasaki Cup ɗin Ramcy tayi saurin tarewa
Lumshe idanu tasoma yi tana buɗewa daƙyar, cikin tsananin maye take cewa “ahh.. ahhm Rammmm.. Rammcyyyy ƙaro min..”
Bata iya ƙarisa maganar ba ma sai shiru tayi tana ci gaba da zuƙan Sheeshan tana fesarwa ta cikin hancin ta, Ramcy itama da tagama buguwa tashi tayi takoma tasake yin musu odan wani Juice ɗin tadawo, zuba musu ƙwayan tayi suka ci gaba da sha, yayinda su kuma mazan nan sai harkan gaban su suke yi, daga ƙarshe ma tashi sukayi ɗaya bayan ɗaya suna barin wajen, yayinda wasu suka wuce wajen ƴan matan su, wasu kuma sukayi gida don alokacin dare yayi sosai
RAUDHA buɗe manyan idanuwan ta da suka kaɗa sukayi jazur tayi tana kallon Ramcy tace “amm… Babe muje.. giii..gida, yauuu banjin zannn iya kaaaiiiii asuba”.
Gyaɗa kai kawai Ramcy tayi tana miƙe wa tsaye, taɗau jakan ta tana ƙoƙarin rataya wa, ita kuwa RAUDHA kasa miƙe wa tayi sai da tafi minti 3 azaune kafin tayunƙura tamiƙe, sai kuma takoma yarabb kamar wacce aka jefar
“Oshhhhhhh”. Tafaɗa tana riƙe kanta da yabugi kujera
Still sake miƙe wa tayi, har ta soma tafiya kuma sai tasake faɗi, dole Ramcy ne tariƙo ta suna tafiya suna layi har suka fice daga Club ɗin
“Babe anyaaa zzzaki iya tuƙi? Kar fa kije ki zubarrr damu?”
RAUDHA dake faman layi takai tadawo tana son buɗe mota but takasa, taɗago kanta tana kallon Ramcy daƙyar, lumshe idanu tayi tasake ware idanun sosai kan Ramcy kana tace
“Kin fini.. sanin.. abinda nake yi ne? Common shiiiiiga… Muje ma..na..”
Bata rufe baki ba tayi taga-taga zata faɗi, har takusa kai ƙasa tayi saurin riƙo motan tana gyara tsayuwar ta, buɗe motan tayi tafaɗa ciki tana mata key, itama Ramcy shiga tayi sannan taja motan da gudun tsiya tafice haraban wajen, izuwa lokacin tsit kake ji a titi domin kuwa wajen ƙarfe 0300pm. Ne na dare, ahankali take jan motan sai dai yanda motan take yawo akan titin zakasan ba cikin hankali mamallakin motan take ba, idan tayi nan sai tayi nan, daƙyar take buɗe idanun ta tana kallon titin, har ƙofar gida tasauke Ramcy kafin sukayi sallama taja motan tayi gaba, tana isa tanƙamemen gidan su tadanna hon ɗin da gaba ɗaya layin gidajen sai anji, Me gadi da yake zaune yana jiran dawowarta yamiƙe dasauri yabuɗe mata, tashigo aguje kamar zatayi ciki dashi tanufi parcking space, parcking tayi tajanyo jakan ta tana ratayawa tabuɗe motan tafito, tafiya take yi tana tangaɗi har taƙarisa bakin ƙofar Main parlour tabuɗe tashiga, ahankali take takawa tana faman layi taje gaba tadawo baya har dai ta’isa steps tasoma takawa tana haurawa sama, tana hawa tashige ɗakin ta tanufi kan gado tafaɗa kai, ahaka barci yakwashe ta batare da tacire ko takalmin ƙafafun ta ba.