NOVELSUncategorized

DIYAM 19

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Nineteen: Inna

Haka ya shige daki ya bar mu da budadden baki. Na kamo hannun Rumaisa muka fito da sauri.muna
fitowa nace “what? Lallai ma mutumin nan” Rumaisa tana murmushi tace “ya hadu ko? Shi yasa nace miki kizo muje mu ganshi” nace “au wai kina nufin saboda mu ganshi kikajawo ni dakin nan? Meye abin kallo a gurinsa? Wai dan wulakanci nice bararoji” Rumaisa tayi dariya tace “au wai haushi kikaji? Ke baki san wasa ba? Wasa fa yake miki dallacan” na bata rai nace “it doesn’t look like wasa yake min, har cikin ransa abinda yake nufi kenan” Rumaisa ta bagarar da maganar tace “to ya kika ganshi? Ya hadu ko?” Na tabe baki nace “ko kusa da haduwa baije ba” tace “ko dai don idonki ya rufe, Sadauki ya tare gaba ya tare baya” nayi murmushi ina jin sanyi a raina nace “yanzu kika kamo hanya yar gari” ta bani hannu muka tafa. Rumaisa ita kadai ce wadda nake zama muyi hirar Sadauki sosai da ita, tasan komai akan yadda muke ji a zukatan mu. Muka samu guri muka zauna, na bata labarin tsarin da mukayi da sadauki na cewa zai ke zuwa zance gurina a matsayin saurayina. Ta rike baki tana zaro ido tace “Diyam? Ba kwajin tsoro? Ba kya jin tsoron a kama ku?” Nace “relax. Kinsan dai gidan nan akwai yammata da yawa ko? Kuma duk suna fita zance so babu wanda zai gane, he will be just one saurayi among others, kuma I will make sure duk wanda yasan fuskarsa bai ganshi ba, ballantana kadan ne a gidan nan suka sanshi”.

Ranar da Sadauki ya fara zuwa gurina a ranar na bashi labarin encounter dina da hamma Saghir. Ya bata rai yace “kar ki sake shiga harkar sa, duk hanyar da kika san yana bi ma karki kara bi ta gurin ballantana ya sake gaya miki wata maganar banzan”. Duk sanda yazo zai gaya min next time da zai sake zuwa, dan haka ni nake fita da kaina in shigo dashi. A gefen dakin mai gadi muke zama, wanda yau da gobe sai muka zama very friendly dashi. Duk ranar da Sadauki yace min zaizo bai taba sabawa ba, koya wuce time din da yace zaizo to kuwa yan minutes kadai zai kara saboda traffic. A wannan lokacin na kara fahimtar cika alkawarin Sadauki, in dai yace zai yi abu to kuwa tabbas zaiyi din sai dai in wani abu ya faru beyond his ability.

Tun ranar da hamma Saghir yace min bararoji bamu kuma haduwa ba, nabi shawarar Sadauki dan haka ko muryarsa naji a guri to bana shiga, inkuwa tsautsayi ya biyo dani ta hanyar da yake to zanyi saurin chanza hanya. Rumaisa ce mai nacin zuwa gurinsa wai burge ta yake yi. Sai ranar nan bayan nayi ten days a gidan, muna tafiya da Rumaisa zata rakani in shigo da Sadauki sai muka hango Saghir a can packing lot, yasha farin voile sai kyalli yake yi kuma daga inda muke muna jin kamshin turarensa sannan muna jin muryarsa yana ta sirfawa baba audu zagi akan wai bai wanke masa motar daya saka shi ba, dan tsohon Allah sai hakuri yake bayarwa kansa a kasa amma kamar kara zuga saghir yake yi “tsabar iskanci da rashin mutunci wajan awa guda kenan nace ka wanke min mota ta amma saboda ban isa ba shi yasa kaki wankewa ko?” Baba Audu yace “kayi hakuri yallabai, Alhaji ne ya saka ni in gyara masa gurin da yake shan iska yana so ya fito anjima” yace “dalla yi min shiru, wallahi in kayi wasa kafin in koma porthercout sai kabar gidan nan. Ka kiyaye ni wallahi” dan dattijo ya durkusa yana ta bada hakuri. Ban san lokacin da naja wani uban tsaki ba, Rumaisa tayi saurin toshe min baki ta jani bayan flowers “rufa ma kanki asiri Diyam. Tsaki? Hamma Saghir? Wallahi in yaji ki zai balla ki” nace “ai kuwa daya gane cewa shayi ma ruwa ne” ta girgiza kanta tace “Sadauki ne dai takamar ki ba wani ba, amma kiyi tunani, do you really want to get him involved with hamma Saghir?” Na juya ina kallonsa, tabbas Sadauki na is very brave and fearless, amma saghir is not his match dan at least ya bashi shekaru goma, ga kudi ga kuma gata. Dan haka hada shi rigima da Sadauki will be like putting Sadauki in trouble. Na ja bakina nayi shiru sannan muka zagaye ta bayan sa muka fita daga gidan. 

Sai three days to resumption date din mu sannan Baffa yazo da kansa ya daukeni zuwa gida. Matan gidan sun hada min goma ta arziki wai tsarabar boarding. Amma ni sai naji duk boarding din ta fara isata amma inaji inagani haka aka daukeni aka mayar dani. Sanda muka dawo next holiday shima ina zuwa na tarar da kaya na a ajiye, ban damu ba na shiga harkokina ina tunanin ai sharada ba nisa amma sai naga inna tana hada nasu kayan ita da Asma’u tace “Kollere zamu tafi, mun kwana biyu bamu je mun gaishe su ba musamman yan uwana da muke uba daya nan take naji bakin cikin duniya ya ishe ni amma haka Baffa ya debe mu a mota gabaki daya har su Ummah muka tafi, naji dama dama saboda ganin da Sadauki ne, amma bayan munje mun kwana daya a gidan Hardo da sabuwar matarsa sai naga su Baffa suna shirin komawa suna ta sallama da mutane, na bishi soro da gudu na rungume shi ina kuka nace “Baffa dan Allah zan biku mu koma tare” ya rike fuskata yace “kiyi hakuri uwata, ba tare daku zamu koma ba ku zaku zauna ku zagaya yan uwan innarku na gurin babanta” ai kuwa a take na kara wani kukan dan ni in akwai abinda bana so a lokacin to zama a Kollere ne. Suka tafi, Baffa da Ummah da Sadauki, suka barmu ni da Asma’u mun rike juna muna kuka, Inna ta tabe baki tace “sai suje ai suci uwar da zasu ci a gidan”.

Mune daga wannan gida mu koma wancan mu kwana anan mu tashi anan muna ta ziyarar yan uwa har sai da muka yi sati biyu, Asma’u ta dan ware amma niko alamar warewa banyi ba, ranar da muka cika sati biyu Baffa yazo daukarmu ashe wai yayi wa inna waya akan mu shirya zaizo mu tafi ita kuma taki. Yana zuwa ta lissafa masa sauran gidajen da bamu je ba shi kuma yace baisan magana ba, “Diyam makaranta zata koma nan da sati daya, kamata yayi taje gida ta huta tukunna” Inna tace “wanne hutu zatayi a gidan? Taje dai gida mayun gidan su cigaba da lasheta” Baffa ya gyada kai yace “in har mayun gidan basu cinyeta ba a tsahon wadannan shekarun, to kuwa ke a garin wannan yawon naku zaki kaita gurin mayun” nan take sai rigima, inna tace ai Baffa yace yan’uwanta mayu ne. Hardo ya goya mata baya yace “to in bata kaisu sunga yan’uwanta yanzu ba sai yaushe?” Wannan yasa Baffa ya shiga motarsa yayi tafiyar sa, yace duk sanda muka gama yawon ma taho a motar haya. 

Bamu koma ba sai two days to komawa ta makaranta, dan haka a gurguje na shirya shima kuma dan na samu Ummah ta fara harhada min wasu kayan kafin inzo. Dan haka wannan hutun ni da Sadauki sai gani da ido. 

A hutun second term ne Baffa ya buga kafarsa yace babu inda zanje hutu, shima yana so ya zauna dani. Nan take rikici ya balle a gidan mu, Inna ta fito da abinda yake zuciyarta na kiyayyar ta a dangane da dangantaka ta da Sadauki, tace “sai dai bayan raina wallahi, wannan yarinyar indai ni na haife ta ba zata auri wannan yaron ba” Baffa yace “saboda me? Menene dalilinki na cewa haka?” Tace “Saboda bana sonsa, na tsane shi tamkar yadda na tsani uwarsa kuma bazan taba yarda in hada jini na da nasu ba” Baffa yace “to shikenan dalilin naki? Kishi ne kawai dalilin naki? To kuma in Allah ya riga ya rubuta akwai aure a tsakanin su fa? Fada min ya zakiyi?” Tace “sai in sallama ta, in dai ta aure shi to babu ni babu ita har abada sai dai ta nemi wata uwar bani ba” na durkushe a gurin da nake ina kuka kamar raina zai fita. Ina da karancin shekaru a lokacin amma nasan muhimmancin Inna a gurina, nasan darajarta ta wuce in hada tada kowa a sauran mutane, amma kuma nasan irin zafin son da nakeyiwa Sadauki, nasan irin soyayyar da shima yake yi min da kuma irin kyawawan halayensa shida uwarsa. Menene laifinsa.

Ta cikin hawayena na hangoshi ya shigo gidan da kayan da yake zuwa gareji dasu a jikinsa duk sunsha bakin mai. Ya tsaya yana kallon mu kawai, Ummah tayi masa alama da hannu cewa ya fita, sai ya ajiye kayan hannunsa ya juya har yakai bakin kofa sai kuma yajuyo yana kallona fuskarsa cike da concern.

Wannan hutun sam ba ajin dadi nayi shiba dan sai dana gwammace ina ma wani gidan aka kaini dan sosai Inna ta mayar dani matar kulle, ko tsakar gida bata bari na in fito daga dakin mu sai palon ta, Baffa ma sai dai in ya shigo in ganshi in kaishe dashi. Yar islamiyyar da nake zuwa in nazo hutu itama ta hana ni zuwa. Asma’u ce kadai abokiyar hira ta duk da ita lokacin bata da hankalin fahimtar me yake faruwa sosai. Rannan ina kwance a daki sai gata da takarda a bakin zanin ta ta miko min a hankali tace “inji Sadauki, yace kar Inna ta gani wai zata dake ki” na karba da sauri zuciyata tana muradin jin abinda yace, na bude na karanta, kalma uku ce kawai “how are you?” Naji hawaye ya taho min, shi concern dinsa akai nane, shi halin da nake ciki shine damuwarsa. 

Ranar nan muna gab da komawa makaranta Baffa yana palon Inna yana cin abinci ni kuma ina zaune kusa dashi na dora kaina a kafadarsa, a gurinshi ne kadai nake samun hope. Sallamar Sadauki muka ji a bakin kofa, nayi saurin kallon kofar amma sai naji Inna tace min “tashi ki shiga daki” kamar zanyi kuka na shiga dakin amma sai na makale a bayan labule. Ina kallonsa ya shigo ya durkusa a gaban Baffa ya ajiye wasu takardu yana yi masa bayani akan wata mota da suka siya zasu gyara su siyar. Amma ni ba abinda yake fada nake ji ba fuskarsa kawai nake kalla, sai naga ya kara kyau fuskar ta dan canza min, sannan na lura da abinda ya chanza, ya fara tara saje. Nayi murmushi na durkusa a gurin ina cigaba da kallon sa har ya gama maganar da yakeyi. Sannan ya juya side Inna ya gaishe ta duk da yasan ba amsawa zatayi ba. Bata amsa din ba har ya mike, sai daya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalli kofar dakin mu, muka hada ido sai ya lumshe idonsa ya bude sannan yayi murmushi ya fita. Yana fita Baffa yace wa inna 

“Amina ni dai bazan gaji da gaya miki cewa ba kya kyautawa ba, kina dora kiyayya akan tushe marar dalili. Su yan uwan namu da suke kara zuga ki kike ganin kamar baki da masoya kamar su duk ranar da babu raina su zasu fara gudun ki keda yayanki, zasu fara ganinku kamar wasu responsibilities a gurin su. Ina ji miki tsoron wannan yaron da kike wulakantawa shine zai zama gatanki ke da yaranki watarana idan babu raina. Shi ɗa na kowa ne.” 

Sai da lokacin komawa ta makaranta yayi sai naji sam bana son tafiya, duk da cewa zaman gidan kamar zaman kurkuku nake jinsa amma haka nan naji bana son rabuwa da gidan. Kamar ko wanne term, wannan karon ma Baffa da Sadauki ne suka tafi dani. Sai bayan da muka dauki hanya sannan Baffa ya fara magana 

“Sadauki, Diyam ku bude kunne sosai kuji abinda zan gaya muku. Tun a gida naso yin magana daku amma saboda rigimar iyayen ku yasa na bar maganar nace mayi a hanya daga ni sai ku. Na farko, kun bani mamaki gaba dayan ku kuma kun bani kunya, yanzu har kunyi girman da har za ace an fara rigima akan auren ku? Yaushe aka haife ku gabaki dayan ku? Waye kuke tunanin zai yi muku aure yanzu? Ba dai ni ubanku ba. Musamman kai Sadauki kai da kake namiji, so nake kayi karatu mai zurfi kazama wani yadda wata rana zan kalle ka ince ‘yes, that’s my son’. Ke kuma Diyam, ko a ranki kada ki saka cewa zanyi miki aure yanzu. Sai kin gama makaranta kin shiga jami’a sannan in Allah ya kawo miji a lokacin sai inyi miki aure da sharadin zaki kammala karatun ki a gidansa, in kuma mijin bai samu basai kin kammala duk lokacin da Allah ya kawo shi sai ayi miki auren” yayi shiru muma duk mukayi shiru, sannan ya dora “in Allah ya kaimu lokacin, kun zama abinda nake fata zaku zama, kuma ya kasance har lokacin kuna son auren junan ku, to ni zan yi supporting dinku. Saboda dukkanin ku yaya nane, nasan halayenku kuma zanyi alfahari daku a matsayin surikai na. Kuma hausawa sunce da arziki a gidan wani gwara a gidan ka. Amma ku sani, daga ni sai Zainab ne zamu goyi bayan wannan hadin, ke Diyam a gabanki kinji kalaman da innarki ta fada, kuma da gaske take, kuma ni bazanyi miki fatan kiyi aure babu saka albarkar mahaifiyarki ba dan haka wannan shine challenge dinku ku tabbatar kafin lokacin dana fada muku kun yi kokari kuma kun dage da addu’ah kun juyo da hankalin ta ta amince.”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button