NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 10

*_Bilyn Abdull ce_*????????

*_NO. 10_*

            Inna dake tsakar gida tana surfen ƴar masarar tuwonsu ta ɗago ta kalli basiru batareda ta amsa masa sallamarsaba, harya ƙaraso gareta bata iya janye idontaba, hannunta ɗaya da taɓarya ɗaya kuma tana ƙokarin janye kan akuya dake saka kai a turmin da take dakan, ƙarasowa yay yana girgizama Inna makullin motar hannunsa, fuskarsa washe da
murmushi.
     “Innata kuma fa ALLAH ya kaiku matsayin dawani mahaluki bai taɓa takawaba a garinnan”.
    Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tacigaba da dakanta tana faɗin, “Nagani kam, yaka baro su baban naka?”.
    Duk da maganar tata ta doki zuciyarsa saboda fahimtar gatse tamasa amma saiya basar ya amsa da “inna suruki dai, iyayena kam ai kune, amma suna lafiya lau, sunce na gaidaku da ƙyau, wani satin zasuzo maganar auren”.
     Inna tasaki murmushin takaici da jinjina maganar a ranta, gidan mazane ke zuwa neman aure, amma su yau ga sabon salo suna gani, gidan mace suna zuwa neman aure gidan namiji.
    Bata sake bi takansaba tacigaba da dakanta, shima saiya miƙe yana mitar ƙurar ƙasa da turmin ke tayarwa zata ɓata masa jiki.
    Ci kanka inna bataceba itadai.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       Ummukulsoom batada labarin dawowar Basiru ɗilau sai a washe gari, shima Mariya ce datazo gidan take faɗa mata, dan itama tazama budurwa yanzu, sunema ƴammata masu tashe a ɗilau, dukda kuwa shekarunta 14 yanzunema suka shiga js3, amma Ummu tasan daganan ba gaba zasuyiba.
      Sosai zancen dawowar basiru da dalleliyar mota ya tsayama Ummukulsoom a rai, ta ɓoye a bayi tasha kukanta dataje wanka, tasan fidda son Basiru aranta abune mai matuƙar wahala da fama, amma zatayi ƙoƙarin kamantawa koda da kokawane da yaƙin ƙwanji dana zuciya.
      Tsaf gwaggo ta lura da halin da take a ciki saboda taji lokacin da mariya ke sanar mata, amma saitayi tamkar bata gantaba, dan tasan yimata maganar tamkar cigaba da fama mata gyambon dake zuciyartane.
     Zama Ummukulsoom tayi ta rubuta doguwar wasiƙa ta ajiye, da nufin gobe kafin a wuce da ita zata bada akaima Basiru.

★★★★★
  
       Shirye-shiryen miƙa Ummukulsoom kaduna yanata kankama, duk abinda yakamata anmatashi, ƴan gyararraki na jiki gwaggo hinde tamata iya iyawa, maganar kayan ɗaki dai Alhaji Mahmud yace su baba karsuyi komai, dan Ummu ma ba kaduna zata zaunaba, legas zatabi mijinta..

        ★★★★★★

Washe gari sukuku Ummu ta tashi tamkar mara laka a jiki, ita kaɗai tasan halin da take ciki, sai Aziza datasan halin mutanen gidan Alhaji Mahmud, dukda gaskiya itama bata taɓa ganin mijin Ummu ba.
        Aranarma dai baba yazo har gidan gwaggo yasake ma Ummu nasiha shida sauran iyayeta ƙannen mamanta, daga nan yace Ummu ta shirya bayan sallar zuhur taje can gida tama su baba yalwa sallama.
     Da to ta amsa masa tana sharar hawaye.
         Gaba ɗaya sai Ummukulsoom ta daina fahimtar komai dake faruwa a gidan, hatta faɗan dasu gwaggo hinde sukai mata dasu inna laraba da babanta babu abinda ta fahimta, saima nanuƙema Gwaggo himde da tayi akan itafa sai da ita indai anason taje.
     “Haba Ummukulsoom kiyi haƙuri mana, kinga yanzu an yanke da mutum biyar kawai za’aje, insha ALLAHU namiki alƙawarin idan ƙura ta lafa zanzo naga matsugunninki kinji”.
     Ummu na kuka tace, “Nidai Gwaggo ban yardaba”.
       “Karki yarda ɗin dan Ubanki, ke koma banzar halayyar matan ubanki bazaisa kiji ɗokin barmusu gidanba yau suci baƙin halinsu suda ƴaƴansu, ga cin fuska da basiru yay mana, amma ubangiji ya nuna masa shine gatanki, ni tashi muje ki canja kaya konayi kutufon lahadi bakwai dake”.
      Jikin Ummu na ɓari tabar jikin Gwaggo tabi Umarnin Inna laraba, dan itace mai masifar.
        
    Ƙarfe biyu dawasu mintuna Ummukulsoom da Aziza suka fito daga gidan gwaggo tana sharar ƙwalla, yayinda su inna laraba kebinsu a baya, dan bazata sake dawowa gidan gwaggo ba, daga can gidansu za’a wuce da ita kaduna.
     Babu abinda zuciyarta keyi sai lugude da dukan goma-goma, saboda dole sai sunbi ta ƙofar gidansu Basiru, fatanta da addu’arta ALLAH yasa karta gansa.
       Sai dai kuma addu’arta bata karɓuba, dan tana karyo kwana dashi tafara tozali, ta sauke manyan idanunta bisa ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa ta asalin jinin fulani, hakan yai dai-dai da ɗago tasa fuskar shima suka haɗa ido, daga ita harshi saida gabansu ya faɗin, Ummu ta sakar masa wani murmushin takaici daya zauna bisa ransa tamkar zane akan dutse. shine yay saurin janye nasa yana wani tamke fuska tamkar yaga mutuwa, danshi fa har yanzu babu wanda ya faɗa masa an ɗaura ma Ummu aure, to baya mu’amula da kowa a matasan garin, dan gani yake shi yafi ƙarfinsu, Inna da baba kam ma ko kallon arziƙi basa masa, daga amsa gaisuwarsa basa daɗawa basa ragawa, hakan kuma bai damesaba, a cewarsa idan sukaga kuɗi zasu sakkone.
      Ummu kam ƙoƙarin haɗiye hawayenta takeyi da wani bahagon ƙududu daya tokare maƙoshinta, saida suka ɗan gotashine ta zaro takardar data rubuta a hijjab ɗinta tabama Aziza da nuna mata basiru da hannu tai gaba.
     Fahimtar da Aziza tayi ne yasata amsa takoma baya tana tamke fusaka dan bama ta buƙatar basiru ya kawo mata raini, ita ƙyansa bawai ruɗarta yayiba.
     A saman motarsa dayake ƙokarin buɗewa ta ɗora masa tana jifansa da harara, “Gashinan inji Ummukulsoom ”.
    Bata jirayi amsarsaba tai gaba saboda kusantowar su inna laraba, bayanta yabi da kallo cikin takaici, wlhy data tsaya da sai ya kifa mata mari, cikin jan tsaki ya ɗauki takardar ya jefa a mota yashiga yana faɗin “baƙauyar banza, dama kinbar wahal da kanki wajen rubutamin wasiƙa, dan ayanzu dai tsakanina dake *Wutsiyar raƙumi tai nesa da kasa*. ban ƙiba zuwa nan gaba ƙila na dawo gareki kema ki dandali arziƙi”.
      Shi kaɗai yake sambatunsa a mota ya na tuƙi, dan zaria zaije.
       
      Haɗuwa da basiru ba karamin miki ya tadama Ummukulsoom ba, shiyyasa kwata-kwata bata fahimtar faɗan da ƴan uwan baba suke mata, itadai tana saurarensune kawai.
      Gab da la’asar motoci uku sukazo na ɗaukar amarya, dan babane yacema Alhaji Mahmud ba mutane da yawa bane zasu rakota, shi soyayma akaita da safe baƙi su juyo da yamma.
    Amma sai Alhaji Mahmud yace sam bazai yuwuba, saisun kwana itama kowa yasan ƴar gatace.
       Bayan an idar da sallar la’asar ne aka fito da Ummukulsoom dake kuka tamkar ranta zai fita, mata sai leƙe suke ta katanga, marasa haƙuri kuwa sunfito tsakar santa inda yara suka baibaye motocin ɗaukar amaryar.
    Mota ɗaya kayan Ummukulsoom aka loda, na gara da wanda zata iya buƙata da kayan sawarta, ɗaya kuma mutum huɗu suka shiga, uku mata namiji ɗaya cikin yayunta.
     Ɗayar motarma mutum biyu sai ummu ta Uku, sai aziza a gaba.
      Kamar haɗin baki yara suka fara raira waƙar amarya ta bankwana, hakan saiya kuma janyo hankalin mata suka makalƙale katangu suna kallo har motocin ɗaukar Ummukulsoom suka lula.

★★★★★
   
      Ganin basiru ba ƙaramin tsayama Ummukulsoom yayi a raiba, har suka ɗauki hanyar kaduna tana kuka ƙasa-ƙasa na tausayin kanta, shikenan yau tabar ahalinta gaba ɗaya tatafi gidan aure, gidan Aurenma inda akafi ƙarfinta, kallon lamari take tamkar wani almara ko film.   
        Abu ya haɗe mata goma da ashirin, kukan rabuwarta da tushenta da mahaifinta datafi ƙauna fiye da kowa da dangin mahaifiyarta, kukan rabuwa da masoyinta basiru wanda alamu sun nuna da gaskefa sun rabu har abada, yaya zatayi da ɗunbin so da ƙaunar da take masa kenan?, ga rashin jin daɗin jiki, sai fargabar sake sabuwar rayuwa a gidan Alhaji Mahmud, ga tsananin tsoro da firgici idan tama tuna wata aura?, dawa zata zauna?.
          Kwata-kwata tarasa jinta da ganinta dama dukkan tunaninta har suka bar garin zaria, tunma tana jin fitar iska sama-sama har idonta ya rufe ruf taji ɗif sai duhu daya mamaye jinta da ganinta.

        
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

            Momcy zaune a ɗaki itada ƙanwarta Mansura da bata wuceba, sai Ummi babbar ƴarta.
       Kallo ɗaya zakai musu ka fahimci duk ransu a ɓace yake, Mansura ta sauke numfashi tana janye tagumin da tayi.
        “Aunty Jamila ga shawara, nifa a ganina kibi gargaɗin da mijinki yay miki, dan kinfi kowa sanin halinsa. Mu tarbi amarya tamkar ranmu babu komai, idan zata wuce legos ɗin nan ne zamu samu damar gudanar da shiri na gaba kuma”.
         “Hum mansura kenan, da kinsan yanda nakejin wani baƙin ciki akan aurennan na Fodio da bakice na danne zuciyata na tarbi shegiyar yarinyarnan da danginta ba, amma kuma ba a ƙin ta mutane inji masu ida magana, minene shirin namu na gaba?”.
      “Yauwa auty, abinda dama nakeson ki tambaya kenan, bayace nanda kwana biyu za’a kaita wajen Amaan ɗinba?”.
      “Eh haka yace”.
“To Aunty anan ne kekuma zaki lallaɓasa akan kinaso kuje duka gidan rakata, zaki samu damar ganawa da Amaan ɗin kema, idan kun tashi tahowa abaro masu Ummayya da Aneesa su zasu ƙarasa mana sauran aiki su hana tsinanniya zaman lafiya, tunda ba koyaushe Amaan ke a gidaba dama”.
      Ummi da tun ɗazun batace komaiba tai saurin faɗin, “Wlhy shawaran ki yayi Aunty Mansura, Momcy mubi wannan shawarar”.
        Numfashi Momcy ta sauke, tace, “Shikenan ALLAH yasa mu dace, yanzu sai a tashi afara shirya abincin tarbar amarya, suma dangin nasa ai musu magana, dannifa nama ƙagara akawo maryar gobe su kama gabansu, duk sunzo sun cika mana gida”.
      Baki Mansura ta taɓe tana miƙewa, “Aini kinama min ƙoƙari wlhy, ni bama zan ɗauki wannan iskancinba dangin miji suzo su taremin agida a hanani rawan gabar hantsi, komai nayi da mijina da ƴaƴana idonsu nakai”.
      Ummi ta haɗe fuska dan zuciyarta ta sosu da maganar ƙanwar mahaifiyar tata, koba komai dai aisu dangin mahaifintane, kuma sune adonta. Tashi tai ta fice tabar musu ɗakin, duk suka bita da kallo mamaki.
    “Tofa, Wai Ummi haushi taji? Tafison dangin Ubanta akanmu kenan?”.
      Momcy kasa cewa uffan tayima ita, dama wannan halin Ummi ne, tatsani a kushe dangin dad nasu, ta nan ɓangaren suna shan saɓani da Momcy ɗinsu, dan itakam tana son dangin mahaifinta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
  
        Sun isa cikin kaduna gab da magrib, Alhaji Mahmud na a harabar gidan zaune yana alwala, direba ya danna hancin motar cikin gidan bayan sojan mai gadin ya buɗe musu gate.
         Inna laraba ce ta fahimci halin da Ummu take ciki na gushewar tunani, dan haka takamo hannun ta fiddota a mota tana mata magana ƙasa-ƙasa.
     “Haba Ummukulsoom dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU lafiya zakiyi zamanki, ALLAH yana tare dake ɗiyata”.
    Guntun murmushi kawai Ummu tayi, zuciyarta nawani irin suya da luguden tsoro tamkar zata faɗo ƙasa, ƴar hayaniyar mutane dake tunkarosu yasata gyara gyalenta sosai takuma rufe fuskarta tana haɗiye hawayenta.
      Dangin Alhaji Mahmud ne na Ajiwa da sukazo biki, shine suka fito tarbar amarya saboda isa yaleƙa ya sanar musu, ganin Hajiya Jamila da ƙawayenta basuda niyyar hakan da danginta saisu sukaga yakamata su nuna halin dattako da cikar mutuncin ɗan uwansu. 

    Yanda dangin Alhaji Mahmoud sukema su Inna harira lale marhabun sai farin ciki ya kamasu, dansu basuyi zaton hakanba, musamman ma Altine matar ƙanin baba da Inna laraba da gidan Alhaji Mahmud ya rikitasu, sai yanzu Inna laraba tafara fahimtar abinda Ummukulsoom ke nufi da mutanen sunfi ƙarfinsu.
        Alhaji Mahmud daya kammala alwalarsa saiya miƙe zai fita masallaci. Ya kalli Ameer daya shigo yanzu da mota, da alama daga wajen aiki yake, janye idonsa yay daga kan Ameer dake tunkaroshi ya maida ga ƴan uwansa, cikin ƙannensa ya yafito ɗaya da hannu.
     Da sauri taje gareshi tana faɗin “Yaya baƙi sun iso kuma, To ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya, yasa abokiyar arziƙinsace”.
       “Amen” kawai yace ya gyara tsayuwarsa, “Amina mike faruwa naga kunbar baƙin anan?”.
     “Babu komai yaya, yanzu muke shirin shiga dasu ciki, saidai bamusan inane za’a saukesuba, dukdama naga basu da yawa”.
      “Ina ita jamilar?”.
“Tana ciki yaya, munga direba yazo ya sanar da isowarsu amma babu wanda ya motsa a cikinsu shiyyasa mukaga yadace mu mufito”.
        Tuni fuskarsa takuma nuna alamar ɓacin rai, kallon Ameer yay daya iso, cikin harshen turanci yace yaje yakira masa hajiya Jamila”.
     Ummu da Aziza kawai sukaji miyace, dukda ita Ummu ma bawani can sosai takejin turancinba.
     Minti baifi Ukuba saiga Hajiya Jamila ta fito cikin kwalliya, fuska ta saki ganin Alhaji Mahmud tsaye a wajen, “Baƙi sannunku dazuwa, Rakiya ashiga dasu ciki mana tsayuwarmi kuke anan?”.
     Kallom mamaki duk sukai mata da jinjina makircinta, sunsan dai dantaga yaya su ne take wannan barikacin.
      Inda yake can gefe tsaye ta nufa, “Abban Fodio gani, ina bayi isa yashiga yana sanar da isowars….”
    Wani banzan kallo yamata na kinma rainamin hankali.
    Hakanne ya saka zuciyarta lugude.
      Cikin kaushin murya yace, “Wlhy Jamala ki kama kanki, karki bari haƙurina yaje bango akan lamarinnan fa”.
       “Haba Abban Fodio kayi haƙuri dan ALLAH, kagama gashican ana kiran salla karka makara”.
      Baikuma cemata komaiba yanufi hanyar fita.
      Taɗan harari bayansa kafin tajuyo gasu Ummukulsoom tana washe haƙora saikace gaske.
     
         Abin mamaki su Ummukulsoom suka sami tarba ta mutunci gasu Hajiya Jamila, wannan abu yabama Ummukulsoom mamaki, dukda dai ta zargi kodan baƙin ido tayi hakan? Dakuma ganin Alhaji Mahmud yana gida.
        Dan gidan babu laifi yacika da dangi da ƙawayenta.
     Aziza ma abin ya ɗaure mata kai over, tarasa ya da zata fassara wannan tarba da akai musu, suko su Inna Laraba basusan dawan garinba, sai suketa jinjina kirki irinna jama’ar gidan.
     Abinci mai rai da lafiya aka baje musu, saida sukaci suka ƙoshi sannan suka fara shirin sallar magrib da aketayi, Ummu dai taƙi cin abincin, tundama suka shigo kwance take abinta, sai kunun aya da Inna Harira ta takura matane tatashi tasha, dama tana fashin salla, dan haka koda suke ta alwala ita bama ta motsaba daga kwancen da take.
     Bayan hajiya jamila da Aunty Nurse Ummukulsoom bataga kowaba a yaran gidan har suka kwanta barci.


★★★★★★★★

      Da safe ma abinci mai ƙyau aka basu, sukaci suka ƙoshi kafin suɗan ƙarama Ummu faɗa suka hau shiri, dan sosuke suje gidan Inna harira su huta zuwa gobe su koma ɗilau kamar yanda ta roƙi alfarma.
     Bayan sun kimtsa aunty Nurse tazo taimusu rakkiya falon Dad kamar yanda yabada Umarni, sun gaggaisa dayima juna godiya, tareda addu’ar sanya albarka ga auren.
    Yayinda Momcy dake gefe ke murmushin yaƙe, dan takaici ya kumeta jitake tamkar ta makesu.
     Mota yabada akaisu gidan Inna harira, zuwa gobe isa yaje ya maidasu ɗilau.
    Cikin mutunci aka rabu, yayinda Ummu ke kwasar kuka tamkar numfashinta zai fita, Aunty Nurse taja hannunta zuwa wani sashe can gefe idan ka wuce nasu Ameer, tunda tazo gidan kusan shekara ɗaya bata taɓa shiga ɓangarenba, saima lokaci-lokaci ta lura ake buɗeshi a gyara, ita tama zata ba’a amfanin komai aciki………..*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button