NOVELSUncategorized

DIYAM 45

Fauziyya

Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama
makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba’a cigaba
da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace “wallahi

Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa
samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a
cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu
yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi
yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da
zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk
ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da
kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki
yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi
ba mu auren mu ke so kawai” na jinjina maganar nace
“amma biki fa? Gara fa?” Tace “wannan kuma mijin ki zaki
yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana.
Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi
abincin biki da shi” nayi dariya nace “kai murja, hadda
sharri kuma?” Tace “wallahi ba sharri bane ba kayan da
yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin
su. Amma ya bar alhajin da yar shara”.
Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su
ya kira ni ya zazzage min bala’i. Bance masa komai ba har
ya gama sannan nace “ni dai bani na kar zomon ba, ni
ratayar ma ba’a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka
neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu
ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya
gansu ba” ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka
dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.
Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min “ke yanzu ko
dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba.
Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai
kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo” sai
naji ma abin ya bani dariya nace “duk wanda ka gama
samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar
Diyam?” Bai musa ba yace “naki special ne. Da gaske nayi
missing dinki fa” sai na kashe kawai. A raina ina jin inama
yayi zamansa a can kar ya dawo?
Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai
na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe
da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana.
Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu
airport ni da Subay’a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai
dai suje da Subay’a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi
wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana
na gida nayi kwanciya ta a kan gado.
Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min
nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay’a ta
shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo
min kaya da jirgi da mota” nace “kice kin gode, sannan
kice masa ga abinci nan a dining” ta fita na koma nayi
kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune
ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da
kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace “shikenan? Babu
oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan
welcome back hug ba zai samu ba?” Nace “na dafa maka
abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?” Ya
saki hannun Subay’a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na
sauka na fita na bar musu dakin.
Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa
dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da
nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma
kasa muka zuba ni da murja muna ci tace “ke ba zaki tafi
gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin
ke kina wulakanta naki?” “Humm” kawai nace mata sai ga
kira kuwa Subay’a tana yi min inzo inji Daddy. Yana zaune
a kujera ya hade rai “ki zo ki zuba min abincin tunda ba
zakiyi min wankan ba” bance komai ba na zuba masa na
kawo table gabansa na ajiye masa. Yace “wai ke ciwon
rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina
mayar min yafi dadi” nace “ba ciwon rashin magana bane
ba, ƴata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta” yayi
dariya yana kallon Subay’a data zauna ta zuba mana ido.
Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace “kai! Matar nan
wani duwawu naga kina yi fa” nayi saurin kallon Subay’a
naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.
Muna kasan Subay’a ta jawo wani karamin akwati da kyar,
murja ta tashi ta taimaka mata suka sauko dashi tana
cewa “Mommy kinga kayan da Daddy ya siyo min” tana ta
bubbuda wa, kayan sawa ne masu kyau da takalma, sai
toys, murja tana ta yabawa, sai kuma Subay’a ta koma
sama da gudu sai gata da karamar travelling bag mai kyau
ta kawo min. “Inji Daddy, wai irin kayan da turawa suke
sakawa ne ya siyo miki kema kike sakawa. Ki koma irin
su” na bata rai nace “to sarkin surutu” na karba na ajiye,
murja ta dan dake ni tace “tashi zaki yi kije kiyi godiya
sosai” na mike na tafi amma sai nayi kwana na shiga
dakina nayi kwanciya ta.
Sai bayan magrib ya shigo dakin yana kallona ina ninke
sallaya yace “zan fita, zan tafi zance” na dauke kaina nace
“ba gidan Alhaji ya kamata kaje ba? Ka gaishe su kuma
kaga abinda aka yiwa gidan?” Sai kawai naga yayi
murmushi yace “au kishi kike dan zanje zance ko?” Na
zauna a bakin gado nace “Saghir, na riga na gaya maka
tun kafin kayi tafiyar nan ni ko mata goma zaka aura ba
zanyi kishin ka ba. Ni da son samu nane ma hudu nake so
kayi, yadda zaka bani takarda ta in kara gaba” ya karasa
shigowa yana cewa “wato kin ganshi ko? Alhaji ya tura ki
kin ganshi ko? To bara kiji, in shi yake zuga kima ki gaya
masa, auren ki yanzu na fara. In kinga na rabu dake to
mutuwa nayi” ya juya ya fita.
Ranar da wuri na yiwa murja sallama na hau sama tana
tsokana ta “wato miji yazo shine zaki tafi turaka ko?” Nayi
dariya kawai na tafi, na shirya Subay’a na kwantar da ita
sannan nima na shirya na rufe kofa ta nasa key nayi
kwanciya ta. Cikin bacci naji karar wayata, na dauka na ga
Saghir ne sai na saka ta a silent na juya na cigaba da
bacci na, sai kuma naji shi yazo yana knocking, ko kallon
kofar banyi ba har ya gaji yayi tafiyar sa. Da sassafe ya bar
gidan, a raina nace “Allah ya raka taki gona”.
Da yamma sai ga Mama tazo, ni na dauka zuwa tayi gani
na sai da naji ta kama yi min fada sannan na fahimci
Saghir ne ya kai kara ta. “Diyam me kike nema wa kanki?
Kin manta abinda annabi ya fada cewa mata sunfi yawa a
wuta? Kuma mafi yawansu sun shige ta ne sakamakon
rashin bin aure? Abinda kike so kenan? Wuta kike so ki kai
kanki? To wallahi ki nutsu kiyi wa kanki fada. Ganin
Sadauki ya dawo ne zaki kuma dorawa kanki kulafucinsa
ko? So kike a lahira shi Sadaukin da kike yi saboda shi
idan ya aikata aiyukan alkhairi ya kasance a aljanna ke
kuma kina wuta saboda shi?” Nace “Mama ni ba dan
Sadauki bane ba, Sadaukin da ko kula ni baya yi?” Tace
“to ya zaiyi ya kula ki? Matar aure ce fa ke. Ke ai har
yanzu ba hankali ne ya ishe ki ba shi kuwa da hankalinsa.
Saghir yace shi yana sonki, yana son zama dake, me yasa
ke ba zaki so shi ba? Shima Sadaukin nan fa dole
watarana aure zaiyi, yadda yake da kudin nan ma sai ki ga
ya auri hudu a rana daya. In haka ta faru kuma ya zakiyi?.
Sai dare Saghir ya dawo gida. Yana shigowa palo murja ta
gaishe shi ya hade rai yace “ki shirya gobe ki koma gida”
tace to sai ya wuce sama. Murja ta kalleni pleadingly, ni
kuma na daga mata kafada. Kamar bazan tashi ba
musamman ganin ko kallon inda nake baiyi ba kuma dai
sai na tashi na bi bayansa. Ina shiga dakinsa naga yana
kokarin cire kaya sai na kama masa ya cire nayi hanging
rigar sai yace “Mama tazo gidan nan kenan” na rike kugu
nace “tunda ka kai kara ta ba dole tazo ba?” Ya zagayo
hannayensa a waist dina yace “naga kina neman ki kaini
lahira ne shi yasa na nemo taimakon gaggawa” ya shafa
fuskata yace “you really are beautiful” na ture hannunsa
nace “bararojin kuma?” Sai yayi dariya yace “wai baki
manta ba, ai bararoji suna da kyau so it was a
compliment” ya saka fuskarsa a cikin gashina yana shakar
kamshinsa yace “tell me duk abinda kike so inyi miki”
nace “ka bar murja ta cigaba da zama a gidan nan” yace
“done. Sai kuma me?” Nayi shiru, yace yana zuge zip din
rigata “ba zaki ce in fasa aure ba? Say it and it will be
done” na sake shiru na rufe idona ina jin daci a bakina
yace “kice ‘hamma Saghir Please kar kayi min kishiya”
bance komai ba ya daga ni ya dora akan gado, hawaye ya
fara bin fuskata yace “kice hamma Saghir ina sonka” nayi
shiru sai yayi ajjiyar zuciya yana hawowa gadon yace
“watarana zaki fada, ina nan ina jira”.
Ina kallon sa yana ta shirye shiryen sa, ni ko su inna ban
gayawa zancen auren sa ba sai da suka ji daga gidan
Alhaji Babba, Hajiya ta kira ni a waya “yanzu Diyam da
gaske Saghir auren nan zaiyi? Shi yanzu kudin da zai kashe
gurin auren ya bawa Alhaji su mana ko shago ya bude ya
fara dan kasuwanci. Yanzu kina ganin kofar gidan nan ma
da kyar Saghir ya saka ta shi ko a jikinsa ma wannan cin
mutuncin da akayi wa gidan nan” “sai hakuri Hajiya” shine
kawai abinda nace mata.
Har dani akaje aka kai lefe, aka saka rana akayi komai
aka fara hidimar biki. Kowa sai mamaki na yake yi wai ni
ko a jikina mijina zaiyi aure. Shi kuma Saghir kullum sai ya
ce ince masa ya fasa aure ni kuma naki fada. Sai yayi
fushi ya daina yi min magana sai kuma dan kansa ya
sauko. Sadauki kuma bai kuma bi ta kaina ba, sai dai
yakanje ya gaida Inna, kudin gidan gona kuwa account ya
bude wa Asma’u ake zuba mata a ciki sai dai kawai su
dauko suyi amfani da abinsu”.
Satin bikin Saghir yana kamawa Hajiya ta kirani tace ita fa
babu wani taro da zata yi, ni kuma sai nace zanyi walima
ranar kawo amarya anan gidan Saghir, yadda kowa yazo
in an kawo amarya sai ya ganta. Saghir yana ji ya fara
fadan wai za’a bata masa gida. Ranar kafi suka zo suna ta
daddaga hanci, na saka murja ta nuna musu spare dakin
da yake sama suka ce “dama yace ba sai anyi mata
komai ba ya saka komai a gidan, gadon ma da cewa yayi
kar ayi mune muka ce sai anyi saboda kar a mata gori”.
Ina jinsu suna gulmar “wannan yar karamar yarinyar ce
uwargida?”.
Aka daura aure Saturday, Sunday kuma aka kawo amarya.
Duk yan uwa sunzo walimar dana shirya, anci ansha sai
kuma aka karbi amarya. Ni dai ina dakina basu kawo ta ba
nima banje ba har aka gama kowa ya watse. Na shirya
Subay’a nima na shirya muka yi kwanciyar mu sai na jiyo
hayaniyar maza a waje, ni na manta ma ashe ana siyan
baki. Sukayi ta hayaniyar su suka gama suka tafi ninina ta
karanta novel din da Rumaisa ta turo min kafin ta tafi, sai
ga Saghir ya shigo dakin. Ya hawo kan gadon ya karbi
wayar daga hannuna yace “uwargida ran gida” sai abin ya
bani dariya ma, yace “ki fito kiga amaryar ki. In ba kyason
ta kuma kinyi alkawarin kula dani yadda ya kamata a yau
zata koma gidan su” na mike ina saka hijab nace “ta sha
zamanta. Tunda ba’a kaina zata zauna ba ni kuwa ina
ruwana da ita?” Sai na wuce na barshi a nan. Ina shiga
palo na ganta a xaune tana kallon kofar dakina. But unlike
abinda Saghir yace na cewa nafita komai ni sai naga
kamar ta fini komai except kyawun fuska. Ta fini shekaru,
daga gani ta fini ilimin boko, ta fini girman jiki dan duk
abubuwan da Saghir yake yawan complain cewa bani dasu
ita tana dasu sosai. Tasha heavy make up da wani uban
attach har gadon baya. Rigarta kusan rabin kirjinta a waje,
na tambayi kaina “a haka akayi siyan bakin?” Na zauna
nace “sannu amarya” ta kalleni tana yamutsa fuska tace
“yauwa, sannu” Saghir ya shigo ya zauna a kusa da ita,
kamar jira take yi sai ta dora kanta a kafadarsa hannunta
kuma a kirjinsa. Nayi murmushi ina kallonsu, yace “Halima
ga Fauziyya, Fauziyya ga Halima” ya kama jawabin zaman
lafiya, baya son hayaniya waye da waye ya gama sai yace
“to yanzu amarya zata gama kwana bakwai dinta da
musulunci ya bata a matsayin ta na budurwa, daga nan
sai kuma ayi maganar rabon kwana. Sai dariya taso kubce
min na rufe baki na juya fuska, yace “kina da magana ne,
Diyam?” Na girgiza kai, yace “no ki fadi abinda yake ranki,
naga kamar kina dariya” nace “kawai dai naji kace
budurwa ne, ni kuma da na ganta na dauka bazawara ce”
sai tayi sauri ta mike zaune sosai tace “excuse me? Shi
da zai aure ni bai gaya miki budurwa zai aura ko bazawara
ba?” Nace “ba muyi wannan maganar dashi ba kuma to be
frank bani da problem da koma wacece, Allah ya bada
zaman lafiya, aci sati daya lafiya, sannan akan sati dayan
na kara muku shekara daya kyauta from me to you” sai na
mike nace “Allah ya bamu alkhairi”.
Ina shiga daki yana shigowa shima, ya jawo ni tace
“what? What was that? Wacce maganar banza naji kinyi a
gurin can?” Nace “kyauta nayi maka ko ba ka so? Ji nake
mai kula da kai a gado kake nema kuma gashi ka samu,
ko shekarar tayi kadan ne in kara muku wata?” Sai na
kwace jikina nace “and don’t touch me kasan ba kwana na
bane yau” na haye gado naja bargo.
Ya tsaya yana kallona sai yace “yanzu har tsanar da kika yi
min ta kai haka? To shikenan, saki kike nema na sani
kuma ba zaki samu ba. Naji, Fauziyya zata kula da gado
na amma duk abinda ya danganci aikin gida ke zaki ke yi,
wanke wanke, shara, girki da komai” na gyara kwanciya
nace “done. Shekara ta nawa ina wanke wanke da shara
da girkin? Dan dai karin kwano daya ai ba zai gagare ni
ba”. Na rufe ido nace “in zaka fita dan kashe mana fitila
Please”.

KU TABA HOTON KASA DON BADA GUDUN MUWAR KU

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button